Showing 15001 words to 18000 words out of 43757 words

Chapter 6 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf

gareshi, wanda ke daga cikin rukunan musulunci, a koma ta hukuncin mai
daukar fansa, wanda bai yarda da hukuncin da Allah ya zartar a kansa ba.
Ubangiji (S.W.T) yace "kuyi hakuri, hakika Ubangiji yana tare da masu hakuri” ya kuma ce “kuyi
afuwa (ga wanda ya saba muku) hakika Ubangiji mai afuwa ne". To ni banyi hakuri ba, banyi
afuwa ba kamar yadda Faruq da Halima suka Bata muhimmin lokacinsu suna nuna mini.
Mafi tashin hankalin ma daukar fansar tawa akan UWA, wadda sai ta daga min diga-diganta ne
zan wuce aljannah, wadda Bacin ranta zai kaini wuta, hawayen ta ya turani jahannama. Wadda
(S.A.W) yace “a bita, abita, ya kuma cewa a bita, kamin yace abi Uba….”.
Nasan inda duk take a yanzu tana can tana zubar da hawaye, ba don bakin-cikin hanata sisaya
ba, sai don bakin-cikin FADUWAR GIRMAN ta, bacin suna da zubewar mutunci, duk a
sanadiyyar diyar data tsugunna ta haifa a cikinta.
Ni ban gyara lahirata ba, gashi dama duniyar tawa gurBatacciya ce. Na kuma kara gurBatata.
Idan da na yi tunani, ai kirari ne nayi na zurmawa kaina wuka, ko babu komai na baro inda aka
sanni, saboda gudun kar a kirani da ‘shegiya’.
Maimakon da nazo inda ba a sanni ba, in rufawa kaina asiri, in nemi dangin uwata da ita kanta,
mu taru mu rufawa juna asiri, a'ah, suma na kawo musu guzurin Bacin suna da abin gori har
'ya'ya da jikokin su….
Numfashi na naji yayi sama, kamin ya gagareni fesarwa, kirjina ya shiga wani irin zafi da
radadi, kwakwalwata ta shiga bugawa dam-dam saboda zazzafan tunanin dana takurata da shi.
Idona ya shiga lumshewa yana budewa a hankali, ban kara tsinkayar abinda yake faruwa da ni

ba, illa jin hannun Qassim daya taroni ina shirin zamewa cikin seat dina, yana cewa "Ayya
Zaynab! Me yayi zafi haka?” Na lalubo shi na kamo kansa dai-dai kunne na, muryata ta dushe
gabadaya, nace
"ko bayan raina… ka roka min gafararta, ka gaya mata nima bada son raia na aikata mata
hakan ba, zuciya ce tafi karfina……, na-nayi in lankwasata, na kasa, na yi kuskure babba da
bani da inda zan sa kayan nadamar shi…." yace “Insha Allahu Zaynabu, ko zaki mutu sai a
kirjin mahaifiyar ki. Ko wannan shine abu na karshe da zanyi a rayuwata, zan yi iya kokarina in
sadaki da ita…”. Bayan wannan, ban kuma tsinkayar meke faruwa a duniyar ba.

***​​ ***​​ ***


A NIAMEY

“Aunty Zaynab, muna yi miki barka da zuwa cikin (family) dinmu na MAINASARA KANGIWA".
Zazzakar muryar wata matashiyar yarinya da bata fi shekaru sha hudu ba, na ji a cikin kaina
kamar a mafarki.
Wadda ta kitsa mata fadin hakan ta kara ce da ita “ki gaya mata dama mun san ko ba-dade,
ko-bajima zata zo ne, in har tana raye”.
​ A hankali na bude idanuna da suke a rufe, a baryar da sassanyar muryar matar ke
fitowa. Fara ce sol, doguwa mai ginannen jiki. Fatar jikinta sumul-sumul jawur, kamar kana
tabawa jini zai yi tsartuwa. Sumar kanta yalwatacciya baka kirin, nannade a gadon bayanta.
Hancinta a mike kamar biro, sai murmushi take tamkar furen fulawa, hakoranta farare tas kamar
kankara, yatsunta na kafa da hannu sun sha adon bakin lalle sunyi shar, santala-santala dasu
jajawur kamar na jariri sabuwar haihuwa.
Mayuwanci ne ka kimanta shekarunta a lokacin daya, za dai ka kirata babbar mace, mai
babban al'amari. Idanunta dara-dara farare sol da kwayar ido mai sheki kamar an diga zyl, sun
sha (kohl) sun fito dara-dara cike da barazana da rashin son waigi. Sanye take da ruwan hodar
lesi (Cotton) watau (dark-pink) mara nauyi, shara-shara, shafal-shafal kuma mai saukin ado.
Wuyanta da kunnenta ya dauki siraran ‘pearls’ na farin dutse, riga da zane ne a jikinta, daurin
kallabin ya zauna sosai a kanta kamar nadin inji.
Gabadayanta sai kace sabon kwai ne da Dawisu ya nasa yanzu-yanzun nan, domin haka take
very delicate. A Bangaren jinsin dan adam (personality) tana cikin rukunin 'phlegmatic people’
watau mutanennan masu fara'a, rashin kuzari da wadatar jini a jika. Mahaifiyatace, Hajiya
Nuratu. ​ Kallonta nake cike da mamakin yadda za'a ce matashiya kamar ta, ta haifi katuwar
budurwa kamana. Zai fi dacewa idan akace ni kanwarta ce, mai bi mata a haihuwa. Lokaci guda
wata irin kauna ta UWA (maternal love) irin ta da da mahaifi, wadda Ubangiji kadai yasan
adadinta, ta rika keta zuciyata. Ba abinda zan so a lokacin kamar ta rungumeni a cikin jikinta,
inji me 'ya'ya suke a dumin jikin uwa?
Amma batayi hakan ba, baya ta juya min tana abinda yafi mun kama da sharar hawaye. kofar
dakin ta bude, mata ne suka rika shigowa farare tas-tas manya da kanana, tsofaffi da masu
tsaka-tsakin shekaru. Kallon sittirun dake jikinsu da yanayin fatar jikinsu kadai ya isheki kimanta

sune iyalin Kangiwa. Tambaya suke ta yi “ina Zaynabu din? Ku matsa na ganta………. Ku
gafara mu ganta. Kauce nan na hangota. Zaynabu ina Yaya Rabi? Zaynabu wa ya kawoki
Niger? Ina kika baro Yaya Rabi, ba tare kuke ba…?”
Na maida idanuna na lumshe, wasu irin hawaye na fita suna shiga cikin kunnuwana.
Cancarakas suka dagani suka tsayar da ni akan kafafuna. Daga masu rungumata sai masu
kama hanuna da masu tube dankwalina don ganin kalar gashin kaina.
Kowanne na fadar albarkacin bakinsa game da kamannu na da mahaifiyata da 'yar uwarta
Rabi. Wata gyatuma tukuf a durkushe tana dogara sandarta ta dogaro ta shigo tana "gafara nan
ku gani in bugi shashasha…” ta daga sandarta ta muka min a baya, wata mace mai
tsaka-tsakin shekaru daga cikin wadanda suka zagayeni ta rufeni ruf da bayanta tace “sai dai ki
bugemu tare Yadudu, amma Zaynab kuruciyarta ke dibarta, ta kuma gaya mata miki abinda
take tunanin shine dai-dai da ita, ko ni ce hakan zanyi. Kuskurenta daya bata fara tunkarar
Nuratu ta ji bayani daga gareta ba.
Zaynabu Allah baya ramurar gayya ba kuma ya son masu yinta. Idan kece hakan ta faru dake,
zaki so 'yar ki ta yi miki abinda kika yi mata?”
​ Ni dai sai kuka nake na rasa ta cewa. Ganin al'amarin nake kamar a mafarki, na kasa
gasganta wannan rana. Wai wadannan duka dangin Inna ta ne jinin ta ne, tsatsonta ne. Na
daga kai domin hango karshen su, iyakar ganina banga adadin su ba, da alamama akwai wasu
a waje, wadanda duk girman da dakin ke da shi, basu samu wurin tsayar da kafafunsu ba. Na jinjinawa zuciya irin ta Innata, da ta iya rayuwa ‘lonely’ cikin karkara, shekaru ashirin da
doriya ba tare da kuwa nata ba, duk da wannan bataliya da Allah yayi mata, ba kowadanne
mutane ne masu zuciyar Inna ta ba.
​ A cikin su dai na ci gaba da hange, don karin ganin fuskar dake yawo in my
imaginations, kwana da kwanaki, wata da watannni, shekara da shekaru; Nuratun Inna Rabi.
Muka yi ido hudu, kallona take babu ko kiftawa, fararen idanunta cike da tarin kaunar da biro ba
zai iya rubutawa ba.
Duk da haka hawaye basu bar ambaliya daga idanunta ba. Ta tako a hankali suna darewa
suna bata hanya, zuwa gadon da nake zaune, na tura 'yan yatsuna guda biyu cikin bakina,
domin toshe kukan dake son suBuce mini, ta tsaya a kaina ta ce “ina Yaya Rabi?”
Da karfi kukan ya kufce, na yi ta yi babu sassautawa, cikinsu babu wanda ta katseni amma
jikkunan su sunyi sanyi, har na yi mai isata ya isheni. Cikin dusashshiyar murya nace “Allah yayi
mata rasuwa sati biyu da suka wuce……..”
Gabadaya falon ya rude da kururuwar mata da tsofaffi, barin tsohuwar da naji an kira da
Yadudu, faduwa tayi tana tana makyarkyata tace "ashe rabon zamu sake ganawa dake ba
Rabi? Cikin wannan satin muke shirin tafiya gabadaya gareki, wayyo Rabi baiwar Allah bamu
rike amanar mahaifinki ba….." hankalin su duka ya koma kanta, suka cicciBeta suka dora akan
gado suna yi mata fifita da bakin mayafan laffayansu, daga baya na fahimci ita wannan
dattijuwa kaka ce ga Innata domin ita ta haifi mahaifinsu Alhaji Sani. Ita kadai ta saura cikin
matan marigayi Kangiwa.
Bana son tuna irin halin da Nuratu ta shiga da jin mutuwar 'yar uwarta. Ta zama jawur kamar
jinni, tana kuka da hawaye da majinarta, ta fita daga dakin ta hau matattakala zuwa sama, har
dare bata kara saukowa ba.
​ A lokacin ne iyaye maza suka iso daga sammacin da 'yar uwarsu tayi musu. Suka tarar

da wannan labari sukace "Allahu Akbar, haka Allah ya so bamu da rabon ganawa dake Rabi sai
a Darusallamu, ki yafe mana ki yi mana aikin gafara, bamu sauke hakkokinki dake kanmu ba.
Tunda Alhaji ya rasu babu wanda ya bi sawunki, tunda 'yar uwarki ta iso ta ce mana kina lafiya
zaman aure kikeyi, babu wanda ya kara bi ta kanki. Hakika idan baki yafe mana ba akwai hisabi
a tsakaninmu, ga gadonki muna ta ajiye da shi har yau ba wanda ya ci, don haka zai zamo
sadakatul jariya a gareki…". Dacin mutuwar 'yar uwarsu ya shafe nawa al'amarin, suka taru kaf
a babban dakin ‘meeting' dinsu dake cikin gidan Nuratu, suka bude al'qur'ani mai tsarki suka yi
ta sassauke mata, aka kada Rakuma, shanu da raguna aka yi ta sadaka. Tun daga ranar garar
abinci kawai ake fitarwa daga (Estate) na Kangiwa nau'i-nau'I zuwa ga kushewarta, har tsayin
kwanaki (7). Ni da Qasism sai dai hange daga nesa a dakin addu'a, ya yi min murmushi in
maida masa, sai ranr bakwai Liliya ta kawo Innarsa daya manto a asibiti.
Jin abinda ke akwai ai sai ta kara faduwa ta suma, ban taBa ganin rarraunar tsohowa irin
wannan ba. Hibbani cousin din Innata wadda ke kareni da Hajiya Yadudu na duka, ita ke gaya
min Goggo Azzo, kanwa ce ga kakan mahifiyata watau Kangiwa Mainasara.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Da na tattago radiyon Rabi, na sauke masa a baki, sai ga
haBo ya biyo baya, na guda-gudan jinni, suna sauka akan hannayensa nace "kadan kenan
daga abinda zaka gani, a duk ranar daka sake gigin shiga harkata".
​ Yadda duk ya dauki abin da sauki, to ba haka yake agareni ba. Ya dauka wannan karon
ma zai sake samun kaina da irin kalaman yaudararsa, bai sani ba, kishi yana maida soyayyah,
kiyayya, sannan, zama da kishiya is not the type of life I planned for.
​ Rabi kam ta yi tsalle gefe tace babu ruwanta da shirgin mu, tunda sanda muka kulla
soyayyar, ai boyewa muke bama so ta sani, saboda mun maida ita 'yar bukulu, saida ta kwaBe
masa zaizo ya isheta da 'yar murya. Haka nace da Malam Ali, muddin ya daura min aure da
Sa'idu, to zan guda kasar mu, cikin dangina, ya samo mai zama da matarsa. ​ Na kara gasgata rashin tabbas, karya, yaudara, da ha'inci irin na da namiji. Wai zai dubi
Sa'idu a haka yace ya taBa yin aure ma balle ya haihu? Wa zai ce ya taba yin soyayya ba a
kaina ba? Na rokI Allah ya saka min akan wannan yaudara da Sa'idu ya yi min, ba kuma don
komai ba yayi min hakan ba, sai don ganina da yake yarinya karama, mara wayo, domin da yayi
aure da wuri tabbas da ya haife kamata.
​ Wai ma ashe tare da matar tasa suke, ya taho da ita ganin gida da kuma bikin auren mu.
Ban san haka ba sai da yamma da tazo ana take mata baya, cikin atamfa English marun kala,
ta yafo wani dan yalolon gyale, kamar na tatar koko, tana tafe kai a sama, kamar kada ta shaki
iskar kauyen, ita a dole ga baturiya. Ta zo har cikin dakinmu yaronta Imran na biye da ita yana
ta kuka, ta coge a bakin kofa don dakin bai isa ta taka baturiyar kafarta a cikin sa ba, ta ce
"zuwa nayi inga BARAROJIN data kanainaye min miji, zuwa nayi inga SADAKA-YALLAR dake
shirin aure min miji?
Ba dai wannan berar bace mai kama da dorawa?” Muka daubi juna ni da Yaya Rabi, cikin
mamaki, dimuwa da rashin abin cewa, ta cigaba da cewa "Bararoji Nijar babu abinci, kun gudo
daga jeji, domin BARA da KARUWANCI, ai da kun tsaya a karuwancin, amma mijina? Yafi
karfin auren sadakar-yallah, koko ince, naïf karfin yin kishi da sadaka-yallah". Ta Balle bakin
jaka ta debo (pounds) na kasar Ingila curi guda ta watso min a fuska tace ​ Yallah, ga
sadaka nan, don Allah a kara gaba. Sa'idu sai Sa’a, sai gani sai hange, ance dake ana yin mata
biyu a Ingila ne? karya yake miki baskwata ya gyara miki, duk kuma mai zaune a baskwata, 'yar

wanke-wanke ce.
​ Kenan gara miki zamanki cikin kauye, yafiye miki rufin asiri, ko kuma a koma Niger ayi
tallan cukui, a kora Rakuma sahara. Muddin kika sake kika biyo shi, wallahi 'yar wanke-wanke
na samu, amma nafi karfi in yi ‘sharing’ miji da sadakar-yalla da tsafta ma bata ishe su ba".
​ Ta juya tana kada mazauna ta fice abinta, daga ni har Yaya Rabi, gudun jini ya daskare
a jikinmu. Ba'a taBa yi mana wulakanci irin wannan ba a tsayin rayuwar mu. Duuiya mai yayi!
Wai mu jikokin Kangiwa ne yau ake kira mayunwata, karuwai, sadakar yallah! Allah sarki!
Mukai ta kuka har muka ji babu dadI, nace "wallahi ko zan mutu babu aure, bazan auri Sa'idu
ba" Rabi tace “shirmen banza, bazaki aure shi ba kawai idan bakya son shi, amma ba don
wannan busashshiyar da aka bashi sadaka ba. Da ta isa ta yi mana wannan zagin a gaban sa,
wallahi saki uku zata karBa babu nadama!” Nace “kayya Yaya Rabi, son ma na daina, indai na Sa’idu ne, koda kuwa shine autan maza.
Yau mu ake kira karuwai Rabi, har ke da kike a dakin mijinki? Allah ya isa tsakanina da wannan
matar dana bari ta fita ban tara mata gajiya ba….”
Rabi sai ta koma yi min dariya, ta ce “a hakan? Da dai kanwar ta kar tsami". Na fada jikinta ina
kuka nace "Allah sai na rama akan wanda ya janyo miki zagi a rayuwarki".
​ Sa'idu kam da gaske yake, ya cigaba da shirye-shiyen aure batare da ya kara bi ta kaina
ba. Dana ga dai da gaske Malam zai daura auren nan, sai na hada kayana da asuba na fice da
niyyar in tafi tasha in hau motar Niger, ko yaya Rabi bata ga fitata ba tana barci. A lokacin kuma
Malam da Sa'idu suka fito daga masallacin dake daura da gidan mu daga sallar asubahi, suka
hango ni ina ta nikar sauri da akwati rindimeme aka kamar wata zararriya.
Gabadayan su suka biyo ni, Malam Ali ya sha gabana, ya ce "Nuratu me yayi zafi, kawo
akwatun ya daukar miki, kin san dai bazan taBa yi miki auren dole ba, domin kuwa ke amana ce
a hannuna da idan naci sai Allah ya tozartani duniya da lahira". Jikin Sa'idu ya yi sanyi, ya
tabbatar wannan karon da gaske nake. Babu komai cikin kwayar idona sai kiyayyar shi
tsagwaronta. Shi ya dauko akwatin muka dawo, Malam yana ta fada wa Yaya Rabi, kan
sakacinta har na fita bata sani ba, yanzu da Allah bai sa sun ganni ba wa yasan inda zan fada?
Nikaina fada kawai nake, amma in za'a kasheni bana ce ga hanyar da zan bi inje Nijer din ba a
lokacin. Ta dinga salati ta ce “haka kike da taurin kai Nuratu ? To shikenan Sa’idu ya fasa
aurenki, ko kece autar mata don Allah ki zuba ruwa a kasa ki sha”. Sabida haushin dana bashi
daga ranar bai sake shiga sabgata ba, suka soma shirye-shiryen komawa. ​ A dan tsukin kwata-kwata bana cikin nutsuwata sakamakon mafarke-mafarken da nake
masu ban tsoro da Sa'a, kullum sai na ganta cikin barcina dauke da jariri tana miko min ina kin
karBa, sai tace “karbi abinki, kiyi gaba, in dai don wannan ne aka ce dole sai kin auri mijina”. Ni
kuma sai in yi ta gudu tana bina da shi, da taga ta kasa cimmani, sai ta wurgo min shi. Yana
fadowa jikina, kafin in rungumeshi, sai ya mike da kafafunsa ya bita da gudu ya rike kafafunta
gam-gam tayi ta kurma ihu. Jariri fa sabuwar haihuwa don haka wannan firgicin ya maidani
wata karamar zautacciya.
Babu kuma ranar da zan kwanta in tashi, ban yi wannan mafarkin ba, idan na farka cikin dare
sai in zauna a tsakiyar gado, inyi ta gursheken kuka. Rannan kuka na ya tayar da Rabi,
hankalinta yayi matukar tashi ta rika lallashina akan in fada mata abinda yake damuna, in dai
auren Sa'idu ne wallahi an fasa, ba zata taBa yi min abinda bana so ba. Na ce da ita ni mafarkin
da nake yi da Sa'a da jariri ne yake bani tsoro.

A hankali ta matso jikina ta ce cikin karamar murya "wane irin mafarki ne Nuratu?” Na fada mata
tiryan-tiryan, ta yi shiru tana kallona cikin nutsuwa can ta ce "in dai zaki ji shawarata Nuratu, kin
san dai bazan taBa kaiki ga abinda nasan zaki cutu ba. Sa'idu yana matukar son ki, Sa'a Malam
ne ya bashi sadakarta bada son ransa ba. Ya gaya mun don bazai iya yiwa Malam musu bane
amma wallahi baya sonta.
Ki kwantar da hankalinki ki fidda ita a lissafin ki, ki auri Sa'idu ina tsammanin akwai rantsatstsen
rabo a tsakaninku, wanda Sa'a ke son yin sanadin salwantar dashi. Ni ban san wane irin kishi
ne dake ba, ni bakya ganin kishiyoyi biyu nake zaune dasu me ya sameni? Wa kika ga ana so
cikinsu yadda ake so na? In gaya miki abinda baki sani ba, matan abzinawa basa boranci ko
kankani". Nace “wallahi Ya Rabi ni ba kishin Sa’a nake ba, kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login