Showing 36001 words to 39000 words out of 43757 words
Chapter 13 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf
na ce “babu komi, kome zai min zai jure, karewa ma hakuri zan
bashi" ya ce “to ki bari zamu zo anjima, idan Mamie ta tashi bakyanan bazata ji dadi ba, kafin
nan zan dage wajen lallasar miki shi, kin san mai hakuri da tausasawa bai iya fushi ba” na ce “to
nagode, my precious."
Sai azuhur Mamie ta tashi, ta sake wanka ta zuba alkyabba tazo ta zauna ta harde
kafafu a falo tana amsar sakonni, wasu cikin (pocket-computer) dinta wasu cikin waya, wasu
kuma daga ‘post’ aka kawo mata yanzunnan. Ta ce Hibbani ta dafa mata abinci, bata son na
Otal. Hibbani tace “tun kan ki sauko na duba firjin kichin din babu komi ciki”. Ta dubeni ta ce
“jeki ki kirawo min direban nan a waje”. Na mike tsam na fita muka dawo tare dashi, tana zana
masa aike kala kala, sannan ta shiga buga waya kantuna da masana’antu tana fadin abinda
take bukata. Cikin minti ashirin sai ga motoci a kofar gidan suna sauke katon-katon na lemuka
da kayan abinci, danyen kifi da danyen nama kilo-kilo. Da kansu suka jera kowanne a
mahallinsa cikin kitchen. Na taya Aunty Hibbani muka shirya abinci sannan na shiga shirya wani
na musamman tace "wannan kuma fa?”
Na yi murmushi kawai, ta ce “au to, na maigida Faruqu ne kenan? To shin yanzu Yaya zaki da
Qassim, da alama bahaushen ya fimu samun shiga” na dinga dariya don ban san amsar da zan
bata ba.
Na fito daga wanka kenan ina shafa na jiyo sallamar su Ya Im, hakannan na nasamu
kaina da rashin jin dadin fushin Ya Faruq dani, na yi gaggawar shiryawa na fito cikin fararen riga
da siket yan kanti (Nina-Ricci) na feshe jikina da turaren (final touch) na cakuda da (Mont
blanc), na nade gashin kaina cikin bakin ribbon na taddasu duka a falo suna cin abinci bias
‘dining’. Kallo daya Ya Faruq ya min ya dauke kansa ya maida hankalinsa ga maganar da suke
yi da Mamie, Imran ne kurum yayi min murmushi.
Mamie da Faruq suka mike, Hibbani ma ta fito cikin shiri sakale da Jakarta, Moiram kuwa tana
mike akan doguwar kujera (tana fama ne da laulayin karamin ciki, don haka ta faya kwanciya).
Ya dubi Imran a gicciye ya ce "yaa! Kai ba zaka bimu ba ne?” Ya girigiza kai, ya kada kafada
"ina bukatar privacy da ‘yar uwata” wani dadi ya ratsani, ina satar kallon Faruq sabida kyan da
yayi min cikin kananan kaya, wadanda ba al’adarshi bace sanyasu.
Ya kyabe baki yace “kai madallah, ai dama mugu shi ya san makwantar mugu, kuma mugu
baya sirri sai da mugu dan uwansa…” amma a hankali, yadda su Mami da sukayi gaba bazasu
jiyo ba.
Na lalubi kujerar da Mamie ta tashi, na zauna da kyar zuciyata na tafasa, na dukar da kaina ina
zukar numfashi da kyar ina fesarwa da kyar. Imran ya maido hankalin shi akaina yayi ajiyar
zuciya yace “kiyi hakuri da Faruq, nima bansan sanda ya koma haka ba".
Na ce “kyaleshi kawai, amma kome me nayi masa, ai sai ya sameni ya gaya min in bashi
hakuri, sai yayi ta ce min muguwa, muguntar me nayi masa?” Yayi murmushi “kin yi masa
mugunta mana, kin daga masa hankali. Duk nasihohin da yayi miki kika shure kika tafi, inda bai
san inda kike ba. Alhalin yana shirin angwancewa. Don ko a kansa bai taba kawowa wai kinsan
sunan Damagaram ba, ya ce min lokacin ya shiga tashin hankali sosai har ya kusan zaucewa.
Musamman wasikar da kika bar mishi wai zaki je yin ramuwar gayya akan mahaifyarki, alhalin
kina mace.
Ya ce inda kin san kina son zuwa wajen Mamie, ki tambayeshi mana? Ki gani idan bai kawo ki
ba, sai kawai ki yi wasa da rayuwarki, ki kama hanyar Nijar ke kadai wannan kasada ce babba.
Haka Malam da Halima har yau basu da cikakkiyar lafiya, sabida zullumin inda kika fada da
halin da kike ciki. Halima duk ta dauki laifi ta azawa kanta, domin kuwa amana malam ya bata
ke. Banda BABAN KI, da akace nisan kwana ne kadai ya kawoshi yau inda muke”.
Na yi ajiyar zuciya nace cikin wata irin murya abin tausayi. “Ya Em ina BABA SA'IDU?” Ni kaina
ban zaci har abada zan kuma furta wannan kalmar ba. To amma BABA SA'IDU, wani bangare
ne na zuciyata, da matsayinsa ya zarta na kowa har da Mamie da Innata.
Ya sadda kansa kasa yana duban kyawawan yatsun kafafunsa yace "nima har yau ban kara sa
shi a idanuna ba. Amma ina samun labarinsa wajen Faruq. Ya ce ya ji sauki har ya koma aiki.
Hajiyarmu ce dai ta gamu da ‘stroke’ (shanyewar barin jiki) tun wata faduwa da tayi data samu
labarin komai, sai dazu ne kawai Faruq ya gaaya mishi cewa duk muna tare anan Singapore,
har Mamie, yace zasu zo Yamai su same mu. Faruq ya ce ya bari sai sati mai zuwa sabida ita
Mamin wata hidimace ta kawota. Amma ni lallai kamin sati mai zuwa zan je gida, don an ce jikin
Hajiya yayi tsanani sosai kuma kullum ni take kira”. Na lumshe idon cikin tausayawa rayuwar
mu bakidaya nace "Allah ya bata lafiya" yace “amin” daga haka sai duk mukayi shiru, cikin
rashin sanin abin cewa.
Na dago bayan wasu 'yan dakikai na dubi ya Im, cikin jin nauyi nace "Ya Im, aure fa, sai
yaushe?”
Yayi murmushi, bayan ya turo hularshi gaban goshinsa ya ce "sai nayi naki da Faruq” nayi
murmushi nima nace "ai ni a yanzu haka Ya Im, babu soyayya cikin al'amarina, sai kauna, kana
tunanin zan iya auren mutumin da bani da birbishin soyayyarsa, ko digo daya, sai kauna ta ‘yan
uwantaka?”
Ya ce “wannan shine aure, na hakikah, Zaynab, mai karko, albarka da dorewa. Amma fa ga
masu hankali.
Soyayya ba komai bace, domin abu ce mai gushewa, musamman idan an kawar da sha'awar
dake tsakanin masoyan.
Amma ita kauna ta fisabilillahi, itace wadda ake aure da ita, daga baya ta sayo soyayya mai
‘lasting’ har tsufa, har mutuwa. A kuma tashi ranar gobe kiyama, cike da kaunar juna.
Kin ganni nan nima ba zan taBa yin auren soyayya ba, zan yi aure ne saboda Allah, da kare kai
daga dattin zina da rudin shaidan. Idan muna da rabon soyayyar, sai ki ga mun sameta a gaba.
Ma’ana a gidan auren. Koda bayan hayayyafa ne.
A wurina soyayya ba komai ba ce face wani abu dake sanya zuciyoyin ‘yan adam cikin halaka,
bakin ciki, nadama, tashin hankali, kiyayya, da kaka-ni-ka-yi. Duk da haka tana da dadi; so
sweat, yet so painful.
Don haka ki auri Faruq da zuciya daya, ina mai tabbatar miki duk duniya bayan iyayenki da ni,
sai Faruq a masu kaunarki.
Ya soki tun kina jaririya, cike da sanin (who you are). Ya cigaba da son ki a girman ki,
cike da tabbacin (ba zai taba aurenki ba). Ya tsayawa rayuwar ki tamkar Uwa da Uban ki. Kuma
har abada wannan itace kauna, wadda ba’a ko’ina ake samunta ba, sai mai sa'ar gaske. Ina
kara tabbatar miki ba zaki taba yin dana-sanin auren Faruq ba…..!”
Na kai hannu na yarfe hawayen da suke ta zuba, nace “nima nasan da hakan, kawai ina ganin
shi kamar wani Baba na ne….” yayi murmushi yace "as time goes on, zai wuce kamar ba'a yi
ba. Zaynab ke mai sa'a ce; iyayen dake matukar son ki, mijin dake mutuwar kaunarki, dan uwan
dake shirye da sadaukar da rayuwarshi kan duk wani mai shirin illata mutuncin ki, saboda haka
ki gode Allah, ki manta komi.
Babu dan adam din da yake cikakke 100%, dukkanin mu muna da gibi a wani fannin daban.
Idan Allah ya baka wannan, sai ya hana maka wancan, domin ya jarrabi imanin ka. Ina cigaba
da yi miki addu'ar samun dawwamammen farin-ciki a gabadayan tsayin rayuwarki……".
Na zamo daga kujerar da nike zaune, nayi zaman rakuma agabansa. Cikin muryar
girmamawa, matsananciyar kauna da tsananin ladabi nace "Ya Im, kai kuma fa?
Me kake shiryawa taka rayuwar? In gaya maka gaskiya, farin-cikina da kake ambato, ba zai
taba cika ba ina ganinka haka incomplete, shattered….!"
Ya kamo hannuna cikin nasa yace "kada ki damu da ni, namiji ne, zan iya karbar rayuwar a duk
yadda ta zo!!"
Sai na fashe da kuka sosai, na ce "ni dai don Allah kayi aure, ka koma gida, ka koma
aikinka ko ka nemi wani. Ka nemi gafarar Baba Sa'idu, me yayi maka haka da zafi? Ni aka yiwa
kuma tuni na yafe mishi, tun ma kafin in san laifin da yayi min na gayawa Innana NA YAFE
MISHI, kaima ka yafe mishi in har da gaske kana son farin cikin nawa…". Ya fiddo hankici yana share min hawaye yace "is o.k Zaynab, na yi miki alkawarin yin duk
abubuwan da kika lissafa. Amma bayan kema kin daure kin nemi gafarar laifin da kika yiwa
Faruq, kun koma dai-dai" na ce “nayi maka alkawari Ya Im”.
A dai-dai lokacin da Faruq ya shigo, niki-niki da kwalaye, Mamie ta biyo baya sannan Hibbani.
Ya dire kwalayen bisa kujera, ya dubemu yayi dariya yace “Allahu Akbar! Mamie kin ga yadda
ake hirar 'yan uwantaka, har da hawaye da majina sabida kauna" ta yi murmushi ta yi daki ta
rabu da shi, shi Faruq sam baya jin kunyarta kamar ba mai shirin zama sarakuwarshi ba.
***
A cikin kwanaki hudu, duk sayayyar da za’a yi wa Haiti an gama ta, sai dai Mamie komi
biyu-biyu take dauka. Mun samu hutu da nutsuwa sosai, amma duk yadda na so da in ba Faruq
hakuri, ya ki hakan, ya ki saurarena. Ana I jibi zamu baro Singapore ne suna tare da Mamie a
falo, suna wasu tsare-tsaren sabon gidan da zata saya a nan don tace wannan da muke ciki
nawa ne, da sunana ta saye shi tun da dadewa. Na karaso na kwantar da kaina akan cinyarta
nace "Nuratu na kawo miki karar Dan dukusurunki".
Ba ita ba hatta Faruq basu san sanda suka fashe da dariya ba. Ya kuma koma yayi dif,
ya dinke, kamar bashi yayi ba, ya ce "ke, wanene Dan dukusurun? Ina wasa dake ne?” Na dube
shi cikin kwayar idanunsa, tuni ya koma Ya Faruq dinsa, ya shiga sosa keya da ‘yan
mukullayenshi domin bayewa Mamie halin da ya samu zuciyarshi da gangan jikinshi a ciki, yace
" Mamie yariyar nan zan soma zane ta, ta fara kawo min wargi” tace "me Dan dukusurun nawa
yayi miki, a gaya mun inyi hukunci” na ce "haka kawai yake shareni, ko ya kirani muguwa,
sannan bashi da lokaci na".
Ta maida dubanta gareshi, tana murmushi ta ce "to kai Dan dukusuru na kaji laifuffukanka, ko
kana da ja?” Yace “eh, ita ce duk ta jawo Mamie” “da ta yi me?” Ta tambaye shi. “Ta taho kan
gaban kanta, bada izinina ba, ta tayarwa da Malam da Halima hankali. Inna Dubu har yau bata
daina kukan tafiyar Abun ta ba. Har da bar min wata banzar wasika wai wani "DA FATAN WATA
RANA ALLAH YA HADA MU CIKIN ALHERINSA". (Sunan littafin Takori mai zuwa).
Mami ta yi murmushi cikin jin dadI, ta jinjina kai tana yiwa Allah godiya, a bisa
rahamomin da yake yi mata. Ta ce "to ai gashi a yanzun ya hadaku cikin alherin nasa, sai ku
yafi juna.
Ita kanta rayuwar da komai dake cikinta dan afuwa ne. Da Allah baya afuwa a garemu, da
dukkan mu bamu kawo yau ba.
Wanda kuma duk yayi afuwa ga dan uwansa musulmi, shima Allah zai masa afuwa. Ba mamaki
a lokain tana cikin ‘tension’ ne da har ba zata tsaya yin tunanin abinda ya kamata ba, ka yi
hakuri ka yafe mata!".
Kallon da yayi min da wani irin murmushin da bai taba yi ba, kuma bata ganinsa da shi
ba. Shi yasa ta tashi ba shiri ta bar mana falon.
Ya taso ya dawo gabana tamkar ya shige cikin jikina, yace "Eye. na'am, maimaita sunan a
bakinki Zaynab?” Nayi kasa da murya sosai. Na ce “YA FARUQ" yace “ashe kin gane, to ko kef
a? Wancan sunan na Nuratuna ne ita kadai. To yaya? Bani labarin hijirarki dalla-dalla, har na
'yan fashin da suka kusa yi min shigar sauri….” na mike na zaura daki da gudu, babu ko
waiwaye, yana kirana amma ban juyo ba.
*** *** ***
Daga Singapore Paris muka wuce, birnin Suisra. Nuratu ta saya min sittiru kamar har abada
bazan sake sayen wasu ba, takalma da jaka da kayan kawa na mata, kai ka ce katafaren shago
za’a bude. Kayan shafa da turare, wannan ba’a maganarsu. Su kansu su Faruq sun girgiza da
dukiyar da take kashewa a kaina. Amma ita din ko a jikinta. Imran tun daga Singapore ya hau
jirgin gida Nijeriya ya koma Sokoto.
Muna shirin tahowa ne wani babban al'amari da ya dimautamu ya faru, an yiwa Aunty
Hibbani waya daga Chadi, ana gaya mata rasuwar Ahmad Fiance din Haiti a sanadiyyar
hatsarin jirgin sama. Jikkunanmu suka yi sanyi kalau. Na daga kai na dubu tsibin kayan auren
Haiti, da ake shirin yin lodinsu, amma wai duk sun tashi a banza. Tausayin 'yar uwata ya kamani. Ni din shaida ce akan matsanancin son da take masa.
A take Mamie ta nemi da a canza mana ‘booking’ zuwa Malaysia domin mu taho da
Haiti, wadda a karshen satin dama zata dawo. Aka sanar da ita babu jirgin sai sati mai zuwa,
tunda ba passenger. Tayi alkawarin saye sauran kujerun gabadaya, muka daga zuwa Malaysia,
inda muka kara hawa wani jirgin muka karasa makarantar su Haiti (University of Malaya) dake a
Kuala Lampur.
Allah sarki Haiti! Da gudunta ta taryemu, ta rungume wannan ta koma ta rungume
waccan. Daga karshe ta kama ni tamakalkale tana kyalkyatar dariyar farin ciki. Tare da ita muka
taho a washegari, babu wanda ya gaya mata sai da muka dawo gida Yamai.
Kwatanta halin da ta samu kanta a dan tsukin ba zai fadu ba, tayi kuka ta yi ciwo daga baya ta
dangana. Shi Faruq ya wuce gida Gwarzo domin sanar da Malam halin da ake ciki.
A karshen satin muna cin abinci nida Haiti, misalin karfe hudu na yamma. Muka ji dirin motoci
da wani irin cin taya mai nuna anyi doguwar tafiya mai dogon zango.
Mami ta sakko daga bene cikin shiga ta alfarma, rike da falmaran din Alhaji Badeggi zata kai
masa dakinsa domin yana shirin fita ne, a cewarsa suna da manyan baki da zasu tara a (Guest
House) din su. Kamin in idasa goge bakina da ‘tissue’ in mike don fita ganin su waye? Iftihal da
Azizah, sun fado a tsakiyar falon mu, suna kira da babbar murya "Ina Aunty Abu? Gamu nan mun biyo ki tunda mu, kin guje mu".
Sai kuma ga Inna Dubu, Hajiya Azumi da Inna Rakiya. Na mike jiri na kwasata, kafin in
kai ga su Ifitihal, na fadi, na sume. Lallai wani fairin cikin yafi gaban kuka, ko dariya.
Na bude ido a hankali, Imran da Iftihal ne suke min firfita. Na mayar na rufe, a hankali na
kamo hannun Ya Em, sannan na Iftihal, Azizah ta dora hannunta akan goshi na tace “haba don
Allah Aunty Abu, ki tashi, me yayi zafi har da suma? In baki son ganin mu ai sai ki gaya mana
mu koma, ba ki fadi ki suma ki tayar da hankalin masu kaunarki ba. Ke dai ban san yaushe zaki
daina yawar nan taki ba!”.
Nayi murmushi, kana na mike na rungume su. Wasu hawayen suka shatato mini, wani na bin
wani. A hankali nace “Azeezah, you are always the way you are (kullum kina nan a yadda kike)”
ta ce
“naji, ki tashi ni don Allah muje, BABA yana kiran ki”.
Dam! Dam!! Dam!!! Zuciyata ta buga, kirjina ya harba, kwakwalwata ta hautsina kamar
ince da ita wane Baban?
To amma wannan tambayar ma ai rainin hankali ce a gareta. Baban guda nawa ne? Banda
Babana ABBA BABA SA'IDU? A hankali dai, cikin matsananciyar fargaba, na yunkura na mike
muka jero mu uku a tare. Su Mama Hajiya Azumi, suka bimu da kallo cikin kauna da sha'awar
da muka basu. Nuratu ta dubi Hajiya Azumi, ta ce
“Allah shine mai GIRMA, amma ba kowa ba!”
Inna Dubu ta ce “wannan haka yake, Allah shine mai GIRMA! Mu duka shirme muke amma shi
kadai yasan abinda ya boye a rayuwar bayinsa". Suka girgiza kai cikin karuwar Imani a
zuciyoyinsu
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Allah sarki Yaya Rabi, koda hakan ta faru dani bata yi fushi
da ni ba. Daga baya ta hakura ta fawwalawa Allah al'amarin. Ta kuma ta dauki dukkan laifin da
fushinta mai tsanani ta dora akan Sa'idu. A cewarta ba hali na bane, koma menene shi ya koya
mini. In ni yarinya ce ai shi mai hankali ne, da har yake da aure har da Da, anjima kuma sai ta
yarfa hannuwa ta ce "wannna rashin tsoron Allah da mai yai kama? Wannan duniya ina zata da
mu? Wanda ka amincewa shi yake cutar ka. Wanda ka yiwa alkairi shi yake maka sharri. Idan
na cuci Sa'idu a tsayin zamana da shi, da yayi min wannan sakayyar, Allah ka fitar mishi. Nima
ka fitar min hakkina akan wannan cuta da cin amana da yayi mini”.
Daga baya har mukan zauna mu koka al'amarin a tsakanin mu. Ina kuka in ce “ni bana
tausayin kaina, sai na abinda zan haifa. Me zan gaya masa ya yafe min samar da shi dana yi ta
dattin zina? Wallahi ni kaina Ya Rabi, ban san ya akai hakan ta faru da ni ba, ji nake kamar cikin
mafarki, sai daga baya na Ankara, na gane ashe ba