Showing 12001 words to 15000 words out of 43757 words
Chapter 5 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf
na Allah, irinsu Ya Faruq
da Yaya Halima, wadanda tunanin su ya sha banban dana sauran mutane, ra'ayin su ya
banbanta dana sauran al'umma. Su irin wadannan mutanen kamar wasu mala'ikun Rahma ne
da Allah ke saukarwa bayinsa masu matsala irin nawa. ‘They are just like angels in the midst of
people' wadanda suke a shirye da sadaukar da kansu domin farin cikin wani.
Wannan ne ya kara sani dubar rubutun da nayi shekara daya da wata daya da ya wuce,
daga bakin Inna ta;
"Kyauta mu ba baroroji bane, sune 'yan kasarmu dake daji, mu 'yan kasar Nijar ne, 'yan
usulin wani gari Damagaram, amma iyayen mu da 'yan uwan mu a babban birni Yamai
(Niamey) suke zaune, har yanzu suna can”.
“In kika shiga Niamey, kika ce kina neman wani daya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko
yaro kankani ya san wannan sunan.."
Don haka na cusa littafin cikin jakata, na kishingida ina jiran garin Allah ya waye in kama
hanyar kasar Nijar neman dangin Innata, in gaya masu rasuwar ta, in rokesu alfarmar su barni
in zauna tare dasu, ta hanyar cewa ni ‘yar ta ce. Kamin a hankali in nemo Imran, inyi masa aure
da Adda Mami, daga nan nasan ina da Uban da zai rikeni ya kuma cigaba da yi min addu'a ko
bayan raina. Wato in zauna tare da shi da iyalinsa muddin rayuwata.
Na dauko wasikar da na rubutawa Ya Faruq, na sake binta a nutse, ko akwai wani gyara
a ciki? Na tabbatar, babu. Ga abinda na rubutawa dan uwana rabin jiki UMAR FARUQ;
"Ya Faruq .
Zuciyata ta kasa amincewa da wai in cigaba da zama da Yaya Halima, bayan sanin ko ni
wace ce?
Gangar jikina ta kasa amincewa da kai wai a matsayin miji, domin tana ganin baka cancanci
hada jiki da kazamtacciya kamata ba;
You are pure as a clean glass, and I'm a green, but rotten leaf. Har ila yau, zuciyar ta takasa
yafewa Nuratu da V.C Sa'idu, don ni ba zan taBa kuma kiran sa ‘Baba’ ba, ba zan taBa iya
kiranta ‘Inna’ ba. Don haka na tafi, inda a hankali nake tunanin zan samu labarinta.
In tambayeta dalilin shegantani da tayi, ta kuma nemo min dan uwana a duk inda yake cikin
duniya a dalilin bakin cikinta. ‘I know it will hurt, but you donno how deeply it hurts the victim’.
Faruq ka yafe mani, ka yi mun godiya ga Innarmu, ina nufin (Inna Dubu).
Ina fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa".
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Ta ce “eyi mana, baki san makauniyar matarnan tana da
alaka ta jini da ita ba? Amma da yake mai bakin kashi ce bata tara komai daga gareta ba, sai
dai ita ta dauki nata takai mata" nayi dariya a raina ina kara jin tsoron mutane, dubi yadda
Maman keta kareta daren jiya a wurin danta, kada ya koreta, amma ita yanzu gashi tana
zaginta.
Tace "unh, bari dai inyi shiru da bakina, don kema dai naga kina yanayi da su, ko dai 'yan
uwanki ne? Kada inje ko shuka ke nake a idon makwarwa”.
Nayi murmushi nace "mutane da yawa sun fadi haka tun shigowata Damagaram, kin san akan
samu haka, baka san mutum ba amma sai kayi kama da shi, ni daga Nijeriya na ke". Ta jinjina
kai cikin amincewa.
Can an jima na sake tambayarta "ko 'ya'yan Nuratu nawa?" Ta sake jinjina kai cikin
jimami tace "abin tausayi da wannan baiwar Allah, bata taBa haihuwa ba. An je turai anje Paris
an dawo jiya I yau. An kwakwale mahaifa an tsageta an wanke, ko kan 'yar tsana, bata haifa ba.
Yanzu kam ta dangana, sai dai tana rikon 'ya'yan kannen mahaifinta, kuma duk ita keyiwa
‘yanmatan zuri’ar su aure, ko kwannan ta aurar da guda biyu a Chadi. Gidansu babban gidane
mai dadadden tarihi a Damagaram, don haka ba zaki taBa gane bata haihu ba".
Wasu zafafen hawaye suka zubo min, na yi saurin dauke su da 'yan yatsuna, a raina ina
cewa su masu abin kunya ai haka suke, da sanya rigar mutanen kirki, son kai da rashin tunawa
da wanda ya zame masu dole, balle halin da yake ciki. Sai wanda ba dolen su ba.
Inna na yanzu tana can ta zama kasa da turbaya, da tunanin inda take, da halinda take ciki.
Itako tana nan tana cin mulki, wasu na can cikin bakin-ciki da kuncin rayuwa duk a dalilinta.
Danadam kenan, mai ban mamaki.
Muna karya kumallo amma hankalina sam-sam baya tareda ni, yana ga tunanin labarin
dana samu ayau na Nuratun Inna Rabi, ganinki yafi jinki. Ya janye ido ga jaridar da yake
karantawa, wadda ke rubuce da harshen faransanci yana kallona.
Na kurawa kyakkyawan hotonta wanda ya zamo (cover) na jaridar idanu ta baya, bana ko
kiftawa. Tana magana akan (racial discrimination) na farare da bakaden abzinawa, tana nasiha
akan su rungumi juna su daina wariyar launin fata a tsakaninsu. Duk yadda naso ta daina
burgeni, na kasa, amma hakan baya nufin zan fasa kudirina a kanta. Ya ajje jaridar ya tashi kamar mai dauko wani abu cikin madafi (kitchen), wannan ya bani
damar daukar jaridar na rubuce adireshin gidan jaridar dake jiki cikin (address book) dina da
lambar waya. Ya dawo a dai-dai lokacin da na aje jaridar inda take, na kuma zuge katuwar
jakata bayan na jefa dan littafin. Ya dubeni yayi murmushi yace "Hajiya babba da jaka, me zamu
ne a cikin jakar?” Nima na mayar mai da murmushin yake na ce "kawunan Damagarawa ne
nake tarawa a ciki” ya yi dariya ya buga kafarsa daya a carpet yace "kin san Allah, kawunan mu
ba (common) bane sabida GIRMAN su, kyawunsu da ingancinsu sunfi karfin shiga jakar bako"
na ce "sai ta dan gari?” Ya basar da zancen yace “in na fita yau sai asubah zan dawo, ko kina
bukatar wani abu in taho miki da shi?” Nace “babu abinda nake bukata, sai kudina da zan baka
kayo min canjinsu da saifa" yace "to ni in baki mana? Ki bar naki in kin koma Nijeriyarku,
jaga-jaga, su yi miki amfani?” Na ce “zan yi godiya kuwa, idan har kayi hakan". Bai fita ba sai
da ya aje min damin Niger-Saifa. Bai dade da fita ba na dauko bakin niqabina na maka, na fito
rataye da jakata. Laliya na gani na ta zura kitchen da gudu wai na bata tosoro, meye wannan?
Na wuceta zuwa dakin Mama na gaya mata zani gidan Radio in sa cigiyar amma ba dadewa
zan yi ba, ta yi addu'ar fatan alkairi ta ce in dauki Liliya muje tare kada in bata, na nuna mata
babu damuwa ai shata zan dauka daga nan bakin titi da zai kaini ya dawo da ni har gida.
Na tari Taxi na nuna masa dukkan adiressikan da zai kai ni, daya bayan daya, ya jira ni
in fito sannan ya maidoni, in mun dawo sai muyi balance. Da haka ya ja motar muka mika gidan
talbijin na jihar Damagaram, ban sha wahalar samun ganin shugaban gidan talbijin din ba kuma
da yake yana jin turanci sosai na gaggaya masa abinda naga dama. Karya da gaskiya harda
shaci fadi, har da cewa a gidan marayu na tashi. Da fari ya nunamin ba zai yarda ba, domin
bani da hujja. Na daga nikab dina muka yi ido hudu nace “ga hujja ta".
Ya dade yana kallo na, ya tabbtar wannan (photocopy) na Nuratu ne a gaban sa, wadda
duk duniya ta yarda bata da kwan haihuwa a doron kasa, ai sai ya dauki camera ya dora min
ina turancina tiryan-tiryan, wani ma'aikacin gidan talbijin din a gefena na fassarawa. Suka
sallameni na fito muka karasa babban gidan Radion kasa wanda keda reshe daga babban birni
Niamey. Gidan jarida kuwa da naje ai abin nema ne ya samu, wai matar dan sanda ta haifi
Barawo, labari da dumi-duminsa;
"Mainasara ta haifi 'ya ba aure a Nijeriya, shekaru goma sha takwas a baya. Ta guda ta barota
da rayuwa gidan marayu duk wannan tarin arziki da Allah yayi mata. A yau ga yarinyar tazo da
kafafunta, tana neman mafaka a inuwar Gwamnatin Damagaram domin daga can inda take
aure a Nijeriya an koreta, a sabili da ganewa da iyayen mijin suka yi ita shegiya ce…. Ga kuma
wanda ya karyata, to yazo ofisoshinmu mu hadashi da yarinyar suyi Magana baki-da-baki,
budurwa 'yar kimanin shekaru sha takwas, wadda a kamanni da zubin halitta bata da maraba
da Mainasara…”.
Na dawo gida a gajiye likis, da yamma lis. 'Yar gyatuma tana zaune a gaban allon talbijin
ta bude kunnuwa tana saurare, na yi mata sallama amma bata amsa ba, bakinta sai kumfa yake
tana masifa cikin abzinanci, da zage-zage cikin harshen hausa, tare da mikewa ta laluba ta
angazo talbijin din daga mazauninta jikake taratsatsatsa…! Talabijin din ta soma fidda wani irin hayaki. Laliya dani muka zura da gudu muka zare soket din
daya soma cin wuta, ta fadi kasa tana kuka tana birgima tana cewa "duk wanda yayiwa Nuratu
wannan sharrin sai Allah ya saka mata, siyasar banza, in banda siyasa mai bankadar da
mutunci, wa ya isa ya yi mata haka…?” Haka muka kwana a kanta ba yadda take, gabadaya ta
birkice mana kamar mai tashin jinnu, tanata jan Allah ya isa da Li'ilafi ga wadda aka hada baki
da ita akayiwa Nuratu sharri, ba zata taBa yafewa ba'
Da asubahin fari ya shigo gidan, ya tadda gyatumar sa cikin wannan hali. A kidime ya dagota
daga gado ya rungumeta yana tambayarta abinda ya faru, sai cewa take ita dai ya kaita
Niamey. Ya dubeni cikin tashin hankali "wai don Allah me ke faruwa ne Zaynab?” Na jinjina kai
kamar gaske "tana magana ne cikin French, bansan me take cewa ba”, ya dauketa muka tafi
asibiti aka bata gado. Aka zurkuda mata allura ta samu barci sannan ne muka kamo hanyar
dawowa don tafiya da abin bukata.
Akan hanyarmu ta dawowa daga dauko kayan amfani ne ya kunna radiyon mota, abinda ya fara
ji shine, an dakatar da Nuratu Mainasara daga takarar gwamnatin Damagaram a karo na biyu.
Tare da koro bayanai dalla-dalla, daki-daki, wannan kuma Oda ce daga kotun kasa (Federal
High Court) a turance, har sai sunyi kyakkyawan bincike akan al’amarinta, daga tsarin mulki ne
littafi kaza, shafi na kaza sakin layi na kaza. Mai tabbatar da haramcin mutum mai tsohon laifi
daga shugabanci.
A nutse yake sauraro, babu alamun razana a tare dashi, niko wani gefen daban nake kallo
gabana na dakan tara-tara ba uku-uku ba. A hankali naga bakaken gilassai suna maye gurbin
farare a cikin motar. Ya fiddo bakin gilashi mai duhu sosai ya saya fararen kwayan idanunsa. Da
na juyo na dube shi don neman karin bayani, game da canzawar glassai, sai da nayi nadamar
juyowar. Gabadaya ya rikide zuwa wani irin mutum mara imani, mara kyawun gani, tamkar bai
taBa dariya ba. Hatta kalar fatarsa sauyawa tayi, daga ja zuwa ‘yellow’, a hankali cikina ke bada
sauti “Kululuuu…!”
Ya sauke motar a gefen titi tsayin mintina biyu kansa na sunkuye bai ce komi ba, ni
kuwa tuni na cure na dunkule wuri guda kamar kashin awaki. Na ji wani abu yana zungurina a
wuya, juyawar nan da zanyi sai na yi arba da hancin 'yar karamar bindiga da nake gani cikin
fina-finan Amurka ‘revolver' a dokin wuyana. Ya rausayar da kai gefe yace "hmh, tell me, who
are you?”
Nayi narai-narai da ido, ina yi masa kallon (ka tuna alkawarin daka yi mun kafin in bika cikin
gidan ku? Ka tuna alkawarin da kayi mun na ba cuta ba cutarwa a tsakanin mu? Ka tuna
alkawarin da kayi mun na zamowa dan uwana na jinni?)
Ya gyada kai sama, tamkar ya san me nake tunani yace "imagine you ‘ve never set eyes on me,
let us draw to my profession….. " ya fiddo katin shaida (ID card) ya manna min a ido "State
Security, Qassim Mainasara".
Maimakon inji tsoro, in amsa masa tambayarsa, kamar yadda yayi tsammani, sai na yi
murmushi na dubeshi cikin bakin (dark-glass) dinsa, na ce “ai ba tun yau ba, na san kai (SS) ne,
kaine dai baka san ko ni wace ce ba. Duk da kasancewar naka mai binciken kwakkwafin dake
alfahari da aikin sa”. Ya ce cikin muryar razanarwa "shine nake tambayarki who are you? Ko
kinsan wadda kika zo kika yiwa sharri, kika bata mata suna wace ce a gareni?”
Na taBe baki nace "tarwatsa kwakwalwata kawai ka daukar mata fansa, ban san wace ce dinka
ba, ba kuma na son in sani. Burin da nazo da shi kasarku a yau, ya cika, don haka ko a yau
rayuwata ta kare ALHAMDULILLAH!”
Yace “kin isa ki mutu, ba'a tagayyaraki an tara maki gajiya a Damagaram ba? Shirmen
banza kike, kin dauka wannan shirmen ne zai cika burin naki? Sai ince kuruciya na dibar ki,
amma Aunty Nuratu ba sa'ar yin ki ba ce, ke har wadanda suka kulla miki karyar su ta sha
karya su ja da Mainasara, domin ita dashen Allah ce, ba dashen mutum ba." Na ce "shine nace ka tarwatsa kwakwalwata da harshashin bindigarka, sannan ne zan yarda
da kaunar daka ke mata. Suna kam na riga na Bata mata, wadanda ma basu yarda ba in na fito
a gidan talbijin suka ganni a zahiri zasu yarda, sannan kotun kasa dake shirin yin bincike don
tabbatar da zahirin maganata zanje su debi jinni na su auna…” yace “…. over my dead body! A
bayan raina ba, amma in har ina raye, bazaki kuma zuwa wani gidan talbijin ba, masu diban
karya da gaskiya sabida su jahilai ne irin ki, sai dai in mika ki ga al'ummar gari su jefe ki, su
kacaccala wannan fuskar da kike tinkaho da ita mai kama data Aunty na…."
Nayi murmushi cikin komawa kallon wautarsa, ga gaskiya kiri-kiri yasa kafa yana takewa da
gangan don son Auntynsa, nace “kai ni tsakiyar gari Qassim, a yagalgala fuskana mai kama
data Auntynka" ya ce “ai idan na yi hakan kuma ban kyauta mata ba, don na tabbata zata so
ganin wace jarumace ce ta aikata mata wannan sharrin? Don haka daga nan, Niamey zan kaiki,
koda akan iska ne.
Ki je gabanta ki maimaita abinda kika fadi, in har kin cika mai tsaurin ido da jarumtaka….” Ya figi
motar da gudu sai filin jirgi, ya kulle ni a cikin motar ta ko’ina yadda ko ihu zan yi ba mai ji na, ya
fita. Bai san cewa ko a bude ya bar kofar bau inda zan je ba.
Nidai tunda burina ya cika, ina maraba da kowacce irin rayuwa ce ta sameni a gaba. To don ya
daukeni ya kaini gabanta sai me? Iyakaci tasani a inji, ta markade, ko jama'arta su harbeni da
bindiga sai me? Bani da wai sauran ‘hope’ a rayuwa sai na fatan cikawa da imani.
Haka kawai kuma naji hankalina ya tashi, bugun zuciyata ya tsananta, wasu irin hawaye kuma
da bana ce ga dalilin su ba, suka zubo mini, na nadama ne koko na dakacen me kenan na yi?
Me yasa nayi haka? Ban kyautawa Innata ba. Nasan duk inda take a yau tana cike da Bacin
raina, ban ji maganarta ba, banyi amfani da gargadinta ba ko daya. Ramuwar gayya bata dace da dan musulmi ba, musulmin kwarai afuwa yake da rangwame
cikin al'amarinsa. Ramuwar gayya da daukar fansa aiki ne na yahudu da nasara, wadanda basu
yarda Allah ke shiryawa bawa rayuwa ta duk yadda ya so ba. Gaskiyar Yaya Halima ne bacin
rai zai sani fita a imani na, zai rauna imanin da nayi da Allah guda daya, shine mai sakamako,
da bin hakikin wanda aka zalunta.
Babban abin takaicin ma ga UWA, wadda ta dauki nauyina cikin mahaifarta wata tara
ras, ta haifeni bayan mawuyanciyar nakuda da Allah kadai yasan adadin azabar dake cikinta.
Idan kuma an bi salsala Nuratu bata yi min laifi ba, Ubangijinta ta yiwa. Idan kuma ta
rokeshi ya yafe mata, ni ba komai ba ce. Babu wadda zata so ta haife Da babu aure, sai dole,
sai tsananin rabo da kaddara. Babu kuma wanda ya isa ya kaucewa kaddarar duk da Allah ya
rubuta masa. Sai kuma wani hukunci na Ubangijin mu da yake son nunawa na baya darasi.
Amma al'umma bazamu taBa hankalta ba.
Laifinta daya gareni, shine na biris din da tayi da Innata, abar ma ta ni kaina, alhalin tana
sane da wahalar data barta da ita, da bakin-ciki gami da abin kunyar data jawo mata wanda
fadar sa ma bata baki ne, musamman a cikin karkara.
Duk da haka 'yar uwarta bata taba budar baki ta fadi kalami na Allah wadai agareta ba. Duk
wasu kalamanta akan Nuratu na kauna da alheri ne. Ta ce dole ce ta sa ta gudu ta barta,
amma Nuratu mutuniyar kirki ce.
To ko bayan Innar, wane ne ya budi baki ya fadi wani abu wanda bana yabo da kauna
gami da fatan alkairi a gareta bane? Ko Ya Faruq wanda zai kasance karamin yaro a lokacin da
ya santa, yace ba halinta bane, kaddara ce ta afka mata. Hakika halin mutum da makomarsa
ana gane su ne daga shaidar da ya samu daga mutanen dake tare da shi. Kamar yadda yace;
dukkannin mu masu saBo ne in one way or the other, na wani ma idan kaji sai kaji kamar ka roki
Allah ya kifar da duniyar, domin babu komi cikinta sai saBo, kalilan ne suke yin saBon suna
kuma tuba. To idan Nuratu ta tuba, Ubangiji ya amshi tubanta, ni menene makomata? Abin nufi,
meye makomar dan da ya bankada mutuncin Uwarsa a duniya? Ya tozartata a idon al’ummar
dake matukar ganin GIRMA da kimar ta? Abar ta zancen hukuncin rashin yarda da kaddara da
fawwala komai a