Showing 21001 words to 24000 words out of 43757 words

Chapter 8 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf

Nuratu taro Abidjan muka hadu da
Ahmed, ma’aikaci ne a ‘airport’ muka kulla. Ada ta ce bata yarda ba wai bare ne, sai dai a
hadani da Qassim, shi kuwa yace ko sama da kasa zata hade ba zai aure ni ba". Na ce “me
yayi zafi, duk kyannan naki Haiti?” Ta ce “uhm Yaya Zaynab, kece baki san Qassim ba, bai aje
kansa anan kusa ba, kema wallahi ba karamin mamaki nake ba da naga yana shiga shirginki,
amma kafin ni 'yammata biyar cikin family dinnan duk yaki su, wasu kwailaye yake kallon mu,
rannan yace cikin mu har yanzu ba'a haifi matarshi ba”.
​ Dariya nayi sosai. Na ce “ya akai shi kadai naji yana turanci sosai a cikin ku?” Ta ce “oh!
Qassim bai yi karatu anan ba, dukkan karatunsa na (Criminlogy) yayi shi a Jami’ar Dundee,
U.K”.
Jiya da daddare daya leko yi min sai da safe, ni da ita munyi shirin kwanciya muna addu'o’I, tayi
murmushi ta dauko filo ta aza a karkashin kanta tace "Allah na lura kamar Qassim na sonki"
cikin rashin kulawa nace “don me kikayi tunanin hakan?” Ta ce "his actions…..baki ji an ce idan
kada kare na sunsunar takalmi dauka zai yi ba?" Nace "to ki ma bar wannan tunanin, babu

wannan cikin rayuwata, duk wani abu da zai sa a binciko mun wannan usulin ina gudun shi ina
nesantar shi Haiti…" Idnuna suka ciko da kwalla, duk da munyi ‘light-up’ taga kyallin su cikin
idanuna, ta mike ta kunna fitila dakin ya gauraye da haske. Ta dubeni sosai ta ce "in har kuwa
zaki cigaba dasa wannan tunanin a zuciyarki, kina tare da Bacin rai kullum. Ki manta da komi ki
dauki komai ‘as a bygone’ ki fuskanci sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da kika samu kanki a
ciki Yaya Zaynab, bazaki dauwama haka ba, dole zakiyi aure ko kinso ko kin ki za'ayi miki bada
jimawa ba, in har ke jinin Mainasara ce.
Idan har da gaske ne abinda kike gudu kenan, to ki auri Qasim, shine ya da ce da rayuwarki,
tunda dan uwanki ne na jini, wanda ba zai taBa goranta miki abinda kike gudu ba, haka duk
danginsa.
Mu tsintsiyane a madauri daya, da wuya kiji an samu saBanin ra'ayi cikin zuri'ar mu, tunannin su
daya, zuciyarsu daya, haka kowa na jin dan uwanshi a cikin jikinshi. Qassim is the right man for
you; shine wanda zai rike ki kamar kina a gaban mahaifiyarki, ba tare da ya kaiki inda za'a taBa
goranta miki ba, tunda abinda kike gudu kenan, haka zai yi duk iya kokarinsa wurin kare miki
martaba da mutuncinki a idon kowa, ko don sabida kaunar dake tsakanin shi da mahaifiyar ki.
Baki sani ba, a hannunshi ya daukoki ya kawo ki har gadonta tun daga Damagaran, a sume,
bakisan in da kanki yake ba.
Yace koda wannan shine aiki na karshe da zai gabatar a rayuwarsa, sai cika maki burinki". Na
ce "amma ai a jirgi? Ta ce "eh, a jirgi”. Na yi murmushi nace "to menene abin wahalar anan?
Akwai wanda yayi shekaru goma sha takwas yana kaunata, duk da a san ko ni WA CECE? Bai
taBa furta min ba, ba don komai ba sai don gujewa rayuwata shiga cikin garari idan na gane
matsayina.
A sanda na gane ni din wace ce, ya tsaya mani, ya gaya mani cewa koda daga sama na fado
he'll continue standing by me, ina kuma da yaqinin abinda ya fadi, haka yake har zuciyar shi.
Domin ya nuna min na gani a zahiri”. Ta ce "don Allah waye wannan?” Na yi murmushi, tare da
jin wani sabon abu da ya dunkule min a zuci, ya hanani sukuni, game da Ya Faruq. Na kai
hannu na latsa makunnin fitilar dake jikin gadon fitilu koraye suka maye gurbi masu haske, na ja
bargo na rufe har kaina saboda raBar A/C dake ratsa kasusuwana nace "sai da safe Haiti".
​ Ire-iren hirarrakin da muke da Haiti kenan, gashi a yau zata tafi ta barni da kewa, daga ni
sai Nuratun da ko gaisheta bana iya yi, don haka kewar tafiyar su ta addabeni, ta hanani sikit,
hakanne yasa da Babannin suka keBe mu a falo, ni da Nuratu, duka raina a jagule yake. Ita
kanta na lura bata son tafiyar tasu sai don ba yadda zata yi ne tunda kowannen su zai koma
dakin mijin sa/bakin aikinsa tare da iyalansa.
Alhaji Aliyu yace “to Nuratu mu zamu wuce, sai mu kara addu’a mu kara Istigfari, wannan wata
ishara ce Ubangiji Subhana ya nuna mana, Allah ya jikan Yaya Sani”. Ta share bawayen idonta
da kyakkyawan hankicinta, ciki-ciki ta amsa da ‘ameen'. Ya cigaba da cewa "ku kwantar da
hankalinku, ke Zaynabu kin zo gida, cikin dangin mahaifiyarki inda ake kaunarta, don haka ko
shegu dubu ta haifa ba zamu juya masu baya ba, zamu kaunace su kamar su Haiti, wannan
tsakaninta da Rabbil Izzati ne.
Sannan ke muna rokonki da ki yafe mata, kiyi mata sassauci ki zamo mai afuwa, ki barta da
bakin-cikin da kika kunsa mata. Alas! Ba rikicin sisaya yanzu, Zaynabu ta rabashi, sai ki zauna
agida, ki huta, ki cigaba da biyayyar aure, dama mun yanke shawarar bazaki cigaba da kujerar
ki ba, su mutane ne suke son ki da hakan, amma Kabiru zai nema a madadinki (mijinta) tunda

shima 'tenure’ dinsa a Sanator ya kare daga wannan shekarar. Allah yasa hakan shine mafi
alkairi”.
​ Alhaji Badeggi ya amsa "Zaynabu feel free with us, ki saki jikinki da mu, ki dadukeni
tamkar Alhaji Sa'idu, inada ‘ya’ya nima don haka nasan ciwon haihuwa, don haka na yiwa Allah
godiya daya karo mana da ke rana daya. Na dade ina shawartar mahafiyarki da mu dauko ki,
tana ki, sabida a lokacin tana kan kujerarta kinsan yanayi na siyasa mai cike da abokan adawa
da bin kwakkwafi. Nida mahaifiyarki kauna ce mai tsabta da yarda da juna a tsakaninmu. Don
haka ki dauki kanki tamkar diyar cikina, kada ki kara tunanin wai ke daban ce cikin al'umma,
babu wanda ya fi wani, sai wanda ya fi tsoron Allah.
Ina fatan daga rana irin ta yau, ba zan sake jin wata kalma wai ita ke "shegiya ce" daga bakin ki
ba".
Na share hawayena na ce "insha Allahu Baba bazan sake ba" ya ja doguwar addu'a muka
shafa, aka rufe taron da raha da dariya. Nasa kai zan fita sai naji Alhaji Aliyu na cewa "Ya
kamata mu nemo shi V.C Sa'idu, don yasan tana hannun mu ko hankalinsu ya kwanta”.

Mun raka su Haiti filin jirgin saman Yamai (Mano-Dayak) inda zasu tashi zuwa Chadi. Sai da
muka ga tashinsu muka dawo ni da Qassim wanda ke jan motar. Muna tafe shiru, babu wanda
yayi magana har muka iso unguwar mu inda ‘estate’ din Mainasara yake watau (Plateux), anan
ne ya rage gudun motar yayinda hankalina ke ga tsari da kyawun anguwar plateux, na kare
nace "da alama babu anguwa mai kyawun wannan a Yamai" ya ce "eh, ai shugaban kasarmu
ma a cikinta yake, shima jini ne ga Mainasara. Zaman anguwar mun gaje shi ne tun iyaye da
kakanni, kuma a kalla mu muka cinye rabinta, kinga tun daga farkon ‘estate’ dinnan har zuwa
karshen sa, gidajen Kangiwa ne" na ce “amma me yasa kuka fi son Damagaram?” Ya yi
murmushi yace "kowa ya bar gida…. Zaynab. Duk cikin Niger babu inda nikeso irin
Damagaram, donnhaka ne ma zabi da inyi aiki tare da gwamnatinsu, waddannan gyatuman da
kika gani duk daga can suke, don ke suka zo, matasa-matsan ke zuane a nan domin itace
(capital territory) namu, akwai wadatar (infra-stuructures) fiye da ko'ina.
Mijin Aunty Nuratu, Alhaji Badaggi, Sanator ne na Damagaram a nan, don haka ne rabin
rayuwarta na nan, ko a sanda take gwamniyar mu. Data sauka kuma kwata-kwata sai ta dawo
nan gabadaya, amma duk da haka duk karshen wata tana Damagaran”. Hirarrakin da muke ta
yi kenan har muka kawo gida. ​ Tana tsaye a jikin madubin dogon yaro tana kulla sarka a wuyanta, na murda kofar dakin
na shiga da sallama. Ta cikin madubin take kallona bata juyo ba, tace "har kun dawo? Jirigin
nasu ya tashi?”
Kaina a sadde na amsa da "eh" tace "zo nan ki daura min sarkar wuyana” na karasa na
amshin sarkar ina sanya mata. Ta cikin mudubin na gane ashe tsawon mu daya, illa ita ta fini
kauri da murzajjen jiki.
Na sanya mata sarkar na juya zan fito daga dakin, har na kawo bakin kofa ta ce "Zaynabu me
zakiyi yanzu?” Nasa hannu na dauke hawayen da suke cike min ido, batare data gani ba, na ce
"sallah zan yi" ta ce “to in kinyi sallar kizo kiyi mun kitso, ai kin iya ko?” Na girgiza kai da sauri
na ce "a’ah ban iya ba". Daga haka nasa kai na fita. ​ Dakin da muke kwana ni da Haiti, wanda a yanzu ya zamo na kwanana ni daya wanda
ke daura da nata na nufa, a bakin gado na zauna. Na kifa kaina cikin tafukana soma girza kuka.

Na yi kuka har naji babu dadi tamkar zuciyata ta fashe. Wai uwar data haifeni ne wannan,
amma kwakkwarar magana wannan ba zamu iya yi a junan mu ba.
Wasu tausasan hannuwa naji sun rungumeni tsan-tsan, dumammun hawaye na sauka a gadon
bayana. Na yi hamzarin dagowa na dubeta, Nuratu ce. Nayi wata irin ajiyar zuciya mai karfi,
wata rahmah ta sauka a zuciyata, nima na rungumeta sosai mukayi ta kukan mu tare, kuka
maras dalili, maras tushe, illa na huce takaicin da zuciya ke ciki, da kuma matsananciyar kauna
irin ta da da mahaifi da bazaka iya ganin dayan cikin damuwa ka iya jurewa ba.
​ Akalla mun dauki mitiuna goma a hakan, kamin ta ce cikin sanyin murya
"Zaynab kin yafe mani?”

Na mike tsaye a hankali na bata baya. Na isa ga taga ina kallon kifayen da ke watsalniya cikin
akwatin ‘aquarium’ dake kudu maso gabas na dakin. Tunanin Inna na ya dawo mani. Na bude
idanuwa sosai na kalli irin rayuwar daular da take ciki. Girman gidanta da alatun dake cikinsa,
fadansa sai ya zama kauyanci. Motocin hawanta da gwalagwalai ba zasu lissafu ba, fadin
abinda ta mallaka da nau'in rayuwarta, abu ne da ba zai taBa yiwuba, illa ince samanta da
kasanta, hagunta da damanta duka arziki ne.
Duk da haka tana sane da irin rayuwar data baro Innata, a cikin karkara, dai-dai da rana daya
bata taBa tunanin ya dace ta nemeta ba, ko bata rabi ni'imar da take ciki ba, taji a wane hali
take bayan halin kuncin da ta barota cikin shekaru goma sha takwas!
A tsayin shekarunnan tsammani take Nuratu na wani wuri daban, Nuratu na cikin mummunan
yanayi. Nuratu na cike da kewarta. Har ta dangana da kushewarta hakanne a zuciyarta Allah
Sarki! A yau ni na gano mata saBani ga tunaninta. Nuratu ‘have already broke a new ground’ ta
manta da ita, ta manta da iskar data debota balle Dan tayin shegen data barota da shi; ya rayu
ko ya mace? Idan ya rayu wace irin rayuwa yake ciki? Wannan ba damuwarta bane tunda kuwa
ita ta tsira da nata mutuncin, tana nan tana zuba mulki su kuwa ko oho…..! Na shiga girgiza kai
da karfi, hawaye na fita min tarara. Ta taso a hankali idanunta jike da hawaye, ta karaso gareni,
na bata baya ne don haka ta yi amfani da hannunta daya soma kyarma ta juyo da ni gareta,
"wanna na nufin… na nufin baki yafe mini ba Zaynabu Abu.
​ Na rantse da Allah abinda kike tunani ba haka yake ba, labarin mai tsaho ne dana san
babu wanda ya taBa gaya miki. Zan kaiki Paris ki sayi duk abinda kike so…. Zan bude miki
(account) da duk abinda na mallaka …. Zan cigaba da kula da rayuwarki muddin rayuwata…..
zan maido maki farin-cikin da baki samu ba shekaru goma sha takwas a gabadayan tsayin
rayuwarki. Zan tsaya tsayin-daka domin inganta rayuwarki da abokin rayuwa nagari… A bayan
raina kadai, wani zai kiraki ‘shegiya’ Zaynab…."
Na dago idanuna daketa ambaliyar da hawaye, na yi mata duban tsaf. Mace har mace, data
baiwa arba'in baya. Amma tana magana irin ta yaran goye.
“Baki da arzikin da zaki saye dattin ki dake raina.
Ban taso cikin talauci ba, cikin rufin asiri na taso. Ban taBa kwana da yunwa ba, a tun bayan da
kika hana mani nononki. Malam Ali yana da shanu, na sha daga nononsu na rayu har na kawo
yau. Nayi dogayen kafafun dana zo na nemeki dasu.
Banzo nan don rashin sutura ba, da zaki kaini Paris din ki saya mani. Ko da nazo ba tsumma
bane a jikina, kaya ne irin na 'ya'yan gata. Baki da farin-cikin da zaki bani, domin dubun ki sun
sadaukar da rayuwarsu domin farin-cikina.

​ Wa yace dake rayuwa nayi cikin kunci? Saboda kin gudo kin barni domin tsira da siyasar
ki? Kina kyashin in sha nononki, sabida ni shegiya ce?
A gidan Ubana na rayu, wanda sanin ta hanyar daya samar dani, bai sa ya guje ni ba,
maimakon haka sai ya tsaya tsayin-daka domin ganin hakan bai takaita rayuwata ba.
Ya jani a ciki iyalinsa, duk da dattin dake jikina. Tun ban san kina ba ya mallakamin duk abinda
ya mallaka. Ban zo gareki domin raBar inuwar arzikin ki ba, sai don daukar fansa.
To amma zuciyar musulunci da kaunar iyaye, ya canza manufata zuwa ta alkhairi agareki.
Tunda kika haifeni kika dire, kin kara waiwayana? Kin kara komawa don ganin wace irin rayuwa
nake yi? Sannan yanzu don kinganni rana daya, a matsayin cikakkar mutum kice wai zaki kula
da ni? To wace irin kulawa? Kashi zaki wanke mini ko tumbidi zaki share mini? Maganar zaki tsaya don ganin ba’a kirani
shegiya ba, kin taBa jin an sakewa tuwo suna….???”
Kallona kawai take cike da mamaki, dimuwa da ta'ajjibi. Don bata zaci ina magana haka ba. Ta
kai dan yatsanta ta saitin kirjinta ta nuna kanta tace “ni kike gayawa haka Zaynab?” Na
sunkuyar da kai, ina share hawaye nace "kiyi hakuri, idan maganganuna sun miki ciwo. Ina
amayar miki da abinda yake tamkar guba ne a cikin raina. Idan na barshi sai ya kassara ni, in
kuma ci gaba da kallonki da shi. Ina kara gaya miki baki da kudin da zaki wanke dattinki da ke
raina."
​ Zuciyarta ta karye, jikinta ya mace murus, “ki saurare ni Zaynab, tsayin mintuna goma
sha biyar, in gaya miki gaskiyar abinda kike zargi, wanda ba haka bane…" na girgiza kai da
sauri "baki da kalmar da zaki gaya mini in yarda kina kaunar Innata yadda take ka unarki. Da
kina kaunarta, wallahi da ba kiyi shekaru goma sha takwas bata san inda kike ba, alhalin kina
da masaniyar bazata taBa samun kwanciyar hankali akan hakan ba, da baki bari bakin cikin ki
ya kaita kabarinta ba…." cikin shesshekar kuka tace
"Waye ya gaya miki bansan halin da kuke ciki ba? Waye ya gaya miki bansan a gidan Sa'idu
kika taso ba? Waye ya gaya miki ban san har soyayya kun yi da Imran ba?"
​ Nayi hanzarin dagowa na dubeta a rikice, tayi murmushi ta juya min baya tace "Zaynabu
ke nan, you are still a baby ina jin sai na sake haifarki. Ina Umar Faruq, ina Imran ina
Babanki…..?"
​ Na bude baki hangangan ina kallonta, ta yi murmushi tace "ki rufe bakin kada kuda ya
fada” sai na yi murmushin da ban shirya ba, ta sake mamakantar dani da cewa "ina 'yan uwan
ki Iftihal da Azizah?”
​ Na kai hannuna duka biyu na rufe baki ina dariya "kina yin maganganu wadanda suke
bani tsoro". Ta lakuce min baki tare da kama fatan kunnena ta ja ta da karfi kamar zata tsinke
min shi, nayi ‘yar kara bata saki ba tace "kamar yadda kudina ba zasu sayi dattin dake ranki ba,
haka zasuyi min amfani ta hanyar samomin labarinki keda Ya Rabi. Abinda yasa ba zanyi fushi
dake akan maganganun da kika yaBa min ba, don nasa kina a cikin zargi ne. Sannan na gane
kina da hankali, kina kuma kaunar mai kaunarki. Wallahi-wallahi Zaynab, baki fini son Ya Rabi
ba".
​ Ta juya da sauri zuwa dakinta, jim kadan ta dawo rike da wata 'yar batta da na soma
tunanin ina na san ta? Ta fiddo abinda ke ciki, haskensu ya dallare min ido, na soma kif-kiftawa.
Idan har ba gizo idanuwana ke mun ba, sarkar da Baba Sa'idu ya bani ce, shekaru takwas a
baya ta dutsen Sapphire, dana baiwa Ya Faruq ajiya. Tana murmushi ta ce “ungo kayanki mai

Uban dake sonta. Ba wannan ne abinda ya mallaka mikin ba, tun kina firamare? Ki tambayi
wanda kika baiwa ajiyar, kafin ki bashi wannan ajiyar, nawa aka bashi?"
​ Wannan na nufin; Ya Faruq na tareda mahafiyata a duk tsawon shekarunnan? Ya san
inda take, kuma ta hanyarsa ne take samun labarina, kai! Nuratu zata fasa mun kai…. Na kai
hannu na dafe kaina da ya soma sarawa tamkar ya rabe gida biyu, ni ban karbi sarkar daga
hannunta ba, ita bata fasa mikomin ba, nace idanuna a runtse "idan ba so kike kaina ya tsage
ba, ki fidda ni duhun da kike sanya ni". Ta kamo ni ta rungume tana dariya tace "ba ke kikace
bazaki saurare ni ba? Zaynab ya zan haifeki, kiyi tunanin bana sonki, alhalin soyayyace mai
tsanani ta kaimu ga aikata hakan nida mahaifinki, tunda an hanamu aure karfi da yaji, sai kuma
sharrin shaidan da bin son zuciya. Shin ko kin san Sa'a, ina nufin matar Sa'idu?" “Ni kuwa na
santa". Ta runtse idonta a hankali cikin tunanin al'amarin daya faru shekaru ishirin da biyar a
baya, a yau ya shiga dawo mata tar-tar kamar a majigi. Taja hannuna muka koma bakin gadon
muka zauna, ta dubeni tayi murmushi ta dauke siraran hawayen da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login