Showing 30001 words to 33000 words out of 43757 words
Chapter 11 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf
ba.
A karshen shekarar ya zo hutu, a ranar na samu kaina da yin kwalliya, da ake kira kwalliya, irin
wadda ban taBa yi ba. Na yiwa gashina gyara mai suna gyara, irin wanda bai taji ba. Na yiwa
kumbana fenti da lalle jawur, kamar wata sabuwar amarya. Yaya Rahi sakin baki tayi galala!
Tana kallona kamar a ranar ta fara ganina, ta ce "Nurtu haka kike da kyau kamar aljana? Shin
ina zaki ne? Wannan kwalliyar bata dace ki yiwa kowa ba sai mijinki". Domin su kansu kayan
jikina masu fidda sura ne, idan a Gwarzo ne ba za'a barni in yi dinkin ba, to Maryam kawata ta
kawomin su daga Lagos a dinke, riga da siket ne ‘fitted’, na wani bakin yadi mai santsi da adon
jajayen fulawoyi.
Ita bata san don Sa'idu na yi wannan kwalliyar ba, don ko a mafarkinta bata kawo wai soyayya
muke a waya ba, abinda ta dauka shine hira ce irin ta wa da kanwa, domin bana fadin abinda
har zata digama ayar tambaya, shine dai yake ta aman soyayyarshi kamar wani Romeo, ni
kuma ina kasancewa cikin nishadi. Na tabbatarwa kaina idan na yi sa'ar auren Sa'idu, na yi babbar sa'a, domin namiji ne mai
masiffaffar soyayya da zai iya mai da kansa sakarai akan macen da yake so. Na kan kissimawa
raina kamanninsa? Ko yaya yake? Dogo, gajere, baki, ko fari? Mai kiba ko siriri? Oho, koma
wada ne, nidai ina son kayana haka, zan kuma cigaba da son shi muddin rayuwata. Sai kawai gashi tsaye tokare da kofar dakinmu, hannun sa daya a jikin kyaure, daya
harde a bayansa. Baki ingarman gaske da a turance ake kira 'giant, yafi fadi daga kafadu
sannan kafafunsa tsayayyu ne. Baki ne sosai da (weather) din kasar England ya maida ‘cool'
kuma bakin shi bai Boye fararen idanunsa ba. A kiyasce yayi shekaru talatin da takwas, a yayin da ni kuma keda sha bakwai. Kenan tsiran mu
ba kadan bane. Gashinan dai fes, kamar wankan inji, ban taBa ganin cikakken namiji mai haibar
Sa'idu ba har yau. Dole duk wata lafiyayyar mace, tayiwa kanta sha'awar mallakarsa,
ba-katsinen usuli, mai tsaka tsakin kyawun sura. Ni da shi tsayawa muka yi cirko-cirko, kamar zakaru muna kallon-kallo. Ba sai an gaya
mani ba jikina ya bani he is the Sa'id I'm dreaming of. Ya saki kofar yana murmushi yace “idonki
kenan Nuratu?”
Na kai yatsuna da suka sha adon lalle, na rufe fuskata ina dariya, cikin wani irin nishadi da
soyayya mai tsanani, ya karasa shigowa cikin dakin yayi ido hudu da Yaya Rabi, dake kwance
tana sauraron rediyo bata lura da tsayin mintunan daya Bata a tsaye cikin kallon soyayya ba, ta
yunkura ta mike ta ce “oyoyo Sa'idu na! Da akwai katon zani da zai goya min katon mutum
kamar ka, yau da na goya ka."
Ya shiga sosa keya cikin alamun sarakuta, yau kunya sosai yake nunawa ba kamar da ba, ita
bata ma san yana yi ba, ta cigaba da oyoyonta. Inda duk ta mika hannu, sai ta zaro mai abin
sawa a baka tana cewa "wannnan ma kai na ajiyewa, kaga gyadar nan yau satin ta guda da
soya maka, na san ka da son gyada".
Tana bada baya domin kawo mashi abinci, ya yi tsalle ya dawo gabana, a yayin da ni nake still
a tsaye tamkar an kafeni da kusa, yace "this is not the kind of welcome I expect from you…"
Na ja da baya ina dariya, na ce “wacce iri ka tsammana? Duk wannan adon da nayi domin ka?”
Ya kuwa bini da ido ‘up to down' ya sauke su a yatsun dana rufe fuska da su, yace "eh, an yi
mun kwalliya kam, to amma ai ba'a barni na gani sosai ba an kama an rufe fuskar" ya kai hanu
ya sauke hannun daga fuskata, wani irin ‘shock’ daya sameni ya tunasar dani tunda na kawo
haka, wani babban namiji bai taBa kama jikina ba. Ya sunkuyo da kuncinsa dai-dai bakina yace
"c’mmon! Give me a welcome kiss…." numfashinsa da lallusar kamshin dake tashi jikinsa na
dukan hanci na, ya tayar da tsigogin jikina gabadaya, nayi ta maza naja baya da karfi na bugu
da bango ina fidda numfashi a wahale. A sannan ne Ya Rabi ta dawo dauke da tray data shako
da kayan abinci nau'I-nau'I, yayi hamzarin amsarta yana ta jera mata sannu, nan ya nade
hannun riga yana kwasar gara yana zuba santi, tare da gaya mata yadda yayi kewar abincinta.
Duk yadda ya so mu keBe a ranar bai samu hakan ba, domin babu hanya. Ya Rabi tana dakin
bata je ko'ina ba, to a wanne dalili?
Haka ya wuni kame-kame, Nuratu in ga littafinki na makaranta? Nuratu naji Halima ta
tsayar da Malam Harisu, ke kuma wa kike tsayar? Duk rabi Yaya Rabi ke bashi amsa, ni dai
iyakata murmushi da daga kai, eh, a'ah.
Tasa wani almajirin Malam ya share mashi daki, na shigar masa da jakunkunansa, da
daddare kenan. Ina shirin fitowa ya tare min hanya "wai ni har yanzu ban ji inda kika sa gaba
ba" na ce "nasa gaba kamar yaya?” Ya fizgoni jikinsa yace "that’s the kind of welcome I like".
Ganin muna neman shiga wani limit, daya wuce tunanina, na kuma san ba dai-dai bane duk da
wata irin duniyar dana tsinci kaina, na kwaci kaina da kyar na ce "a’uzubillah da kai Sa'idu.
Kana mantawa nan ba Ingila bane, mu musulmi ne diyan musulmi, idan ka manta in tunasar da
kai. Ban zanci a duk inda ka samu kanka, duk runtsi zaka yada tarbiyyar Malam ba. I really felt
disappointed…" hawaye suka zubo min, na juya na fito na barshi kamar mara lafiya ko magana
baya iya yi.
Dana dawo daki na kwanta ina tunani, sai na rinka tambayar kaina anya Sa'idu yana kaunata?
He didn’t seem a real lover, but an expert deciever, watau kwararren mayaudari ne kawai. Ban
san mecece soyayya ta hakika ba, amma na sha jin kawayena na cewa, duk namijin dake taBa
yariya a waje, ba aurenta zai yi ba, kuma ko ya auretan ba zatayi wata daraja a wurinsa sa ba.
Na yi kuka na yi kuka amma na kasa yakice Sa'idu a raina, duk yadda na so yin hakan kuwa.
Da safe suna gaisawa da Rabi ni ina shan koko, ko kallo bai isheni ba. Babu ko kunya
ya badawa idonsa toka wai "Ya Rabi, me na yiwa yarinyar nan ne take ta hararata?” Ta dubeni
na sadda kai ina mamakinsa, da tsinewa bature daya murje wa dan bahaushe kunya. Ta ce
"haushi take ji kaki kunce jaka har yanzu ka miko mata tsarabarta”, haushin Ya Rabi ya kamani
amma ban tofa masu ba, yayi murmushin daya kara masa kyau yace “ayya Nuratu - hasken
al'umma, me kike ci na baka na tsiyaya? Ai ke tsarabarki ‘exraordinary’ ce, ba sai an bude jaka
ba, jakarki daban ce, sukutum za’a miko miki ki bude abinki da kanki".
Sa'idu yana da wata tafkekiyar gona, tana can a bayan gidan mu. Yana kiwon fararen
dabbobi da shuke-shuken kayan marmari. Duk zuwan da yayi a can yake karar da yawancin
lokutansa, haka duk dan abinda ya tara a gyaranta da kara ingantata yake tafiya. To balle
yanzun da yaje ya karo ilimi kiwo irin na turawa ai san abin ya kara haBaka.
Kullum zai fita tun safe yana can tare da ma'aikatan suna ta gyara gidan gonar, don haka in ya
fita sai yamma lis zai dawo gidan. Don haka Rabi ta dauki nauyin aika masa abincin ranarsa
can gidan gonar, kuma wani kuskure da tayi, a wuyana. Ta haka Sa'idu ya samu ya lallasheni
da dadadan kalamai na yaudara, tareda yin amfani da masifaffen son da nake mishi ya wanke
kansa daga wancan zargin da nayi masa a baya.
Ya ce shi bai yi da wata manufa ba, is just to show me how much he is eager to see me. An ce
so hana ganin laifi, tuni na yafe masa muka shimfida soyayyah mai korran ganyayyaki. Haka
dana yi la'akari daga kasar da yake rayuwa sai nayi masa uzuri, nasan kuma soyayya ta kansa
komai, kuma shi yana kokari ma sosai musaman ta fannin Ibada ina jinjina masa, dole kowanne
Dan adam yana da ajizanci, kuma daga ranar koda wasa bai sake kwatawaba.
Mukan wuni sur cikin gonar cikin fararen dabbobin nan, shi yana watsawa tantabaru
gero, ni ina tusawa dokin sa abinci a baki, haka muke ta hidima da dabbobi da tsintsayen har
sai rana tayi anyi sannan mu koma gida, da yake nima ina cikin hutu ne.
Ya gaya min watanni uku zai yi ya koma amma kafinnan saida wata kwakkwarar magana a
tsakanin mu, sai yaje yayi mun shirye-shiryen da suka dace kafin in zana jarrabawar WAEC ya
dawo a daura mana aure ya tafi dani. Hakan kuwa aka yi, ya sanar da Malam Ali maganar mu,
amma nauyi da jin kunya ya hanashi sanar da Ya Rabi wadda a lokacin ta soma zargin soyayya
a tsakanin mu, ko yaro kankani ya dubi kwayar idanun Nuratu da Sa'idu, zaiyi shaidar zuzzurfar
soyayya.
Tunda Sa'idu ya tafi, sai na koma wata irin sukuku, gani nan mai lafiya, ba mai lafiya ba.
Na koma yin komai ‘slowly’ na zamo ‘calm’, kamar mai ciwon sikila. Hoton Sa'idu cikin ‘snow’ da
na sace cikin dakinsa ba tare da sanin sa ba, shine na mayar abokin barci na, kullum yana
karkashin pillow, motsi kadan in jawo in kalli abina. Haka a daddafe na zana WAEC na kammala sakandire, sai zaman jiran dawowar abin
kauna. A kullum ranar Allah sai mu share awa gauda muna hira a waya, ko tausayin aljihun sa
baya yi shida yake dalibi, saidai ni inji tausayinsa in katse layin yadda ko ya kira ba zai shigo ba.
Watanni suka shude suka zama shekara, na soma kidaya ranar zuwan Sa'idu, domin yace
wannan karon bagatatan zai yi min ko ya kamani da saurayi na muna zance. Don haka ne
tunda aka shiga watan 'December' na kasa tsaye na kasa zaune, a kullum sai na share dakin
Sa’idu sau uku, lalle kuwa da yake yana son ganina da shi, kullum cikin tisawa nake. A kuma ranar wata laraba ne malam ya yiwa Yaya Rabi maganata da Sa'idu da yace da shi
yana dawowa sai a daura auren, domin hatta gidan da zan zauna ya kama mani a can London,
da visa ya samar min.
Da daddare inata faman tisa lalle a kumbata, Rabi na zaune a gefena tana kame min
kalbar data yi min da robar kyauro don kada ta warware, ta dubi lallena tayi dariya ta ce "su
Nuratu manyan duniya, duk wannan lallen na tarbar zuwan maigidan ne?”
Na cusa kaina a cikin rigarta, saboda matsananciyar kunyarta da naji, tace "a’ah ni cikani, kada
ki karya ni banga auren naki ba. Amma Nuratu duk kwalisar nan taki, da yangar da kikewa
samari, ki rasa inda zaki kare sai a mai mata?”
Na wani irin zaro kaina daga jikinta cikin ‘slow motion’ nace "MATA? Wane ne mai
matar?”
Ta yi tsaki tace "kina nufin baki san Sa'idu yana auren Sa'a 'yar kanwar Dubu ba? Tana can
Ingilan da yaronsu Imran kamar Faruq, a cikin gidannan aka yanka ragon sunan sa………"
Na dora dukkan hannuwana aka na kwarara ihu, nace "Wayyo Allah! Wayyo Babana….."
A take na fadi a wurin na suma. Wuni nayi bana cikin hayyacina, koda na farfado surutai kawai
nake barkatai ina cewa "Sa'idu ka cuce ni…. ka yaudareni sai Allah ya saka mani……"
Sai bude ido nayi na ganshi tsaye a kaina, rike da hannayena da suka yi sanyi kalau. Yana
murmushi kamar a mafarki naji shi yana cewa "ban cuceki ba Nuratu, ban yaudareki ba. Yaya
za'ayi in yaudari abinda nafi so fiye da rayuwata? Shine me, don inada mata, sai aka ce Allah
ya haramta mani yin aure uku a gaba?” [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na fiddo ido cikin kaduwa, ta yi murmushi ta girigiza kai
cikin tabbatarwa,
“Zaki iya tuna ranar da kika hawo Acaba daga makaranta? Motar da nake ciki tana biye dake,
har kofar gidan. Imran da abokinsa suna tsaye jikin mota, da alama daga ke har shi ranku a
Bace yake, don duk kuna ta hararar juna, kika shige cikin gida baki kula su ba. Sannan naje
makarantar ku watarana inada daga cikin mota mai duhun gilassai, ina ganin ki da wata
malama, Kabila, a zaune bisa benci a bayan ajin ku, kun dade kuna magana da bansan me
kuke cewa ba kina ta kuka. Sai na ji hankalina ya tashi, don abinda na kawoma raina kawai
Sa'a ce take takura miki.
Na yi wa Faruq magana yace kwata-kwata ba haka bane, shima ya lura a kwanakin kina cikin
damuwa, watakila sabida tafiyarshi Singapore ne. (Ni na samo mishi makarantar ba tare da
sanin ku ba, ba don komi ba sai don jin Sa’idu ya samarwa dan shi aiki mai tsoka shi bai samu
ba, to ashe gajen hakuri nayi, don ba’a fi sati uku a tsakani ba ya sanar dani shima nashi aikin
ya fito a Bankin Nijeriya (central bank) a lokacin komi na tafiyar ya rigaya ya kammala, sai ya
zabi tafiya karo karatun akan aikin) yace amma Hajiya Sa'a babu ruwanta da ke, sannan ne
hankalina ya kwanta.
Faruq kafin ya tafi Singapore ne ya zo Damagaram ta jirgi, na yi masa kyakkyawar tarba
a gidana (Govt. House Damagaran), ya kawo min wadannan zobban naki na (Sepphire) da kika
bashi ajiya, tsayin shekaru goma, yace “halin rai, komi na iya faruwa”, sai na ce “balle ma
insha-Allahu zaka je ka dawo lafiya, sannan komai na Zaynab ai naka ne”. Na dade ina bashi
takardun kadarorina da shares gami da takardun wani gida dana dade da saye a Paris, duk da
sunanki. To duk ranar sai ya tattaro ya dawo min dasu, jikinsa a masifar sanyaye yake. Na ce
"Faruq zaka tayar min da hankali. In hakane ka fasa tafiyar mana, ka kama aikinka?”
Yace “nima dole ce zata sani tafiyarnan Yaya Nuratu, akwai dalilina na zaben karatun akan
aikin. Al'amarin yana neman kwaBewa; ZAYNAB IS DEEPLY IN LOVE WITH IMRAN, and I
cannot tolerate it". Nace saboda me?”
Ya sunkuyar da kai cikin matsananciyar kunya da fidda rai, yace "don nima ina sonta".
Nayi murmushi na ce “kawai kace Zaynabu ta kusan nemana da kafafunta, ta kusan
biyoni mu zauna tare. Shine me don tana son Imran, ba dan uwanta ba ne?”
Ya zazzaro ido yace “baki gane irin soyayyar da nake nufi ba, soyayyah, ta soyewa fa Zaynab
kewa, Imran?”
Na tuntsire da dariyar data kara kular da shi, nace “so what, wanene mahaukaci tsakanin Sa'idu
da Malam? Ka kwantar da hankalinka, inshaAllahu Zaynab bata da miji sai Umar Faruq".
Sai yayi murmushi. Na kuma cewa “ka yarda dani, am her mother, kwanannan zata biyo ni cikin
tsana da kiyayya, and am ready to welcome her (a shirye nake da in karBeta) da duk wacce ta
zo". Ya ce “ni nasan Zaynab bazata yi miki da dadi ba. Kuma tafi son Babanta a kanki, idan ta
gane shine Babanta, bazata gujeshi ba, amma ke baki da uzurin da zata karBa, she is quite
strict (me ra'ayin rikau ce) ba zata taBa karBarki a matsayin Uwa agareta ba…..”
Na lumshe ido cikin jin zafin kalaman shi, na budesu a kanshi na ce "sai dai idan BANI NA
HAIFE TA BA". Da wannan Faruq ya tafi".
Ta yi shiru tana murmushi, nima murmushin nake kamar gonar auduga, cike nake da kunyarta
kuma. Ta dago haBata tace "to Zaynabu 'yar Babanta, kin ji kowace ce Nuratun da kike zagi….
da gaske ne ba zaki taBa karBata a matsayin UWA a gareki ba….????”
Nayi azama, na rungumeta, ita ma ta rungumeni, sai hawaye sharr! sharr!! Daga idanun
kowannen mu. Na ce “ki bar fadin ina zaginki, waye zai zagi mahaifiyarsa? Sai mai nemawa
kansa masifa. Na koyi wani abu ne daga Ya Im, na rashin Boye abinda ke cikin zuciyata, koda
zai Batawa mutum, zan ji dadi idan na amayar da shi. Allah tun daga jin sunanki a bakin Innata,
nake kaunar ki, nake begen in ganki…kawai ina yakar zuciyata ne da yin hakan, sabida haushin
ki da nake ji akan Innata…"
Na zame daga gefen gadon, na kwantar da kaina a cinyoyinta, gwiwoyina bisa kafafunta nace
"ki yafe mini".
Ta kai hannunta cikin lallausar sumar gashin kaina, tana shafawa a hankali ta ce "ya
wuce Kyautar Inna, nima ki yafe mini, Allah ya yafe mana bakidaya”.
BAYAN WATA DAYA
Yadudu, Hajiya Azzo, Hibbani da Moiram matar Baffa Aliyu, suna zaune falon Nuratu suna
tattaunawa akan tafiya sayayyar kayan auren Haiti da za'a tafi Singapore.
Na fito daga daki rike da shaddodi guda biyu 'yan Mali, yellow da brown dinkakku dukka dinkin
Mali na manyan riguna. Nace "Nuuratu wanne zan saka?” Ta dago ta dubeni tace “sanya
wanda duk yayi miki, ai na Nuratunki ne". Hibbani tayi salati tace "wannan ba kayanki bane?"
Yadudu ta muskuta ta ce "umh, Zaynabu me kika ce? Sunan Uwar taki kike fadi gatsar-gatsar?”
Na juya daki da gudu ina dariya, in ajiyo Aunty Hibbani tana cewa "yanzu saboda Allah Nuratu
kaya daya kuke sawa? Ai sai ku sa a samu a jarida, wannan ai tsiya ce" ta yi dariya tace
"nayi-nayi ta bari taki dainawa".
Na fito shar da ni cikin yellown shadda babban riga da zane da dan gyale. Wuyana da
kunne na cikin ‘emirald’ rike da karamar jaka, na coge a bakin kofar dakin barci ban shigo cikin
falon ba na yi kan-kan da ido, ina murmushi nace "Nuratu.., au Mamie…, yaushe zamu je ki
sayo mini kayan?” Ba tare data juyo ta dubeni ba, tana fuskantar Hibbani, tace “sai ranar