Showing 9001 words to 12000 words out of 46825 words
Chapter 4 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
fito
ciki d'aya Allah ya kawar da idon makiya a tsakanimu." Ya amsa da "Ameen ya Allah, kafin
suyi sallama da juna.
*****
To a daran ranar da sukayi wannan tattaunawar da Asp din ya yanke wata shawara wacce yake
ganin zata taimaka masa gurin tantance nagarta da kamun kan yarinyar........ da yake yana
amfani da layin waya biyu sai yayi amfani da d'aya layin da ba kowa ya san shi dashi ba, wata
irin rikitacciyar wasika ya tura mata mai dauke da zafafan kalaman soyayya da tsuma zuciya,
sosai yayi amfani da hikima gurin shirya kalaman wanda yake da tabbacin cewa dole su rikirkita
mata lissafi, bai fayyace mata kansa ba asali ma babu suna a wasikar yana tura mata ta in box
ya cire sim card din ajiyeshi cikin cover shi sai an kwana biyu zai mayar.
Kamar yanda yayi tsammani hakan ne ya faru, domin tunda ta karanta wannan text din
gabadaya ta rikice ta rasa abinda yake mata dad'i a duniya, macace mai bala'in son soyayya
da kulawa shiyasa kullum cikin kallon indian film take amma irin na soyayya, tana bala'in san
wanda kullum zai dinga kasheta da kalamai yana rarrashinta ita kuma tana masa shagwaba da
sangarta irin yanda take so, kasa hakuri tayi tabi layin da kira, sai dai ta kisa sau goma ana ce
mata layin baya aiki a halin yanzu, hawaye masu zafi ta share tana tunanin daga wace duniya
sakon wasikar yazo gareta? wanene wannan wanda yake da kalamai irin haka? shin a ina ma
ya samu number ta, hakika zata so ganin sa ido duk talaucinsa zata iya zama dashi mutukar
zai dinga lallabata yana bata abincin zuciya irin wanda take bukata.
Hanci taja tasa hannu ta goge hawayen dake karakaina a saman fuskarta, me za tayi da
wancan ba 'kauyen mutumin da be iya komai ba sai 'bakar maganar magana, tunda take
dashi bai ta'ba yi mata kalami mai dadi ba, ko a lokacin zaman su a daji ta lura kan dole yake
rarrashinta idan wata masiba ta sameta, a halin yanzu ya kamata ace ya kwantar mata da
hankali domin samun soyayyarta amma saboda girman kai ya kasa duk sanda zaiyi mata
magana cikin gadara! da isa! shi ba kowa ba sai iko yake nuna mata ita kam ba zata yarda da
wannan ba, tunda dai a zahiri tana ganin ta fishi da komai ba zata yarda ya mulke ta ba har
yanzu tana nan akan bakanta ko auran sukayi.
Kullum sai ta gwada kiran layin sai ace mata baya aiki, duk ta susuce! tunaninta ya kammanin
mutumin yake? ba abunda take so taji sai muryarsa.
A na gobe daurin auran da daddare kowa yai bacci ta gwada kiran layin, jin yana shiga yasa ta
tashi zaune da saurin gaske farin ciki gabadaya ya cika mata zuciya burinta kawai ya daga
wayar taji sautin muryarsa.....
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[1/31, 9:53 PM] Matar Malam: *49&50*
Cikin wata murya mai sanyi da ita kanta bata san tana da ita ba tayi sallama kafin ta dan
lumshe idonta tare da sauke ajiyar zuciya tace." ina so na san da wanda nake magana a halin
yanzu."
Shuru yayi bece uffan ba, gabad'aya mamaki ya gama kashe shi jin irin salon da take masa
magana ashe ta iya tausa murya haka.
Shuru be ce mata komai sai saukar numfashinsa da takeji a kunnawanta.
sai gabadaya jikinta ya sake rikicewa, haka kawai Allah ya jarabce da son wanda bata ta'ba
gani ba.
Cikin 'yar shagwaba tace." Please don Allah waye ne? kwana biyu da suka wuce naga text
dinka shine dalilin da yasa ma na kira ka domin san kowaye kai ."
Idonsa a lumshe yayi d'an gyaran murya kamar zai yi magana sai kuma yaja bakinsa yay shuru,
gabadaya ta gama kashe masa jiki da salon da take masa magana yana masifar son
shagwabbiyar mace.
Jin yayi shuru ta sake narkar da murya dan a zahiri saura kadan ta fashe da kuka tace." Ba za
kayi min magana ba ko? ka san kuwa halin da ka jefa zuciyata."?
Zaune ya tashi yana sake rike wayar a kunnunsa, kafin ya aro wata murya da duk bin diddigin
mutum ba zai gane muryarsa bace yace." Wani bawan Allah ne yazo da kokan baran shi a
k'urataccan lokaci."
Jikinta ya 'kara saki jin sanyayyiyar muryarsa ya jefa ta cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa,
tace." Kayi min bayanin kanka daga ina kake kuma ina ka samu number ta."?
Dan murmushi yay kafin yace." Sunana FARUK ni dan asalin hajar katsina ne." Gabanta yay
fadi jin ya ambaci garinsu ma'kiyinta.
Jin tayi shuru ba tace komai ba ya cigaba da cewa." Na tsinci hotonki a social media gurin wani
biki sai kawai Allah ya jarabceni da tsananin sonki da kaunarki, talaka ne ni amma ina da
zuciyar nema, duk da na san cewa ke ba tsaran aure na bace, hakan bai sa na saduda ba sai
da nayi fafutukar samun number ki, amma wanda ya bani number ya sheda min cewa aure za
kiyi hakan be firgitani ba, tunda dai ba'a daura auran ba zan fito na nuna miki tawa soyayyar da
take gudana a cikin jikina."
Tun sanda ya fara maganar take share hawaye, tayi duk yanda za tayi ta tsayar da kukan abun
ya fassakara, tana kukan tace." Kazo a 'kurataccen lokaci bawan Allah, sosai nake son mai
sona kuma ina alfahari da soyayyarka, hakika da kazo a kan ga'bar da iyayena suka yanke min
hukunci to babu shakka kai zan nuna musu a matsayin mijin aure, babu ruwana da talaucinka
mutukar zaka bani abincin zuciyata bani da damuwa, yanzu maganar da nake maka gobe za'a
daura min aure da wani wanda bana ra'ayinsa." Cikin wani irin kuka mara sauti takarashe
maganar.
Jikinsa ne ya mutu jin kukanta yake har tsakiyar kansa, Cikin taushin murya da sigar rarrashi
yace." Yi shuru ki daina kuka kinji ko wannan kukan da ki ke yana ta'ba min zuciyata ina jin
kamar nazo inda kike na rarrasheki bana son zubar hawayenki.
Hannu tasa ta goge hawayen amma ba tace komai ba.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Yanzu ya za kiyi dani da soyayyata Gimbiyata bana jin zan
iya rabuwa dake fa.''
A sanyaye tace." Nima bana tunanin hakan a zuciyata, ka bari a kwana biyu zan yanke shawara
akan soyayyarmu."
Murmushin takaici yay kafin yace." Okey na fahimta yanzu zamu cigaba da gaisawa ne ta waya
babu matsala hakan."?
Shuru tai na minti biyu kafin tace." Babu matsala amma ka bari ni zan dinga kiran ka"
'Yar dariya yay da fadin." Shikkenan my love yanda ki ke so hakan za'ayi amma inaso muna
gaisawa koda ta charting ne."
Ba tare da damuwar komai tace."Wannan babu damuwa zanyi serving number naka yanzu."
Yace."To ina godiya my princess bari na barki ki kwanta ki huta ko, amma ina tabbatar miki da
cewa yau ba zan iya rintsawa ba."
Da sauri tace."Saboda me."? Cikin tausayawa kansaYace. " Saboda gobe za'a daura miki aure
da wani."
'Karamin tsaki taja kafin tace." Ka kwanta kayi barcin ka, kada kasa damuwar komai a ranka
domin wanda za'a daura min aure dashi, bashi da wani muhimmanci a zuciyata, bana sonsa
bana ra'ayinsa, da auransa da babu duk daya suke a gurina, ka kwantar da hankalinka nayi
maka alkawari kai zaka mallake ni, domin da kai zuciyata ta aminta duk da ban ta'ba ganinka
ba ina hasaso fuskarka a idona, ina sonka a duk yanda kake, zanyi mana duk wani kokari da
zai tabbatar mana da biyan bukatarmu."
Yaji haushi da takaicin maganarta amma sai ya danne a zahiri ya nuna mata farin cikinsa,
sallama yay mata da jin zafin maganganunta a zuciyarsa ya kashe wayar yana tsaki da fadin."
Sakarai mara wayo kawai."
Kwanciya yay yana tunaninta, gabadaya ma ya raina wayonta da dubararta, koda yake macace
mai rauni zata iya yin abinda yafi haka.
Agogon ya d'an duba, yanzu minti talatin kenan da wayarsu, ya kama sha daya dai-dai na
dare, yanzu da Asalin number shi ya kira ta.
Sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka tana cin magani, wayar tasa a kunne amma ba tace
komai ba.
Yay mata sallama cikin asalin muryarsa mai cike da amo!!
Ciki-ciki ta amsa tana ya mutse fuska.
Yace." Tun dazu nake kiran wayarki sai ace dani busy shin dawa kike waya a cikin wannan
daran."?
Cikin tsiwa da gadara irin yanda take masa magana tace." Ina ruwanka da wanda nake waye?
ko kana da damuwa da hakan ne."?
Daurewa yay yace." Ni nake da damuwa da hakan kuwa, dalilina kuwa nasan baki nutsuwa da
kamun kai zaki iya raba dare da wani namijin a waya saboda rashin kintsi."
Zuciyarta ta dinga wani irin zafi da tukukin bakin ciki!
Abinda yake had'ata dashi kenan bakar magana, kwata-kwata be iya rarrashin mace ba, haka
kawai zai tayar mata da hankali tana zaman zaman ta.
Murya na rawa kamar me shirin fashewa da kuka tace." Bagidaje kawai kana da matsala
wallahi, haka kawai zaka shiga rayuwata cikin daran nan to ta Allah bata ka ba"
Yay dariyar cusa takaici yace." Naji bagidajen ne dole kuma a zauna dani a haka na kuma bada
umarni ayi ko ana so ko ba'a so."!
Tsaki mai tsayi taja irin wanda ta san baya so tace." Wahalalle kawai bani da lokacinka." Da
sauri ta kashe wayarta domin bata so ta sake jin sautin muryarsa!
Bacci k'auracewa idonta yay ta dinga zubar da hawaye tana tunanin boyayyan masoyinta daya
bayyana mata kansa a yau..........Shin wai ya za tayi da wannan takad'irin mutumin da ake
kokarin aura mata bayan be tara duk abunda take da bukata ba.
Haka ta kasance cikin tsananin damuwa gami da juye-juye sai gefin asubah bacci mai nauyi ya
d'aukata.
Shigar aunty Hassana dakin yayi daidai da bude idonta gari ya waye tarwai.
Zaune ta mike tana dan ya mutse fuska! wani irin ciwo kanta yake ba komai ya janyo mata
hakan ba illah kwanan kuka da tunanin da tayi.
A nutse ta 'karasa kusa da ita ta tsira mata ido na minti biyu kafin tace." Sai yanzu ki ka tashi
kenan."?
Kai ta daga a raunane tace." Aunty an d'aura auran ne."?
Girgiza kai tayi da fadin." Sai goma da rabi tukkuna, na shigo ne domin naga ko kin gyara jikinki
ashe ke kina ma kwance."
Kai ta dafe da fadin." Jiya ban samu bacci ba sai gefin asubah, shiyasa ban tashi da wuri ba ko
sallah fa banyi ba."
Tace." Zinat ba zaki sanyayawa ranki ba ko? me yasa kike so ki jefe kanki cikin wani hali,
iyayenki fa ba zasu ta'ba cutarki ba."
Tace."Aunt Hassana don Allah mu bar wannan maganar domin ni ba wannan ne dalilin ya
hana ni bacci ba, ai na hakura na barwa Allah."
Tace."Okey to idan hakane ki tashi ki gyara jikinki kiyi kwalliya sosai tunda kinqi yarda da ayi
miki kitso da kunshi (lalle) irin na amare kada dai ki yarda mu da muke 'yan gayya mu fiki kyau
zakiji kunya.
Murmushin takaici tayi tana kokarin saukowa daga gadon tace." Bana ra'ayi ne kawai, amma
ban ha naku kuyi kwalliyarki ku ba, ban damu ba idan kun fini kyau."
Hanyar toilet ta nufa jikinta duk a sanyaye........Aunty Hassanar ta bita da kallo tana girgiza
kanta, ta rasa wane irin hali ne da ita gabadaya a baud'e take.
Wani dan'kareran les ta fito mata dashi kudinsa ya kai dubu dari da wani abu rigar bubu ne anyi
ado da wani irin net bayan stones din dake jikin les din an kuma baza wani stones din masu
walwali a jiki, c-green ne, color shi tayi kyau sosai.
Duk wani abu da ta san za tayi amfani dashi sai da ta fito mata dashi ta ajiye mata.
Tana kokarin fita daga dakin, kira waya ya katse mata hanzari.
Ta dawo ta dauki wayar tana dubawa, sunan ba'kauye ne yake yawo kan fuskar wayar.
Cike da mamaki take duba wayar, waye wannan kuma? toilet din ta kalla, ta san halinta tun tana
yarinya take da nawa bata da zafin nama haka take idan ta shiga wanka sai an manta da ita.
Yanke shawarar daga wayar tayi a nutse tai sallama.
Jin sabuwar murya cikin nutsuwa yasa shima ya amsa a nutse da fadin." UMARU ne."
Da sauri tace." Angon ne ashe kayi hakuri tana bandaki sai dai idan ta fito ko."
Yace."Babu damuwa idan ba matsala ina so na san da wa nake magana."
Murmushi tai kafin tace."Hassana ce yayar amaryar taka.
Yai murmushi da fadin." Ai kinga tambayar tayi amfani Auntynmu ya hidima da jama'a."?
Tace."Alhamdulillhi wallahi, Allah dai ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya UMARU kayi hakuri
da yarinyar nan daban take a cikinmu tana da wani irin hali, amma kuma idan ka'iya zama da ita
tana da sauki kai da iya mu'amula."
Yace." Kada ki damu aunty insha Allah zan rike amanarku zan iyakar bakin kokarina."
Tace." To mungode sosai Allah ya baku zaman lafiya."
Ya amsa da ameen ya Allah ya dora da fadin "bari na bari zuwa an jima zan sake kira."
Tace."To shikkenan babu damuwa." Sallama sukayi ta zauna zaman jiran fitowarta.
Ido suka hada lokacin data fito daga toliet din tace."Wai dama kina zaune har yanzu."
Tace."Nazo fita ba k'auye ya kira wayarki."
Saurin kallonta tayi suka hada ido ta girgiza kanta rai a bace tace." Kin ji kunya ko."?
Girgiza kai tayi tana dan tabe baki tace."Wane irin kunya kuma." Gaban dressing mirror ta wuce
tana ya mutse fuskarta.
Aunty Hassanar tace."Kullum kina nuna mana cewa kin saduda ashe ba haka bane, a zuciyarki
don iskanci ki rasa da wane suna za kiyi serving number sa sai da ba k'auye wai shin ma dame
ki ka fishi kin san dai baki fishi kyau ba."
Tana 'yar dariya tace."Aunty Hassana ai sunan da ya dace dashi kenan, d'an k'auye ne dashi da
family sa, kinga kuwa babu laifi don an kira shi da wannan sunan ba kauye bagidaje."
Ta girgiza kai cikin takaici tace." ki cire wannan sunan bai dace ba, gwara kisa masa sunansa
na Asali hakan shi yafi mutunci."
Saboda bata san suyi ta ja'in ja yasa tace."To shikkenan aunty zanyi yanda ki kace din, amma
da ya kira me yace miki."?
Tana kokarin mikewa tace." Be ce komai ba zai dai sake kiran ki abinda fada kenan.
Ta'be baki tai ta cigaba da shafa mai a fatar jikinta.
Aunty Hassanar tana kokarin fita daga dakin ta dakatar da ita da fadin." Aunty Hassana ya
maganar mutanan da aka tura su shirya min daki."
Tace."Ai babu wannan maganar domin mijin naki ya shedawa Maimartaba cewa ke kadai yake
bukata akwai komai na bukata a gurin da zaki zauna wannan dalilin yasa aka rushe wacan
maganar.
Ta girgiza kai da fadin." Wannan ai zubar da kima da mutunci ne, Aunty Hassana cikinku wa aka
ta'ba yiwa haka? ai na dauka kowacce sai da aka cika mata daki uku da kaya amma ni saboda
ba'a sona za bar ni haka, to wallahi babu wanda ya isa na dogara dashi da kayansa.
Hannu ta daga mata da fadin." Wannan maganar Maimartaba zaki samu ki fada masa bani da
kika raina ba, Zinatu kije ki samu mahaifinki ki nuna masa cewa baki yarda da hukuncinsa ba,
wannan shine zai tabbatar mana da cewa kin fita zakkah a cikinmu."
Tana gama maganar ta bude dakin ta fita ranta a mugun 'bace! addua ce kawai zata shiryar
musu da ita.
Hawaye masu zafi suka dina sauka a saman fuskarta, wannan tozarci dame yay kama? kamar
ita 'yar gata gaba da baya amma a kaita gidan aure babu kaya sai kayan miji wanda ta raina
bata daukashi a bakin komai ba, kwata-kwata ba'ayi mata adalci ba.
Kiran wayarsa ne ya katse tunaninta, da sauri ta dauki wayar tasa a kunne sai ajiyar zuciya ta
saukewa cikin kuka tace." Bana bukatar komai naka a gurin da zan zauna, ka kwashe
komatsanka zanzo da nawa baka isa na dogara da kai da abunka ba."
Tun wayewar gari ya tsinci kansa cikin walwala da farin ciki, wanda shi kansa ya kasa gane
dalilin.............Wannan shine dalilin yasa maganganunta ba suyi masa zafi ba, yay murmushi
irin wanda ya saba kafin yace." To ke meye na damuwa bayan baki da niyyar zaman auran, ai
zuwa da kayan daki zai miki wahala shiyasa na hutashsheki, bayan haka kuma nima haka na
samu gidan cike da kayan more rayuwa gwamnati ta zuba min, kada ki damu sashenki daban
sai kin so zaki ga wani kuma baki da matsalar komai, wannan dalilin yasa na shedawa
Maimartaba cewa ke kadai nake da bukata."
hanci taja kamar za tayi magana sai kuma taja bakinta ta tsuke