Showing 21001 words to 24000 words out of 46825 words
Chapter 8 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
da kayan, na kune
duk wanda kuke so zaku bawa bani da matsala."
Tace." To masha Allah mungode sosai Gimbiyar mata ga abinci nan a jiye duk sanda kika
kammala sai kici kada ki zauna da yunwa."
Ta kalleta a karo na biyu tana yaba k'okarinta, koda yake dole tayi duk wani kokari a kanta
tunda tana kwad'ayin ta zauna da jikanta.
Girgiza kai tayi kamar tace mata fita da kayan ki bana bukata, sai dai kawai tayi mata shuru har
ta fita daga dakin ba tanka mata ba ballanatana tayi mata godiya.
Asp ne ya kira ta suka gaisa cikin sakewa yana tsokanarta tana amsawa sama-sama, kafin
yace" bari na baki kawarki ku gaisa ko."?
Tace" Bata wayar daman yanzu nake tunanin kiranta."
Yace." Kin dai yar da Madam bayan da tsohowar zuma ake magani baki kyauta ba."
Aunty Zeey dake zaune a kusa dashi ta dinga zabga masa harara.
Ita ya ambaci sunan matar ma bata so saboda tsananin kishinta.
Daga daya bangaran Zinat din tace." Aa ba haka bane wallahi Mommy uwa ce a gareni kuma
har yanzu ban mance alkairinta ba, sannan ka tambayeta ai muna waya sa'i da lokaci muna
gaisawa har da Nabila."
Yaji dadin hakan a ranshi yace." Masha Allah naji dadin haka ki dauka cewa da Madam da ita
Zainab din duk 'yan uwanki ne.''
Tace."Dama ai haka na daukesu a cikin raina.''
Ya mikewa Zeey wayar ta kar'ba tana jin haushinsa, da ya lura da hakan sai kawai yayi
murmushi yana girgixa kansa, ya rasa mai yasa ta zafafa akan al'amarin uwargidanta.
Ba suyi wata hirar kirki ba a tsakaninsu, dalili Asp din yana gurin shiyasa Aunty Zeey din ta
katse hirar da fadin.'' Zan kira ki an jima idan na sallami Oga zai tafi gurin aiki."
Tace."Okey to babu damuwa." Sallama sukai kafin kowa ya kashe wayarsa.
Da ido kawai ta kalli funkason da miyarsa ta tabbatar da cewa zai yi dadi, duk da cewa bata cin
abinci mai nauyi da safe, ganin funkason shar da miyarsa da take tashin kamshi yasa yawun
bakinta tsinkewa, ta bude fulas din kunun gyadan shima yay kyau fari tas dashi sai k'amshi
yake, dama can tana son kunun gyada da k'osai saboda haka ta kansu ta fara, tana kurbar
kunun tana had'awa da kosan, zuciyarta cike da mamakin yanda tsohowar ta iya girki dad'i
gaske, wani irin gardin dadi kunun keyi mata, kamar kunnanta ya tsinke.
Saboda tasha kunun da yawa funkason biyu kacal ta ci, ba don ta hak'ura ba, sai an jima za ta
zauna taci a tsanake idan cikinta ya samu sassauci.
Koda Marakisiyya ta shigo ta sheda mata cewa ta kammala aikinta, sai kawai tace taje dashi
suci bata bukata har da ta nuna mata kwandon abinci Uwale da fadin." Ita ta samu wani
wanda ya gamsar da ita.
Marakisiyya taji ciwon abunda tai mata, amma ba yanda za tayi haka tayi godiya tabi umarni ta
fita ta kwashe tarin abincin da tayi ha'kilon dafawa ita da Baraka sukaci wanda zasu iya kafin
su fita da sauran su kaiwa 'yan uwansu maza da suka zo tare.
Ta kira wayar Sakina ya kai sau biyar amma sai ace da ita busy, tsaki taja tare da mi'kewa
tsaye, falo ta nufa gabadaya babu kuzari a tattare da ita, dole tana bukatar wanda zai dan
d'ebe mata kewa, amma bata tsammanin sauraran boyyayan masoyin nata a kusa duba da irin
abinda yay aikata mata saboda kawai ya samu fuska a gurinta, dole ne ta nuna masa
kuskuransa.
Aikuwa tana tsaka da wannan tunanin kiran sa ya shigo wayarta, tana kallo har wayar ta katse
bata daga ba.
Ya kira ya kai sau biyar bata dauka ba.
Text ya tura mata cewa ta daga wayarsa yana so yayi magana da ita.
Ta mayar masa da amsa kamar haka.
_" Saboda kawai ka samu fuska shine zaka turo min hotonan banza ko an fada cewa ni din 'yar
iska ce."?_
Murmushi yay lokacin da ya karanta text din ya mayar mata da amsa kamar haka.
_"My love kiyi hakuri ba zan sake ba tunda bakya so amma ki daga waya ta ina bukatar jin
muryarki."_
Share shi tayi bata bashi amsa ba, koda ya sake kira ma tana kallon wayar taki dagawa.
Yaji dadin hakan a ranshi amma duk da haka ba zai kyaleta ba zai cigaba da gwadata domin ya
tabbatar da nagartar ta.
****
Sai bayan isha'i ya samu kansa dan gabadaya yau a tsaye suka wuni, yayi wanka ya fito cikin
k'ananun kaya t- shart da 3Qutar masu haske kai tsaye falo ya nufa ya samu Adewale yana
kallo ga plate din abinci nan a gabansa.
Kusa dashi ya zauna yana kiran sunan Allah, hannu yasa ya dafe kanshi da fadin." Ba haushe
yace Aski idan yazo gaban goshi yafi zafi Adewale kwana Biyu nan wallahi a gajiye nake gashi
bana samun bacci isasshe."
Cokali cike da abinci ya kai bakinsa yana taunawa yace." Oga aikin nan namu ai sai mai juriya
akwai tarin kalubale wanda ba kowa ne zai gane ba sai wanda ya san ya al'amarin yake, ni
kaina na matsu na koma gida domin dukan yayi yawa ban ta'ba kwana uku babu sex ba sai da
nazo garin nan, shiyasa wani sa'in nake fita na rage zafi."
Yana girgiza kansa yace."Adewale baka da magana sai ta sex kai kenan kalle-kallen blue film
ko gajiya ba kayi wallahi ka kiyaye kuma kai hattara kada garin son zuciyarka kaje ka dauko
ciwo neman mata bashi da fa'idah."
Shiru yay na minti biyu kafin yace." Oga ina kiyayewa fa bana yarda na kwanta da mace ba tare
da kariya ba, bani da juriya akan wannan al'amarin Oga haka Allah ya hallice ni, kai kam ai
ina ganin k'okarin ka don ban ta'ba ganinka da wata mace ba."
Yace." Kariyar banza, ai duk wayonku ba zaku hana Allah zartar da ikonsa ba, wallahi ka
kiyaye domin inganta rayuwarka data 'ya'yanka."
Yana 'yar dariya yace." Oga kullum aka zauna da kai sai ka kashewa mutum jiki da nasiha,
duniyar nan fa ita kenan to me zai sa mutum ba zai ji dadinsa ba."
Ya kai hannu ya janyo plate din abinci dake rufe ya bude da fadin." Kayi nisa Adewale sai dai
kawai na taya ka da adduar shiriya."
Ya mike tsaye yana kyalkyala dariya da fadin." Yanda yau muka yini a tsaye da zaka bani hadin
kai da na kawo maka wacce zaka sauke gajiyarka."
Shuru yay masa be iya ce masa komai ba, domin al'amarin mutumin yana nema yafi k'arfinsa.
Ya cigaba da subararsa yana jinsa uffan bece masa ba, abincinsa kawai yake ci yana nema
masa shiriya a gurin Allah.
Gajiya yay da surutun ya kama hanya ya fita da niyyar zuwa ya samu wacce zai sauke
gajiyarsa a kanta.
A nutse ya kammala cin abincin ya yagi tissue ya goge bakinsa, hamdala yay ga Allah, kafin ya
kishingida kan kujerar ya dauki wayarsa yana dubawa.
Ya kai mintina goma yana duba wayar kafin ya lalubi number abokiyar rigimar tashi.
Daf da zata katse ta daga wayar, wannan karon ma a maimakon tai masa sallama sai kawai ta
shiga sauke masa ajiyar zuciya a kunne.
Lumshe idonsa yay ya janye wayar daga kunnansa yana jin wani irin yanayi na shiga jikinsa, ya
ci ya 'koshi ga gajiya jikinsa yayi tu'bus! ta bakin Adewale san samu ya samu wacce zai sauke
gajiyarsa, cikin wannan yanayin ita kuma tazo tana masa numfarfashi a kunne sai kace wacce
take cikin wani yanayi.
Jin shuru bece komai ba yasa ta cire wayar tana dubawa, har yanzu yana kan layin bai kashe
ba.
Zum'bura baki tayi ta ya mutse fuska da fadin.'' Ina jinka ka kira waya kuma kayi shuru"
Gyaran murya yayi ya saisaita yanayin sa da fadin." Ya kike ina fatan kin wuni lafiya."?
A takaice tace." Lafiya."
Yace." Masha Allah haka ake so menene labari."?
Tai masa banza tana jin kamar ta kashe wayarta.
Yace." Baki da labari me dadi wanda zaki bani."?
"Umm." tace tana jin wani irin haushinsa a zuciyarta.
Yace." Okey d'azu da safe munyi waya da Uwale ina fatan ta sheda miki hukuncin dana yanke
akan wannan kayan garan da ki kazo dashi."
Tace." To ni me ya dame ni da wannan, al'adah ce ta masarauta cewa duk yarinyar da za'ayi
wa aure sai an had'a da kayan masarufi da turaman atamfofi da sauransu, kai akayi wa hidima
da sauran family naka duk yanda kukayi dai-dai ne."
Yace." Eh na fahimta bana bukata ne shiyasa nace a bayar dasu kafin na dawo Uwalen take
sheda min cewa lallai sai an fada miki kin yanke hukuncii tukkuna."
Tace." Kai har kafi 'karfin wani abu kenan."?
Yace." Ban fi k'arfi ba kawai bana bukata ne."
Ranta yay masifar baci tace." Nawa kake dashi? me ka ajiye a banki? shin yaushe ma ka zama
mutum! ka samu sutturar sanyawa da har za ayi maka kyauta kace baka so, shin wanene kai a
cikin mutane da har zaka nuna cewa kai kafi karfin wani abu."!? Cikin daga murya take
maganar."
Yace." A'm human being ni mutum ne kamar kowa nace bana bukata idan da akwai wanda
ya isa ya sauya min ra'ayi ina jiran sa."
Taja wani mugun tsaki irin wanda ta san baya so a kufule! tace." Nonsense kawai." Kashe
wayarta tayi zuciyarta na wani irin turiri, sosai taji ciwon abinda yayi, shi din har waye da
mahaifinta zai masa kyauta ya k'yama ta, yaushe har ya zama mutum yayi arziki gami da
sutturar sanyawa da har zai nunawa duniya cewa shi yafi karfin a taimaka masa, wannan abun
yayi mata ciwo sosai! a ganinta hakan kamar tozarci ne....
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/8, 9:24 AM] Matar Malam: *59&60*
Da tsananin bacin rai ya kwana ya kuma tashi dashi, a cikin ranshi yana raya irin tsauraran
matakan da zai dauka akan yarinyar mutukar ya koma gidan tazo masa hauka da rashin hankali
makamancin wanda take masa a yanzu, wanda yayi imani da cewa don baya kusa da ita ne
amma da ba don haka ba da kudi a kace ta zage shi ko taci masa fuska ba zata iya ba.
Yana tsaka da shiryawa Hamra'u ta kira shi a waya. beyi a kasa a gwiwa ba ya d'auka tare da
gyaran murya kafin ya ambaci sunanta." Hamra'u."
Ta amsa da 'yar dariya a tare da ita tace." amma bana son wannan sunan nafi bukatar da ka
kira ni da my love din ka kamar yanda ka saba kira na."
Murmushi yayi tare da kokarin kawar da damuwarsa yace." Ashe nayi laifi don na kira ki da
sunanki na hakika okey to My love dina haka kike so ko."?
Ta shiga kyalkyala dariya farin ciki duk ya cika mata zuciyarta tace."Ina son wannan sunan a
bakin ka yaya na."?
Murmushi kawai yayi, yana k'ok'arin d'aura takalminsa tace." Na san dai yanzu kana shirin fita
ko."?
Yace." K'warai kuwa kiran wayarki ne ya dakatar dani, ina fata dai kun tashi lafiya? idan Uwale
na kusa bani ita mu gaisa."
Tace." Yau ma tana kicin tana aiki."
Shuru yayi ransa ya b'aci sosai, shin wai mai yasa Uwale ba zata zauna ta hutar da kanta ba.
Yace." Kema kina da laifi Hamra'u me yasa ba zaki kar'be ta ba."
Tace."Wallahi babu yanda ban yi da ita ba akan cewa ta bari amma taki amma dai bari naje
kicin din na same ta."
Yace." Yawwa kiyi min wannan k'okarin kafin na dawo kema zaki zauna ki huta tunda baki da
hakki akan hakan na ma fasa daukar masu aiki, ita matar gidan da kanta zata shiga kicin tayi
ayyukanta, babu ruwana da wani mulkinta."
Farin ciki kamar ya kasheta tace." To shikkenan Yaya na Allah ya dawo da kai lafiya."
Ya amsa da "Ameen kafin ya kashe wayar, ya cigaba da shiryawa.
To da kyar dai Hamra'u ta shawo kan Uwale ta fita daga kicin din, ita kuma ta d'ora a inda ta
tsaya, amma inaa! sai da hannu ya bambamta girkin tsaffi ya fita daban.
Ta kammala ta tsaf ta shirya wanda za'a akai wa Zinat din a kwando ta fito ta sheda mata cewa
ga abincin can a kicin.
Tace." Ai sai ki 'karasa ladan ki, ina nufin ki d'auka abincin ki kai mata, dama naga baki ta'ba
shiga kun gaisa da juna ba."
Tace." Uwale nifa bana san shiga sabgar matar nan tunda naga bata da kirki wallahi yanzu ma
kawai umarnin yaya na ne, amma ba don haka ba wallahi ba zanyi mata bauta ba, kuma kina
maganar na shiga gurinta domin mu gaisa ai ita ya kamata ta fara zuwa inda muke tunda mu ta
zo ta samu a gidan."
Tace."Hamra'u duk na gane inda kika dosa, kada kice zaki fito da kishin ki a fili har yarinyar nan
ta gane akwai wata ala'ka a tsakaninki da mijinta, ina so kibi komai a sannu a hankali."
Cike da jin haushin maganarta tace." To ni ina ruwa na don ta fahimci da akwai soyayya a
tsakanina da mijinta, dama abunda nake so ta sani kenan cewa akwai alkawarin aure a
tsakaninmu, bayan haka kuma Uwale naga kamar kin fi k'aunar ta a kaina, to bari na tuna miki
idan kin manta nice taki kafin ki nuna kulawa da kauna akan wata a kaina ya kamata ki nuna."
Ta ri'ke baki da mamakin maganganunta tace." Hamra'u rashin kunya zaki min daga fada miki
gaskiya shine zaki gaya min magana."
Fashewa tayi da kuka da fadin." A'a ni ba nufi na kenan ba, kawai dai naga abunda kike bai
dace ba shiyasa nai miki magana domin ki gyara dan gaskiya ba zan boye miki ba ina jin
takaicin halin ko'in kulan da kike nuna min wallahi da kin so da tuni UMARU ya aure ni amma
kin mayar da abun wasan yara." Tana kuka sosai take maganar.
Uwalen hankalinta ya tashi domin tunda take da yarinyar bata ta'ba yi mata rashin kunya irin na
yau ba, kuma tabbas ta sheda cewa yarinyar 'yar halak ce."
Tace."Kiyi hakuri ki daina kukan hakan, idan da wacce nafiso Umaru ya aura to kece ta farko,
sai dai kuma kin san komai nufi ne na Allah, duk yanda muka so ki auri UMARU idan Allah bai
nufa babu yanda za muyi, wannan auran kuma da yayi daga Allah yake domin shima da
bakinsa ya fada cewar kece za'bin sa, sai gashi kuma Allah ya kawo masa wata bayan ke,
bamu san alkairin da yake tattare da al'amarin ba, sannan kuma idan kin kwantar da hankalinki
kema idan da rabo zai aureki tunda yana sonki, amma ki daina fito da kishinki a fili akan
wannan al'amarin.'
Duk cikin maganganun Uwale babu na son zuciya gaskiya ce amma ita kuma sai ta kasa
fahintar hakan, ta juya al'amarin wata siga daban, ta kuma 'kullaci Uwalan a cikin ranta a
ganinta kamar itace bata so UMAR din ya aureta.
Hawayen fuskarta ta goge ta nufi dakinta mayafi ta yafo a jikinta, kicin din ta nufa ta dauki
kwandon abincin kai tsaye sashen Zinat d'in ta nufa.
Ta same ta zaune a falo cikin shiga ta alfarma, Alkyabba 'yar gasken, gold yaji a ko'ina har a
yatsun kafa, falon ban da k'amshi na mussaman babu abunda yake, kallo daya tayi mata taji
gwiwarta tai sanyi, Gimbiyar tana da wani irin k'warjini na mussaman wanda Allah ya huwace
mata.
Jin motsi yasa ta dago kanta tana kallon bakin kofar, lokacin ita Hamra'un ta juya tana rufe kofa,
bata dauke idonta ba har sai da ta juyo suka had'a ido.....Wani irin kallo ta kai mata wanda
gabadaya ya kashe mata jiki, daman abinda ta guda kenan.
Ta daure tayi mata sallama tare da k'arasawa kusa da ita da kwandon abincin a hannunta.
"Auntyna barka da asubah fatan kin tashi lafiya."? Cikin nutsuwa take gaisheta.
Kafin ta amsa sai da ta mula tukkuna!
Ta d'an janyo kwandon abincin da fadin." Ga kayan kari kummalo nan Uwale tace a kawo miki."
A d'age tace." Tsakanin ke da ita wacece tayi girkin."?
Kai tsaye tace." Ni ce nayi saboda Yayana ya bada Umarnin hakan cewa ita Uwalan ta zauna ta
huta, ni na gabatar da komai kafin ya dawo."
Ta jima tana kallonta gami da auna maganarta tace." Shin kece kika fada masa cewa kakarsa
tana min hidima."?
Shuru tayi ba tace komai ba.
Ta ta'be bakinta da fadin." Okey shurun ki ya bani amsa, ki tashi ki bani guri tare da wannan
tarkacan k'azantar da ki ka shigo min dashi bana bukata."
Ba tace