Showing 18001 words to 21000 words out of 46825 words
Chapter 7 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
ka san haka."_
Yace." _Kada kiyi mamaki da sanina halin da kike ciki, ko kin manta nima d'an cikin garin
katsina ne, ai shiyasa ban cire tsammanin had'uwa dake a kurkusa ba tunda muna cikin gari
daya._
Amsa ta bashi kamar haka..
_"Faruk ina sonka sosai irin wanda ban ta'ba yiwa wani namiji ba, hakika zan so na ganka a
zahiri sai dai wannan mijin nawa yana da zafi! kuma ma'aikacin tsaro ne ina jin tsoron ka shiga
hannunsa ba za kaji dadi ba._
Murmushi yay lokacin da ya karanta sa'kon ya gyara kwaciyarsa kafin ya bata amsa kamar
haka.
_"Na san da haka my love bana tsoron had'uwa dashi ballanatana naji tsoron gwabzawa dashi
ina mai tabbatar miki da cewa a kanki babu abunda ba zanyi ba, zan iya fansar da raina akan
soyayyarki ina so ki cire tsoro a cikin zuciyarki, ki cigaba da kokarin ganin kin rabu dashi kizo
gare ni muyi aure, ni nayi alkawarin baki dukkanin kulawar da kike bukata."_
_Cikin jin dadin maganarsa tace."Nagode sosai wannan manganun naka sun kashe min jiki
wallahi na rasa abinda zance maka nagode sosai da kulawarka kuma nayi maka alkawari cewa
zanyi kokarin ganin mun hadu da juna, kada ka damu bukatarmu ta zata biya da izinin Allah."_
_Yace." Nagode my love yanzu me kike bukata nayi miki wanda zai faranta ranki."?_
Shuru tayi bata iya ce masa komai ba, gabadaya ya gama kashe mata jiki da salon
soyayyarsa.
Ganin tayi shuru ba tace masa komai ba kuma yana ganinta a online bata sauka kawai ba tare
damuwar komai ba ya tura mata sticks masu tayar da hankali gami da tayar da sha'awa
mussaman yasa Adewale ya tura masa su, a cewarsa shima zai turawa matarsa domin taga
irin style din da yake so tayi dinga yi masa idan ya dawo gari.
Adewale abun nema ya samu a take ya tura masa kala-kala wanda har sai ya rintse ido gurin
kallon wasu daga ciki, don dai ma yana da kok'arin danne sha'awarsa amma da anyi katari da
mara hakuri ganin sticks din zai sanya shi aikata aiki mara kyau.
Yana tura mata ya sauka daga layin ya dauki daya wayar tasa kai tsaye what'sApp din ya shiga
tana online har yanzu.
Sai kawai yay mata magana.
_"Me kike a online? karfe goma sha biyu da rabi."_
Ganin shigowar sakonshi yasa gabanta mugun faduwa!.
Koda ta duba sai ta kasa magana, baki da jikinta gabadaya sun mutu in banda faduwa babu
abunda gabanta keyi a dabarbace ta kashe wayar ta kwanta lamo kan gado ganin sticks din
ya sanya ruwan ni'imar da ya saba zuba a jikinta yin 'karfi, gabadaya pant din ya jike ta dinga
takure jikinta guri guda yanayin yana sake shiga jikinta sakamakon tashi da tsigar jikinta keyi
nipples dinta basu ta bayi mata 'kai'kaiyi irin na ranar ba.
Haka ta kasance cikin mawuyacin hali har asubah bata rintsa ba sakamakon ciwo da cikinta ke
mata.
Da 'kyar tayi sallah ta koma ta kwanta lamo kan daddumar ..........dole taja masa kunne kan
cewa kada ya sake turo mata da hotonan iskanci.
Misalin bakawai da rabi na safe, Baraka wato daya daga cikin hadimanta tayi knocking din
kofar dakin.
Ta mike zaune da kyar da fadin." Waye."?
Cikin girmamawa tace." Baraka ce ranki shi dade."
Sai da ta dauki kusan minti biyar sannan ta tashi taje ta bude mata kofar.
Tana shigowa ta zube gwiwa biyu tana gaisheta.
Da kyar ta amsa ta nemi saman sofa ta zauna yanayinta kadai shi zai nuna maka cewa akawai
abinda ke damunta.
Ta kalleta da kulawa tace."Ranki ya dade ko bakya jin dadi ne? domin naga alamun haka."
Girgixa mata kai tayi da fadin."Lafiya ta lau ina Marakissiya."? tana nufin 'yar uwarta da suka zo
tare.
Da sauri tace."Tana kicin domin had'a miki abin kari."
Tace."Okey ki hada min ruwan wanka, sannan ki shirya min kayana cikin wardrobe ki ajiye
komai a muhallinsa."
Cike da bin umarni ta amsa da "an gama Gimbiya." Mikewa tayi da sauri ta kama hanyar toilet
din sai ta dakatar da ita da fadin." Ruwan da d'umi sosai zaki had'a min kinji ko."
Ta amsa da "To ranki ya dade." Toilet din ta nufa cikin bin umarni.
Bayan ta hada ruwan ta fito sheda mata sannan ta fara sauke akwatinan kayan domin gabatar
da aikinta na gaba.
Ta dauki kusan minti goma a zaune kafin ta yunkura ta tashi domin shirin wankan, kira ya shigo
wayarta dake can kan daddumar da tayi sallah.
Kafin ma ta bata umarni taje ta dauko mata wayar, ta karba a yatsine tana dubawa.
*BA 'KYAUE* sunan dake yawo kan fuskar wayar kenan.
Tsaki taja da fadin.'' Da sassafe ya kira waya kamar wanda yake bin bashi.....Daf da zata tsinke
ta daga tasa a kunne.
A maimakon tai masa sallama sai kawai ta sauke masa ajiyar zuciya a kunne, tai shuru da
bakinta.
Shi yay mata sallamar ta amsa kamar bata so, yace."Kin tashi lafiya ya kwanan ba'kunta."?
A takaice tace."Alhamdulillh." Ya dan ja fasali kafin yace."Jiya na gan ki a online misalin daya
na dare ke da waye."? Cikin sigar zargi da tuhuma yake mata tambayar.
Gabadaya duk sai ta daburce! tana so ta tonawa kanta asiri........."Wac....Wace irin tambaya ce
wannan.''?
Yace."Alamu sun nuna baki da gaskiya ga yanayin yanda kike magana a daburce! okey duk
wani abu da za kiyi ina ji a jikina domin bani kadai bane akwai masu sheda min halin da kike
ciki saboda haka ki shirya dawowata sati biyu masu zuwa."
Da kyar ta iya saisaita muryarta amma inaa! sautin muryarta rawa yake yaki saisaituwa duk ta
tsure jin yace bashi kadai bane dama tun haduwarsu a daji ya ta'ba fada mata cewa yana da
aljanu tana jin tsoron kada su sheda masa halin da take ciki, Ta daure da 'kyar tace." Bana
neman tashin hankali ko wata 'bakar magana zargin da kake min ba zan ha naka ba ka cigaba
sannan duk sharrin da aljanunka za suyi min sun jima ba suyi ba, dai kai dasu duk baku dame
ni ba." Tana gama maganarta ta kashe wayarta ba ta jira amsarsa ba.
Shi kam dariya ma ta bashi ya tsaya ya dara yana jin dadin yanda game din yake tafiya a
tsakaninsu, Hamra'u ya kira suka gaisa ganin zata jashi da hira alhalin fita zai yi yasa a
tausashe yace." Kanwata yi hakuri yanzu ba lokacin hira bane lokacin aiki ne idan na dawo na
samu nutsuwa zan kira ki muyi hirar soyayya, yanzu ki bani Uwale idan tana kusa mu gaisa
domin na kira wayarta bata shiga ba."
Taji ciwon hakan a cikin ranta amma sai ta danne a sanyaye tace" Bari na kai mata wayar tana
kicin.?
Cikin mamaki yace."Kicin kuma me takeyi? Hamra'u keyi menene amfaninki."?
Da sauri tace."Aa nima ba laifina bane domin babu yanda banyi da ita ba akan ta zauna ta huta
ni zanyi mana komai kamar yanda na saba tace ita lallai sai ta shiga kicin da kanta tayi wa
amaryarka girki."
Ya dinga girgiza kai yana mamakin rigima irinta kakar tasa, yace." Yanzu je ki kai mata wayar za
muyi magana."
Ta amsa da "to" kafin ta je ta kai mata wayar.
Tana kicin taa dage sai soya funkaso take gefe guda kuma had'addiyar miyar taushe ce wacce
taji nama da gyada da alayyahu sai turiri take tana tayar da kamshi mai dadi.
Tace."Uwale yayana yana son magana dake."
Da farin ciki ta karbi wayar tasa a kunnuwanta da fadin." UMARU ina kwana.''?
Ya amsa da "Lafiya lou Uwale kun tashi lafiya ya kuma hidima da jama'a."?
Tana 'yar dariya tace." Alhamdulillhi an yi taro lafiya jama'a kowa ya koma gidansa lafiya "
Yace."To alhamdulillhi haka akeso nima insha Allahu sati biyu masu zuwa na kammala komai
na dawo gida."
Tace."Alhamdullhi, Allah abin godiya UMARU Allah ya dawo da kai lafiya ya kuma cigaba da
baka nasara akan duk abunda kasa a gaba."
Ya amsa da "Ameen ya Allah." Ya dora da fadin." Yanzu Hamra'u take sheda min cewa kina
kicin kina aiki Uwale me yasa ba zaki zauna ki huta ba sai kin wahalar da kanki Hamra'un za
tayi duk abinda ya dace."
Tace."Hakane maganarka UMARU bahaushe yace YABA KYAUTA TUKWICI yarinyar nan 'yar
babban gida ce wannan shine dalilin da yasa nake dawainiya da ita ba wai don naga gazawar
ita Hamra'un ba."
Yace."Duk da haka dai ki samawa kanki lafiya domin ba na so kina aikin wahala saboda
shekaru sun ja miki, idan ya kama na dauko masu hidima a gidana ina da ikon yin hakan, domin
itama Hamra'un ba ita take da alhakin haka ba tunda dai ba auranta nake ba."
Tace." To yanzu dai nayi laifi kenan don na nuna kulawa a kan matarka."? Ya girgiza kai da
fadin." Ba kiyi laifi ba Uwale cewa nayi ki zauna ki huta ita Hamra'u ta cigaba da aikinta kafin na
dawo gari."
Tace."Ai shikkenan tunda kai baka san gwaninta ba sai anjima." Sallama tayi masa ta mikawa
Hamra'u wayar tana mita akan abunda yay mata.
Yace." Hamra'u bata wayar da sauran magana dani da ita.
K'in kar'ba tayi yana jinta tana fadin." Oho!oho! ai ka gama magana UMARU har da zan nuna
kulawa kan matarka ka gwasale ni."
'Yar dariya yay ya daga murya yanda za taji sosai yace."
Yanzu dai mu bar wannan maganar haka Uwale kina ji na ko."?
Shuru tai masa ta cigaba da soya funkasonta.....Ya cigaba da cewa." Wannan kayan abincin da
aka jibge a store ba na bukatar na dawo na samesu, ki tara 'yan uwa da abokanan arziki da
kuma yara na ina nufin su Alba kenan duk ki raba musu, ni a bar min kadan sun isa."
Tace."Kana da hurumin hakan amma sai an shedawa ita GIMBIYAR domin itama tana da
hakki."
Ya jima yana mamakin maganar kafin yace." To shikkenan ki sheda mata cewa Umarni na ne
nace rabawa mabukata kayan masarufin da tazo dasu sannan kuma nagode da hidima."
Tace." UMARU ba haka sharad'in kayan gara suke ba, kana da hakki tana da hakki, saboda
haka ni sai naji hukuncin da ta yanke idan bakinku yazo daya shikkenan sai ayi yanda kace."
Takaici ya ishe shi, kawai ya kashe wayarsa ba tare da yayi mata sallama. aljihu yasa wayar,
ya janyo takalmansa ya fara kokarin sanya wa a kafafuwansa dake cikin safa, yana ganin
idan an jima kadan, ya samu sukuni zai kira yarinyar ya sheda mata hukuncin da ya yanke,
bawai don baya bukatar kayan masarufin ba, kawai dai yana so ya tsira da mutuncinsa domin
ganin tsarin yarinyar watarana zata iya yi masa gori akan wani abu daya dangance ta.
*SAI RANAR MONDAY ZA MU CIGABA DA IKON ALLAHí ½í¹í ¼í¿» NA 'DAUKI HUTUN KWANA
BIYU A CIKIN SATI DAYA, INA GODIYA A GARE KUí ½í¹í ¼í¿»*
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/6, 11:42 PM] Matar Malam: *G-J-S-U-R*
*57&58*
'Daure da towel mai dan girma wanda ya sauko mata har kasan gwiwa ta fito daga toilet din har
yanzu akwai sauran damuwar a tattare da ita sai kace wacce ta jima tana kuka idonta yayi
wani ja bayan 'kan'kancewar da sukayi wannan shine dalilin da ya sanya Baraka baiwar ta
dake aikin jera mata tufafinta a wardrobe ta fara lallaminta saboda duk wani abunda yake
faruwa suna da labarinsa.
Rarrashinta take sosai tana kara 'kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari masu kyau
wanda idan ta dauk'esu to tabbas za taci riba anan a gaba.
A 'kalla Baraka za ta iya shekaru talatin da biyu a duniya, ta girmeta da wasu shekarun
shiyasa take da sinkaye da hangen nesa, kuma dai itama haka kawai take sha'awar uwar dakin
nata tayi zaman aure kamar yanda sauran 'yan uwanta suke zaune a dakinsu lafiya, sau daya
ta ta'ba ganin mijin nata a zahiri amma duk iya bin k'wa'kwkwafin ta bata hango wani nakasu a
tattare dashi ba, namiji ne na nunawa sa'a irin mazan da suke da wahalar samu, 'yan mata da
yawa ire-iren ta gasu nan birjik duk a zaune babu mijin aure, wannan dalilin ne yasa take
mamakin wasu 'yan matan idan dadi yayi musu yawa suke tsula tsiya iri-iri, ita dai kam ba
taga abun gudu a cikin auran mutumin ba domin ya tara duk abunda ake da bukata.
Jiki a sanyaye ta zauna kujerar mudubi tana dan goge guntun hawayen da suka sauka a
fuskarta, maganganun Baraka sun kashe mata jiki mutuka, ta rasa mai mutane suke hango
mata a tattare da zamanta da mutumin nan, duk wanda zai bude baki sai yace mata shine
alkairinta, ba ta'ba gani ko jin wanda ya soki al'amarin ba, sai mutum daya wato Sakina kawarta
amma tun daga kan family nata har zuwa kan bayin dake cikin masarautarsu dukkaninsu farin
ciki da al'amarin suke, ita da Sakina su kadai ne suke nuna adawarsu a fili, tana ganin dai
mutumin bai zauna haka ba sai da ya nemi jama'a domin gabadaya ya siye zuciyoyin duk
wanda ya shafe ta.
Tana shirya jikinta tana auna maganganun Baraka a zuciyarta da kuma tunanin yanda za tayi
zaman aure da mutumin bayan har yanzu ya kasa fuskantar alkibula ma'ana ya kasa fahintar
abunda take so da wanda ba ta so.
Tazo ta gurfana a gabanta da fadin." Ranki ya dade na kammala komai akwai bukatar wani
abu."?
Ta kalleta cikin rashin walwala tace." Babu bukatar komai a yanzu, sai ko zuwa anjima kina jina
ko."?
Da sauri tace."Eh ranka ina jinki."
Tace."Kada na kuskura naji kin sake yi mib magana makamanciyar wannan, ki kiyaye ki kuma
zauna a matsayinki."
Baraka jikinta yayi sanyi cikin bin umarni tace."Allah ya huci zuciyar Gimbiyar mata insha Allah
zan kiyaye ba zan kuma."
Ba tare da tace komai ba ta nuna mata hanya da hannu, ta mike cikin rashin kuzari ta kama
hanyar fita tana zancan zucci, itama mantawa tayi da halin uwar dakin nata ta san ta da gwale
mutum, amma meye laifinta anan don ta nuna mata hanyar gaskiya, shikkenan ai daga yau
zata kiyaye harshen ta ko don ta tsira da girma da mutuncinta.
Kacibus sukayi da Markisiyya ta gama shirya daining zata shiga ta sheda mata.
Ta kalleta da fadin." Ya naga kin fito da jiki a sabule."?
Girgiza kai tayi kafin tace." Marakissiya kin san halin mutuniyar sai ana kai zuciya nesa shiyasa
kwata-kwata ban so dani a cikin wannan tafiyar ba.
Tace."Nima haka wallahi kin san bamu da ikon da zamu nuna rashin yardar mu akan haka to
kinga dole muyi hakuri kuma mu kiyaye zama da ita."
Tace." K'warai hakane maganarki ki shiga ki sheda mata kin kammala ina jiran ki anan."
Tace."To shikkenan jira ni na fito.
Zubewa tayi kasan gwiwa ta gaisheta kafin ta sheda mata cewa ta kammala shirya gurin cin
abinci.
Ta kalleta da fadin." Me ki kayi.'?
Ta shiga lissafo mata abinci har kala uku.
Sosai ta rufe ta da fad'a da fadin taje ta kwashe kayan abincinta bata bukatar cin abinci mai
nauyi da safe, tayi maza ta soya mata k'wai da indomee da kuma ruwan tea, Cike da bin
umarni ta amsa kafin tai saurin fita daga dakin..
Ita da Barakan suka fita suna munufurcinta da irin munanan halayen ta marasa kyau.
Bayan fitarsu da 'yan mintina Uwale ta shiga hannunta rike da kwando wanda yake dauke da
kayan abinci.
Ta kai tsayin minti goma tana sallama, ta naji ba ta amsa ba ballanatana ta fito.
Ta jima a tsaye tana shawarwari da zuciyarta kafin ta yanke shawarar shiga uwar dakin jikinta
yana bata cewar ko babu lafiya.
Tana tura kofar dakin kawai ta sameta a hakimce a kan kujera tana latsa wayarta, kamar bata
so ta amsa sallamar still hankalinta gabadaya yana kan waya bata dago ta kalleta ba,
ballanatana taga da me ta shigo.
Uwale ta samu gefe ta ajiye kwandon kayan abincin da 'yar fara'a ta tattare da ita tace."
Yarinyar arziki ina fata kin wayi gari lafiya ya kwanan bakunta kuma."?
Shuru tay mata still dai hankalinta na kan wayarta.
Tace." Ga abinci nan nayi miki da kaina na shiga kicin, funkaso ne da miyar taushe da kuma
kunun gyada da 'kosai nasan zakiyi sha'awar ci, bayan haka kuma dazu UMARU yayi waya
yake cewa wannan kayan masarufin da ki kazo dashi da kuma atampopin duk yace a bayar
dasu ga mabukata shine nace lallai sai naji hukuncin da ki ka yanke."
Kamar ba taso ta kalleta kafin tace." Bani da damuwa da duk abunda kukayi