Showing 51001 words to 54000 words out of 99941 words

Chapter 18 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1523

tayi tace “eh na
tashi naga missed naka Ina fatan ka sauka lfy" Amsa mata yayi sukayi shiru na dogon lkc can

yace “fushinki gareni Yana azabtar dani Meenah kiyi hqr don Allah" a kasalance tace “yafa
wucce Baffa'am kawai dai Raina baya dadi ne idan na tuna kana raba Mana Abu mafi daraja da
wasu wadanda basu cancanta ba.
Yaji dadi sosai sukaci gaba da hirarsu har zuwa wani lkc sannan sukayi sallama cike da kewar
juna tana kashe wayar wayar Amrah ta shigo ta daga shigo ta dauka daga yanayin yanda suke
gaisawar tasan da wani saqo a zuciyarta Amma ta maze taja numfashi tace “burinki ya cika
hankalinki ya kwanta kin yaudareshi kin Sanya masa ciwon zuciya kawai saboda wani quduri
naki Meenah Ya Kareem bai cancanci wannan sakayyar daga gareki ba yasoki lkcn da bakisan
komai ba shine yanzu dan kin zama komai kika gujeshi......"
Dakatar da ita tayi da cewa “kina mgn da yaen da bana ganewa Amrah meye ma laifina ne cikin
zarginki nima kamar yanda kowa yaji sama taka hakanan naji bansan wani abu bayan abinda
kuka sani ba nidai na wayi gari naganni matsayin matar Baffa'am dina Kuma na yarda da
abinda Allah ya tsara na karbeshi to meyece tawa a ciki?" Wata dariya Amrah tayi tace “bawai
inayi miki mgn don kaina bane domin ni da eh dinki da aarki babu abinda zata qaramin Amma
dai ki sani baki auri mijin daya dace dake ba domin kuwa ya rainanki hankali ne kawai saboda
sha'awa ya aureki Kuma bazai taba canza hali saboda ke ba ke mufa a qarshe ma godiya
mukayiwa Allah da Allah baisa mun dauko Kara da kiyashi ba maita ai bala'i ce a qarshe dai Ina
Mai farin cikin sanar dake Ya Kareem zaiyi aure zai auri wacce tafiki asali nasaba da nagarta
kinsan dama rayuwar duniya qwarya tabi qwarya akeyi"




Dukkannin kalaman Amrah babu Wanda ya daki zuciyar Juhud kamar Wanda tace Allah ne ya
taimakesu Basu dauki Kara da kiyashi ba maita ai bala'i ce....." Kashe wayar tayi cikin dimuwa
tayi tagumi itadai tana ganin jarabawa Wai ya akayi ta zama mayya ne? Tana tsaka da tunanin
nan Kiran Mom ya shigo ta daga a sanyaye cikin rawar murya tace “Mom.... Momy Ina yini"
zuciya Mom taja tace “me Amrah tace miki?" Saita muryarta tayi cikin kuka tace “babu komai
Mom" shiru Mom tayi sannan ta kashe wayarta ta miqe ta shige daki ta fada gado ta rushe da
kuka yau ce Rana ta farko data fara jin shauqi da tunanin Ina zata Sami wani dazai zame mata
abokin shawara dazai bata mafita cikin matsalarta maita? Maita?
Ta maimata yakai sau goma sannan ta iya miqewa ta shiga bathroom tayi wanka tayi magrib ta
dauki qur'ani tana karantawa har akayi Isha tayi ta haye gado zazzabin dare ya aurenta ga
kadaici hakanan tayita juyi da missing din Baffa'am dinta bacci ya fara daukarta taji wayarsa ta
dauko ta gyara kwanciyarta ta Kara wayar a kunnenta tace “tsarki ya tabbata ga ubangijin daya
halicci zuciya biyu makusantan juna" numfashi ya sauke yace “Same to ur my Meenah meye ya
hanaki bacci 11:40pm" kasa tayi da muryanta tace “kewa da tunanin mijina gami da missing
lallausar fatarsa" dariya abin yabashi yace.
“Au haba dama kina jina a zuciyarki haka"

Murmushi tayi ta shafa saman kanta tace “komai na duniya hawa yake Yana sauka nikam sonka
baitaba sauka a zuciyata ba Baffa'am tunda ya riga ya hauhawa don Allah ka riqemin amanar
kanka kaji" qaramar ajiyar zuciya yayi yace “bakida matsala matata am dama mom ce tace
tanason ki koma Daura a fara shirye shiryen biki dake Wai harda bikinmu zaa hada ayi" abinne
ya bata dariya tace “biki Kuma Baffa'am nikam na yafe nawa su Bari su hada dana suna...." Duk
da baa gabanta yakeba Saida ya zabura ya miqe yace “suna Meenah mun samu qaruwa be?"
Jikinta ne yayi sanyi tace “hakane Baffa'am kwana hudu da lkcn period dina ya wucce......"
Wani ihu ya saki Hadi da kabbara yace “wayyoh dadi Meenah shine baki fadamin ba na fara
tanadi me zaki haifamin mace me kama dake ko?" Rufe idonta tayi tana share hawaye me hade
da murmushi yace “amma kamar murnarki batakai ba my Meenah meye damuwar ne ko har
yanzu fushinne?"
Girgiza kai tayi yace “talk me Mana" aa tace tare da cewa “bacci nakeji Baffa'am" da murnarsa
yace “aikuwa zan fadawa Mom tabarki kada hayaniya ta damarmin ke ki huta kinji rayuwata"
qit ya kashe wayar baa dauki 10 minutes ba saiga Kiran Mom tace mata “yayimin kwatancen
gidanku gobe zanzo na daukoki gara ki dawo nan gidan ki zauna a bangarensa da zamanki
anan Babu kowa bakisan kowa ba ga lalurar ciki Allah ya inganta ya rabaku lfy kinji me sunan
yaya" a kunyace ta amsa suka Dan taba hira suka aje layin tana ajewa Kiran Ya'isha ya shigo
tace mata “ke wlh banza ce daga zubar da wancan sai kika bude abu kika Kuma karbar wani
nifa wlh banyi miki sha'awar haihuwa yanzu" shiru tayiwa Ya'isha jin hakan yasa ta gane yan
iskan na kusa bazata kulata ba ta gimtse wayarta washegari kuwa 12:00pm a KD tayiwa mom
da Muntaz tunda suka shigo yake binta da kallo yana hadiyar yawu a ransa yace “wow! Manyan
kaya wannan guy chege ne yasan takan dadi dubi yanda wannan babyn take qara hauhawa
abin kamar....." Mom ce ta katse masa tunanin da cewa ai saika tashi ka Debi kayan mu tafi
salmanu"




Zungi² ya miqe yabisu Mom na gaba Juhud na binta shikuma Yana qarewa halittar bayan Juhud
kallo har suka isa mota ita da mom ne a baya shike driving har Daura suna tsayawa motar Mai
Martaba tana tsayawa ya fito Mom ce tace da Juhud “kije ki gaisheshi" da faduwar gaba ta
nufeshi ta rusuna ta kwashi gaisuwa Babu wata alama ta bacin rai ko damuwa ya Amsa mata
tare da cewa “Meenah kawai saiji mukayi kinbi Wanda ya kawoki" da sauri tayi qasa da kanta
saboda fitowar Kareem a part dinsa da yanda ya zubanta ido.
Tsayawa yayi cak Yana kallonta ta miqe tabi bayan Mom data nufi part din Rasheed tana cewa
“wlh sakarcin Rasheed yawa gareshi Mai Martaba yabarta ita kadai a gda ga kadaici ga laulayi
shine nace gara a dawo da ita nan kada dukan yayi mata yawa" tana tafe take mgnr suka gifta
Kareem dake tsaye kamar dashe cikin sanyin yanayi tace “sannu Ya Kareem ya jikinka?" Wani
yawu ya hadiye me daci ya juya yabar gurin gabadaya sai taji Babu dadi hakanan dai tabi Mom
suka shiga abin mamaki bayine keta gyaran ɓarrayin fita mom tayi tace "bari na turo miki yan
uwanki su tayaki shirya kayan"

Gdy tayi ta nufi ƙofar shiga dakin shima kamar falon an canza komai taja numfashi ta kulle qofar
ta fada wanka ta fito daidai lkcn taji muryar Ya'isha ta bude mata suka rungume juna tace
“wayyoh aure dadi gsky Big Cele Yana ban ruwa ke Kinga yanda kike wani glowing hajiyata
fadamin meye sirrin 2 months kacal kamar kin shekara ana miki bayin ruwa" harararta tayi tace
“kefa yar iskace meye Kuma bayin ruwa ana zamne qalau an fada miki Kuma kowa ma dan
iskanne irinku ni zikiri kawai muke da karatun qur'ani da shaikh Baffa'am dina tunda ya saceni"
dariya suka sheqe da ita Ya'isha tace “shegiya aifa dama Mana shiyasa naganki da sabon ciki
ashe a ruwa ya baki kika kurba" gumtse dariya tayi tana cewa “hmmm yarinya kina wasa da
mazan fama komansu na baiwa ne wato idan My Baff na bada darasi ji nakeyi kamar babu wani
sauran gwani a duniya ke Bari fah kiji Allah Baffana akwai iya tsinko fure nakusa nayiwa kaina
asar....."
Shigowar jakadiya ne yasasu gimtsewa ta rusuna cikin ladabi tace “Allah ya taimakeki Mai
Martaba ne yake kiran taron gaggawa a gidannan yace maza kizo kema tunda Allah ya dawo
dake" Saida taji wata faduwar gaba ta dai dake tace “ok muna tafe" kallon Ya'isha tayi tace
“meye ya janyo taron?" Miqewa Ya'isha tayi tace “akwai matsala ne kinsan fah Mai Martaba
yasa Yaya Salman da Yaya Arman duk sun dawo da matansu gdannan wannan dalilin yasa
Mom ta matsa kema ki dawo to tunda ya sauko ya amincewa dawowarki aketa tuka rigima da
wadannan matan biyu Hajiya Bilki mahaifiyar su Aunty Zulaihat tana zugasu ita da Addah wai
karsu yarda a kawo musu mayya tazo duk ta lashe musu kurwar yara a banza da mazan Basu
daukar abinda muhimmaci Amma suma naga yanzu kamar maganganun sun fara tasiri ke harfa
cewa sukayi wai kece kika lashe su Zulaihat da Ado driver saboda qudurinki na auren Big Cele"




Jikin Juhud Bari yakeyi dajin wannan sabon bala'in data fara karo dashi a wannan sabuwar
rayuwa tata bata gama yanke abinyi ba Amrah ta shigo bakinta dauke da “la'ilaha illah anta
subhanaka inni kuntu minazzalumin" Saida ta tofa kusurwa hudu sannan tace “saqo daga Mai
Martaba yace ku kadai ake jira" badon Juhud taso ba ta sanya hijjab dinta suka fito Ya'isha na
qarfafa mata gwiwa suka Isa meeting hall din gdan kowa ya zubawa Juhud idanu harda Kareem
ta sunkuyar da kanta tana neman gurin zama Mom ta riqo hannunta ta zaunar da ita kusa da
Aliya matar ya Arman aikuwa tayi zunbur ta miqe tana qunquni itadai Juhud zama tayi Mai
Martaba yayi gyaran murya ya fara bude taron da addu'a yace.
“Banso Kiran taro a daidai wannan lkcn ba so wata yar jumurda ce tasa dole na kiraku
musamman akanki Aminatuh alal haqiqa a baya an zauna zaman gsky da rashin sani so yanzu
abubuwa sun fasu Wanda mukayi qoqarin ganin mun kare zuri'a daga darsa zargi ko kokwanto
Amma abin ya faskara wannan dalilin yasa na yanke shawarar kiranku nidai nasan iyakar
zamanmu dake na shekara uku baki taba cutar da kowa ba duk da cewa akwai maganganun da
naji suna yawo a bakin mata bamu daukesu seriously ba wannan tasa na Kira domin roqonki
domin shi wannan abu a boye yake idan har da gaske hakanne mu bazamu qiki ba tunda mijinki
yanasonki Amma kiyiwa Allah kici gaba da riqe kanki kada ki gwada Mana wannan mugum abu
idan Kuma sharri ne to Allah ya saka miki sannan mgn ta qarshe banason qyara ko tsangwama

a tsakanin ahlina wannan abu itama ba ita ta dorawa kanta ba gadar mata dashi akayi sannan
alamu sun nuna batama da qarfi a jikinta Ina fatan kowa ya fahimta....."
Tunda Mai Martaba ya fara mgnr ta rushe da wani kuka me gigita zuciyar me sauraro tana
girgiza kai bakinta Yana rawa Mom ta riqota da sauri jikinta tana shafa bayanta cikin kuka tace
“Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fih musibati wlh tallahi billahil lazi la'ilaha
illahuwa niba mayya bace sharrine kawai ku yarda dani nikam meye nayiwa rayuwa ne me
nayiwa su Baffa Ribado suke bina har gidan aurena da wannan mugum sharrin meyesa kakata
ta mutu da baqin cikin sharrin maita Innatu ta harta mutu tana maimata min basuda wata alaqa
da maita kyaune yaja musu da hassada ake kiransu mayu nima Kuma saita tsallako kaina
wayyoh Allah Baffa wayyoh Innatu wayyoh mijina don Allah ka dawo ka fada musu niba mayyah
bace....."




*littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe
miki haqqina dake kanki*

*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or
card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba
94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*




*_Oum Hairan_*
[8/1, 11:13 AM] Oum Hairan: *JH0024* Tabe baki suka rinqayi suna miqewa suna sulalewa da
daidai ya rage saura iyakar yan dakinsu Rasheed Aunty Hamida Ya'isha Muntaz da Mom
iyakar shaqiyancin Muntaz wannan cin mutumcin da akayiwa matar yayansa Saida yasashi
hawaye shima. A wahalce ya miqe ya iso garesu sunata aikin rarrashinta kamar suna qara mata
qaimin kuka yace “ni dama Mom saboda tsoron irin wannan abubuwan da ka iya tasowa naso
kibarma Big Cele matarsa a inda ya barta Amma kika dage Saida kika dawo da ita yanzun ga
irinta nan.
Hamida ce ta quta tace “wlh nima Raina baiso dawowar Aminah cikin gdannan ba so abune dai
da bakada yanda zakayi dashi Mom gsky a dauki mataki akan lamarin nan wlh idan aka barsu a
gdannan zasu dorawa baiwar Allah hawan jini a banza ita gata mijinta ba mazauni ba balle yake
rarrashinta" miqar da ita Mom tayi ta kama hannunta suka fito wani abun mamaki duk inda
sukabi sai suga bayin gidanma suna darewa suna barmusu gurin lamarin daya qara tashin
hankalin su.

Zama tayi a parlour tanaci gaba da kukanta da iyakar rarrrashin mutum bataji a ranta zai iya
fada mata kalmar da zata iya kwantar mata da hankali ba, sai yanzu mom ta magantu da cewa
“duk wani abu da zai faru ko Kuma yake faruwa Aminatuh kiyi watsi dashi ki durfafi rayuwarki ta
gaba kisa mijinki da yayan da zaki Haifa masa a gaba shine komai zaizamo miki me sauqi
Amma indai kika sake mutane suka jefa miki qulli a ranki to zaki samu matsala kinsani babu
wani abu daya gagari Allah wlh Meenah banida ikon hana wannan mgnr fita da tun farko ban
Bari ta fita ba balle tazo ta damemu hqrn dai shine zakici gaba dayi domin shine ya kamaki
tsarin gdannan mijinki ya taka shiyasa komai ya dada lalacewa Kuma nasan komai akanki zai
kware"
Har Mom ta gama mgnrta Meenah kallonta kawai takeyi daidai lkcn wayar Mom din ta dauki ruri
ta duba taga number Rasheed ce gabanta ya fadi tayi kamar bazata dagaba ya sake Kira tadai
sanyawa kanta nutsuwa ta daga suka gaisa yace “meye yake faruwa da Meenah ne na Kira
wayarta yakai sau goma bata dagaba" cikin daburcewa tace “eh wlh batajin dadine tunda muka
iso kasan yanayi na me qaramin ciki dan gwajab² din hanyar nan yasa mata zazzabi Amma dai
Alhmdllh yanzu ta samu bacci, ya aikin?"




Aje numfashi yayi yace “alhmdllh hankalina yaqi kwanciya ne da zaman Meenah a gidannan
Mom inajin tsoron kada a Dora mata damuwa ba iya ramawa zatayi ba sanyinta yayi yawa ni
kadai ne Meenah bata bari Amma Urwat ma idan yayi mata qyaleshi zatayi" “nasan da hakan
Rasheed babu abinda zai faru insha Allahu ka kwantar da hankalinka ai bama dadewa zakayi
ba ko?" Gyara kwanciyarsa yayi yace “wata uku zanyi saidai fah banjin zan iyashi ni kadai tun
jiya nasa a gyaramin gda a barreck idan naga yanayin garin Daltan Babu matsala zanzo ko na
turo a tafi da ita"
Fatan Alkhairi Mom tayi masa sukayi sallama ta dubi Meenah tace “ko ya Kira kada ki daga
kinsan halinsa idan yasan abinda ya faru bazatai kyau ba ki taimaka wajen boye koma mene
daqyar nasamu na dsidaitashi da Mai Martaba mijinki akwai kafiya kamar kafirin farko don Allah
Meenah kiyi hqr ga yar'uwarki nan ko kowa yaqiki naji a jikina jinina bazasu gujeki ba su kansu
yayyenku sun gamu da kaidin matane musamman Arman saidai addu'a"
Juyawa Mom tayi ta fice Ya'isha ta zauna tana qara bata baki harsaida ta Dan saki jikinta suka
qara gyara abinda baiyi musu ba tayi hamma Ya'isha tace “yadai da miqa ko a Kira Big Cele
ne?" Murmushi tayi tana shafa cikinta tace “nazama jaka wlh bana jure yunwa Kuma da naci
zanji an yasheni kamar wacce mukeci da wani kiga fah jikina har rawa yakeyi" dariya Ya'isha
tayi tace “tab kice Big Cele ya qara daure dammara da saqale bindiga" duka takai mata sukayi
dariya tace “hankali ne baa kwance ba bari na Kira Mom ta turo a kawo Mana abinci" sallama
tayi tace “unborn din danki ne yakejin yunwa Yana neman wahalarmin da yar'uwa" dadi sosai
Mom taji dajin ta saki jikinta tace “ok Bari na turo kausar ta kawo muku abinci tun dazu na hada
wani abune ya daukemin hankali"

Suna nan sunata hirarsu gabadaya hirar akan bikinsu Ya'isha ne Kausar ta shigo ta aje musu
abincin ta fice Ya'isha ta dauko abincin ta zubansu abincin sunaci suna hirarsu ya sake Kiran
wayarta ta dauka ta manna a kunnenta tace “girman kujerarka duniyata" ajiyar zuciya yayi yace
“har naji dadi nakasa aikata komai banji lfyr rayuwata da babyna ba hope dai qalau kuke?" Murmushi tayi tace “ni qalau nake saidai ko kai naji yanayinka a kasalce" qasa yayi da murya
yace “meye yake faruwa a gdannan ne jikina na bani ba lfy ba kamar akwai abinda ya faru"
shiru tayi tanajin bugun zuciyarta na qaruwa Ya'isha ta zungureta tayi firgigit kamar wacce ta
tashi a bacci yace “akwai abinda yake faruwa din kenan ko?" Saurin girgiza kai tayi tace “babu
komai kawai dai naji Babu dadine dazun Amma yanzun na warke" bawai yarda yayi ba domin a
muryarta kadai ya fahimci akwai damuwa so baison takurawa da tambayar hakan yasa yace
“shikenan lkcn la'asar yayi ki huta My Meenah Baffa'am dinki Yana kewa dama shekaran jiya
baki baniba Kinga sai kumburamin wando qawanki takeyi" dariya tayi shikam baijin kunyar
kalaminsa tace “idan ka zaneta zata nutsu fah....." “Wht?" Ya furta da qarfi tasa dariya shima
yayi dariya suka aje wayar tare ta juya zatayima Ya'isha mgn batanan ta miqe ta kulle barayinta
tayi sallah ta qara gyaggyarawa shiru tana jiran Ya'isha har dare tama hqr tayi kwanciyarta a
falon tana kallon wani Korian series tana latsa wayarta lkc zuwa lkc tana duba agogo sai goma
ta miqe ta bude sashin da dakunan baccinsu suke ta shiga ta watsa ruwa ta haye gado ta
qudundune yanayinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login