Showing 27001 words to 30000 words out of 43757 words

Chapter 10 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf

da Faruq, don na sha gaya miki yana matukar son ki. Wannan rubabben son na shekaru
goma sha takwas, duk a yau zai nuna miki shi. Kiyi dauriya ki kiyi juriya ki zama mace tagari
Zaynab, kuma in gaya miki Imran ya cika alkawarin da ya daukar min. Bamba goma sha biyu,
suna nan ya bani na kai miki dakinki”.
​ Dariya tayi cikin annashuwa, hasken farin wata na kara haskaka kwalliyar amarcinta.
Tace “Yaya Halima bani da kalmar da zan gode miki".
Ya karaso cikin kaguwa ya kasa kunne yace “wai gulmar me ake yi ne? in ji dai ba gulmata
bace. Ke Yaya Halima dadi na dake in baki ki kulla nunkufurci ba bakya jin dadi ('yar mace, da
dan namji suke)”. Ta harareshi, ta juya tana cewa
"kai nan har ka isa in nunkufurceka? Sai dai in maka kan mai uwa da wabi" (ta zuge Zaynab taki
yarda da shi). Yana dariya ya sakalo Zaynab suka shige bukkarsu.
​​​
***​​ ***​​ ***

Duk wata rawar jiki da karkarwarshi, ZAYNAB ta fishi. Duk wata zakuwa da nuna zalamarshi,
ZAYNAB ta fishi. Duk wani kokarinsa da jarumtakarsa da kyar ya iya ya gamsheta. Halittarta na
daga cikin halittar matan da turance ake kira ‘nymphomaniac’. To amma shima ai namijin gaske
ne. Yayi mamaki amma yai shukurah ga Allah abisa halin da ya risketa. Ya rungumeta sosai
tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, hasken farin wata da alfijir daya soma kokarin ketowa, ya
haskaka mishi kayatacciyar fuskarta, yace cikin shauki “Zaynab are you O.K?”
Gyada mishi kai kawai tayi, kamin wasu irin hawaye su mirgino su jika kundukukinta. Tana
fatan Allah ya dorar da soyayyarsu da rayuwar su da Faruq cikin GIRMA da daukaka kamar

yadda ta faro. Shi kuwa addu'a yake Allah ya bashi tsawon rai, karfi da lafiyar da zai cigaba da
iyawa bukatar gangar jikin ZAYNAB, har zuwa ranar da suka daina numfashi.
***
GIRMA YA TASHI!
SHEKARU ASHIRIN A GABA.

Zaynab Mainasara, na daya daga cikn jami'an majalisar dinkin duniya (United Nations) dake
wakiltar Nijeriya, sannan (member) ce a kungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Africa ta yamma da
aka fi sani da (ECOWAS). Gabadayan karatun ta har zuwa digiri na kololuwa, ta yi shi ne akan
tattalin arziki (Economics) daga Jami'ar Porstsmouth, U.K. ​ Danta na farko data haifa tun a shekarunsu na biyu da aure (Aliyu) ta bada shi ga
Mamie Nuratu tun daga shekarun yaye. Ta yi masa aure da Sa'adatu diyar Haiti da Imran, yana
da shekaru goma sha takwas. Ta aurar da Rabi'a tun tana da shekaru goma sha hudu, ta aurar
da Nuratu (Mamie) tana da shekaru sha biyar. A nan gaba kadan tana shirin aurar da Halima
(Dubu), da kanwarta Hibbani, wadanda ke aji uku na sakandire. Sai dan autanta Sa’id, mai
kimanin shekaru goma a duniya.

Na daga jaridar (New-Nigeria), mai dauke da kanun labaran bikin cikar su shekaru ishirin da
aure. Ban taBa ganin fuskokin mata da miji da suka dace da juna irin ZAYNAB da FARUQ ba. A
kasan hoton an rubuta “an extraordinary lady, ZAYNAB MAINASARA, in celebrating her 20th
wedding anniversary” da aka yi a Niamey, cikin wannan shekarar. Duk da irin runguma mai cike
da kauna da maigidanta yayi mata, cikin hoton, tana kuma murmushi, akwai wasu dunkulallun
hawaye cikin fararen idanunta.

​ Na samu kaina da maimaita lakabin da akayi mata watau ‘extraordinary’, kwarai sunan
ya dace da ita. Ban taBa ganin mace mai ban mamaki irin Zaynab Mainasara ba; mijin da Allah
ya nufe ta da samu, dukiyar da Allah ya hore mata, ilimin da Allah ya bata, da daukakar da yayi
mata cikin kasar mu mai dinbin albarka, bai goge Bacin ran dake cikin zuciyarta ba, bai shafe
Boyayyen bakin cikin dake boye cikin kwayar idanunta ba.

Masha Allahu lakuwwata Illa Billah!

Masoyana a duk inda kuke cikin duniya, wadanda na sani, da wadanda ban sani ba, na gode da
yabo da fatan alkairin da kuke yi min. Kamar Zaynab, nima nake cewa ;

"Da fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa!"
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: A kasuwancin fatar shi ya tara duk abinda yau nake da shi,
ko in ce muke dashi nida marigayiya Innarki. Duk wannan arziki da Allah ya keta buda masa,
hankalinsa ba’a kwance yake ba saboda larurar Ya Rabi, da wani lokaci zasu nannadeta kamar
alkaki ko su hana hannaye da kafafunta motsawa. Aka dukufa neman magani har Tumbuktu,
Morocco, Mali da Mouritania. Amma mayun sunki rabuwa da ita, ko sun tafi kwana biyu sais u
dawo. Mahaifinmu yana da dadadden burin yin Gwamna a Damagaran, ba don komai ba sai
don ya kara fito da jiharsa ta tserewa sauran jihohin mu, don haka a dai –dai wannan lokacin ya

kacame cikin hayaniyar siyasa Allah kuma ya bashi jama'a magoya baya kamar me, domin
al'umma Nijar bakidaya sun yaba da shugabancin Kakanmu Kangiwa, don haka ne duk wani da
ya fito takara daga tsatson Mainasara nan da nan yake lashewa, sai dai in bai tsaya ba.
Su kance “Mainasara ba don sata kuke mulki ba, sai don kishin mu”. Ana sauran watanni ukku
zaBen, a irin tafiye-tafiyen da yake cikin Nigeria, ya jiyo labari Malam Ali Mai Almajirai ta hanyar
wani dan kasuwar fata mazaunin garin Kano, shine ya bashi labarin irin wahalar da yake yi na
nemawa Rabi magani, inda shi kuma yayi mai hanyar Malam Ali, ya je suka gana yace ya je ya
zao mai da Rabin.
​ Da fari Yadudu taki aminewa, inda ta ce sai dai shi Malamin ya biyoshi wato a daukoshi
yayi mata maganin a can gidanta, inda ya nuna mata Malam Ali ba malamin ciwon hauka bane
kawai makiyayi ne mai nasibobi daga Allah, baya karBar ladar aiki sai sadaka, itama ba ko
yaushe ba. Ni kuwa nace kafata kafar 'yar uwa ta, don haka ne mahaifinmu ya dauko mu mu biyu kacal ya
taho da mu Kano ta jirgi, muka yi a kalla sati biyu gidan Malam Ali ana yiwa Ya Rabi magani,
muna kwana dakin Innar Faruq wato Inna Dubu. A lokacin Faruq bai fi shekaru biyar ba, inda ni
kuma nake da goma sha biyu, Yaya Rabi sha biyar. Allah cikin ikonsa yaba Malam Ali sa'a ya rabata dasu cikin 'yan satittika, muka soma shirin
tahowa. Lokacin da Babanmu ya tambayi Malam Ali me zai bashi ladar aikinsa? Budar bakina
sai cewa ya yi, ya aura masa Rabi, baya karBar ladar aiki sai sadaka. Baban mu bai duba
yanayin rayuwar karkara ta malam Ali ba, ko wadata ko waninsu, illa tunanin ya zai yi dani idan
ya rabani da 'yar uwata? Alhalin ko barci baya rabamu. Yana tuntuBar Ya Rabi ga mamakinsa
sai ta amince farat daya, ni kuwa nace kafata kafar 'yar uwata.
​ Haka ya aurawa Malam Ali Ya Rabi, akan sadaki kalilan. Damuwar sa shine, me zai ce
da Yadudu da su Baba Aliyu? Da wannan damuwar ya hawo jirgi, kwata-kwata baya cikin
nutsuwarsa, akan hanya ne Allah ya aiko a jalinsa, jirgin su ya kife, babu wanda ya tsira a cikin
jirgin. ​ Malam Ali ya samu labarin hatsarin a radio. Hankalin sa ya tashi, don bai san kowa
namu ba, sun rabu ne akan bayan zabe zai dawo tare da dangin mu su ga inda take, nikuma su
tafi dani in cigaba da makaranta. Ya yiwa mahaifinmu addu'a sosai tare da alkarwarta ma ransa
rike mu amana. Shi da bakinsa rannan yace bai tunkari mahaifinmu da neman auren Rabi haka kai tsaye ba,
saida ya kwana uku yana Sallah yana rokon Allah a kansu shi da Rabin. Don haka da yaji
rasuwar mahaifinmu ya kara kafe Rabi a cikin gidansa kar ta gudu, domin ba karamin so yake yi
mata ba. ​ Sai kuma Allah ya hada jinin Rabi da Faruq, kullum yana dakinmu, tare da shi muke
zuwa makarantar boko shi yana aji uku ni ina aji biyar. Haka in mun dawo muna tare muke
daukar karatun allo sai dai shi ya wuceni nesa ba kusa ba a karatun allo saboda inada tangarda
a harshe, har rige-rigen wanke allo muke yi, inda ni kuma na yi masa fintinkau a makarantar
boko saboda na samu tushe mai kyau a makaranta mai tsada a Damagaram.
Innar Faruq mutuniyar kikice, bata dauki Rabi a matsayin kishiya ba sai kanwa, domin a haife ta
haifeta. Rabi shekarunta goma sha biyar kacal a lokacin. Wannan sai Goggo Rakiya (kishin).
​ Sunan da Faruq ke kirana dashi a lokacin shine (Nuratu-mai-dogon-gashi), ni kuwa ince
Faruq dan dukurkusu), don ni na fisi tsayi sosai, haka nake kama hannunshi mu tafi makaranta

ko in daura hannu a tsakiyar kanshi in tasa shi a gaba, shi kuwa haushin hakan yake ji, domin
shi a lallai sa'a na ne, bayan shekaru bakwai rigis na bashi. Idan na dora hannu a kafadunsa sai
ya ture, shi sai dai mu jera, bayan kuma rabi na ne.

Akwai wani daki a soron gidan Malam, da kullum yake a rufe, tunda muka zo gidan ban taBa
ganin an budeshi ba har na kammala karamar sakandire, da yake makarantar kwana nake yi a
Garko wato (Garko Science) ban san Sa'idu a gidan yake ba, kuma wannan dakin nasa ne, ban
kuma san sanda suka shaku da Ya Rabi ba fiye da Faruq, ya zamanto hatta kwanon sa a dakin
Rabi yake, kuma da yake yana da cutar gyambon ciki (ulcer) sai take tsaye sosai akan
abincinshi. Rabi ita ce uwar dakin Sa'idu, wanda yake almajiri ne ga Malam, kuma Malam ya
sanya shi a makarantar boko cikin Kano, sanda yake zuwa gidan sau tari ina makaranta. Rabi
na son Sa'idu sosai fiye da duk 'ya'yan rikon dake gidan da sauran almajiran Malam, har ta kai
ta kawo duk wani sirrin shi da Rabi yake yi, idan zai koma makarantar haka take kulla 'yan
canjinta ta bashi, haka ko daga can makarantar yana aikowa ta aika masa da abinda yake so ko
ta karBa a wurin Malam ta bayar akai masa.
​ Rannan shiryawa tayi ta tafi Bindawa zaman makoki, wai Baban Sa'idunta ne ya mutu.
Lokacin da Sa'idun zai zana jarrabawar tafiya kasar waje. Rabi bata yi barci ba, kwana take
sallah da addu'ar Allah yaba Sa'idunta sa'a. Har bashi take ci wurin Goggon Dubu ta baiwa
Sa'id yayi hidimar karatunsu, inta dauki adashinta ta biyata. Sanda ya soma daukar alawus daga kwalejin horas da malamai ta jihar Kano sai ya sayo mata
keken dinki da gabadayan kudin ta soma dinki, amma wallahi duk abinda ta samu a dinkin a
wani katon banki take tarawa, idan na tambayeta me zatai da kudin da take ta tarawa a banki,
sai tace gudunmawa take tarawa Sa'idu in yazo yin aure. ​ Amincin dake tsakanin Rabi da Sa'idu ba zan iya kwatantashi ba. Ta daukeshi tamkar
dan data haifa a cikinta, shi kuma ya dauketa da muhimmancin uwar sa. A haka ya tafi Turai ya
soma karatu, amma duk sanda ya samu dama sai ya yo mata aike ita da Malam.
Zuwansa hutu na farko daga Turai ma ina makaranta, sai tangamemen hotona a dakin Rabi.
Ya dade yana kallon hoton yace "amma nan baki fi shekaru goma sha bakwai ba, aka dauki
hoton ko Innata?” Ta yi dariya har taba uku lada, tace "yanzu da gaske Sa'idu baka san
kanwarka, Nuratu ba?” Ya cika da mamaki ya ce "itace ta zama budurwa haka? Lallai girman
'ya mace, ba wuya, ba kwanakin baya-bayannan nake ganinta ta kama hannun Faruq sun tafi
makarantar firamare ba?” Tace "eh to, gatannan ko yanzu akayi mata aure, gobe zata haihu”.
Ya dade yana kallon hoton, cikin wani sabon yanayi atare dashi ya ce "Inna Rabi, Nuratu
kyakkyawa ce”. Ta yi murmushi tace “don ma baka ganta tana shekaru biyar ba, sai kace 'yar
tsanar roba ce. Da bakin mutane na kama Nuratu, da bata kawo yanzu ba. Hatta kank nin yaro
Faruq ya kance Nuratu mai dogon gashi, duk garin nan babu mai kyanta. Da bata fini tsawo ba
da na aure ta" suka yi ta dariya. Bai tafi ba sai da ya jona mata kan ‘telephone’ a dakinta domin
su rinka gaisawa, ta kuma rika jin halin da yake ciki. Haka ya koma cike da tunanina a ransa.
​ Da na dawo gida na tarar Ya Rabi tayi kan telephone, na cika da mamaki, kafin na kama
tambayar dalilin da zai sa Malam yayi haka, wato ya sanya mata bai sanyawa Inna Dubu ba, ya
yi dariya yace “bani bane na sanya mata, danta Sa'idu ne”.
Ba tun yau nake jin sunan Sa'idu a gidan ba, to amma ban zaci yayi girman da har zai sayi
telphone ba, a wancan lokacin kam ba karamin mutun ne zai sanya kan telphone a gidansa ba,

sai ya zamanto har makotanmu masu mu'amala da birni, kanzo cin aziki dakin mu, har numbar
suke badawa a bugo musu, in je in kira su suzo su amsa. To nima sai na sahiga karbar lambar
kawayena na makaranta da suke a nesa, muna gaisawa.
Rannan Ya Rabi ta shiga wanka, ni kuma ina sharce kaina dana wanke. (Telfon) ta shiga kira,
tayi har ta tsinke ban dauka ba, ina cigaba da abinda nake mai kiran dai bai hakura ba, ya sake
kira a karo na biyu, wannan karon ma sai data kusa tsinkewa kamin in aje kum din in amsa da
"sallamu alaikum, mai telphone din ce ta shiga wanka" yayi dariya yace "hala kece Nuratu?” Na
cika da mamaki bance komai ba, ya sake cewa "ko ba Nuratu bace, Nuratu mai dogon gashi?”
Na yi murmushi nace "hala kaine Sa'idun dake England?”
Ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi yace "na dade da son jin muryar Nuratu, na dade da
son ganin Nuratu a zahiri. Ban zaci muryar Nuratu yayi taushin haka ba, ban zaci ajin Nuratu ya
kai har haka ba, ashe Nuratun classic babe ne? Irin wannan JAN AJI haka?”
Ban san sanda nayi murmushi mai sauti ba, nace "ina wuni Yaya Sa'idu, yaya sanyin England?”
Yace "Sanyin nata har ya kai sanyin muryar Nuratu?” Nikam ban saba jin irin wannan
maganganun ba, don haka na ji duk na takura, don ni ban taBa tsayawa wai in saurari wani
saurayi ba, tunda nake, ko irin malaman mu na makaranta da ke cewa suna sona, kara nake
kaisu a koresu, don a ganina ai iskanci ne ace ana son ka. Don haka da Sa'idu ke min
wadannan maganganun da basu dace da wadanda na saba ji a bakin mutane ba, sai naga to
me yayi zafi da zan takurawa kaina da cigaba da hira da shi? Na yi hanzarin cewa "ka sake kira
in an jima kadan, lokacin ta fito". Ba kuma tare dana bashi damar kara cewa komai ba, na ajiye.
​ Tun daga ranar ne kuma idan na lura Sa'idu ya kira Ya Rabi, sai in fita daga dakin in
Buya a bandaki. Kiran duniyar nan zatayi min ba zan amsa ba, sai sun gama yayi mata sallama
sai na shigo, ta ce “Sa'idu yana gaisheni, tayi ta kirana mu gaisa bata ganni ba”. In ce “ina
amsawa”. Shi kuma ba yadda za’ai ya kira bai ce ta nemoni mu gaisa ba kamar maye. Kai tun
bata ganewa da gangan nake fita, har ta gane, sai ta yi min dabara, ban sani ba.
Da lokacin kiran nata da yake yi yayi, sai tace dani "au dazu kin fita ke da Halima, kawarki 'yar
Hadejia ta yi kiranki, nace bakyanan amma bakiyi nisa ba, ta ce zata sake kira nan da rabin
awa". Don haka na zauna bakin waya a kalla awa daya zaman jira kiran Maryam Hadejia,
calssmate dina. Kiran yana shigowa kuwa na dauka babu ko sallama nace "shegiya Maryam,
kina can mukus a Lagos abinki, kin bar mu da zafin Arewa" daga can Bangaren aka ce "ke
kuma kina nan mukus a Gwarzo ba, wai Nuratu ashe daman baki da kirki?” Nayi murmushin
gane mai Maganar, a shagwBe nace “kai Yaya Sa'id, amma ka shammace ni…” yace "in
tambayeki Nuratu, samari nawa kike jawa aji, irin yadda kike ja min?” Na kyalkyace da dariya
nace "Allah ni bani da wasu samari, ka tambaya Ya Rabi ma" ya ce “to don Allah, gani, ko nayi
maki tsufa ne in aske furfurar?”
Nayi dariya don ni maganarsa a wasa, na dauketa nace "lalle ma Yaya Sa'idu, zolayata kake yi,
kai da kake can kana kallon masu jajayen kunnuwa da jan gashi, me zakaci da wata 'yar
kuayen Gwarzo?” Yayi murmushi cikin nishadi yace "ai kema jajayen kunnuwan gareki. Allah
Nuratu baki san irin aji mai matsayi da muhimmanci da na sakaki bane. A hoto kawai na ganki,
kin hana mani barci. A tafe nake, a zaune, a tsaye ko a kwance, tunanin Nuratu nake, mafarkin
kasancewarta matar aurena nake kowanne dare. Jiya ma ganinta na yi cikin barci na, rungume
da 'yan tagwayena, mace da namiji, tana shayar dasu nono, baki gansu ba jawur dasu kamar
Nuratu ………” na katse shi ina dariya da cewa "kai don Allah Yaya Sa'id?” Yace “Allah wallahi

da gaske nake Mummy Nuratu" muka yi ta dariya kamar wasu shashashu, ya bini ya maida
kansa yaro kamata muka yi tayi. Wallahi tun daga ranar na fara kaunar Sa'idu.
Son sa da kaunarsa ya soma bin jinin jikina, domin yana daga cikin irin mazan da nake burin
aure ta kowanne fanni. Ina son na auri namiji mara girman kai, karya da nuna isa, barkwanci da
nuna kauna hakanan mai ilimi. To Sa'idu duk ya tattara wannan har ya zarta da wasu.
Ban taBa ganin shi ba, a waya kawai na soma kaunarsa, a waya ya ginawa kansa babban
matsayi a zuciyata da ni kaina ban san iyakarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login