Showing 42001 words to 43757 words out of 43757 words

Chapter 15 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf


Ya Rabi da mahaifinmu ya bayarwa malam Ali, na ce malam Ali mutumin kirki ne, ba'a rasa ci
ba ba’a rasa sha ba cikin gidansa, kuma yana sonta, ku kwantar da hankalinku. Ku barta ta yi
zaman aurenta, haka Allah ya tsara mata. In ya so sai a dinga kai mata ziyara akai-akai, abinda
har yau Allah bai basu ikon yi ba, kuma da wannan nadamar suke kwana suke tashi a halin

yanzu.
​ Sannan na gangaro ga labarina da Sa'idu, na fada musu komai ban rage ko kalma daya
ba, saboda nasan su iyayena ne da bani da kamarsu, hakannan mutane ne masu ilimi,
tawakkali da barwa Allah komi. Wannan shine ginshikin rayuwar iyalin Mainasara, wadda ke
kara bunkasa su har gobe. Mutanene da suke muhimmanta yarda da kaddara da hukuncin
Allah, mai kyau ko mara kyau a gare su. Na kare da cewa duk hukuncin da kuka yanke a gareni
dai-dai ne. Ni dai kwanciyar hankalina kadai shine kada yarinyar ta gane ba Ya Rabi ce ta
haifeta ba, amma ba don bana son ta. A da, tunanina shine in dauko ta in taho tare da ita, sai
nayi tunanin yaya zan dauko 'ya in kawo masu alhalin ban yi aure ba? Mu kuwa 'yan siyasa ne,
jinin mu da Bargonmu, masu tarin makiya, amma ba wai don ni in yi siyasa ba kamar yadda
tunaninki ya baki. Don a lokacin kwata-kwata ban taBa kawowa raina in cika burin mahaifina ba,
wato in zamo makwafinsa. Kawai ina jin su Baba Aliyu ne, da tasu siyasar. Na tabbatarwa kaina
zamanki tare da Ya Rabi, shine babban kwanciyar hankalinki, mutuncinki, nasaba da martabarki
amma ba wai nawa ba.
Wallahi-wallahi tilas ce ta sani baroki da Ya Rabi, domin abin zai yi mata yawa. Naga yadda
kaunarki ta shigeta tun sanda take yanke miki cibi, ko ido bata iya daukewa akanki. Na san in
na bar mata ke, kamar na zauna tare da ita ne, ko babu komai zaki debe mata kewar
abubuwana da yawa, domin duk wata halittata irin taki ce, hatta sumar kanki, kuma babu
maraba da ita, sai ki rantse itace ta haifeki.
Yadudu kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita. Su Baba Aliyu kuwa sun kasa magana. Sun kuma
rasa me zasuyi dani su huce. Shettima yafi kowa zuciya cikin danginmu, shine ya fara tamaula
da ni a falon, ya rika duka kamar ba zai barni ba. Ganin irin jinni da majinar da ya haDa min ne
Yadudu ta mike jikinta na kyarma ta rufu a kaina. Ta ce “ka kashemu mu biyu, mu tadda
mahaifinta. Daga nan sai in yi masa bayanin irin rikon da kuka yiwa zuri'arsa a bayan ransa.
Shida ya kari rayuwarsa gabadaya cikin hidimar ilmin ku, cikin kyautata muku. Tunda ya rasu
cikinku wa ya kara waiwayar 'ya'yan da ya tafi ya bari, alhalin kuna da tabbacin suna raye cikin
kasar Nijeriya? Sai yau da ta biyoku da kanta, ta fada maku abinda ba matse bakinta kukayi ta
fada maku ba? Da Nuratu lalatacciya ce, tana kuma son lalacewar, da bata dawo cikin ku ba.
Da ta karasa cikin duniya ta cigaba da lalatar ta. Amma dawowa ta yi ta fada maku amanar
kanta, wanda daga ita sai Allah sai 'yar uwarta suka sani, sabida tana da yaqinin ku iyayenta ne
bazaku taba yanketa ku yar ba, babu abinda zai faru ga dan adam, face ya kasance rubutacce
a lauhul mahfuz, don haka ita Nuratu haka Allah ya rubuta mata. Amma dubi kwayar idanunta,
ba tayi kama da shaidanun 'ya'ya ba.
​ Don haka Nuratu ko a yau ki koma kizo da diyarki, ni zan rike maki, kina da dukiyar da
zaki rike 'yarki, ba tare da taimakon kowa ba. Babu wanda yake sama da aikata kuskure, sai dai
wani yafi na wani, kuma idan kika roki Allah da cika sharuddan tuba, hakika zai yafe maki. Ya
yafe wanda yafi wannan. Ban taBa ganin yarinya mai tsoron Allah irinki ba. Nawa ne suka yi cikin, suka je suka zubar, ko
su haife su kashe, ko su yar a bola? Ba tare da iyayen su sun sani ba?
Amma ita tazo ta gaya muku abinda baku sani ba, don tana da tabbacin kune iyayenta, a cikin
kowanne hali, ba zaku kita ba. Yau da mahaifinta yana raye ….. Shettima zakayi mata irin
wannan dukan fitar ran daka yi mata a gabansa?” Ta kama hannuna ta tayar dani, jinni na
bulbula ta hanci ta baka mika ni har gabansu, tace "gata nan ku yankata, sai dai ku sani, in

gemun dan uwanka ya kama da wuta, to ka shafawa naka ruwa…..".
​ Kamilu yace “Yadudu ai baki bari kinji me muka ce akanta ba, shi kuwa Shettima kin san
zuciya irin tasa. Me yayi zafi? Me ya kawo wannan maganar? Allah ya huci zuciyar ki.
Nuratu tamu ce, haka ko me tayi ba zamu yada ita ba, amma dole mu ladabtar da ita, don ta
kiyayi gaba, da yiwa 'yan bayanta hannunka mai sanda, kuma ko Yaya Sani yana raye, bazai
kalubalanci hukuncin da Shettima yayi mata ba.
​ "Ke Nuratu!”
Ya kira ni da kakkausar murya. Na dago kumburarrun idanuna na dubeshi, amma ban ce komi
ba. “Da gaske ne abinda kika gaya mana?” Na daga kai ina hadiyar zuciya "to waye Uban 'yar?”
Nace almajirin mijin Ya Rabi ne, sunansa Sa'idu, a yanzu haka yana karatu a Ingila, nasan
kuma bada jimawaba zai dawo ya tadda ita. Wallahi-wallahi Baffa Aliyu, nima ban san ya akai hakan ta faru da ni ba, kawai na bude ido ne
na ganni da cikin a jikina, ko shima Sa'idu bai san da zancen cikin ba" yace “to kun shirya yin
aure ne idan ya dawo?”
Na share wasu ambaliyar hawaye daga kundukukina, nace “har abada babu zancen aure a
tsakaninmu. Ina nufin ba zan iya auren sa ba". Ya ce “zancen banza, to waye zaki aura wanda
ya fishi?” Nasa kuka sosai na ce "wane irin aure, GIRMAN JUNA YA FADI? Nidai kuyi hakuri
makaranta zan koma". Dukkan su sai suka yi shiru, aka rasa mai bakin magana.
Daga karshe suka hadu suna yi min nasihohi, kowa da irin tashi, masu ratsa zuciya, at last,
suka ce “Allah ya zaBa min abinda yafi alkairi ga ryuwata,” akayi addu'a taron ya tashi.
​ Bada jimawa ba na bawa Baffa Aliyu takarduna na sakandire ya samo min gurbi a
jami'ar Niamey, na soma nazarin kimiyyar siyasa (Polictical Science), sai dai muna yi da
harshen faransanci ne. Ina shekara ta biyun karshe Badeggi ya fito gaba-gadi da son aurena,
duk da gaskiyar labarina da Shettima ya gaya masa, yace ya ji ya gani. Ya taBa aure matarshi ta haifa mishi 'ya'ya har biyu, ta rasu a wajen haihuwar na ukun. Biyu
maza ne, duk sun girma, AbdulHakim da Abdulsamad, a yanzu haka manyan ma'aikata ne
sa'annin Qassim, macen kuma itace Niyaz, wannan 'yar budurwar da nasa ta yi miki magana
ranar da Qassim ya kawo ki. Kai tsaye na nemi alfarmar Kawunnina da suyi min uzuri in kammala karatu na, zanfi samun
nutsuwa. Duk da matsananciyar kaunar dake tsakaninmu, maza tsoro suke bani. Na kudurce a
raina na daina baiwa soyayya muhimmanci akan ingancin rayuwar diya mace.
Na fito da (First Class Degreee) a shekara ta (1990). Na kuma yi (winning scholarship abroad)
daga jami'armu zuwa babbar jami’ar Paris. Daga Baffa Ali, Adam, Shettima Kamilu da Kabiru,
babu wanda yayi yunkurin hanani tafiya karatun digiri na biyu na tsayin shekaru biyu kacal, a
cewar Baffa Aliyu a kyaleni in je, tunda yanzun ni ba karamar yarinya bace zan iya kula da
kaina. ​Don haka na tafi tsawon shekara daya da rabi kacal na dawo da kwalin digirina na biyu,
muka yi aure mai suna aure, wanda yayi tambari cikin kasar Nijar ciki da bai dinta, cike da
matsanancin so da kaunar da har yau ba'a taBa samun ma'auratan da suka dade tare da juna,
ba tare da wani saBani ya gitta a tsakanin su ba, kamar ni da Badeggi, a gaba dayan Kangiwa
family.
​ A lokacin Kabir ya samu damar darewa shugaban jam'iyyar mu, wadda tafi kowacce
jam'iyya karBuwa a kasar Nijar. Haka kawai kamar da wasa rannan na soma tunanin me zai

hana in cikawa mahaifinmu burinsa, da ya tafi da shi a zuciyarsa?
Wato tsayawa gwamnatin Damagaram, domin kara fiddo ta da banbantata da sauran jihohin
mu. Na samu Baffannina muka tattauna, mijina ma ya bani goyon baya dari bisa dari. Ba jimawa
na tsaya takara, Kangiwa suka tsaya mini, talakawan garin Damagaram suka yi min alkawarin
kuri’unsu, domin Babana. Ana yin zaBe kuwa na lashe, wannan wani abun tarihi ne da ba’a taba samunshi cikin kasar
Nijar ba, wato Gwamantin diya mace. An samu sabanin ra’ayi da yawa, musamman daga
Malaman addini da abokan hamayyar zuri’ar mu, inda gari ya rincabe, domin talakawa sun
maya sun rantse idan ba ni da suka zaba ba, sai dai a kone garin kowa ya huta, sabida basu ga
me mazan suka yi masu ba banda wawashe dan arzikin su, wanda bai kai ya kawo ba, da kyar
aka samu aka sulhunta da babbar kotun kasa, wadda ta tabbatar da tsarin mulkin kasar Nijar
bai haramtawa mace yin gwamnati ba. Don haka aka rantsar da ni.
Muka tattara muka koma (Govt. House) nida mijina da 'yan uwana masu yawa. Na karBo Haiti
da Qassim, da 'ya'yan Baba Shettima uku, da dyar baba Adam wadda kwananan na aurar da
ita, da kuma Niyaz diyar Bedeggi, duk na hada na rungume suna karatu a wajena. Haihuwa
mun nemeta sama ko kasa Allah bai bayar ba. Likitoci sun tabbaar matsalar daga gareni ce,
amma Kabiru yace ko zamu dawwama a haka, ba zai auri kowa ba, na ishe shi rayuwar duniya
da lahira.
​ Ya dade yana yi min zancen mu daukoki a lokacin, ina kin amsawa. Abinda bai sani ba
shine na tada dan aike musamman da lambar wayata ya kaiwa Faruq, a lokacin ya fara karatu a
Sokoto, yana sanar dani komai kuke ciki. Akwai kakkarfan aminci tasakanina da Faruq dina,
daga baya ma na shirya masa tikiti na aika mai don yazo ya same ni, yace mun a’ah suna tare
da Imran koyaushe, bazai iya yin tafiya batare da sanin sa ba, sai na aika Qassim ya gano min
gidan Sa'idu, ba tare da yasan dalili ba, ba kuma tare da shi kansa Faruq ya sani ba.
Na yi Badda kama nazo Sokoto fiye da sau biyar, har kofar gidan Babanki…..”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login