Showing 33001 words to 36000 words out of 43757 words
Chapter 12 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf
da
nayi arziki, har yanzu bani da arzikin da zan saya maki kaya…."
Na karaso da gudu na rungumeta nace “haba-haba Mamie, ni da ke bata Baci.. " Hibbani kallon
mu take, muna burgeta, ta yi murmushi tace "kyaleta ki shirya tare dake zamu tafi Singapore,
siyayyar kayan auren ‘yar uwarki, daga nan sai ki sawo duk duk abinda kike so" nayi tsalle na
makalkaleta. Qassim ya shigo cikin shiri har da trolley dinsa, kamar hadin baki mun yi ankon yellown
kaya, sai dai shi shet ce yellow da bakin wandon Jeans, idanunsa akaina ya dubi Mami yace
"Aunty ni nayi harama, zan koma bakin aiki” tace "to Qassim, Allah hokku sa'a”.
Ya dubeni yace "inye, su bera anyi kilin, to a zo a yi mun rakiya ‘airport’ mana? Irin wannan
kwalliya bai kamata ki dankare a gida ba” nayi murmushi (tun ranar da muka fahimci ‘yar mace,
da dan namiji muke, muke bugawa), ba don komi ba nake bude baki ina ramawa ba sai ma don
kada zancen Haiti ya tabbata, wato ya furta min soyayyar da ya dade yana Boyewa. Gashi a
yanzun ta gaza Boyuwa ta fito karara cikin fararen kwayar idanunsa. Na ce “ba dole in yi kilin
ba, ko na dinga razana matar ka, tana nan-nan- da ni ba?” Haka muka fita muna tayi, suka bimu da kallo cikin jin dadi. Muna fita Yadudu ta soma furzar da
abinda ke ranta, wanda ya taso da ita takanas tun daga Damagaram, wato burinta na a hada
mu aure da Qassim, babban abinda ya faranta mata kuma shine fahimta da tayi yanzunnan
muna son juna. Shiru tayi bata yi magana ba, amma su Hibbani suna ta sawa abin albarka.
Muna bayan motar Nuratu Roll-Royce wadda (personally) ta hawanta ce ita kadai, ni da
Qassim, sanyin raBa na ratsamu. Direban Mami na jan mu. Ya lumshe ido ya kwantar da kansa
a bayan kujera cikin damuwa. Hasken hantsi yana haska bakin gashin kansa, wanda ke kwance
lub, a wuyansa sai sheki yake kai ka ce ‘shampoo’ yake yi, amma wannan halitta ce. Qassim
jajur yake fiye da ni, kamar ka taBa jini yayi tsartuwa, ga kuma yanayi irin na arzikin da hutu sai
suka taru suka mai dashi kamar wani balaraben Kuwait.
Ganin damuwar da yake ciki duk sai nima na ji na damu. Nace "yaya ne my Qassim?” Sai ya
bude idanunsa da suka kankance, cikin mamaki yace “don Allah sake fadi, 'yar kanwalle?” Na
harareshi nace "wannan ne kuma baka isa ba…" maganar ta makale a makoshina, ganin irin
kallon da yake yi min cikin kwayar idanun shi, da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, jikina
yayi sanyi, ya mace murus. Na sadda kai ina wasa da yatsun hannu na dana kawata da jan
lalle, tun sanda na fahimci yana daga cikin abinda Mami ke ado da shi, yake kuma kara maida
ta cikakkar mace, nima na dimance shi.
Yayi murmushi yace "wannan (pretending) din naki, bashi zai hanani furta maki abinda bakya so
in furata ba, Zaynab ina sonki, ina kaunar zamowarki abokiyar rayuwata a tun ranar da na fara
haduwa dake, tun kuma kafin in ganki. I love you in your veil (na sonki cikin niqabinki) kuma na
so ki yau a zahirin ki. Mene ne amsar ki? You are no more a child now (ke ba yarinya ba ce a
yanzu) nasan tuntuni kin fuskanci inda nasa gaba, sai dai ban san dalilin da yasa kike basar da
ni da gangan ba”.
Na yi shiru banyi magana ba, a dai-dai lokacin da direban ya karya kan motar muka
shiga cikin airport, ya tsare ni da ido cikin jiran amsa. Na bude murfin motar zan fita, ba tare da
nasan amsar da zan bas hi ba, cikin wata rarraunar murya ya ce
"May be am not good enough to be your husband)……”
Na juyo cikin mamaki nace "me ya sa kace haka?” Jinin mu daya, tushen mu daya. Sannan
kana da wani matsayi mai GIRMA a gareni, domin kayi mun abinda har in koma ga mahalicci
na, bazan taba mantawa ba.
Kai ne ka hada ni da mahaifiyata, kaine silar cikar farin cikin rayuwata, wanda ban taba tunanin
zan tsinci kaina ba a tun barowata gida…." “akwai wani matsayi da zaki bani Zaynab, daya
wuce na zama mijin ki?” Ya katseni. Na girigza kai “baka gane bana Yaya Qasim, ba zan taba
yin auren soyayya ba…...” Idanuwansa sunyi nauyi sosai, da kyar yake iya bude su yace "….well-well, sai wane iri?
Kodayake na gane; you are a multi-millonnaire, waiting for a billonnaire like you…. (ke miloniya
ce, kina jiran biloniya dan uwanki), haka ne ko ba haka ne ba?”
Ya tsatstsreni da idanunwasa da suka kada suka yi jawur. Na soma tababar ko Qassim ya sha
kayan maye ne? Kai, babu kama, tunda nake a gidan su ko taba, sigari, ban taBa ganinshi da
ita ba. Kenan soyayyar dake idanunshi ta bugar da shi babu mamaki.
Na fita daga motar na barshi nan, na jingina da sassalkar motar cike da tunanin
al'amuran rayuwa. Na mika tunanina ga kalamin Qassim, eh, nima na yarda a yanzun kam
(billonnaire) ce. Ko daga motocin da aka mallakamin makullansu, ba'a maganar abin banza
sarkokin (Gold). Duwarwatsun ado na Diamond (farin yakutu), emerald (jan yakutu), sapphire
(shudin yakutu) da ni kaina bansan adadin su ba.
Inada gidaje guda biyu nawa na kaina cikin birnin Paris da Singapore, (inda harkokon Nuratu
suka fi yawa) da makeken shagon sayar da turarurruka ‘designers’ nawa na kaina shima a
Paris, ba’a maganar (estate) guda cikin Damagaram da makeken gida a unguwar plateux
(Niamey), banda kananun abubuwa watau hannun jari na bankuna. To amma Qassim ya manta
cewa duk wannan dukiyar shi ya fini GIRMA?
Ya fini gata, ya fini daukaka ya fini komai. Ko babu komi tsarkakakken asali shine komai, amma
duk wannan agareni aikin banza ne. Ko na daga ido na dube su nayi farin-ciki, tunani daya
zanyi ya sani dakacen…. inama ba'a haifeni ba.
Wannan ciwo ne da har abada ba zai gushe daga zuciya ba, sai karfafa Imani kadai.
Ban taba tunanin yin tutiya da dukiyar Nuratu ba. A tunanina da ni da shi duk daya ne a gareta,
tunda tare na gansu.
Shi kansa ya lura zancensa ya taBa zuciyata, don haka ya fito ba tare da ya kara magana ba.
Muka jera tare cikin (reception) kai kace wasu zarah ne cikin taurari, muna matukar kama, mun
kuma yi bala'in dacewa da juna, sai dai zuciyar kowanne babu dadi.
Sai da naga dagawarsu na juya muka komo gida. Ina dakin da ya zamo nawa ina rage
nauyin kayan dake jikina. Ta shigo niki-niki da butar shayi da 'yan kananun kofuna irin nasu,
nayi hanzarin karBarta na ja kankanin teburin gilashi na aza, ta zauna akan ‘stool’ ta zuba tana
firfitawa, ta kurBa a bakinta taji zafin yayi dai-dai yadda take so, sannan ta miko min. Raina a
jagule yake, duk da haka na daure na amsa na kai baki na. Dacin shayin yayi min dadi, zafinsa
ya ratsa har cikin hanjina, na samu relief daga bacin ran da na samu kaina aciki babu gaira
babu dalili.
Idanunta masu kaifi a kaina tace "me ya dadar dake haka? Kun biya wani wajen ne kamin ku je
(airport) din?”
Na yi murmushi, tuni na gano tsabar tsoron, dake cikin kyawawan idanunta. Amma sai na yi
kamar ban gane ba, ina kurbar shayin ina kallonta ina murmushi nace “ina kuwa zamu je bayan
can din?”
Ta dan saki fuskarta ta ce "ko nan gaba, kada ya kuma cewa ki zo ki raka shi wani waje ki
kwashi jiki ki bishi, duk wata rakiya ayi ta iyaka bakin gate….,” nace “to Nurtu….” Karaf, a
kunnen Yadudu dake shigowa, ta dauki kofin shayi daya ta muka min a tsakiyar kaina ta ce "ba
zaki daina kiran Nuratun nan ba?” Na dafe kaina ina dariya, ita kuwa ta mike tana hada kan kofunan shayinta ko a jikinta, tace da
Yadudu “rannan ma cewa ta yi wai Nuratu Mainasara, yaushe zamu je wajen Haiti?”
Yadudu sai muka koma bata dariya. Don ta lura itama Mamin, ta fi son Nuratun da nake kiranta
da shi.
*** *** ***
Mun sauka a Singapore, da sanyin asubahin safiyar litinin. Nade nake cikin jar liffayar
Mouritania mai ratsin fari. Takalmina mai tsayi ne sosai sanan na yi amfani da abin kare hancin
da na fito da shi daga jirgi, na toshe hancina, daga sanyin dake barazanar jawo min mura.
Nuratu na cikin shudiyar liffaya itama, takalminta ‘flat’ ne, don haka da muka jera yau sai
na fita tsaho. Aunty Hibbani da Moiram suma suna tare suna hirar su, sai 'yan sandan ciki mata
guda biyu cikin fararen kaya, dake bin Mamie inda duk ta aje kafarta.
Ta fiddo waya cikin ‘reception’ ta bude ta sanya layinta na kasar ta maida ta rufe ta shiga
lallatsawa, na kwantar da kaina a gefen kafadunta na dama, domin ba karamin gajiya na yi ba.
Sai muka yi wani irin kyau kamar kawa da kawa. Tana magana cikin harshenda ta san ko (alif)
bana ji a ciki, (french). Tun daga fuskarta har cikin zuciyarta cikin nishadi take. Ta dubeni tana cigaba da maganar ta, sannan ta rufe wayar. Ta kai hannunta na dama ta rufe
min ido, ta ce " I 've a green, great, giant surprise for you… what would I 've in return? (Menene
tukuici na?)"
Na ce “karki damu Mamie, fara bani albishir din tukunna, zan baki kyautar turare, bayan shi
kuwa zan kai ki makkahh….” Maganar ta kakare a makoshina. Sakamakon wata 'yar ubansu
mulmulalliyar motar da ban taBa ganin irinta ba, ta yi parking nesa damu kai kace kwai ne. A
kullum malam bature na kara kero motoci, da kusan ba wacce ban gani a (Kangiwa Estate) ba,
amma ban taBa ganin irin wannan ba.
Domin kankantarta ta isa, har nayi tunanin yadda mutum uku zasu iya zama a cikinta.
Glassanta masu duhu ne, amma ba (tinc) ba, domin zaka iya ganin adadin kawunan mutanen
dake cikin motar, saidai banda kamanninsu. Na kuma fahimci mutum biyu ne a ciki.
Gabadaya hankalina ya tafi ga maotar, da son ganin wadanne irin mutane ne zasu fito daga
cikinta? Don haka Nuratu ta zame ta bar ni nan ina kauyancin mota, ta nufi inda su Moiram ke
zaune suna cin gugguru.
Matasa ne guda biyu masu jini a jika, suka bude murafen motar suka fito a tare, dayan ya saya
idanunshi cikin bakaken (dark glasses), ya zaga baryar da dayan yake, suka tsaya suna
Magana, ba tare da ya juyo ba.
Dukkanninsu suna sanye cikin farar shadda dinkin Dakar, da hula zanna-bukar. Ban san abin da
ya dauki hankalina haka kan wadannan matasa ba, tunda ba'a yau na fara ganin kyawawan
maza ba. Karewama ga jar fata nan sunata sha'anin su a harabar ‘airport’ din, amma wadannan
masu duhun, su suka dauki dukkan (attension) dina. Kamar yadda suke cikin shiga daya, to ba haka halittar su take daya ba. Daya dogo ne, siriri
mara kauri, sannan yana da hasken fata, wanda ya hadu da jin dadin rayuwa ya maidashi
kamar wani ‘half-caste’, watau ruwa biyu. Daya mai matsakaicin tsawo, baki kuma kakkaura,
yana sanye da farin (medicated glass) wanda ya zamo (everyday-glasses) a gareshi. Kirjina na
ji ya fara bugawa da sauri-da-sauri, numfahsina ya soma samun tangarda, kafafuna suka soma
kokarin kayas da ni. Gabadaya suka juyo fuskarsu dauke da murmushi. Suka nufoni cikin
sassarfa da takun GIRMA kai kace wasu 'ya'yan saraki ne. Idan har ba karya zuciyata ke gaya
min ba, ba kuma gizo idanuwana ke min ba, to IMARAN ne bakin mai hasken kuma UMAR
FARUQ din Nuratu da Inna Rabi.
To gun wa zani? Yayan ko Faruq din da har yau ban san matsayin da zan kirashi ba? Ko
dai inyi amfani da Kalmar nan ta bature da yace (blood is thicker than water?) In tafi ga dan
uwana da nake nema ruwa a jallo? Kwana da kwanaki wata da watanni? To amma anya
Faruqun ya cancanci hakan? Wani zubin ruwan ya kan fi jinin karfi, koda shi jinin ya fishi kauri. Don haka maimakon haka. Sai
na juya da gudu na kankame Mamie. Nuratu zata kashe ni da ban mamakinta.
Na kasa gasgata abinda idanuna suka gane min. Watakila dai irin mafarke-mafarken nan ne da
bana rabo da su, masu nuna min wai wata rana….,, zamu hadu da Ya Em a inda ban zata ba.
Dariya suka yi suka karaso gaban Mamie, suka zube a kasa suna gaisheta ita kuma sai
kokarin kwakwaleni take a jikinta cike da jin kunya ta ce "wallahi ko ki cikani ko ince su koma
inda suka fito”.
Da gudu na saketa na karasa da gudu na rungume Ya Em, sannan ne wasu irin
hawayen farin ciki, suka zubo mini. Yana sharemin da hankicin sa yace "is o.k Zaynab, ina nan
tare dake, muddin rai, ba zan kuma zuwa ko'ina ba" ya cirani yayi min nuni da Faruq din daya
juya mana baya yana masa waya. Dai-dai lokacin shi kuma ya juyo yana cewa "eh, muna nan
Singapore har shi Imran din, ita Hajiya zasu yi wata sabga ne sai sati mai zuwa.." ya kashe
wayar yana karasowa inda muke. Imran yace "shi Faruq ba za’a gaishe shi ba?”
Na kai hannuna na rufe fuskata ina murmushi, yau wata matsananciyar kunyar Faruq nake
sosai, irin yadda ban taba jin kunyar wani da namiji ba. Yayi kwafa yace “kada ta gaishenin,
kyale yarinyarnan Imran yadda ka ganta, muguwa ce”.
Ko kallona bai yi ba yayi gaba wajen su Mamie. Abin yayi min ciwo kwarai. To amma ganin Ya
Em a yau yasa na soma tunanin babu abinda zai kuma sani bakin-ciki a rayuwata.
Mota ce ta musamman tazo ta debi su Mami, ni kam nace kafata-kafar dan uwana.
Faruq ya harareni, harara sosai ya ce "wannan mota tawa ce, bata dan uwanki ba, babu ko
kwabon shi wajen siya min ita, kuma bana daukar mugaye a cikinta.
Wadanda basu damu da halin da wasu zasu fada a dalilin su ba, kansu kadai suka sani da nasu
farin cikin. So ki nemi mai daukarki a mota, tun wuri, tun dare bai miki ba, ko ki jira in maida dan
uwan naki gida, ya aro mota ya dawo ya daukeki, don shima tsintarsa nayi, a titi, bashi da
komai sai muguwar zuciya irin taki, data kware wajen jefa iyayenku a halin kaka-ni-kayi….”
sakin baki nayi galala! Ina sauraron cin mutunci, amma shi Imran da yake bashi da zuciya ko a
jikinsa, sai dariya yake yana gyada kai kamar kadangaren bakin tulu. Ai ni ko mayyace wallahi
na hakura da motar nan. Ban ankara ba ya ja kayarshi a guje suka yi gaba. Na tabbata da da
kura a wurin, da sun bade ni, mugun badewa kuwa. Sai Allah ya taimakeni duka wajen ‘ceramic’
ne.
Motar su Mamie ce tayi ribas ta dauke ni. Raina ya baci sosai da wannan wulakancin da Faruq
ya yi mani, ban san sanda hawaye suka zubo min ba. Na ce babu komi, indai nice maganin 'yan
maza ce. Wanda ya fika wulakanci ma na ganshi ya dawo, ya zube gwiwoyinsa a kasa da
hawayensa yana rokona gafara. Kai haye kayi ba gada kayi ba. Moiram da karin abin haushi
tace “ya basu daukeki ba?” Hibbani ta ce “sabida batayi wanka ba, ta kwana a jirgi, tana tsami”.
Mamie abin ya bata dariya, don haka ta yi murmushi.
Wani gida ne hawa daya, korran (grass carpet) sun yanyame shi tun daga kofar shiga
har rufin gidan. Karamin gida ne (Flat) babu gate sai kofar shiga gidan. Fasalinsa kamar
kwale-kwale, sannan gefensa (stream) ne mugadanar ruwa yana bulbular da ruwa, garai garai.
Mamie tasa mukulli ta bude muka shiga falon, kowanne ya zube a kujera a gajiye. Gidan a
gyare yake fes, kai kace da mutane a ciki, tuni Moiram ta hau barci. Mamie 'shower’ ta je tayi ta
kwanta a dakin barci bata kara saukowa ba, ni kuwa zugum nayi cikin tagumi. Ina son in
tambayi ina su Ya Im bana son taga gajen hakuri na. Na shiga tunanin inda Faruq ya samo Imran, to ko dama wajensa ya gudo? Dana ga wannan ba
zata kai ni ba, na yi dakin da Mamie ta shiga, tayi nisa cikin barcinta sosai sabida kwanan
zaune da mukai cikin jirgi, na bude jakarta na fiddo wayarta na dawo ‘corridor’ din gidan na
jingina da karfen (balcony) ina fuskantar mugudanar ruwan dake gudana garai-garai da shi
(Spring), na soma laluben sunayen mutanen dake cikin wayar a nutse, har na iso wada ta yi
‘saving’ da wani suna Dan dukusuru, hakanan akwai “Imin Sa’idu”.
Na sha mamaki kwarai, ashe tuntuni Nuratu tasan inda Imran yake? Ko da yake bai
kamata inyi ta bata lokacina wajen mamaki ba, tunda ‘kudi’ sune kare magana. Na kira IMIN
SA'IDU (kamar yadda ta kirashi) tayi ta ‘ringing’ har ta kusan katsewa kamin ya amsa, cikin
tsananin ladabi yace "Yello Mamie, kun huta ne, mu zo?”
Nayi ajiyar zuciya nace “kuna ina ne Ya Im?” Yace “ba zaki kwanta ki huta ba?” Na ce "ni
dai don Allah ka gaya min inda kuke” Yace “muna gidan Faruq, cikin ma’aikatar su (Informatics)”
nace “to ka yi min kwantance in zo” yayi dariya yace “iye, ‘yar gari, zaki bata, kuma ke don baki
da zuciya duk wulakancin da yayi miki yanzunnan sai ki zo gidansa?” Na girigiza kai nace “babu
ramuwar gayya tsakanina da shi” yace “wonderful! Sai da ni Imran ko?” Na lumshe ido ina
dariyar TUNA BAYA…. “kai haba Ya Im, shi Faruq din ne ni kaina nasan ban kyauta masa ba".
Yace "zancen gaskiya Allah-wallahi kika zo korar kare zai yi miki, ranshi a bace yake
dake fiye da tsammaninki"