Showing 1 words to 3000 words out of 46825 words
Chapter 1 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
[1/26, 10:59 PM] Matar Malam: í ½í²«
*41&42*
Shigowar mahaifyarta d'akin ne ya katse tunaninta, cikin mutuwar jiki ta tashi zaune ta tana
kallonta har ta k'araso ta zaune gefen gado babu walwala a fuskarta.
A d'an raunane tace."Mamnah barka dare." Tana nazarinta ta amsa da fadin." Barka dai me
yake damunki ne baki fito kin ci abinci ba."? Kamar me jiran kiris sai kawai ta fara share
hawaye murya a sarke tace."Mammah ya za'ayi na iya cin abinci a irin wannan halin, gabadaya
kun kasa fahintata kuna nema ku jefa rayuwata a cikin masifa, yanzu tsakani da Allah a gidan
nan wa aka ta'ba yiwa auran dole acikin 'yan uwana, kowacce fa wanda takeso aka aura mata
amma ni an d'auke ni kyauta an bawa wani wanda bashi da cikakken asali wallahi ba'ayi min
adalci ba."
Ta dinga kallonta tana tunano wani lamari daya shud'e shekaru masu yawa, Ajiyar zuciya ta
sauke kafin tace." Yanzu Ke a ganinki hakan da akayi miki rashin adalci ne." ? shuru tayi ba
tace komai ba, ta cigaba da cewa." Ke ba kiji kunyar fadin wannan maganar ba? shin wai to ya
kike so ayi miki da har kike fadin ba'ayi miki adalci ba, ai na dauka sai da aka baki lokaci
domin fita hakkinki me yasa baki fitar da mijin aure ba, ko kuma kin fiso kiyi ta zama a haka
babu aure mutane na zarginki."?
Girgiza kai tayi da fadin" Mammah sati biyu yayi kadan, har yaushe na dawo na samu nutsuwa
komai fa yana bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali, amma sai kawai a yanke min hukuncin da
bai cancanta ba, gaskiya ni ba'ayi min adalci ba don banga abunda zanyi da wannan ba'kauyen
mutumin ba."
Murmushi mai ciwo tayi kafin tace." Wannan ba'kauyen da ki ka raina shine marufar asirinki
domin a halin yanzu idan bashi din ba babu wanda zai aureki ki samu zaman lafiya saboda
haka ki kiyaye ni wallahi, kada na kara jin kin furta wata mummunar kalma akan wannan
al'amari, idan ban da butulci ma irin naki wannan yaron ai bai cancanci haka daga gurinki ba."
Hawaye ta goge da fadin." Ni dai kawai bana son shi ne ko kadan a raina domin ba tsaran
aura ne bane, amma shikkenan tunda kun gaji da zama dani zan aure shi kamar yanda kuke so
sai duk abunda ya biyo baya kada kuyi kuka dani."
Cike da mamaki! take kallonta kafin tace." Zaki caka masa wuka ya mutu kenan."?
Girgixa kai tayi tana share hawayen dake zuba a saman fuskarta.
Taja dogon tsaki da fadin "Karshen k'iyayye dai ki caka masa wuka a mak'oshi! ko kuma ki
zuba masa guba a abinci ya mutu! to idan baki fasa aikata daya daga cikin wannan ba bakya
kaunar Allah da Annabi, wallahi ki ka kashe shi kema sai an kashe ki! kina ta'kamar gata ko?
ubanki yana da kudi da mulki idan kin kashe rai yana da abunda zai fanshe ki, to bari kiji
wallahi nayi miki rantsuwa da Allah ki ka kashe rai! sai na tsaya kai da fata kema kin fuskanci
hukunci dai-dai da abunda ki ka aikata! idan wannan ne kud'irinki akan UMARU to kada ki
fasa."
Tana gama k'are maganar ta tashi ta fita daga dakin ranta a b'ace! al'amarin yarinyar yanzu
tsoro yake bata, dole ta tsananta da addua akan al'amarin.
Bayan fitar ta daga dakin komawa tayi ta kwanta hawaye na bin gefen fuskarta, ita ba nufin ta
kenan ba, kawai ta fadi abinda yake cikin zuciyarta ne, bata fatan kashe kiyashi ballantana
wani dan adam.
Bacci rabi da rabi tayi saboda tsabar damuwa.
Da asubar fari ta kira wayar Asp dama duk tana da numbers su. A lokacin data kira wayar
dawowarsa kenan daga massallaci, ganin sabuwar number besa shi mamaki ba, wayar yasa a
kunnansa da sallama a bakinsa.
Murya a dashe ta amsa kafin ta gaisheshi.
Sai ya shiga tunanin inda ya san muryar don dashewar ta sanya ya kasa tantance muryarta.
"Wacece ne bangane mai magana ba."?
Hanci taja ta dan sake bude muryar da fadin." ZINAT ce."
Gabansa ya fadi kadan, yace." Zinatu kece ashe ina fatan dai lafiya."?
"Numfashi ta sauke kafin tace."Ai kai ma tunda kaga wannan kiran kasan ba lafiya ba."
Tafad'a cikin dusashewar murya.
Lokaci guda ya harbo jirgin, gefen gado ya zaune da wayar a makale a kunnansa yace." To
menene kiyi min bayani Ina jinki."
"Asp me yasa za'a hada baki da kai a cuci rayuwata."? cikin sigar tuhuma take tambayarsa
Yace." Bangane maganarki ba." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Ba zaka gane ba tunda
bakinku daya amma ina so ka sheda masa cewa ni ba tsaran auransa bace idan yana farin ciki
da dariya to ya dena domin aure na zai zame masa tashin hankali."
Da sauri yace."Subahanallahi! Zinatu duk me ya janyo wannan maganar."?
Tayi saurin tare shi da fadin."Ni dai sako na baka, ka fada masa cewa bakin rijiya ba gurin
wasan makaho bane."
Maganar sai ta bashi dariya, ya d'an dara kafin yace." Aa ni wannan maganar bana cikinta
amma bari na baki number sa sai ki fada masa baki da baki."
Tace."Ai ba tsoronsa nake ba turo min number. " Yace."Yanzu kuwa.'' Kashe wayar yayi yana
mamakin al'amarin, gaskiya akwai matsala babba.
Kafin ya tura mata number sai da ya kira shi ya sheda masa abunda ke faruwa yace." Don
Allah kada ki biye mata ku lalace gabadaya na fahimci rarrashi take bukata, ka rarrasheta kada
ka kara mata wani takaicin."
Dariya kawai yayi kafin ya amsa masa da "to shikkenan zanyi yanda kace din." Yaji dadin
hakan sosai domin shi haka kawai yake so yaga tabbatuwar auran.
Yana tsaka da shiryawa ta kira wayar, da yake Asp ya bashi numberta koda ya duba yaga itace
sai ya share yaki dagawa.
Sai da ta kira sau uku sannan ya daga babu wargi yayi sallama.
Ba tare da ta amsa ba cikin gadara da fitsara! tace. Kana jina ko."?
Shuru bece komai ba, taja dogon tsaki! da fadin." Nasan a halin yanzu kana nan cikin murna da
farin ciki da samun abunda ba kayi tsammani ba, to bari kaji wani abu farin cikin ka zai zama
bakin ciki! haka zalika dariyarka zata zama kuka domin daga ranar da akace an d'aura mana
aure zaka gane cewa kayi tsaurin ido! na bawa abokinka sako yace sai da ya bani number ka,
nace ya bani domin bana tsoron sheda maka abunda yake zuciyata."
Ta'kare maganar tana numfarfashi!
A nutse yace." Kin san macen da ake kira da (Matar ladan noma."?) shuru tayi tana nazarin
sunan.
Yace."Tunda baki gane ba bari na ganar dake, mahaifinki ya bani kyautarki sadaki kawai zan
bayar, ban ta'ba jin sonki a raina ba, domin baki ma da abinda zaki ja ra'ayi na, ina da wacce
nakeso yarinya mai kyau mai hankali nutsuwa da tarbiya ke kam (Matar ladan noma ce) banyi
noma ba, amma taimakon da nayi miki yasa mahaifinki ya bani ke ni kuma na kar'ba saboda
kada na watsa masa k'asa a ido, zan zauna zaman aure dake ba don ina sonki ba."ya kare
maganar hankalinsa kwance.
Bakinta ne ya mutu murus! bata tsammaci ya iya cin mutunci haka ba, ta kasa ce masa komai
sai wata irin zazzafar ajiyar zuciya da take sauke masa a kunne.
Cikin rashin damuwa Yace."Zan kashe waya idan baki da magana."
Da 'kayar ta iya danne kukan bakin cikin da yake kokarin kufce mata tace." K'azami bagidaje
ba'kauye kawai."!
Tayi saurin kashe wayar ta jefar saman gado, zaman 'yan bori tayi kasan kafet taci kukanta ta
koshi. kalmar ce kawai take mata amsa kuwwa a kunne *Matar ladan noma!* lallai in baki ya
san abinda zai fada to be san abunda za'a mayar masa ba.
Sam maganganunta basu bata masa rai ba, hankalinsa a kwance ya cigaba da
shirye-shiryensa, besa damuwarta a ransa ba tunda ya riga ya san dole hakan zata faru,
yasan cewa akwai jan aiki a gabansa, amma hakan be daga masa hankali ba ya riga ya shirya
ya kuma tanadi hanyoyin da zai bi cikin ruwan sanyi yayi maganinta.
***
Tafi sati biyu tana jinyar kanta, tare da bakin cikin ba'kaken maganganunsa! duk sanda zata
tuna sunan daya kira ta dashi sai tayi kukan takaici (Matar ladan noma) wannan sunan yakan
sanya duk wani alkadari nata ya karye duk shirin da tayi a kansa daga zarar ta tuna cin
mutuncinsa sai jikinta ya mutu! gabadaya ta rasa yanda za tayi da rayuwarta gashi ta kasa
gane kan mahaifiyarta fushi take da ita sosai! hakan ya k'ara daga mata hankali mutuka, dole
haka ta sanyawa zuciyarta dangana ta aro walwala da farin cikin tasa a cikin ranta ta nuna
sadudarta a zahiri. sannan har dakinta taje ta nemi afuwarta akan furucin da tayi a kwanakin da
suka wuce.
Ganin yanda ta saki ranta tana walwala da farin ciki sai itama ta sakar mata fuska ta fara janta
a jiki tana yi mata nasiha tare da nuna mata yanda rayuwa take gefe guda kuma tana gyara
mata jiki da magungunan mata masu kyau da inganci.
Hakuri kawai tayi ta daure zuciyarta take amfani da kayan matan, duk dan ta nuna mata
cewa ta hakura da auran kuma babu wani mummunan kudiri a cikin zuciyarta. .........Hakan da
tayi sai tasa 'Yan uwanta farin ciki dama kullum adduarsu Allah ya shiryi ta ta gane hanya
me kyau.
Tun ranar data kira shi a waya yaci mutuncinta bata sake kuskuran 'kara kiran sa ba saboda
tana gudun ya kuma dan'kara mata wata mummunar maganar.
A nasa bangaran shima be tsammanci kiran nata ba harkokin gabansa kawai yake, ya manta
da ita da lamarinta, shirye-shiryen tafiyarsa training yake, sai dai be manta da adadin kwanakin
da suka rage a d'aura auran ba.
A daran ranar da zai tafi suke tattauna maganar da Asp yace." UMARU tafiyarka training ba
zata hana faruwar komai ba, meye amfanin abotarmu ni zan tsaya maka akan komai kuma
zan wakilce ka, sannan kuma ni ne zan bada sadaki domin a gabatar da komai anyi hakan ba
daya ba kuma sau biyu rashin hallatarka d'aurin auran ba zai hana ace aure be d'auru ba,
saboda haka ka kwantar da hankalinsa insha Allah sai dai kawai ka dawo ka samu amaryarka
na jiranka." Cikin zolaya ya 'kare maganar.
Murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya Yace." Nagode sosai mutumina Allah ya saka da
alkairi ya kuma bar abota da amana."
Ya amsa da ''Ameen ya Allah amma yana da kyau kafin ka tafi ka shedawa mahaifin yarinyar
halin da ake ciki koda ta waya ne."
Yace."Eh dama ina da tunanin hakan, a daran nan zan kira shi mu tattauna maganar."
Ya bashi hannu da fadin."Hakan yayi Allah yasa ayi sa'a." Ya amsa da ameen ya Allah abokina.
To koda ya shedawa Maimartaba Omar halin da ake ciki sai shima ya nuna masa cewa hakan
ba wani abu bane, kamar yanda Asp din ya tabbatar masa da cewa ana yin hakan ba matsala
bace mutukar akwai wakilinsa shikkenan magana takare, ya kuma karfafa masa gwiwa tare dayi
masa kyawawan adduo'i. Cikin mutunci da karamci sukayi sallama da juna...........Mutunci da dattakon dattijon yana
mutukar burgeshi wannan dalilin ne kadai yasa har ya amince da auran yarinyar, tabbas da
babu wannan bega dalilin da zai sashi auran mace mara nutsuwa da tarbiya irinta ba.
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[1/27, 5:10 PM] Matar Malam: *43&44*
*GSR*
A daran ranar dai zai yi tafin ya samu Uwale da maganar domin su tattauna, ya sheda mata
duk abunda yake faruwa ya kuma tabbatar mata da cewa halin da ake ciki a yanzu saura sati
biyu kacal a daura auran, saboda haka ta shedawa duk wanda ya dace acikin 'yan uwa da
abokan arziki.........Sosai tayi farin ciki da al'amarin dama shi aure lokaci ne gashi lokacin da
ba suyi tsammani ba Allah ya nufa , sai dai kuma bata bar shi ya tashi ba sai da tayi masa
maganar Hamra'u da yanda za'ayi da al'amarinta.
Yace."Uwale Hamra'u itace za'bi na kuma har yanzu ina sonta, aure na da wannan yarinyar ba
zai hana na aureta ba, wannan auran yazo min bagatatan cikin rashin shiri, insha Allahu itama
zan aure ta idan na samu nutsuwar da nake bukata.
Ta kalleshi da fadin." UMARU idan fa baka auri yarinyar nan ba ka yaudareta sai Allah yayi
mata sakayya domin dai kai kanka kasan tuntuni kai take jira kuma da bakinka kayi mata
alkawarin aure kasan dole idan ta samu wannan labarin ta shiga damuwa tare da iyayenta don
Allah kada ka bani kunya UMARU kada ka raba zumuncin da yake tsakanina da mahaifin
yarinyar nan."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Uwale kin san fa komai nufi ne na Allah, mutum kan iya
tsara rayuwarsa amma Allah sai ya sauya masa, mahaifin yarinyar nan yafi karfin komai a
gurina dalilin kenan da yasa na karbi kyautar da yayi min, na kuma fada miki cewa hakan ba
yana nufin na janye auran Hamra'u ba, zan aure ta da yardar Allah saboda haka ki kwantar da
hankalinki itama yarinyar ki taushi zuciyarta."
Tace."To shikkenan UMARU Allah ya tabbatar da alkairi amma kafin ka tafi ka samu yarinyar ka
sheda mata abunda yake faruwa kamar yanda kayi min bayani."
Agogon dake hannunsa ya duba, sha d'aya shaura na dare, yace." Ban 'ki maganarki ba, zan
sameta mu tattauna maganar ko ba yanzu ba tunda yanzu dai dare yayi watakila tayi bacci."
Tace." To shikkenan Allah ya kai ka lafiya ya kuma dawo da kai lafiya." Ya amsa da "Ameen ya
Allah." Sallama yayi mata ya nufi wajensa.
Da Asubah bayan sun fito daga massalaci suka tsaya suna sake tattauna maganar, Asp din
yace."Naga tunda aka fara maganar auran nan ba kayi maganar lefe da sauran abubuwan
bukata ba, kasan yarinyar nan fa 'yar rigima ce yana da kyau a rarrasheta ta wannan hanyoyin.
Yace."Asp ban san me yasa kake jin tsoro da shakkar yarinyar nan ba, mahaifinta fa kyauta ya
bani ita sadaki kawai zan bayar to akan me zan takurawa kaina saboda ina gudan rashin
kunyarta."
'Yar dariya yay da fadin." UMARU har yanzu ba'ayi macan da zata tsorata ni ba, kawai dai ina
nuna maka yanda za'ayi ka zauna da ita lafiya ne idan kana mata butsu to ba zaku ta'ba samun
zaman lafiya da juna ba, maganar lefe kuma abunda ya dace ne koda kyauta aka baka kai
kuma sai ka duba cancanta da abunda ya dace."
Yace." A yanzu dai bani da kudin had'a mata lefe sai dai idan tazo daga baya nayi mata."
Asp din ya dinga kallonsa yana mamakin furuncinsa, wai bashi da kudi bayan irin tarin miliyoyin
da yake dasu account ko sati biyu ba'ayi ba daga can abuja mai girma shugaban kasa yayi
masa kyautar manyan kudi da dan'kareriyar mota harda gida a garin abujan amma shine yake
maganar rashin kudi.
Girgiza kansa kawai yayi da fadin." UMARU wato abunda dai kayi ra'ayi shi kake ba'a baka
shawara ka d'auka to ai shikkenan."
Yanda Asp din yayi maganar da b'acin rai a tare dashi yasa jikinsa sanyi ya bashi hakuri da
fadin." Afuwa abokina ba wai naki daukar shawararka bane akwai dalilina na yin hakan, amma
na janye domin farin cikin ka, yanzu nawa zan bayar ayi lefen tunda kaga ni yau zan bar gari
sannan kuma ban ma san yanda ake hada lefen ba.
Yace."Ai magana ta wuce ko sisin ka bazan kar'ba ba, lefe kuma ba za'a fasa ba, zan bawa
madam kudi ta shiga kasuwa ta had'a duk abunda ake bukata." Yana gama maganar yayi
tafiyarsa.
Murmushi kawai yake yana binshi da kallo har ya k'urewa ganinsa, tunda Allah ya had'asu yake
nuna masa 'kauna da sadaukarwa Asp ya zame masa dan uwa na jini, yanda yake sonsa da
kaunarsa shima haka yake kaunarsa saboda duk wasu alkairai yayi masa kuma duk wani
mataki da yake kai yanzu dalilinsa ne da jajurewarsa, hakika bashi da wani abu da zai saka
masa dashi face addua.
*****
To kamar yanda Asp din yayi wa kansa alk'awari sai da cika, don kudi masu yawa ya fitar aka
had'a lefe dasu akwatina goma sha biyu cike da kaya set din gold har uku kuma duk masu
nauyi, da yake da akwai fahimta a tsakaninsa da matansa babu wacce ta daga hankalinta, sai
dai kuma sa'bani ya kusa giftawa a tsakaninsa da yarinyar da zai aura a matsayin ta uku ,
al'amarin ya dinga bashi mamaki yana tunanin a inda ta samu labarin Zinatu da har take kishi a
kanta, ganin yanda ta tashi hankalinta ne yasa ya zauna yayi mata bayani cewa yarinyar da