Showing 84001 words to 87000 words out of 99941 words

Chapter 29 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1520

sai kisan komai na
daukeki nakaiki har Senegal da Mali kiga dangin mahaifiyarki ke yar gata ce mu goma ne gurin
mahaifinmu biyu sun mutu mahaifiyarki Indo da Abdulrasheed babbanmu Wanda shine yasa
mukasa sunan yayanki dan'uwanki Rasheed yanzu saura mu takwas maza hudu mata hudu
zakiga kowa zakisan kowa Kakarki mahaifiyar Ummanki Kumbo Hami tace tana tafe cikin satin
nan zatazo tayi aikinta tamayi na gayyar sodi balle me dalili".......




Sosai yinin ranar Juhud ta yini da damuwa me gauraye da farin ciki yanzu hankalinta ya tattaru
guri daya a baya Baffa'am dinta sunan mataimaki ya Amsa a gareta ya rasa mahadi ya rasa
madadi yanzu Kuma matsayinsa ya nunku yayanta ne dan qanwar babarta shin meye sakayyar
daya dace tayima wadannan mutane?" Ta rasa mafita ta rasa mahanga amfanin abokin
shawara kenan yanzu da ace tanada mashawarci da ya bata mafita.
Yini tayi tana safa da marwa a falonta zuciyarta tayi baqi Rasheed kawai ke haskata shine keyi
mata yawo a cikinta shaidan Yana raya mata abubuwa da yawa saidai tayi a'uziyya ta kawar da
tunanin kawai da haka Kareem ya shigo ya sameta da kula a hannunsa ya zubanta ido yayi
murmushi yace “duk kinbi kin takura kanki kwana biyun nan akan abinda baki isa canzashi ba
am bama wannan ba wainar fulawa naga Fadila nayi nace Bari na taho miki da ita" zama tayi
don tun shigarta da taji Fadilan na cewa tanason yin wainar taji tanaso nutsuwa ta kasa samu
da tuni tayi aikuwa ta bude kular sai tiriri takeyi ta mangyada taji lawashin albasa da attaruhu ta
hadiyi yawu ta gutsura zatakai bakinta tayi Bismillah kenan taji an tankwabe hannunta tana
dagawa taga Amrah cikin hawaye tace “Karka barta taci wannan wainar sun zubanta guba ne
don su kashe dan dake cikinta Ya Kareem nayi tunanin lkcn da Addah ta tabbatar da cewa
Meenah ba mayyah bace zata sauko ta dawo hanya Amma abin mamaki sai naga dawa ta qara
shiga su Hajiya Bilki da Dada Hanne suna zugata, Ya Kareem meye ribarsu idan sun kashe dan
dake cikin Meenah sunada tabbacin zaka qara samun wani ne kaida Meenah waye yafi asara
tunda ita ko ba komai tanada Sarki junior kaifah?" Tunda ta fara mgnr gumi ke karyowa Kareem
tana kaiwa nan bata Ida rufe bakinta ba taji an daki hancinta Addah Abulle tana huci tace
“shegiya munafuka nayi danasanin Bari Mom ta shayar dake dana sani Madara na dura miki
qila da bakiyi sakaryar zuciyar nan ba ni dama nasan haka zata faru to bari kaji na riga na tsani
Meenah tun daga lkcn da tabarka ta auri Rasheed bakuma zan taba sonta ba ban qaunarta ban
qaunar jininta Abdulkareem zabi biyu zan baka kodai ka saki Meenah ko Kuma ka dawo da

Zahrah idan kaki zabar daya cikin biyun nan zan dagsnka nono nabarka da duniya da macen
daka zaba akaina ka gani idan zaka qare qalau kanadai kallon yanda qarshen Rasheed ya qare
daya zabeta yabar uwarsa da ubansa shima da takeso kenan bakai dan karere ba da ake maleji
dakai a rashin uwa akai uwar daki dakai".................




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/16, 8:25 PM] Oum Hairan: Tunda ta fara mgnr Juhud ta zubanta ido tana murmushi har Saida
ta ida kaiwa qarshe sannan ta tabe baki tace “dama zabi daki kika bashi na rabuwa dani da yafi
muku Alkhairi dukkanku dama neman gaba nakeyi banji a Raina zan iya rayuwa ta har abada
da danki ba saboda haka ki kwantar da hankalinki saura kadan lkc yazo....." Daganta hannu
yayi da qaraji yace “Meenah ya isheki haka" dubansa tayi tayi murmushi tace “akanme zan
shiga hankalina bayan nasan cewa ko nayi shiru din ba gwani zanyi ba Kareem nagaji da rashin
mutuncin danginka wlh bazan dauka su doramin ciwo a banza ba...." Daga hannu yayi zai
mareta ta riqe hannunsa tana murmushi tace “karka soma wlh ramawa zanyi" ji tayi an dauketa
da mari ta dafe gurin tare da dagowa Mom tagani hawaye ya zubo mata tace “akan wannan
mutumin zaki mareni Mom na rantse da Allah na gaji Mom nagaji ni nagaji...." Riqeta Mom tayi
ta jata suka shiga ciki ta zaunar da ita tace “bana tunanin haka daga gareki Ina hqrnki yafara
tafiya ne Meenah komai fah na duniyar nan lkc garesa don Allah kici gaba da kawar dakai akan
lamarin gdannan huccewa zaiyi kamar baayi ba" haka Mom ta rinqa bata baki hardai taga ta
russuna tace “ga rubutun an kawo miki" karba tayi tayi Bismillah ta shanye Mom taja numfashi
tace “ki huta Rasheed ne yaje yacemin Yazo gurin qawarsa Kareem ya hanashi shiga" gdy
tayima Mom ta tafi itakuma ta zauna tana tunanin Wannan rayuwa tata idan nan ta kau sai nan
ta bulle tabbas akwai aiki a gabanta.

Har goman dare Kareem bai nemeta ba itama bata nemesa ba haka suka kwana washegari ya
fice tun kafin ta tashi itama data gama abinda takeyi tayi tafiyarta sashin Mom wajen la'asar
Kumbo Hami ta iso tana zuwa ta rungume Juhud tana kuka me tsuma zuciya tana shafa kanta
tana cewa “tun ranar dana fara ganinki naji Ina qaunarki a jinina ashe kedin jinina ce kaicon
rashin sani Meenah Ina tare da jinin Aysho bansani ba Ina tare da gudar jikata bansani ba Allah
na gde maka daka nunamin wannan Rana duk da banga Aisha ba naji sanyi a Raina domin
naga jininta" itama kukan takeyi tana qara shigewa jikin kakarta yau gata gata cikin gata gata ga
kakarta data haifi uwarta sun jima suna kukan tuntunin kafin su samu nutsuwa suka balle
sabuwar hira wasa² batabar sashin Mom ba sai taran dare data shiga bata isheshi a falo ba tayi
shigewarta dakinta domin yanzu ba shine a gabanta ba mafita ta gaba take nema.
Sun shafe ya kusa kwana biyar suna kallon kallo ita dashi shi a izza irin tasa jira yake ta
nemesa tabasa hqr ita Kuma tunaninta baima bata laifi tayi ba balle taji a ranta zata iya
nemansa ta wani basa hqr, lura yayi da batama fahimci abinda yake nufi ba hakan yasashi dole
ya nufi dakinta ya tarar da ita ta kwanta ya zauna a gefen gadon Yana shaqar iskar dakin data
hade da qamshin turarensa yace “wato ke ban isa kiyimin laifi kibani hqr ba ko?" Tanajinsa tayi
masa banza yasan tajisa hakan yasa yaci gaba da cewa koma meye Addah zatayi miki bata
cancanci fada ki fada ba domin kinsan bazanji dadi ba Amma wai kece zaki tsaya gaban
mahaifiyata tana fada kina fada"




Yunqurawa tayi ta tashi zaune ta zubansa ido yanata maganganunsa tana kallonsa qurrr har ya
gama tunaninsa zatayi mgn sai yaga ta gyara kwanciyarta taja bargo tace “idan ka gama ka
rufemin qofar" kallonta yayi da sauri Yana mamakin qeqashewar zuciyarta cikin dan qanqanin
lkc tabbas Meenah akwai abinda take nufi a zuciyarta shiyasa takeyi masa wannan iskancin a
zuciye ya tashi ya fice daga dakin yaja mata qofar da qarfi ta diro daga gadon ta sanyawa qofar
key ta koma ta kwanta ashe yanzu wasan ya fara daga wannan gabadaya ya fita a harkarta
idan ya shigo gdan bai nemanta idan zai fitama saidai taji fitarsa abun Yana qona masa zuciya
itakam ko a jikinta harkar gabanta kawai takeyi da yan'uwanta da kakarta haka lkc ya rinqa
tafiya har ubangiji ya kaita gabar haihuwarta ta shima Tasha wahala kafin ta haifo qatuwar yarta
mace kyakkyawar gaske.
Wannan haihuwa ta mantar da Kareem abinda ya faru ya rinqa rawar qafa akanta da babyn
komai yagani ya kwaso ya kawo musu dake haihuwar dare ce da safe aka sallamesu suka
dawo gda wani abin mamaki daya soki zuciyar Kumbo Hami da Mom Addah Abulle da Fadila
duka suna gdan Amma babu wanda ya leqo domin ganin mai jegon da diyarta hatta Amrah da
Ya'isha da suke waje sunzo Aunty Hamida kuwa da ita suka kwana a asibitin ashe ba iyakar
Mom da Kumbo Hami abin yayima ciwo ba Kareem yafi kowa jin ciwon abin aikuwa dif ya
daukewa bangaren mahaifiyartasa qafa har akayi kwanaki hudu da haihuwar wannan karon
Aliyah da Nana matan Ya Arman da Salman kunya ce ta ishesu irin abubuwan da suka rinqa
yima Juhud ita Nana ashe ma Juhud jininta ce kullum dasu ake yini gdan Juhud sai yammaci

kowa ya kama gabansa.




Ranar kwana hudun ne ya fita yayo siyayya a mai jego ya dawo Urwat ya tareshi a parking
space yake fada masa Addah na nemansa Saida ya shiga yaga babynsa sannan ya dauki
hanya ya nufi bangaren Addah Abulle suka gaisa shiru ta ratsa ya dago yace “Urwat yace
kinason ganina" dagowa tayi ta kafesa da idanunta kusan 6 minutes tana kallonsa sannan taja
numfashi tace “ya mgnr da mukayi dakai? Meye makomar zabin dana baka?"
Gumine ya fara karyo masa ya dago zaiyi mgn ta daga masa hannu tace dakata ba shawara
nake baka ba fah umarni ne Kuma ban baka don banasonka ba saidon nema maka mafita jin
cewa Mom ta hada kutungwilarta tace Aminatuh yar yayarta ce bazai gamsheni daga abinda
dangin ubanta suka fada akanta ba maita yanzu da kudi ma siyanta akeyi saboda haka wlh kaji
na rantse a yau saika saki yarinyar nan ruwanka ka dawo da Zahrah ruwanka ka zauna a haka
ba damuwata bace, tunda kunce rabo naji rabo Kuma gashinan an haifa saboda haka ayi komai
a gama"




Miqewa tayi ta dauko masa biro da takarda ta miqa masa ya kawar dakai a zafafe tace “wlh
muddin baka saki Meenah ba saina tsine maka...." “Abdulkareem karbi rubuta mata" muryar Mai
Martaba suka jiyo ta bakin qofa ya tako ya shigo ya dubi Addah Abulle yayi murmushi yace
“saki nawa kikeso yayi mata?" Shiru tayi tana hura hanci ya dauki biron da takardar ya miqawa
Kareem yace “kayi mata abinda takeso hakan zai faranta ranta...." Hawaye ne ya zubo masa ya
bude baki zaiyi mgn Mai Martaba ya dagansa hannu yace “kada kace komai kayi" hakanan ya
dauki takardar ya rubuta mawa Meenah saki daya" Yana rubutawa Yana hawaye bayan ya
gama ya dago ya rushe da kuka jikinsa na rawa yace “don Allah kubarni da matata wlh
inasonta" murmushi Mai Martaba yayi yace “tayi biyayya a baya bata taba qin jinina ba ta
faranta min itama tana buqatar farantawa Kareem kayi hqr, ke Kuma na juyo gareki daya
yayiwa Juhud ke Kuma kije da biyu in an hada uku kenan"........




Dafe qirji tayi cikin tashin hankali tace “nashiga uku Mai Martaba...." Murmushi yayi ya fice
yabarta da danta da yake neman ficewa a hayyacinsa har yakai bakin qofar ya tsaya yace “nayi
miki hakane domin kina iqirarin kina da haqqi amma banson ki manta nima inada haqqi ga
Kareem nan ciwon kai idan yayi ki dauki nauyinsa banida lkc ko kudin da zan kashe abinda
kikeso ne anyi miki fine"
Ficewa yayi daidai lkcn da Kareem ya zube a qasa sumamme tayi kansa a guje cikin tashin
hankali shikam Mai Martaba yana fita part din Kareem din ya nufa ya ishe Mom tana yima

takwararta Ayshatu baby wanka ya zubama jaririyar ido kyakkyawa da ita Masha Allah yayi
ajiyar numfashi yace “idan kin gama inason ganinki"
Amsawa tayi da to ya fita Saida ta gama shirya babyn sannan ta kaiwa uwarta ita daki tana
kwance tun safe batada walwala hakanan gabanta yake faduwa batasan dalilin ba tun kafin ta
haihu rabonta da ganin Rasheed sai jiya takeji a gurin Kumbo Hami wai Yana gurin magani
dauke hawaye tayi a fili tace “Allah ya baka lfy Baffa'am" murmushi Mom tayi tace “amin ya
Allah Bari naje Mai Martaba yakeson ganina" jinjina kai tayi ta fice itakuma ta dauki yarta tana
bata abincinta bayan kamar Awa daya taji Kumbo Hami tana salati tace “saki Kuma Aishatu me
yayi zafi haka?" Bataji me Mom tace ba Amma Saida gabanta ya Fadi ta miqe Kumbo ta shigo
ta dauki jaririyar tace “aikuwa shima Mai Martaba din bai isaba wlh sai tabar gidannan Mom
tanason mgn ta katseta tace “karma kicemin komai idan zaki iya ki nemomin me kaini inda zani"
a sanyaye Mom tace “Amma Kumbo magaruba tayi koma me kikeson yi kibarma gobe Mana"
murmushi tayi tace “matsiyaci shine yake jira nikam bana jira" da haka ta dubi Meenah data
kasa gane komai tace “muje Aminah" mgn takeson yi Kumbo Hami taqi sauraronta ta figi
hannunta suka fito suna fitowa taga Muntaz yace “ina Kuma zaku tsohuwa da daren nan"
kallonsa tayi tace “yo jiyemin fah dannan wannan Tataccen ne da gantalalliyar uwarsa suka
wulaqantamin jiki wai saki a halin jego to debemin albarka gyatuma tayi da zan Bari mukai gobe
a gdannan"




Jinjina kai Muntaz yayi yace “Ya Kareem din ne ya saki Meenah Kumbo...." Daquwa ta watsa
masa tace “aa tatsunniya nakeyi maka ja'irin yaro zo ka kaini cikin gari akwai wata yar qasarmu
mu kwana acan da safe saimu tafi" yasan rikicin Kumbo Hami idan ta fusata hakanan ya
debesu da Meenah da taketa matsar hawaye batasan dalili ba sai taji abin yanayi mata yawo a
kwanya ta tambayi kanta yafi sau goma ashe Kareem zai iya rabuwa da ita ashe dama duk
abinda yake fada mata na ta rayu dashi forever itane zuciyarsa itane rayuwarsa qarya yakeyi
mata?
Sosai takejin qunci a zuciyarta batasan zafin saki haka yake da qona zuciya ba hawaye ta rinqa
daukewa lkc zuwa lkc har suka Isa unguwar da Kumbo tace akaisu dake tayima matar waya
aka taresu gdane babba na masu hali suka shiga bayan Muntaz ya tafi komai ya nutsa Kumbo
take fadawa qawar tata abinda ya faru sun jima suna jinjina lamarin Meenah binsu kawai takeyi
da ido wani bangare na zuciyarta na ayyana mata lallai dole ta canza takunta lkc yayi da zata
tsayawa rayuwarta.




_Kuyi hqr da wannan naso yi muku typing me tsayi wani uzuri ya katseni ma hadu gobe._

Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan
account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton
katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/18, 2:25 PM] Oum Hairan: Batasan ya akayi ba da safe Kumbo Hami ta tasheta suka duma
zuwa Kano kwanansu biyu a Kano ta Kira Muntaz tace ya kawo mata passport din Meenah ta
bashi address na inda suke ranar ta kama kwanan yarinyar bakwai a duniya hakanan Muntaz
ya taho ya kawo musu passport din ya nan yake fadawa Meenah Kareem bashida lfy Amma fita
dashi waje.
Fatan sauqi tayi masa da rangwame gurin me ikon bada sauqin ya dauko kudinsa Dubu dari
yabawa Kumbo Hami yace “wai Addah ce ta bayar tace a siya rago ayima yarinyar hakika"
murmushi tayi ta debi kudin ta watsar tace “kace mata mu harkar arziqi mukeyi bama ta tsiya
saboda haka ragon dubu dari yayi kadan a hakikar jinin mu tabarshi ta rage zafi" da wadannan
kalamai ya dauki hanyar Katsina sukuma sukaci gaba da abubuwan da zasuyi na tafiyarsu Mali
domin taci alwashin Meenah ta gama zaman wannan gda da can a baya ma don bata da ikone
da shi kansa Rasheed saita rabasu don sama mata salama da yancin rayuwa.
Sun qara kwana uku kullum suna waya da Mom suka dauki hanyar qasar Mali nan Meenah ta
Raina kanta gdan kakanta mahaifin Mamanta ya rikita lissafinta yasata jin sabuwar izza ba gdan
sarauta bane Amma barorin gdan sunfi dari ko Ina sukabi zubewa akeyi ana gaishesu har kawo
suka isa asalin harabar gdan inda zata sadasu da asalin cikin gdan Hajja Kharimatu tayi tsalle
ta rungume Juhud tana dariya tace “wayyoh dadi ga yata ga jikata. Narkewa tayi a jikinta tana
murmushi suka zube a falon kafin kace wane wannan falon ya cika maqil da yan uwan
mahaifiyarta kowa ta kalla fuskar Innatu take gani a fuskarsa ta share hawaye tace “na yarda na
dawo cikin gatana cikin ahlina




Wani dattijo dake shigowa yace “kuma bazaki qara barin ahlinki ba har gaban abada Qanwa
inayi miki barka da dawowa cikin zuri'armu bayan wahala da mukasha ta dogon lkc akan neman
inda zamu samoki"

Kumbo Hami ce ta nuna matashi tace “tashi kije ga kakanki Meenah yayi kukan boye yayi na fili
saboda rashinki ke kadai duk jikokinnan da suka kewayeshi" miqewa tayi da sassarfa ta Isa
garesa ya rungumeta yana shafa bayanta tana kuka Yana hawaye yace “tsarki ya tabbata ga
ubangijin daya rayani har naga Aminatuh na a raye cikin aminci" janta yayi suka zauna yace
“naji quncin watsi da nayi da mahaifiyarki hakan ya jawo tabarbarewar komai naso na gana da
Aishatu kodon na nemi gafararta ita da mahaifiyarta ubangiji bai nufa ba saiya kawomin ke
madadinta ajiyar numfashi tayi shima ya aje numfashi nan sukayita hidima da ita da
Muneefanta har dare sannan aka kaita makwancinta sashine guda da yasha kyau da gyara
sosai part din ya qayatar da ita Saida Kumbo Hami ta dafanta ruwan zafi ta gasanta jiki sannan
ta qyaleta ta kwanta bacci kuwa me dadin da ta dade batayi irinsa ba ranar shi tayi.





Haka rayuwarta a Mali taci gaba da kasancewa cikin annashuwa dangin mahaifiyarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login