Showing 18001 words to 21000 words out of 43757 words

Chapter 7 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf

dai auren da Sa’idu ne nake
jin ko za’a tsige min rai, bazan taBa yi ba. Na gwammace in shiga duniya. Amma don so har
gobe babu wanda zan so tamkar sa".
Sai tayi tsai da ranta tana kallona cikin tunani, tace “Nuratu kwanta kiyi barci, lamarinki na
bukatar addu'a, ina tsammanin ba haka Sa'a ta barki ba. To idan ita asiri take, ni kwana nake
sallah! Aurenki da Sa'idu bazai yiyuwa ba kadai idan dama ba rubutacce bane".
​ Ta bani addu'oi irin wadanda Malam ke bata, tace kullum kafin in yi barci in karanta in
shafe jikina.
​ Washegari da safe ta bani karin kumallon Sa'idu tace na kai masa, duk dai a kokarinta
na son ganin mun shirya kan mu. A yau ban san me yasa kwata-kwata ban yi musu ba, karewa
ma cike nake da dokin ganin sa, dana azabtu kwarai da rashin yi har tsayin sati biyu.
Dama na shirya koda bata aike ni ba, ni din zan je da kaina idan ta fita, domin tun jiya take
shirye-shiryen tafiya Bindawa dubo Uwar Sa'idu da bata ji dadi ba, tace zata kai dare. Shatar
mota guda Sa'idu yayi mata ya biya zuwa da dawowa tun daga Gwarzo har Katsina.
Tun safe nake jin wani irin motsi-motsi a cikin kwakwalwata, kamar ana yi min kida, haka komai
nake yi ji nake kamar umartana akeyi da yin hakan. Hatta kokon dana duka zan dauka, sai naji
kamar ance dani “baki zuba masa sukari ba”.
Na kuwa dauko sukari wurin gongoni hudu na antaya a kwanon koko. Na sunguma na tafi
idanuna na wani irin juyawa ko hanyar dakin Sa'idun na manta, amma sai na ji kamar an kama
hannuna, ana yi min jagora.
Ina shiga shi kuma kamar dama jirana yake yi, sai ya taso ya karBi kokon daga hannuna. Cikin
mu babu mai iya kallon fuskar dan uwansa, ya mika hannunsa ya rungumoni ya ce "Nuratu
mai-dogon-gashi yaya? Har yanzu kina nan nan akan bakanki, na bazaki aure ni ba?
To 'ya'yan da kikayi alkawarin haifa mani fa? Wallahi bazan iya rayuwa mai kyau agaba ba, in
kin guje mani Nuratu...." Daga haka ya soma rabani da duk wasu suttirun jikina. Ban yi wani
yunkurin ba ko kankani na hanashi hakan. Sai ma kara armasa mishi al’amarin da nayi. Don
haka ba zan kirayi al'amarin da sunan ‘raping’ ba illa ‘cooperation’ na dukkannin mu”. ​
Ta sunkuyar da kai daga kallona, tana wasa da kyawawan yatsunta da suka sha adon lalle.
Bata yarda mun hada idanu ba. Ta kai yatsunta ta dauke wasu makalallun hawaye daga
idanunta. Ni kuma sai na kai hannuna biyu na rufe fuskata da karfi, na kwantar da kaina a
cinyoyinta. Domin yanzu na fara fuskantar abinda ada, ban fahimta ba. Na kuma fara gane
Hajiya Sa'a mahaifiyar Ya Em, itace silar shigar mahaifiyata cikin halin da ada, nayi alkwarin har
abada bazan yafe mata ba.

​ Bata saurari sheshshekar kukan da nake yi mata ba kasa-kasa, ta cigaba da cewa “koda
Ya Rabi ta dawo ranar, ta so ta fuskanci wasu sauyuka a tare da ni. Domin na koma daga
kwanciya, sai kwanciya, daga daki sai daki. Data matsa min da tambaya na sanar da ita ciwon
marana ke matsa min. Da yake kuma ta san yadda nake fama da shi duk wata, wani zubin har
suma nake, sai bata wani tsaurara bincike ba. Illa ta hadani da kwayoyin felgin.
​ Wannan shine ya zamo mafari.
Daga ranar kullum da kafafuna nake fakar idon kowa in tafi dakin Sa'idu, kullum ta Allah babu
fashi kamar masu ibada. A lokacin Sa'a bata gari, taje Gombe can wajen dangin mahaifiyarta.
Wata irin kazamar soyayya muke aiwatarwa wadda a duk ranar dana tuna, na kan ji na tsani
kaina Zaynab, inyi kuka inyi istigfari, in yi nadama in la'anci soyayyah, domin komi dai mene ne,
akwai sharrin soyayya a ciki. Na samu kaina a wata irin sabuwar rayuwa, da ban taBa mafarkin
tsintar kaina ba. Sa'idu ya koyar dani wata irin soyayya mai wuyar bari. Yayin da ni kuma na
bada hadin kai da zuciya, gangar jiki da ruhina duka.
​ Kaka-tsara kaka! Kwanakin da zasu yi suka kare, suka yi shirin tashi washegarin wata
litinin. Zuwa lokacin ya lallasheni na hakura da zancen auren mu, to ma idan ban hakura ba, ina
zan iya barin wannan rayuwar mai gardi daya jefa ni a ciki.?
Ya samu Malam Ali suka gama magana kan cewa bayan watanni uku zai sake neman sarari ya
dawo a daura mana aure mu tafi. Hatta kudin auren da wanda za'a yi min kayan aure ya barsu
a hannun Malam. Ita kuwa Inna Dubu ya bata na sayen kayan sa rana.
​ Faruq yafi kowa murna da jin za’a yi mana aure da Yaya Sa'idu, ya ce "Nuratu mai
dogon gashi nine dan zamana dakin ki" na ce “to dan dukusuru, in ba kai ba dama waye?” Sai
Rabi ta bige min baki, wai bani da kunya, da kaina nake zancen aure na.
​ Tun komawar su Sa'idu, ban sake ganin al'ada ta ba. Ban damu ba don a wautata ai na
huta da shegen ciwon dake naman hallakani duk wata. Koda yaushe muna waya da Sa'idu
muna sanarwa da junan mu kewar da muke ciki. Ya kan ce “kiyi hakuri Nuratu, wallahi karatu ne
yayi min zafi, ga (financial difficulty) dan kudin da gwamnati take bamu na tallafin karatu ya
tasamma karewa. Dama wani bature nake yiwa aikin gidan gona yana biyana kuma a komawar
nan da nayi na taras Allah yayi mishi rasuwa shiyasa abubuwan suka cude mini. Ita kuma Sa'a
shegen kashe kudi ne da ita, bata barina in tara komai balle in kama maki wani gidan hayan,
wannnan da muke ciki daki daya ne sai kitchen da toilet. Ga rayuwar London mai tsada sosai,
ko abinci zaman kansa yake. Amma alhamdulillahi idan na hada wadannan takardun ne
Masters da nike yi, Jami'ar mu sun yi alkawarin zasu bani ‘lecturing’ daganan komai zai
dai-daita, don haka ni da zuwa ina jin sai farkon sabuwar shekara”.
​ Ko ciwon kai ban taBa yi ba, bana amai bana tofe-tofen miyau, sai dai na ji cikina yana
wani tamkewa da kumbura kadan kamar sabuwar kwarya. Abinki da dagowar mace sambal. Ga
kuma manyan riguna dinkin Nijar na shadda su nake zurmawa, hankali na a kwance, don ni har
zuwa lokacin ban taBa kawowa a raina wai ciki ne dani ba, har tsayin watanni biyar ris. A lokacin ne jarrabawar mu ta fito, na fito da (credentials) bakwai cif. Na yiwa malam Ali
maganar inason cigaba da karatu kamin Allah ya dawo da Sa'idu, ya ce sam ba zai barni in tafi
Kano ni kadai ba, inyi hakuri in Sa'idu ya dawo shi da kansa zai samar min gurbin karatu kamar
yadda ya samarwa Sa'a a Ingila. Kwanaki suka shura har watanni bakwai a bayan tafiyar
Sa'idu. To a wannan lokacinne fa ciki ya soma bayyana kansa.
Kafafuna suka kumbura, kumatu na sukayi sutu-sutu da yake irin cikinnan ne na samu mai bin

jiki. Na bude na zama wata ingarmar mace danya shakaf. Yaya Rabi mamakinta ya kasa
Boyuwa, rannan ta ce “Nuratu maganin kiba kika hadiya ne?” Da yake ita bata taBa haihuwa
ba, bata san wasu alamomin ciki ba. Na yi dariya na ce “hutu ne kawai Yaya Rabi, tunda babu
zullumin karatu”. Ta ce “haka ne fa, Allah dai yayi gaggawar dawo da Sa’idu mu sha biki”. Nayi
murmushi.
​ Duk wasu al'amuran gidan na daina shiga, na koma kullum ina kuryar daki, manne da
hoton abin kaunata. Shiga bandaki kawai ke fito dani. Sai dai ni kaina abun yana damuna,
sabida nauyin da jiki na yayi da kumburin da kafafuna ke kara yi. Ga wani wutsil-wutsil da nake
ji cikin cikina lokaci zuwa lokaci kamar mai macijin ciki. Ni da kaina sai na fara zargin kaina. ​
Al'amarin ya samo asali ne ranar wata talata, na fito domin yin alwalar sallar mgariba. Inna
Dubu ma ta fito da butar ta ta zauna a wani kututturen icce kusa dani zata yi alwala, ni kuma na
zauna bisa wani dutse. Zamana ke da wuya nepa suka kawo wata wuta mai karfi, ta dago tana
yi min magana ganin yadda na gacire kugu ina yamutsa fuska na kasa yin alwalar. Ta yi kasake! Tana dubana kafin idanunta su sauka a kafafuwana. Ta ajiye butar idanunta a
jirkice ta mike, har tana tuntuBe da turmi, tayi turakar malam shi a lokacin ma ya fito zai tafi
masallaci. Sai ganinsu na yi sun fito tare sunyo dakin Yaya Rabi.
Suka kulle kansu me suka ce, me suka ce Allah a’alam. Na kammala alwalata na nufo dakin sai
na taras sun sa sakata. Sai na jingina da bango duk nasha jinin jikina, a sannan ne na samo jiyo
sheshshekar kukan Malam Ali. Hankalina ya tashi, don ban taBa jin malam yana kuka ba, ko a
sanda aka aiko mai rasuwar gyatumarsa da ke Funtua. ​ Ji nayi an zare sakatar, Inna Dubu ta fito ko kallona bata yi ba ta nufi dakinta, nasa kai
cikin dakin Malam yana ta kuka, ita kuwa Yaya Rabi sai ta sa min ido kawai tana kallona.
Can anjima ta soma wani irin gurnani da huci kamar macijiya. Mika hannun nan da zata yi, sai
ta zaro wata sharBeBiyar wuka da suke yankan naman sallah ta yiwo kaina. Ban taBa sanin
Rabi nada karfi haka ba sai ranar, don kuwa daga ni ta yi cancakas ta kayar dani dai-dai lokacin
da Dubu da Rakiya suka shigo suka rirrikita suna “Subhanallahi. Rabi kada ki yi kisan kai ayi
nadama goma da ishirin”. Tuni ta watsar dasu ta yiwo kaina ta dora min wukar a wuya ta ce
"Don Ubanki, gidan Uban wa kika je kika yo cikin? Wallahi ko ki gaya min ko in kashe ki, in yaso
nima a kashe ni daki jawo min bakin-cikin da zai kaini kushewa…” Idona suka firfito ganin
mutuwa muraran. Malam Ali ne yasa karfi ya kwace wukar a hannunta, sai ta sakeni ta soma
kuka. Ta ce “Nuratu kin cuce ni, Allah sai ya saka min ya sakawa mahaifinmu. Ki fita daga
dakina ki koma wajen wanda yayi miki cikin, bani ba ke ko a lahira kada ki ce kin sanni….
​ Allah ya gani Malam Ali bashi da hakkinki. Duk wata tarbiyya da ubanki mahaifi zai baki
ya baki. Ya baki sani na Alqur'ani, addini dana book. Ya daura dukkan burin sa na samun
nagartattun jikoki daga gareki, amma sakamakon da ya samu daga gareki kenan, ki tashi ki fita,
ki tafi duk inda zaki bana son ganinki…….” Malam Ali ya tsagaitar da hawayen idanunshi, ya
kirayi sunan Allah nutsuwa ta zo mishi, cikin lallashi da kwantar da murya yace
"yaki Nuratu!”
​ Jikina in banda tsuma ba abinda yake, hankalina ya tashi, tsigar jikina gabadaya suka
tashi. Na soma rokon Allah ya dau raina da wannan abin da nake ji. Na roki Allah ya dau raina
kafin furucinsu ya zama gaskiya.
Na ja jiki na rarrafa gaban Malam Ali, hawaye ko dis basu diga daga idanuna. Lallai ne da ake

ce wani tashin hankalin yafi gaban kuka.
Idan ya tabbata cikin ne da gaske a jikina, ni Nuratu yaya zanyi da rayuwata? Cikin zuri'armu
kaf, babu wanda ya taBa yin wannan abin kunyar. Abar ma ta kunyar duniya mai sauki, to
kunyar lahira fa, da tsaywa gaban Sarki Allah!
​ Sai a lokacin al'amarina da Sa'idu ya soma dawomin tar-tar. Tamkar wadda ta warke
daga shafewar kwakwalwa (lose of memory). Shin ya aka yi ma har na bari hakan ta faru da ni?
Ya aka yi na bari soyayyar Sa'idu ta rufe min ido har hakan ta faru? Ni Nuratu na yi asara! Haka
Sa'idu ya cuce ni!! Duk wata soyayya da nake masa na nemeta na rasa. A karo na farko na ji na
tsaneshi, na tsani kaina na kuma tsani soyayya a rayuwata.
​ Malam Ali ya lura na koma kamar mutum mutumi, ya tabbatarwa kansa ni kaina bansan
cikin ne dani ba. Dubu da Rakiya duka sun hada tagumi, sai gumi ne yake yanko musu. Yaya
Rabi kuwa kuka take kashirBan, irin wanda ban taBa ganin ta yi ba a rayuwarta, har kuwa
lokacinda aka anar da ita rasuwar mahiafin mu, kuma ba abinda zai sa, ba abinda zai rage. ​ Ba abinda yafi damunsu a lokacin kamar mutuncin Malam Ali a idanun jama'ar Gwarzo.
Ba karamin abun kalubale bane a ce haka ta faru a cikin gidan sa. Malam Ali shahararren
malamin Alqur'ani ne, da babu ya shi a garin Gwarzo, haka halayensa da tsoron Allah irinnasa,
sun zamo ababen koyi ga duk wani da ya kwana ya tashi a Gwarzo. Su kenan. Ni kuwa tunani na ai rayuwata bata da sauran amfani; 'ya mace nike, wadda wannan
tabon bazai taBa goge mata ba, har 'ya'ya da jikoki. Maganar tunanin aure da Sa'idu ma kwata
kwata bana yinta, na shafe ta kamar yadda ake shafe mataccen abu a doron kasa. Yo wane
aure kuma bayan abinda ake yiwa auren an gama samunsa a titi! Mutunci ya zube, ganin
GIRMAN juna YA FADI! Sai a sannan ne na samu wasu hawaye dunkulallu, suka mirgino a
kundukukina.
​ Na kai bayan hannu na ina sharewa, a yayin da dan cikina ya shiga wutsil-wutisl! Cikin
koshin lafiya, da tuna min yana jin yunwa. Na runtse ido da karfi, wai ni Nuratu ce yau zan haifi
SHEGE! Wannan tunanin kadai ya kusa sani in fita a hankalina.
​ Cikin tattausar murya Malam Ali yace "Nuratu cikin jikin ki na wane ne?” Babu musu,
babu ja’in’ja, babu jinkirtawa nace "wallahi Malam, Sa'idu ne!".
​ Sai ganin Yaya Rabi mukayi ta yanke jiki ta fadi. Malam ya fita da gudunsa ya debo ruwa
yayi bisimillah ya shiga yayyafa mata. Tun daga ranar ta koma wata shiri-shiri, ba mai hankali
ba, ba taBaBBiya ba. Kullum sambatu ta ke da Sa'idu, da cin amanar da ya yi mata, da take
cewa har abada ba zata yafe masa ba! ​ Tun daga ranar ko nan da can ban kara lekawa ba. Bayan kunyar Malam Ali da sauran
mutane, ina jin kunyar Ubangiji na. Abinci sai Dubu tasa ni a gaba da fada kamar ta duke ni,
sannan zanci kamar ina taunar madaci. Fassara halin da zuciyata ke ciki ma a wannan lokacin
ba zai yiwu ba. Dubu ce ta tsaya tsayin daka wurin ganin cewar na dage da yin istigfari, da
kuma Innalillahi… domin samun gafara wurin Ubangiji da sauki acikin kwakwalwata.
​ Ban taBa ganin kishiya irin Inna Dubu ba, har inda nan ke motsi. Zuciyarta me kyau ce,
kudurinta na alkairi ne ga kowa. Itace tace abar maganar nan a tsakanin su. Babu maganar
zubar da ciki, domin ya shiga wata na shidda, kuma malam Ali yace ko da wata daya ne, shi
bazai zubar da halittar Ubangiji ba, da bai ji ba bai gani ba. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Data farfado ne ta fara kuka, ta laluboni ta rungumeni tace
"'yar ikon Allah kenan, Allah yasa kece jarrabawa ta karshe da zamu gani cikn zur'armu, Nuratu

kam bata kyauta ba, to amma ta tuba taga isharori iri-iri a kanki, sannan kuma wannan al'amari
ba yinta bane, kaddarar Allah ce. Mu nan Musulmi ne masu imani da yarda da kaddara don
haka bamu bambance ki da sauran jikokinmu duka daya kuke. Allah yayi miki albarka Allah ya
sanyaya miki zuciyr ki, Allah ya baki hakuri. Mantawa nayi da al'amarin data bamu labarinsa tun
dawowarta, shiyasa nayi tunanin abokan adawa ne suka kulla mata sharri. Ashe ni ina zaune da
jinina tsawon sati biyu rashin ido bai sani na gane ba. Sau tari na kanji kamar muryar Nuratu
cikin gidan ashe diyarta ce, kai amma (Mon amour) anyi sauna da bai gane ta ba". Ashe yana
tsaye a bakin kofar shigowa falon ya tokare hannunsa na dama da kofar yana murmushi yace
“wa yace maki ban ganeta ba? Dalilina na takurawa da nacewa ta biyoni ai sabida dan fashin
dana ji ya fasa ‘raping’ dinta saboda kamanninta da Gwamna Mainasara….." gaba daya suka
hada baki “'yan fashi? Menene kuma raping?" Ya yi musu bayani dalla-dalla suka yi salati ni ko
don kunya sai na ruga daki da gudu wurin Haiti diyar Aunty Habbani, da zamuyi tsara da ita, ina
gaya mata shi Yaya Qassim baya jin kunyar tsofaffin nan. Daga can fa lo suka ce "shi yasa ake
ce ka shuka alkairi, a ko'ina zaka tsinci abinka. Alkairin Nuratu ga al'ummarta, bazai bari a taBa
tozarta jininta a duniya ba".

Ranar da aka yi addu'ar bakwai ne Alhaji Aliyu Mainasara, Alhaji Kamilu Mainsara, Adam
Mainasara, Shettima Mainasara, da mijin mahaifiyata Senator Alhaji Kabiru Bedeggi, wadanda
suke masu fada aji ga iyalin Mainasara suka keBe mu ni da ita, daga ni har ita kamar surukai
muke, ba mai iya kallon dan uwansa cikin ido sai satar kallon juna kasa-kasa. Nafi sakewa da
Hibbani, kome nake son gaya mata sai dai in gayawa Hibbanin ta gaya mata, gashi a ranar ne
zata koma can kasar Chadi in da take aure. Haiti kuma zata koma makaranta a Kuala Lampur
(Malaysia) dama tazo hutu ne al'amarin ya ritsa da ita. Ita kadai ce budurwa don tace duka
tsarrakinta a family dinmu anyi musu aure, itama da sanya ranarta akanta da masoyinta Ahmad
yana aiki a Abidjan, watanni biyu ya rage ta kare karatunta ayi bikinsu, cikin kwanaki bakwai ita
ta yi min bayanin kowa cikin zuri'ar da matsayinsa gareni.
Ita Aunty Hibbani diya ce ga wan Baban Nuratu Alhaji Aliyu Mainasara kuma itace mahaifiyarta.
Ta ce mu anan family dinsu tun daga kan labarin Aunty Nuratu, ba'a aje budurwa sama da
shekaru sha shidda ba'a yi mata aure ba, nima don ban samu mijin da wuri ba ne, har Baba
yace wai sadaka zai bada ni, sai kuma ranan na raka Aunty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login