Showing 9001 words to 12000 words out of 43757 words

Chapter 4 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf

wani ya tabbatar min da
cwa ni shegiya ce, haka sai bayan ranta na samu amsoshin tambayoyin da suka addabi
kwakwalwata, suke banbantani da sauran 'ya’ya, suka tabbatar min da cewa ni 'yar gaba da
fatiha ce.
​ Na daga kaina sama a hankali, ina karanto rayuwata ta baya, dana tabbatar na yi
sallama da ita. Yanzu ne zan shiga rayuwata ta hakika (ta marassa galihu, marassa ‘identity’).
Inna ce galihu na, Malam ne ‘identity’ dina, duka a yau na rabu dasu (ita ta tafi, shikuma zan
rabu da shi). Ba zan iya rayuwa cikin kasar ba tare da Innata ba. ​ Na sanya kafata cikin gidan, cinkoson mata ya kara tayar min da hankali, tamkar in ce
da kasar ta tsage in shige. Tsoro nake kada wata cikinsu ta kirani da 'shegiya' babu mai kare a
min a yau, tunda babu Innata cikin gidan. Ala dole na ja baya zan juya da gudu.
Yaya Halima ta ratso cikin mutane itama da gudunta ta kamo ni, ta kankame ni tana kuka haka
daga bayana naji nayi karo da mutum ashe Malam ne ya sawo kai, Ya Faruq na biye da shi, sai
kallon su nake a tsorace, don gani nake kamar korata zasu yi daga gidan su.
Sai makyarkyata nake yi kamar mazari. Malam ya shiga tofa min addu'o’i iri-iri a tsakar kaina.
Ya Faruq ya kama hannuwana duka biyu hawaye cike da idonsa, yace "Baba Malam, don Allah
Halima ta tafi da Abu gidanta bazata iya nutsuwa cikin taron matan nan ba, ina gudun kada ta
samu matsala a kwakwlwarta, ka yi hakuri don Allah tabi Halima tunda kace baka yarda in kaita
gidan Baba Sa'idu ba…." na gwalo ido da karfi jin abinda yace, na ce "nima bazani ba Malam
dukana zasu yi, kora ta zasuyi, ba zasu barni in zauna musu a gida ba. Ni da gidan Baba Sa'idu
har abada…. har shi Baban….. Babu ni, babu shi har abada……." Na fashe da kuka shima
Faruq sai ya shiga share hawaye da hankicinsa duk irin dauriyar da yake yi kuwa. Ban taBa
ganin Ya Faruq yana kuka ba, tunda nake. Don haka nayi saurin tsayar da nawa, ba don na
zuciyar ya kafe ba. Malam ya ce "bude mata dakinsu ta dauki abinda za tayi amfani da shi, ki
kula min da Zaynabu amana Halima, kafin zuwa ranar sadakar uku in daura auren ta da Umar
Faruq…”

Cikin tsananin firgici, mamaki da zargi, na daga ido na dubi Malam Ali, cike da mamakin wane
Uba ne na kwarai, zai aurawa dansa dan halak 'SHEGIYA?' Ba mamaki mutuwar matarsa ta
samar masa motsuwa a kwakwalwa, domin ni kaina shaida ce kan matsanancin son da yake
mata. Ban ce komi ba, na sunkuyar da kaina kasa, domin idanuna sun gano min abubuwa
saBani ga tunanina, sun gano min Malam ragas yake, ragagasgas kuwa, sai dai in nice ban ji
sosai ba. Amma kwayar idanunsa na tabbatar da abinda yake fadI, haka yake har zuciyarsa.
​ Na maida dubana ga Faruq, don ganin wace irin karBa ya yiwa zancen mahaifinsa?
Idanunsa akaina suke, cike da tarin abubuwa da dama, wanda a lokacin rashin kwanciyar
hankali bai barni na tsaya ga son tantance ma'anar su ba. Ya lumshe idonsa cikin nawa, ya jefa
ni da wani irin 'loving smile’ da har yasa 'ya'yan hanjina sai da suka karkada, domin babu
tantama al'amuransa a yanzun, sun juye sun rikide na IMRAN ne sak. Sai naki gasganta hakan
da gangan, domin ni ban yarda da abinda ake kira (love at first sight) ba, sai dai tausayi da
ceton rai.
​ A ganina ni ba abin tausayi bace, tunda ina da lafiya zan nemawa kaina madogra, in
daukarwa kaina da Inna ta, fansa, wanda ba zasu yiyuwa ba, in har da aure a kaina. Ko zanyi
aure ai Faruq yafi karfina; shi dan gatane, dan halal ne, mai dangi, sai dai in je duniya in nemo
shege dan uwana, wanda ba zai taBa goranta min (illegitimacy) ba. ​
Na shige dakin Inna na da zummar dauko kayana, to amma me? Duk inda na juya ita nake gani
a kowacce kusurwar dakin tana 'yan hidimdimunta da basa karewa. Na zauna a gefen gadon
karfenta, na dauki bargonta da muka kwana a cikin sa daren jiya na rungume a kirjina, hawaye
na malalo mini. Nayi kuka na yi kuka har hawayena suka kafe, sai dai kukan zuci, wanda akace
ya fi na zahiri radadi a zuci.
​ Yaya Halima ce ta shigo ta soma hada min 'yan komatsaina, cikin ka tuwar akwatina da
na zo da su daga gidan Baba Sa'idu, ta daurawa Zilkiflu ya tafi da shi gidanta, ta kamo hannuna
muka fito daga dakin tasa kuba ta rufe. Idanun matan nan dai har yanzu suna kaina, suna ta
kus-kus din dake kara daga min hankali. Daga can dakin Inna Dubu Hafsisi ta fito, ta dubeni shekeke, daga ni har Yaya Halima dakatawa
muka yi muna kallonta, domin daga ganin irin tsayuwar da tayi, hannu a kugu, ta kuma tare min
hanyar wucewa. Kasan bata arziki bace. Cikin daga murya yadda duk wanda ke gidan zai ji, ta
ce "to Abu, burin ki ya cika, naji ana zaki auri Faruq ba ni ba. Dadin abun dai ni ba ‘shegiya’
bace 'yar sunna ce. Igiyoyi uku kwarara na aure suka samar dani kuma kowa ya shaida. Kenan
ba sai an rufa asiri za'a aureni ba. Ashe dama duk wannan kumbiya-kumbiyar da mahaukaciyar
ki Innarki ke yi dake, don kar mu san ke SHEGIYA CE? To ai gara ma da ta mutun, da bazamu
sani ba, sai a cigaba da dinke mu a bai-bai. Don haka ba Faruq ba, in ma ALHAJI SA'IDU,
dadironki zaki aura, ki je na bar miki, nafi karfin in hada kishi da shege wall….”. Ganin Hafsisi
mu kai tayi sama ta kuma fado tik, a kasa. Ya Faruq dake shigowa yayi kwallon ‘tennis’ da ita da
kafarsa ta dama, sai jini ta hanci ta baka. Ta kwala ihu iya karfinta shi kuwa ya sake bin ta yana
tumurmusa da kafa a tsakar gidan, duk cikin matan an rasa mai kataBus din kwatar ta sabida
irin mugun dukan fitar hankalin da yake mata da kafafaunsa, sai mahaifiyarta Goggo Lantana
data dora hannu aka ta kwarara ihu, tace "Dubu kawo dauki, zai kashe min 'yar akan 'yar gaba
da fatiha……
Karya ake ba shegiyar bace? Ka dauka yau aka haifemu a garinnan bamu san 'yar Nuratu ba

ce karuwar Sa'idu.....?"
​ Idanun Yaya Faruq suka rufe ruf, baya ko ganin gabansa, ya fizgo Inna Lanto ya maka
da bango, ta kuma kurma ihu data fadi tim, akan kwankwasonta. Ya dunkule hannu ya nausa
mata a bakin sai ga hakora biyu, wanda dama lallabasu ake sun biyo jini da yawu sun zubo
akan cinyarta. Malam ne da Inna Dubu suka shigo da gudu daga can dakin soro inda suke karBar gaisuwar
Hakimin Gwarzo da tawagarsa, suka kwaci Hafisisi da Innarta da kyar, bayan ya hada musu jini
da majina, ya fita yana huci ya dauki motar sa a guje ya bar garin kwata-kwata.
Rungume Yaya Halima na yi, ina ta kukan fitar hankali ko uffan ban ce ba, haka muka baro
gidan zuwa gidanta. A ranar ne labarin da jama'ar garin Gwarzo suka dade suna kokontonsa,
ya bayyana gare su. Abinka da dan karamin gari, cikin daren labari ya bazu a ciki da wajen
kauyen Gwarzo, cewa ashe Abu diyar Malam Ali, ba 'yar sa ba ce, SHEGIYA CE. ​ A daren daga ni har Halima bamu rintsa ba, ita cin kuka take saboda tausayin raywata ni
ko a lokacin idanuna sun bushe, zuciyata ta kekashe. Kalamin Hafsisi sun kyafar da hawayena.
Babu shakka abinda ta fadi haka yake babu kuskure a ciki, domin ta fini kusanci da Faruq, ta
fini sanin ciwonsa ta fini sanin muhimmancinsa, don Innarta kanwar Inna Dubu ce uwa daya
uba daya, dole ta taya dan uwanta jimamin kakaba mishi 'yar zina da za'a yi, ko ni na jajanta
masa, haka duk wani mai kaunar sa dole ya jajanta masa. Maganar ta daya ce ta taBa zuciyata
kuma ta sani fidda hawaye, (dadironki Alhaji Sa'idu), me wannan kalmar ke nufi?
​ Tana nufin…. zaman da kikayi kina karatu gidan Baba Sa'idu, zama ne na karuwanci, na
zina, irin wanda mahaifiyarki, NURATU, ta yi tare da shi har suka sameki…….. Ban san sanda
ba na ce "Ya Allah, ka dauki raina in huta da wannan rayuwar, Ya Allah kada ka barni in kara
kwana cikin duniyar nan, Ya Allah ka bi mun hakkina akan Nuratu da Baba Sa'idu…" Yaya
Halima tasa dankwalinta ta toshe min baki, cikin kuka ta ce “Abu kada bakin ciki ya fidda ke a
addininki, kada Bacin rai da maganar mutane ya raunana imaninki, kada bacin zuciya ya kaiki
ga aikata dana sani. Naji dadin yanda kika karBi al'amarinki da farko, amma kina nemn lalata
ladan da kika samu na yarda da kaddara da fawwalawa Ubangiji komai da kika yi. Wannan ba
zai hanaki shiga Aljanna ba, idan har kin kyautata ayyukanki sai ki wuce cikin aljannar mu
'ya'yan halal din bamu wuce ba.
Rayuwar duniya duka guda nawa take? Kada ki manta, bafa zama muka zo yi a cikinta ba, to
na meye zamu damu kanmu da kaluben dake cikinta?
Ki yi saurin yin Istigfari ga kalamunki, tun mala'iku basu rubuta ba………."
​ Na share hawayen da suka yanko mini, na daga kai sama nayi duba ga al'arshin
Subhana, wadda ya kawata da wata da taurari, ya maye duhun dare da hasken su. Na saukar
da idanuna akan yatsaun kafata nace
​ "Mutane suka koma bani tsoro Yaya Halima”.
Itama ta share hawayenta ta ce “Ba kiyi tuban da nace kiyi ba har yanzu Zaynabu-Abu".
Na daga kai sama a hankali, tsigar jikina na tashi, kana na sunkuyar. A hankali nace
“Astagfirullah!”
Ta kamo ni ta rungume a kirjinta, hawayena na sauka a gadon bayanta, nace "ni yanzu ina zan
dosa ne Yaya Halima? Ba Uwa ba Uba balle dangi. Ga tabon da duk inda na shiga baza’a goge
min shi ba, bayan ba ni na dorawa kaina ba. Ko zan rika kwana a titi, ba zan doshi hanyar
gidan Baba Sa'idu ba, ba kuma zan kara kwana gidan Baba Malam ba, sai dai gaisuwar neman

albarka daga gareshi da Inna Dubu, haka ko zan mutu ba aure, ba zan auri Ya Faruq ba.
Idan nayi hakan na tauye shi, domin shi cikakken mutum ne mai cikakken hali da cikakken usuli,
bai cancanci auren mai gurBataccen usuli kamana ba…" ta katseni cikin daga murya “ki daina
fadar haka Abu, Faruq na sonki a tun ranar da aka haife ki, shekaru dai-dai yau kusan goma
sha takwas….” A razane na dago ido na dubeta, tunanin maganganun Inna na ya zo mani. Wannan na nufin
Faruq shine mutum na hudu, cikin masu tabon bakin-cikin BABA SA’IDU, shine ma’abocin
soyayyar shekaru goma sha takwas, amma bazai bayyana ba sabida Baba Sa’idu?”
Ta lura da yadda maganarta ta taba zuciyata, ta daga min kai (in affirmation), “kwarai ni na sani,
Innarki Allah ya jikan rai ta sani, haka Malam da Inna Dubu. Sai dai ya rantse zai iya hakuri har
illah masha Allahu, don ba zai taBa ba bari ki gane ba Baba Malam ne ya haife ki ba.
Wannan zai dagula rayuwar ki ne, ya jefa ki a wani hali na tsanar duniya da abinda ke cikinta,
hadi da ke kanki. Ga kalamunsa a yau sun tabbata. Haba Abu! Sai kace ba musulma ba? Me
hakan zai kara ga rayuwar ki me hakan zai rage? Wannan ba shine karshen rayuwar ki ba, idan
har kin kyautata zuciyar ki. Ya dawo a dai-dai lokacin da kika suma, da girgizar mutuwar Innarki, da abinda kika tsinkaya su
Malam suna fadi, shine ya daukeki ya kaiki asibiti. Ki bar cewa ina zaki Abu, in har kin yarda da
ni, kin yarda ni din mai kaunar ki ce, ki zauna tare da ni. Ki bar cewa bazaki ki auri Faruq ba,
domin kaunar da yake maki da wadda Baba malam ke maki bata shafi abinda ke kike tunani ba.
Wallahi-wallahi Abu saboda ke ne Faruq ya tafi Singapore, saboda lura da yayi cewa kin fada a
kaunar dan uwanki, shima Imran din yana son ki, yace shiyasa ya tafi, don a cewarsa ba zai iya
jure ganin wannan abin takaicin ba, ya san dai ko yaya ne su Baba Malam ba zasu taBa bari ku
auri juna ba”.
​ Na ja gefe na hade kaina cikin gwiwoyina, cikin kuka na ce "kema kinyi mun laifi Yaya
Halima. Don me yasa tun a sanda muka zo miki nan ni da Imran, a matsayin muna son juna,
baki gaya min ba? Wannan kaunata kike yi ko neman jefani a halaka? Daga ke har Faruq baku
da abinda zaku gaya min a yanzu, har da ku aka hada baki aka lalata rayuwata ni da dan
uwana. Ko kin san Imran ya tafi inda ba’a san inda yake ba, ba’a kuma san a halin da yake ciki
ba? Na hada ku duka na tattara cikin littafin su Baba Sa'idu, har daku aka nakasta rayuwar
mu…" Na mike ina kuka sosai kamar raina zai fita, na yi cikin daki, ta kamo gefen zani na, na
fizge "Abu kada ki ce min haka, ta yaya kike tunanin zance dake Imran dan uwanki ne, abinda
duk duniya babu wanda ya taba tarar ki ya gaya miki? Kina son Innarki tayi karata ne, ko nima
ta tsaneni? Wace irin dauka kike tunanin Malam da Faruq zasu yi mini idan zancen ya fito daga
bakina, munafuka ko maciya amana……?”. Na toshe kunnuwanada ‘yan yatsuna nayi ciki ina
cewa "Ba wani malam da Faruq, amma ai kya dan nuna bakya ‘supporting’ al'amarin, amma har
wani cewa kike zaki saya mani Banbar aurena da dan uwana…?” Wani abu yazo ya tokare a
makoshina “kai Yaya Halima kema kin cuceni…" na cigaba da kuka. A lokacin ne Halima ta
harzuka, ta ce “shikenan Abu, kome kike tunani kije ki yi, nagane da gangan kike kin fahimtana.
Tunda kuma kince bana sonki, to na gode, amma kar ki sake cewa ba zaki auri Faruq ba, in
kinyi haka kinyi butulci kuma ko Allah ba zai barki ba".
Ta haura tabarmarta ta shiga daki ta hau gado ta kwanta, ban sake kulata ba jakar hannuna na
dauko na dauki (jotter) nayi wa Faruq 'yar gajeriyar wasika, na kirga kudina dake cikin jakar
dana dawo da su daga gidan Baba Sa'idu, kudi ne masu yawa ire-iren kudin da shi Baban yake

bamu ne da wanda bakki masu zuwa da abokan su Ya Em ke bamu lokaci zuwa lokaci. Na
dauki 'yan kananan abubuwan amfanina da bazasu fi karfin jakar ba na zuba, na zuge. Na jawo
akwatina ina binciken sarkar da Mama (Hajiya Azumi) ta bani randa zan taho daga Sokoto,
wato sarka da dan kunne gami da zobe da abin hannu guda daya (English Gold) da kyar na
ganta, a kasan 'DIARY dina. Jikina na rawa na dauko shi domin na fidda rai da tsammanin inda
yake, rabona da ganinsa tun ranar da mukayi maganganun dana rubuta da Inna na.
A yau dana bude shafukansa, tun daga farko har karshe na irin al'amuran da nake rubutawa,
sai naga na samu cikakken ma'ana na abubuwan da suka shige min duhu, na samu amsoshin
tambayoyinda suka dade suna addabar kwakwalwata.
Wato dai ya tabbata gareni, Inna ta tsani Baba Sa'idu ne ta kuma kasa yafe masa a dalilin ita ta
dauki amanar rayuwarsa, tamkar danta na cikinta, inda shi kuma ya sakamata da yiwa kanwarta
ciki na bata hanyar aure ba.
Ta ce “zata yafe masa ne kadai ranar dana yafe masa" wato ranar dana gane ni 'yar shi ce, da
ya samar dani ta hanyar zina. Na kuma yafe masa.
​ Ta kasa komawa cikin danginta ne domin batasan me zata ce dasu ba a game da
Nuratu, da bata san in da take ba. Amma a duk ranar da ta ganta, to a ranar ne zata dawo
garesu.
"GIRMAN su Hajiya Sa'a yana hannunta." Wanda ke nufin, a duk ranar data fadawa duniya
Sa'idun nada shegiyar diya, GIRMAN SU ZAI FADI!
"Ita Hajiya Sa'ar ce kece dani SADAKA YALLAH? Bata fadin babban? Wato (Bata fadin ni
shegiya ce?)”
Wannan na nufin Hajiya Sa'a, tasan tsakanin Abba Baba Sa'idu da mahaifiyata, Nuratu, ta kuma
san rayuwar su ta baya. To amma abinda ban sani ba shine shin Hajiyar ta san cewa sun
haifeni? Kai babu kama, sai dai ya zamanto cewa ta san soyayyar tasu, amma bata sanda suka
kai ga yin cikina, har suka haife ni ba. Tabbas da bata dinga aibatani akan su Hassan ba. Da
bata dinga yin fariyar "su da gidan Uban su ba". In haka ne akwai sauran kallo a gaba. Domin
kuwa ko ba-dade, ko ba-jima, sai na je na tsaya a gaban Hajiya Sa'a, na gaya mata ko ni WACE
CE? In tabbatar mata da cewa BARAROJI kuma SADAKA YALLAH 'yace ga V.C Professor
Sa'idu Bindawa.
​ Na kai hannu na shafe hawayena. Idanuna ya kai ga shafin karshe, wanda ya warware
min rudanin da zuciyata ke ciki, na kokonto da tunanin ina zan dosa? Wa nake da shi a halin
yanzu da ya wuce Baba Sa'idu?
​ Wani farin ciki ya ziyarci zuciyata, ban san sanda fatar bakina ta suBule da murmushi
ba, naji kamar an dauke min wani nauyayyan dutse ne aka. To amma ina da tabbacin in sun
san ta hanyar da 'yar tasu ta haifeni, zasu yarda su karBeni a matsayin JININ SU har su bari in
zauna a cikin su? Inada tabbacin in sun san cewa ita kanta 'yar tasu, gudu tayi ta barni, tun
ranar data haifeni don tsira da mutuncinta, zasu yarda su karBeni?
Wata zuciyar tace " na Allah basa karewa Zaynab, a ko'ina ba'a rasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login