Showing 39001 words to 42000 words out of 43757 words

Chapter 14 - GIRMA YA FADI 3 Complete Hausa Novels By TAKORI.pdf

mafarki nake ba, zahiri ne". ​ Sai ta share hawayenta ta ce "ni kuma ke nake tausayi. 'Ya mace kike, komi Sa'idu ya yi
nasa ado ne, kece keda kaico!
Duk wanda ya aureki nan gaba sai ya goranta miki. Haka dan cikinki da kyar idan zai yafe miki.
Ki daina cewa kina jin tausayin sa, muddin ina raye, ba zai taBa sanin cewa bani na haife shi
ba".
​ Na fiddo ido na ce "me kike nufi?” Tace “ina nufin ni zan zamo uwarshi. Malam Ali ya
zamo Ubanshi. Idan har su Dubu sun rike wannan amanar. Shi kuwa Sa'idu bar ni da shi, yace
ya taba sanina ma balle abinda kika haifa, sai ya gwammace uwarsa bata haife shi ba, sai ya
gwammace bai taBa sani na ba. Zan nuna masa bakar Rabi, don farar Rabi ya sani". Anan
kuma sai ta koma irin sambatunta na tsinuwa da la'anta Sa'idu, wani zubin kuma sai ta sa kuka.
​ A lokacin Faruq ya fara hankali, domin ya gama aji uku na sakandire. Ya damu da rashin
walwalata da rashin fitowata muje yawo yadda muka saba.
​ Sai yazo dakin mu ya sani gaba yayi tagumi yace "Nuratu na baki da lafiya ne?” Inyi ta
muku-mukun Boye cikina, cikin katon hijabin da nake zurmawa, hawaye ya zubo mani. Yau nice
na zama daddawa, daga daki sai daki, ko baki akayi a uwar daki Rabi ke kulleni, idan an
tambaya ina Nuratu, tace bata nan. Ba’a gaya masa ba, amma shi da kansa ya fuskanci halin
da nake ciki. Jikinsa ya yi sanyi lakwas, ya zama wani zalau, kamar bulala, sai dai ya bude baki
yayi magana ya kasa, sai dai ya yi ta bina da ido.
​ Cikin wannan halin ne a watan July, a wata laraba nakuda ta kamani. Cikin daren nayi
ta murkususu ni kadai, kamin asuba na haifeki. Ko irin kukan da jarirai keyi a yayin da suka iso
duniya, ke baki yi ba, wanda ya sani tunanin watakila kema kina bakin cikin zuwanki duniyar,
kuma har zuwa wannan lokacin babu Sa'idu, babu labarinsa. Sa'a ta janye kayanta tsaf, don ko
'yar wayar da yake yi min fiye da watanni uku ya daina.
​ Yaya Rabi ta daukeki ta yanke maki cibi, idanunta cike da kwalla da bakin cikin da
harshe ba zai iya bayyanawa ba. To amma wata kudura ta Ubangiji, daga ni har ita mun kasa
dauke idon mu a kanki. Wata irin kauna irinta da da mahaifi ke ratsa zuciyar kowannen mu,

kamar mu dake, har ta Baci, kwata-kwata baki yo komi na Sa'idu ba. Gashi yala-yala har ya rufe
idonki, sai da ta dauki sabuwar reza ta rage shi, sannan kika samu kika bude idanunki, farare
kal, kika kuwa tsayar da su a kaina.
Hankalina ya tashi, tsoron ranar da zaki sake tsareni da wadannan idanun, ki tambayeni dalilin
gurbata maki asali da nayi, shine ya gigita ni, wanda ni kaina ban san amsar da zan baki ba.
Hakannan bana jin zan iya kara hada ido da mutanen dake cikin gidannan, musamman Inna
Dubu, Malam Ali da kanina, Faruq. Wace irin tambaya zai min idan ya ganni rungume da jariri,
alhalin ya san bani da aure? Me zan yi in wanke bakin cikina da zai sameki, idan kika fara
hankali? Tambayoyin suna da yawa, wadanda suka gigitani, har na fara tunanin guduwa, in da
ni kaina ban sani ba, ba don komai ba sai don tserar da mutuncina da naki, wanda na tabbata
furucin da Yaya Rabi tayi, na maisheki diyar cikin ta, ba zai yiwu bw in har ina nan.
Domin kauna ta da da mahaifi ta wuce misali, ta kuma wuce duk wani bad-da kama da za'a yi a
Boyeta, na kuma tabbata Rabi zata kula da ke, fiye da yadda ni zan iya sakin jikina in yi hakan.
Uwa-uba ina neman yadda zan yi inyi nisa da Sa'idu, nisan da har abada ba zai taBa sanin in
da nake ba. Ban san dalili ba, amma na tsani Sa'idu, ko sunansa ba na son ji. Ko mai irin kamanninsa bana
fatan sake gani a rayuwata, balle wata mu'amala ta hada mu. Ban taba sanin soyayya na
komawa kiyayya ba, sai a kaina da Sa'idu. Allah kuma shine masanin wannan sirrin.
​ Cikin duku-duku asubahin dai Yaya Rabi taje ta taso Dubu, ta zo ta daukeki tana share
min hawaye tana istigfari. Ta je ta taso Malam shima ya zo jikinsa babu inda baya rawa, abinda
ya fara yi bayan lakanta maki kalmar shahadah, shine ne tofa miki addu'ar kariya daga zina a
al'uararki. Ya kuma ce Allah yasa ke cikon addinin musulunci ce. Ya kuma dauke ki a matsayin
wata kyauta gareshi daga Allah (S.W.T), saboda duk 'ya'yan da ya haifa mutuwa suke, Faruq
kadai ya tsaya. A lokacin ne yayi maki huduba da Nana Zaynab. Ya kuma kiraki ‘Kyauta’.
​ Dubu ta je ta dora ruwan zafi a murhu don yi min wanka. Malam ya tafi masallaci don bin
jam'in sallar asubahi, a daki kuma Rabi ta shiga ban daki domin gabatar da alwalar sallar
asubahi. Na daukeki na rungume a jikina tsan-tsan, hawayen dake ambaliya a kuncina na jika
taki fuskar, na kuma kura maki ido, kurr! Sai dai a raina nasan ba kallon karshe nake miki ba, ko
ba dade ko ba jima nasan zaki bi ni, duk inda nake, in har ni na haife ki, in kuma muna raye.
​ Maganar kulawa kuma bani da kaico akanki, inada yakinin zaki samu kulawa ta uwa da
uba da dan uwa, irin wanda in ina nan, ba zaki sameta ba. Don haka nayi gaggawar ajiyeki, ina
da kudi masu yawa ire-iren wadanda Sa'idu ke bani in zai koma, ba kuma abinda nake yi da su,
don haka na kwaso su na zuba a jaka. Duk ciwon dake jikina, rashin karfi da jirin dake kwasana,
amma a haka na dafa bango na yafa mayafi na fito.
Dubu na daga can madafi, ta durkusa tana ta hura wuta a murhu idanunta sai tsiyaya suke abin
tausayi, da gani irin azababben utacennan ne Allah ya hadata da shi, nayi sanda na wuce
zaure, malam bai rufe kofar ba bayan fitarsa masallaci, don haka ban wani Bata lokaci ba wajen
ficewa. Almajiran Malam duk suna cikin shagon su, wasu kuma suna kwankwance suna barci a harabar
gidan, yayin da masu hankalin sun bi malam masallaci. Sai bayan da na danyi tafiya ne na
fuskanci jini yana zuba a jikina. Don haka nasha kwana a wani lungu da babu kowa, na sunto
dankwalina nayi kunzugu dashi sannan na cigaba da tafiya ko gani bana yi sosai. Ban dauki hanyar tasha ba don nasan can ne waje na farko da Malam zai sa a fara bi na. Na

rika bin gefen titin fita garin Gwarzo bana ko waiwaye. Na yi tafiya a kalla (kilo mita uku da rabi)
kafin in ji wata mota ta makeni akan kwalta. Saboda jinin da ke kwasata, ban san cewa a
tsakiyar titi nake tafiya ba.

***​​ ***​​ ***
​ Na bude ido ne na ganni kwance a gadon asibiti, ana yi min karin jini. Domin na zubar
da jini da yawa. Hannuna na dama daure cikin bandeji, gwiwoyina da wasu bangarori na jikina
duk sun kukkuje. Daga baya ne likita ya shigo yake gaya min na samu karaya ne har biyu a
hannuna na dama, sai 'yan kujewa da ba'a rasa ba, sannan ya fadi abinda yayi matukar bani
mamaki, wai mijina daya kawoni ya tafi gida, yana dawowa zuwa karfe shida na yamma. A
lokacin kuma hudu ta yi har da mintuna ashirin.
​ Ya sake kallona sosai, ya ce ina "Baby din naki? Ai zaki iya zama tare da shi anan
gadon asibiti, ko don kada nonon ki yayi ciwo. Idan yazo kice yana iya dauko miki shi" na bishi
da “to" kawai.
​ Na lumshe ido a hankali, in saka wannan in kwance wannan. Ni Nuratu kuma kaddarorin
da Allah ya dora min ke nan? Na tabbatarwa kaina ba zan zauna har sai na warke a sibitin nan
ba, koma yaya ne, ina bukatar yin nisa da Kano. Nan kuwa nasan ba zai wuce Kano din ba, don
kuwa itace mafi kusa da Gwarzo. Na kai dubana ga mamana da suka cika tam. Suna shirin fara zuba, wani gululu yazo ya
tokareni kamin in balle da kuka. Kuka sosai wanda ba zai wanke radadin dake raina ba, ba zai
wanke tausayinki da tausayin halin dana baroki ciki ba, ba zai wanke takaicin rabuwata da 'yar
uwata ba, da muka taso tare tun zuwana duniya, ba zai wanke tunanin masifar dana jawo mata,
na gudu na barta da shi ba, ba zai wanke radadi da kulafucin uwa ga danta, dake narkar da
zuciyata ba.
​ Misalin karfe shidda na yamma, aka turo kofar aka shigo. Wankan tarwada ne
makimanci ga shekaru arba'in. Yana da tsagin barebari biyu-biyu a kuncinsa, mutum ne mai
cikar kwarjini da kamala. Akwai alamun tsoron Allah a tare da shi, rashin son wasa ta ko’ina,
yanayin sutturarsa, agogon dake daure a hannunsa, da irin takalminsa mai walkiya da sheik, ya
nuna ba karamin mutum bane. Wasu mutun biyu ne a bayansa, ga alama daya ‘escourt’ ne
dayan kuma direba, rike direban yake da kaya niki-niki cikin kwali, da ledoji abincin (city
sweats), ya daura bisa lokar dake jikin gadona, yayin da mai tsaron lafiyar tasa ya ja masa
kujerar dake fuskantar gadon da nike kwance, suka juya suka fita.
Yafi mintuna uku bai ce min komai ba, da alamunsa ni yake son in fara yi masa magana. A
raina nace amma zaka kwana anan, ka kade ni da mota sannan ka yi min iko?
Ko tunani ya yi bai kyauta ba, sai ya ce "Sannu da jiki ko?” Na amsa da ka, ya sake cewa "Garin
yaya kike tafiya a tsakiyar titi, kuma da sanyin asubahi ke kadai, alhalin kina mace, wadda bata
yi mun kama da mai taBin kwakwalwa ba?” Nace "Eh, lafiya ta dalau, yanayin rayuwa ne yasa
hakan”. Yayi murmushi, cikin sanyin murya kuma ya ce "kiyi hakuri, Im not here to interfere (bana zo
don na inyi miki shishshigi bane), kawai dai nayi mamaki ne. Ko zaki daure ki gaya min wurin
aikin mijinki, in je in zo da shi domin anan na yi musu karyar nine mijinki, kuma ni na kadeki a
bias rashin sani a kofar gidan mu, don kurum su karBeki ba tare da sun Bata mana lokaci ba.
Ba yadda direbana bai yi ba don ya kauce miki, kina kara shan gabansa, karshe dole motar ta

shafeki, sun gaya miki kin samu karaya a hannu ko?” Na gyada masa kai, ya ce "to a ina za'a
samu mijin naki, ko can kauyen zan koma in bincika?” Ban san sanda na muskuta ba, hannuna
ya amsa, azabar har cikin kwakwalwata, har kuma yatsar kafata amma na cije leBBana nace
"bani da aure". ​ Ya zuba min ido curiously (cike da son sanin abubuwa da yawa da suka shafe ni) ya ce
“sunana Kabir BADEGGI. Iam politician (watau dan siyasa ne). Ni mutumin Nijar ne, amma na
girma a Maiduguri, hannun gyatuma ta, saidai a yanzu haka da girma ya hauni, na koma
mahaifata ina tafiyar da harkar siyasata a can. Kina yi min kama da wasu mutane acan na
kwarai dana sani, nake kuma tare da su.
Ki daure ki dubi girman Allah, ki gaya min gaskiyar inda kika fito, in sadaki da iyayenki. In ma
wata matsala ta fito dake, ni na yi alkawarin zan tsaya maki. Ba zan barki ki fada a lalataccen
hannu ba, hannu da hannu zan danka ki ga iyayenki, ki yarda dani".
​ Na runtse ido cikin tababar in yarda dashi din ne ko a’ah? Bai yi min kama da mutumin
banza ba, bai yi min kama da makaryaci ba, haka bai yi min kama da mayaudara irin SA'IDU
ba. Magana yake daga fatar bakinsa, har zuciyarsa, haka idanunwasa na tabbatar da abinda ke
fita bakinsa. Har da mulmulen sallah a goshinsa, abin nan da ake kira "sujjadah". Shi ba wani
kyakkyawa bane, kawai kamili ne, da babu alamun wasa da yaudara cikin al'amarinsa”.
​ Ta yi murmushi, nima murmushin nayi. Don sanin ko wa take nufi. Amma can a
karkashin zuciyata ina KISHI, da nake kalubalantar zuciyata mai cewa BABANA SA'IDU nake
tayawa.
​ "Kabir Badeggi kenan. Wanda zuciyata ta aminta da shi a lokacin daya. Naji ya kwanta
min tun bai furta wata kalma mai nufin soyayya a gareni ba. SaBanin Sa'idu da yayi amfani da
wayewar shi, wayonshi da kyawun halittarshi ya saye soyayyata. Hakannan na jishi da wani
GIRMA a idanuna, ta yadda nake jin har ba zan iya bude su gaba daya in dubeshi ba. Ban san sanda furucin ya suButo daga bakina ba, na samu kaina da cewa cikin rada, sannan
idanuna a rufe "Nima ai asali na 'yar Nijar ce".
​ Yayi murmushi yace "what a coincedence! Nijer, a wace Jiha?” Na ce "Damagaram" ya
yi dan dumm! Yana kallona da dukkan fararen idanunsa, yace "Damagaran, ikon Allah, ina
yawan zuwa wajen aminina Shettima, yaya sunan ki?" Na sake runtse ido sosai, saboda yadda
sanyin muryarsa ke kassara gabban jikina, na ce cikin rashin kuzari. ​ "Nuratu Mainasara".
​ Jawo kujerarshi yayi gabana, yana kallona sosai kamar ya cinye ni, ya kai hannu ya zare
hular zanna dake kansa yace "kina nufin ke, jinin KANGIWA ce, kuma kanwa ga Shettima
Mainasara?”
Na bude hakorana duka ina dariya, jin wani ya ambato min wani suna daga cikin sunayen da
nike matukar girmamawa, dana dade ban ji ba, shekaru masu yawa nace "a’ah Baba Shettima
Baba ne a gareni. Shine dan autan su mahaifin mu".
​ Yace "Nuratu ke kamar kanwace a gareni. Akwai mutunci da harkar neman abinci sosai
tsakanina da Babanninki. Don haka ba sai kin warke ba zan sayo mana tikitin Yamai, in danka ki
ga Iyayenki duk da ban san abinda ya fito da ke ba, sannna in komo in tafi inda da nayi niyyar
zuwa kika hanani. Amma don Allah kiyi alfarma gareni, ki gaya min me ya kawo ki dajin dana ganki? Me ya kawoki
Nijeriya?" Gaba daya fuskata sai ta sauya, da wani irin lulluBaBBen Bacin ran da shi kanshi sai

da ya fuskanci hakan. Ya yi saurin gyara zancen sa da cewa "kodayake ‘this may be your
personal issue, am sorry, very sorry" na yi murmushi kadan, ganin yadda ya damu sosai da
damuwata.
​ Ban san bayanin da ya yiwa likitocin ba. Washegari ya dawo ya kira Nurse ta
taimakamin na shirya, bayan ya bata wani bakar leda shake da kaya. Na sha mamaki da naga
har da su (always pad) kodayake hatta gadona Bace yake da jinni, duk da kunzugun dankwalin
dake jikina. Ta hada min ruwan zafi mai matukar zafi ta yi mun wanka, bayan ta zaunar dani sosai a cikin
ruwa zafin don ta lura haihuwa nayi, tana yi min tambayoyi game da Babyna nace bakwaini ne,
an sanya shi cikin (incubator). Ta hada min shayi mai kauri sosai, ta kuma hadani da
gashashshiyar kazar (Capetano) daya kawo cikin plate ta badeshi da yajin daddawa tace in ci
sosai, don mijina ya gaya mata doguwar tafiya zamuyi zuwa Jamhuriyyar Nijer.
​ Cikin kayan daya kawo ta fidda min sabuwar doguwar riga dal daga cikin ledarta, irin
wadanda ake kawowa daga Dubai da mayafin su, kalar su toka-toka (ash) har da sabbin
(panties) duk sai naji ina jin kunyar hada ido da shi kuma. Ita kuwa ko a jikinta, aikinta kawai
take sai cewa take maza sanya mana, yana jiranki a mota. Da ganin irin kulawar da take min na
jinjinawa asibitin. Don hakane dana fito na daga kai na ga ‘sign board’ mai dauke da sunan
asibitin, an rubuta PREMIER CLINIC. Sai na ce a raina ashe ba'a banza take yi ba.
​ Haka ta kama hannuna har gaban motar. Direbansa da ‘escourt’ dinsa suna gaba, ni da
shi muna baya. A sannan ne wata nutsuwa tazo min, sanyin A/C dana dade ban ji ba ya ratsani.
Na lumshe ido na rausayar da kai gefe muna hira jefi- jefi akan su Baba Aliyu, har muka zo
Airport din Aminu Kano, inda kai tsaye muka hau jirgin da zai kaimu Niamey. Zuciyata cunkushe da tunanin fuskar da zan fuskanci dangina da ita, sai da zuciyar ta yi
amanna da in fadawa Yadudu gaskiyar abinda ya rabo ni da gidan Ya Rabi. Da kuma dalilinmu
na kin neman su alhalin mun san inda suke, wannan kam ni kaina bani da masaniya akai,
nasan dai Malam Ali yana addu'a sosai a kanmu, wadda tasa ko sunan dangin mu bama
tunawa. Gara ma ni wani lokacin nakan tuno Yadudu, amma Ya Rabi ko zancen kasar Nijer bata
son ta ji anyi a gabanta.
​ Tun a filin jirgi yayi wa Baffa Aliyu waya yace gashi nan tare da diyarsu Nuratu. Baffa ya
ce "wace Nuratun? Ba dai 'yar Yaya Sani mai rasuwa ba?” Ya ce ita dai, shima Allah ne ya
hadasu, yayi-yayi kuma na ga fada masa daga inda na fito na ki. Don haka kafin minti goma sha
biyar filin jirgin saman (Mano-Dayak) ya cika taf, da motocin, iyalin Mainasara. Na hangesu
kwansu da kwarkwatarsu KANGIWA FAMILY, maza da mata, tsofaffi da 'yan mata. A tsakiyar su
na hango tsohuwa Yadudu, ta kara tsufa kwarai da gaske fiye da yadda na barta. Amma kayan
alfarma ne a jikinta. Na karasa da gudu muka rungume juna muna ta kuka. Ta ce "Nuratu ashe
Allah yayi zan kara ganinki ina raye? Ina 'yar uwarki, me yasa bata taho tare dake ba?” Nace
“labarin mai tsawo ne Yadudu, muje gida tukunna".
A babban falon Baffa Aliyu cikin unguwar nan muka hadu, aka sallami yara-yaran irin su
Qassim, lokacin Hibbani tana budurwa kamar ni. Ina kuka na fede musu biri har bindi, tun auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login