Showing 24001 words to 27000 words out of 43757 words

Chapter 9 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf

suka cika mata ido da
kyawawan yatsunta, yayin da kaunar Uwata ya cigaba da bunkasa a zuciyata, na kasa cigaba
da jurar ganin hawayen da take fitaswa, a hankali na matsa na kwantar da kaina a cinyoyinta.
Sai naji tamkar Innata. Tana share min hawayen da yatsunta ta soma……



KAUYEN GWARZO (1970)
LABARIN NURATU.

Kamar yadda kika sani, ko kuma kika fahimta Zaynab mu haifaffun kasar Nijar ne, cikin garin
Damagaram. Zaman mu anan Yamai ya samo asali ne tun daga lokacin da Kakana Mainasara
Kangiwa ya lashe kujerar shugabancin kasar Nijer. A lokacin su mahaifinmu basu da wayo, su
biyar ne 'ya'yansa kuma duk in gansu. Aliyu, Adam, Shettima, Kamilu, da mahaifinmu mai
rasuwa. Hajiya Azzo da kika sauka a gurinta kanwarsa ce, cikin su daya, ita ta haifi Hibbani
Babar Haiti. Qasim ba danta ba ne, jikanta ne, tunda kuwa da ne ga Baba Aliyu mai bin
mahaifinmu.
Zamanta tare dashi ya samo asali ne tun daga wajen haihuwa, da mahaifiyarsa ta mutu ta
barshi, ita ta daukeshi ta raine shi, har ya zamo tamkar da a gareta.
​ Tun Kangiwa yana da rai ya shaci wannan filin wanda daga baya ya zamo anguwar
plateux dinnan da muke ciki, ya assasa ginin wannan ‘estate’ yayiwa su mahaifin mu aure a ciki,
wanda aka cigaba da canza ginin yadda zai tafi da zamani har kawo na yau da kika gani,
wanda duk fadin kasar Nijar, an tabbata babu gini kamar namu, domin duk bayan shekaru uku
magina daga kasar China suke kara sabunta ginin da sabon nau'I na zamani. Wannan gidan da
nake ciki shine kason mahaifinmu, wanda ya zamo gadon mu ni da Ya Rabi.
​ Bayan rasuwar Kangiwa, dukkansu sunci gaba da harkar siyasa daban-daban,
mahaifinmu ne kadai yafi bada karfi ga kasuwancin fata, wanda ya amshe shi sosai kuma Allah
ya sanya mishi Albarka a ciki. Yana fitar da fatar rakuma da sauran dabbobi zuwa
masana'antun kasar China da Thailand, daga baya kuma har Nigeria saboda suma akwai
sana'ar kayan fata, inda ya san manyan mutane da yawa a Kano ta wannna hanyar.
​ Duk cikin matan Kakanmu, Yadudu Babar mahaifinmu kadai Allah ya yiwa tsawon rai,

tazo nan kin ganta, itace tsohuwar data dake ki da sanda, domin inda akwai wanda tafi so duk
cikin zuri'arta to ni ce. Wannan ya samo asali ne da kaunar da take yiwa mahaifinmu. Inada
shekaru biyar mahaifiyarmu ta rasu ta bar mahaifinmu ta sanadiyar ciwon kansar nono (breast
cancer). An ce mahaifin mu hauka ne kadai bai yi ba, saida 'yan uwanshi suka tafi dashi
Saudiyyah suka yi tayi masa addu'a, da taimakon su da taimakon Allah ya koma dai-dai,
saboda yadda yake kaunar mahaifiyarmu. To bayan rasuwarta sai ya dauki dukkan kaunar nan
ya daura akan mu nida ‘yar uwata. Haka ya shafe shekaru biyar bai kara aure ba yanata harkar
fatarsa, mu kuma muna hannun Yadudu a Damagaran, inda a can ne Ya Rabi ta gamu da
lalurarta ta shafar aljannu, a lokacin kam mahaifinmu ya bunkasa ya tara arziki sosai. Akwai
wata rijiya ta Man fetur da Kangiwa ya gadar masu tun yana raye, tana nan a Damagaram,
kinsan yanayin kasar mu (sahara) don haka mallakar rijiyar man fetur a cikin kasar nan ba
karamin abu bane. Shi kansa Kangiwa an ce ba'a san ta ina ya hako wannan rijiyar ba, kawai
an wayi gari ne an ganshi da ita (just a mirage). Ko da akazo rabon gado bayan rasuwar
Kangiwa, mahaifinmu shi ya mallaki wannan rijiyar shi daya, bai karbi ko kwandala na daga
dukiyar mahaifin su ba. Banda wannan gidan da muke ciki komi ya tafi ga su Baba Shettima.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Kishingide yake a falon alfarma na Baffa Aliyu wanda ke
daura da gidan Nuratu. An cika gabanshi da kayan marmari dana ciye-ciye da tsotse-tsotse. A
gefe cinyar rakumi ce aka gashe aka kyafe masa ita sai naso take da tashin tiriri. Ga wukar
yanka da cokali mai yatsu an soke a jiki, suna hirarsu da Aliyu da Shettima muka yi sallama a
tare.
Duk da GIRMA daya soma samunshi, da furfura tsilla-tsilla a cikin kanshi, still yananan a BABA
SA'IDUna dana sani; Baki ingarman gaske, ma’abocin gargasa, gagara-gasa a cikin maza.
Fi-sauran Babanni ( kamar yadda marigayiya Innata ta rada mishi).
​ Ya dago fararen idanunsa ya dube ni, sai na fadi ragwaf, akan gwiwoyina domin sun
kasa daukata. Saboda wani irin GIRMA da kwarjini da yayi min, koko ince, Allah ya rigaya yayi
masa. Baba Sa'idu dashen Allah ne kuma murucin kan dutse, abin nufi, Allah ya rigaya ya
tsayar da shi, babu wanda ya isa/ba abinda ya isa ya FADAR dashi, yayi masa haiba da
nasibobi da dama. Irin wadannan mutanen tsiraru ne, a cikin al’ummah.
​ Yayi murmushi yana nunawa Baba Shettima ni da dan alin sa, yace “ZAYNABU kenan,
KYAUTAR ALLAH, KYAUTAR INNA RABI, ABUN FARUQ, ABUN BABA SA'ID, BABBAR
MACE, MAI BABBAN AL'AMARI!
​ Suka yi dariya sosai ya ce "Allah ba da wasa ba Shettima, Zaynabu tana da babban
al'amari irin na NURATU! Ni na gaya maka nan gaba Zaynab wata ce, sai ta zama ZAYNAB
MAINASARA…..!!”

Da gudu na runtuma na rungume Babana, ina kuka yana sharemin hawaye da hannunsa, ni ke
neman afuwar, amma maimakon yayi afuwar, sai tawa afuwar yake nema. Su Iftihal sai suka
zama 'yan kallon kauna irin ta da da mahaifi. Ashe​ ‘YAYA DUKA ‘YA’YA NE, amma abin a zuci
GIRMA-GIRMA NE……!!!​​​ ​​
***​​ ***​​ ***

​ A ‘family meeting’ din da aka gabatar, wanda dukkan Kangiwa sun halarta. Malam Ali,

Alhaji Sa'idu, Nuratu, Azumi, Alhaji Badeggi, Faruq, Imran da Inna Dubu, gami da Yaya Halima,
itace kadai mai kananan shekaru a dakin taron bayan su Ya Im. Bayan tattauna duk abinda ya
dace, an nemi afuwar juna. Nuratu da Sa'idu sun yi afuwa ga junansu. Imran ya sunkuyar da kai
yace "akwai sako daga mahaifiyata ga Nuratu da Baba Sa'idu”. ​ Nuratu da Sa'idun ne kuwa suka juyo suka dube shi. Ya lumshe ido ya cije lebbansa
masu sulbi, yana mai kawar da dubanshi daga idanun Nuratu masu kaifi kamar reza, ya mayar
ga mahaifinsa, ya ce "Hajiya tace ku yafe mata, domin wai itace silar duk abinda ya faru da
rayuwarku data Zaynab, amma baku da kaico!” ​ Falon ya dauki tsit, Inna Dubu tace "ka bude baki kayi magana sosai yadda ta fadi
maka”.
​ Yayi ajiyar zuciya yace
"A cewarta, sanda Baba yazo mata da maganar auren sa da Nuratu, hankalinta ya tashi sosai,
saboda ta san Abba baya sonta, saboda darajar malam kawai ya aureta, yake kuma zaune da
ita.
A tunaninta muddin ya auri zabin sa, ita kuma tata ta kare, wulakantata zai yi, ko kuma ta kari
rayuwarta a zaman boranci, saboda irin tanadin da yake yiwa Nuratu ba kadan bane.
​ Da farko ta dauki Nuratu yarinya karama kuma 'yar kauye mara wayo, ta dauka idan tayi
mata barazana kawai zata hakura ta ji tsoro ta fasa auren Abban, sai taga Nuratu da Inna ko a
jikinsu. Shima Abban babu abinda ya fasa na shirye-shiryen aurensa da Nuratu.
​ Saboda haka ne ta tafi garinsu can Gombe, a wani kauye, Kumo, ta sami wani
hatsabibin malami ta yi masa bayanin matsalarta na a lalata maganar auren Nuratu. Malamin
yayi duba yayi mata bayanin cewa yayi bincike yaga akwai rantsatstsen rabo a tsakaninsu. Don
haka tayi hakuri ayi auren, in yaso sai su san yadda zasu lalata auren daga baya. Ita kuwa tace
da ta ga auren Abba da Nuratu, gara taga karshen rayuwarta.
​ Malamin ya ce to akwai mafita guda daya, zai iya yi musu asirin da zasu haife duk wani
rabo dake tsakanin su a titi, daga nan kuma babu maganar aure, zai cusa matsananciyar
kiyayyar junansu a zuciyoyinsu.
​ Bata taba sanin cewa Zaynab diyar Abba bace sai ranar da ya fadi musu da bakin shi
dukkansu a asibiti. Lokacin ana cuku-cukun fidda shi kasar Jamus. Tun daga lokacin data
yanke jiki ta fadI, ta samu (stroke) wanda har yanzu tana nan a kwance”.
​ Ya yi shiru yana maida numfashi a hankali, idanunsa sun kada sun yi jawur. Duk cikar
falon an ransa mai magana. Ba Nuratun ba, ba Sa'idun ba, kowanne ya fada a tafkin tunanin
al'amarin da ya faru dashi, shekaru goma sha takwas a baya.
​ Sai kuma tausayin junansu ya zo ya lullube su, idanuwan su suka kada suka yi jawur,
tsohuwar soyayya ta soma tashi, dama ance wai ita soyayyah, bata tsufa, duk GIRMA, sai dai
masoyan su tsufa. Wannan haka yake. Amma Allah bai kaddari suna da rabon aure a tsakanin
su ba. Ko sun yafe din ko basu yafe ba Allah masani.

***​​ ***​​ ***

​ A taro na gaba. Nuratu ta mike kokon bararta ga Sa'idu, na nemawa kaninta Faruq
auren diyarsa, Aliyu Mainasara ya nemawa nasa dan Qassim auren diyarsa Azeezah, sannan

shima Baban ya nemawa Imran dinsa auren Haiti.
​ Jin haka Badeggi shima yace ba za'a barshi a baya ba. Ya matso ya zauna gaban
Sa'idu, yace “BABA SA'IDU nima ina yiwa Abdulhakim, kamun Iftihal, yana Parisa, jibi-jibinnan
zai dawo a hada shi". Gabadaya falon aka sa dariyar aminci, yarda da GIRMAMA juna.

***​​ ***​​ ***


​ Biki yayi biki! Sha'ani yayi sha'ani!! Ba'a Damagaram ba ba’a Yamai (Niamey) ba, ba
Sokoto Birnin Shehu ba, har Gwarzo ta Jihar Kano, inda anan akayi kamun amaren cikin dakin
Inna Rabi.
​ Angwaye da Amare sun gaji tulis, har sun soma tunanin shafe wasu ‘acitvities’ don su
samu hutu da amarensu da Nuratu ta babbake ta hana masu ko da jin kamshin su.
Haiti 'yar hutu tuni ta fara ciwon baya. Azeezah kuwa kullum kara fiddo sababbin ‘programmes’
take wanda zai yi dai-dai da irin burinta, ga mijin Allah ya bata a hannu sai yadda tayi da shi, bai
san irin wannan hayaniyar ba, sannan an bashi wata irin mata 'yar giggiwa, mai shirin maida shi
waina a tanda. Iftihal da Abdulhakim ko sai shukurah, komai nasu yayi dai-dai. Abdulhakim Kabiru Badeggi
(Managin Director na Nuratu's World) watau shagunan Nuratu dake birinin Paris, mutum ne
nutsatstse mai sassaukar rayuwa, komai nasa yayi dai-dai da Iftihal wadda dama ita babu karya
da nuna isa acikin al'amarinta. ​ To ga Haiti da Imrananta sai ince kusan burin Imran ya cika, na auren farar mace,
ba'abziniyar usli mai jinni a jika wadda tafi Zaynab hasken fata da murjewar jiki, kai kace tocilan
ce a cikin duhu, sai dai fa kowanne na jin kansa, ita tana jira a fara neman soyayyarta, shi yana
jira azo a tsuguna ana lallashinsa tabdi! Baka san Haiti ba malam, don haka in ma mafarki kake
ka farka, ko kuwa a dawwama a hakan.
​ A Sokoto ne Faruq ya kira wayar Zaynab yace "kina ina ne? Am almost, nearly to die
Zaynab, na gaji, na gaji da wannan takunkumin na Mamie, rabon da in ganki fa tun kafin a
daura aure, in ba so kike in mutu ba sai ki ta biye mata. Ita Haiti da yake tana da wayo ba gashi
nan ba ta san yadda tayi ta fito ba suka fice da Imran, sannan Azizah da Qassim gasu can cikin
lambun Abba kin zauna kullum kina biyewa kauyancin Iftihal" murmushi ta yi mai fidda sauti,
“kai Ya Faruq, ba mun gaisa ba ranar daurin aure, ni yanzu dilke ake yi min" ya ce “in ma dinke
ki ake ki taso kizo nan dakin Imran, I seriously want to tell you something, Allah ko in shigo ciki
in jawo ki wallahi” ta dinga dariya ta ce "to bismillah, ai ga Aunty Hibbani nan itace ma take min
dilkan, ga kuma Mamie da Mama nan a bakin kofar shigowa" ya dinga jan tsaki, tsut-tsut a
kai-akai yayi cilli da wayar. Ya suri hularshi bisa ‘centre-table’ din Imran yayi cikin gidan fuuuu…
kamar guguwa.

Da gaske take Mamie da Hajiya Azumi ne a bakin kofar. Don haka daya hango su sai ya rage
taku ya koma cikin nutsuwar shi. Ya duka ya kwashi gaisuwa suka bashi hanya ya wuce ba tare
da tambayar shi komai ba, hakan ba karamin dadi yayi mishi ba da bai san amsar da zai bayar
ba, abinda ya sani kawai shine yan tsananin son ganin matarsa inda hali, har ya ji duminta cikin
jikinshi whatever the case! Kai tsaye yasa kai dakin Mama, da gaske dilkan Hibbani ke mata

daga ita sai daurin kirji, ya zauna dab da ita yana fuskantar Aunty Hibbani wadda sam bata ji
shigowar shi ba ta dukufa tana aikinta tukuru, na lailaya da kalailaitar fatar jikin ‘yarta, sallamar
ma a ciki yayi masu, ita Zaynab din dake fuskantar kofar shigowa itace kadai taga shigowarshi,
don haka Hibbani sai ganin shi kawai tayi a gabanta kamin ya soma kokarin cire riga. Ya ce
“nima ayi mun dilkan, ai nima, ango ne!" Hibbani tayi salati ta yar da wanda ta kunso a
hannunta ta mike ta fice tana cewa “ban san baka da kunya ba Faruq sai yau".
Duk da abin ya bata dariya amma ta sha mur ta ce “haba don Allah Ya Faruq, zuwa fa zatayi ta
gayawa su Mamie…." wani kallo daya watso mata, ba shiri ta kama bakinta ta dinke. Duk da
dilkan dake jikinta da karnin danyen kwai da ba’a kai ga wankewa ba. Haka ya tarairairayo
kayarshi yana sakin wata irin ajiyar zuciya mai karfi, tare da cigaba da abinda yake ganin shine
kadai kwanciyar hankalinsa, cikin ranshi yana yiwa Allah mai girma, godiya mara iyaka.
​ Hibbani ta fito tana ta fada, ta ce "kun san Allah ku ba yarannan matan su hakannan,
bikin nan na menene? Tun ana abu cikin marmari ana dariya har ya gundire su. Duk hakuri da
kawaici irin na Faruq yau kun kureshi yayi muku keke da keke. To wallahi in baso kuke a maida
su mata cikin dakunan ku ba, akan idanun ku, to yau dinnan ku lullube matansu ku kai masu". ​ Hajiya Azumi ta iso bakin kofar tana kwankwasawa da yatsunta, amma bata shigo ba,
tace “Faruq” ya ce "shigo mana Mama, dilkan da Hibbani ta ki karasa mata nake karasa mata"
ta ce “to hakan yayi kyau, amma fito in shiryota in kawo maka ita gabadayanta yanzunnan”.
Daga shi har Zaynab suka sa dariya yace da ita cikin rada "kin ga ai na yi mana maganinsu" ya
dago murya yace “Allah Mama ki shigo, ko kwarzane ban yiwa 'yar ki ba, hira kawai muke yi” ta
ce "wai ina wasa da kai ne? Nace ka fito ko?” Ya fito yana murmushi, ta daddage ta zuba mishi
rankwashi a tsakar ka ta ce "bace min da gani, mara kunyar banza" sai da ya kai bakin kofa ya
juyo yayi mata gwalo. Tuni Nuratu ta bace a sama.

***​​ ***​​ ***

Acikin gidan-gonar Zaynab da ke garin Gwarzo, walima ce ta musamman Zaynab ta hada musu
su takwas kacal. Tana sanye da fararen ‘wedding gown’ dogaye har suna jan kasa, tayi lullubi
da farin ‘net’ amarya dai sosai sai walkiya take ta inda duk ta juya, ta matsa jikin bishiyar ‘guava’
ta aje ‘yar karamar (automatic video camera). Bata kai ga dagowa ba Faruq ya karaso ya
kwantar da kanshi a bayanta, yace I luv u Zaynab".
​ Qassim ya sakar masu flash din Camera a hakan. Imran dake zaune can gefe kan wani
dutse, Haiti na zaune daga gefen kafafunshi, tana yi mishi jan yatsu a hankali, suka juya suna
hango abinda ake yi, wato irin soyayyar da ake zubawa tsakanin Zaynab da Faruq dinta, ya
lumshe ido yana murmushi yace "kin ga inda ake soyayya can, ba irin tamu ba" ta harareshi,
cikin wata siga mai jan hankali tace “au daga gareni ne ma?”
Ya dirgo daga kan dutsen ya kwantar da kai a kafafunta, ya rintse ido yace “na yarda daga
gareni ne, amman nima daga yau na daina Haiti I luv u, I luv u more than I can say. Don Allah
mu rike amanar juna.
Ba soyayyah ce ta hadamu ba, iyaye ne, daga baya kauna ta hadamu, in sha Allah bazamu
taba ganin ba dai-dai ba a rayuwar auren mu".

“Ya Im! Ya Im!!”

Zaynab ce ke kira daga nesa, cikin siririyar muryarta "ka taho gashi na yi ‘serving’ dinka” ya ce
“to Zaynab dina”. Ya kama hannun Haiti suka nufi inda suke.
Makekiyar ledar cin abinci ce aka shinfida, aka shaketa da ‘warmers’, sunkin ‘foil-papers’ da
tangarayen abinci. Manyan ‘picinic-coolers’ suma shake suke da nau'i-nau’in kayan abin sha
masu dan karen sanyi. A gefe tirkeken rago ne guda aka gashe. Yana tsaye jikin karfe cikin
ramin da ake gasa shi sai naso yake ya gasu yayi lugub, mai so sai ya je ya yanko iya yadda
yake so ya ci.
​ Suka soma cin abincin suna nishadI, aka ci aka sha akayi hani'an. Ko kafin su gama
duhun dare ya fara shigowa, wato an kirayi sallar maghriba. Suka matsa ga (pipe) din da ake
ban ruwan shukoki suka dauro alawala. Faruq ya ja su jam'in sallar magriba, sukayi addu'a ta
musamman akansu, domin neman zaman lafiya a tsakaninsu da zuri'ar da zasu haifa a gaba.
Ko kafin su shafa Inna dubu ta aiko Halima ta kwaso mata amaren za’a kaisu gidajen
mazajensu.

Faruq da Zaynab suka ce da Halima, ta gayawa Inna Dubu su a cikin gidan gonar-nan zasu
kwana cikin (Hut), wato irin bukkar nan ta zamani, da ake yi cikin gidan-gona, tuni sun sa an
sanya masu dindimemiyar katifa, gobe zasu tafi nasu gidan da kansu.
​ Halima ta kama baki, cikin dimuwa. Ya daga mata gira yana murmushi yace "Yes, muna
son kafa tarihi ne!”.
Ta ce “to Allah ya tashe mu lafiya". Ta juya tabi bayan su Imran.
​ Har ta kusan tadda su sai ta dawo, ta kamo hannun Zaynab ta jata gefe tace “sai kin yi
hakuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login