Showing 39001 words to 42000 words out of 46825 words

Chapter 14 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf

ganin kamar rainin
hankalin yayi yawa.

Yace." Asp ban doki yarinyar nan ba, ban kuma tozarta a gaban 'yan uwana ba, duk
maganganun da ta fada maka akaina ta fadi ne domin ta kare kanta, kuma babu yanda za'ayi
ta sheda maka laifinta, ni ne dai mugu! kullum kalmar da take kira na dashi kenan, to bani da
damuwa da hakan, amma ina so ka san wani abu, kamar yanda yanzu ka gama magana cewa
yarinyar amana ce a hannun mu to babu shakka ba zan zauna na zuba ido ina kallonta tana
aikata kuskure na kyaleta ba, dole na nuna mata kuskuran abinda ta aikata kuma ba zan yarda
da sakarci da rashin kunya ba."

Cikin tsare gira yake maganar har ya gama Asp din na auna maganganunsa kafin yace."
Gaskiya ne abokina amma kamar yanda na sheda maka cewa babu duka a sharadin aure to
don Allah ka kiy...........Cikin fusata! ya katse shi ta hanyar fadin." Wai shin waye ya fad'a maka
dukanta nayi ne? Asp ashe har yanzu ba kasan sharrin mace ba, ni Umaru na san abinda nake
kuma ina da ilimin addini dai-dai gwargwado ban doke ta ba kamar yanda kake tsammani face
na musulunci, amma kada ka sake yi min maganar duka domin na san abinda ya cancanta."


Asp din yay murmushi ganin yanda abokin nasa ya fusata! sai numfarfashi yake masa a kunne!
yace." Allah ya huci zuciyar *MAI DAWA."!* Ayi hakuri na fahimci maganarka naga ranka ya
'baci da wannan al'amari amma bari na bari ka sauka tukkuna sai mu karasa maganar."

Yana fesar da wani irin huci! na tsantsar bacin rai da damuwa yace." Ranka ya dade wannan
yarinyar bata isa ta shiga tsakanin abotarmu ba domin naga abinda yake shirin faruwa kenan to
ba zan yarda da hakan ba tun kafin tafiya tayi nisa zan dauki mataki."


Yace." A'a wannan gugar zana kawai kake min kace dai kawai na daina magana a cikin
al'amarinka kuma zan kiyaye hakan da ikon Allah." Kashe wayarsa yayi ba tare da ya saurari
da amsarsa ba.

Wani 'baci rai mai tsanani ya sake rufeshi, wai yau shi Asp ya kashewa waya ta dalilin abinda
bai taka kara ya karya ba, tunda suka hadu wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninsu ba, sai ta
dalilin yarinyar, dama sai da ya tsammaci faruwar hakan, ya rasa mai yasa Asp din baya ganin
laifinta, duk abunda zata aikata dai-dai ne a gurinsa, kullum shine mai laifi, ya kasa fahimtar
abinda yake kudundune a cikin zuciyarsa abokin nasa, yana zargin kamar sonta yake to idan ba
haka ba mai zai sanya ya damu da damuwarta haka?

Ya jima da wannan tunanin a cikin ransa kawai yana kokarin kawar dashi ne saboda baya so
zuciyarsa ta gazgata zargin da yake can cikin ransa.


Kai tsaye sashensa ya nufa yaje ya samu hayakin Shisha ya banka, ya samu relief a
zuciyarsa kafin yayi wanka ya fito har yanzu zuciyarsa babu dadi, saboda yanayin garin ana zafi
yasa ya shirya cikin 3qutar da t-shirt mai gajeran hannu, koda ya fito kai tsaye sashen Gimbiyar
ya nufa, yanayin yanda yake taka 'kasa da karfi shi kadai ya isa ya sheda maka cewa shi din
jarumi ne a gida da waje.

Koda ya shiga sashen nata hadimta ya samu suna kai kawo Baraka na gyare-gyare yayin da
Marakisiyya ke kokarin shiga kicin.


Sallama yayi suka amsa kafin su tsuguna har kasa su gaishe shi, amsawa yayi bayan ya
sassauta fuskarsa, sai da wuce tukkuna kowacce ta tashi domin cigaba da aikinta.

Tana zaune a bakin gado da kayan bacci a jikinta, da alamu ba ta jima da tashi a bacci ba tun
ba bayan sallar asubah da ta gabatar.

Kallo d'aya tai masa gabanta ya fad'i! tai saurin dauketa kanta tana auziyya a cikin
zuciyarta........Kayan dake sanye a jikinsa sunyi masa bala'in kyau! kwana biyu gani take yana
wani irin kyau! shiyasa ba ta fiye kallonshi ba saboda kada tayi abun kunya.


Shima nasa 'bangaran namijin kokari yayi gurin danne zulamarsa domin duk sanda zai tozali da

wani bangare na jikinta muguwar sha'awa kan taso masa yanzu ma abunda yake shirin faruwa
kenan, ya shiga dakin da karsashi da power! amma ganin ta a haka yana nema yasa ya rasa
kuzarinsa.

Ya iske inda take kawai yaja tunga ya tsaya a gabanta.

K'amshin turaran dake jikinsa ya dinga fizgarta haka kawai taji kamshin ya kwanta mata a rai.

Sun jima a haka babu wanda yayi magana, ita hankalinta yana kan wayarta tana tunane-tunane
shi kuma ya zuba mata na mujiya yana mata wani irin kallon kurrula.

Gabad'aya gabu'bin jikinta suka saki idanuwansa na da wani irin dafi, ko shima ya san da haka
wannan shine ba ta sani ba.

Shawarwari take da zuciyarta shin ta gaisheshi ko kuma ta tashi ta bashi guri.

Tana so ta dauki nasihohin da Asp yake mata a koda yaushe amma tana wani tunani gani take
kamar idan ta rusina masa ajin ta zai zube wannan shine abinda take gudu.

Da k'yar ta iya bud'e baki tace." Ina kwana."?

Bai tsammaci haka daga gare ta ba, dalilin da ya jefa shi mamaki kenan, a cikin kaso d'ari na
damuwarsa kashi hamsin ya zube dalilin wannan gaisuwar.


Bai amsa ba amma ya sassauta fuskarsa still idonsa na kanta kafin yace." Yanzu ki ka tashi
kenan."?

Shuru kawai tai masa domin a ganinta wannan ba hurumin sa bane.

Ya duba agogon dake daure a hannunsa, 10:30 na safe ya kalleta da fadin." Goma da rabi a
halin yanzu ina fatan kinyi sallah."

Ba tace masa uffan ba, ta mike tsaye, ya bita da wani mayataccen kallo kayan baccin sunyi
mata masifar kyau, lebansa ya dan ciza ya fesar da wani numfashi kafin yayi saurin tare mata
hanya don ganin tana kokarin barin gurin.

Karo na farko kenan da ta kalleshi.

Yanayin kallon da yake mata da yanda k'wayoyin idanuwansa suka rusuna yasa jikinta mutuwa,
ta dinga jin wata irin kasala na kokarin rufeta.

Hanya take kokarin sanjawa ya sake tare ta, gabadaya ya zuba hannuwansa cikin aljihun

3qutar din dake jikinsa.



Cikin bacin rai tace." Wai meye haka ka bani hanya na wuce."

Ya girgiza kanshi ido a lumshe yace." Ba zan baki hanya ba sai kin bani amsar tambayata."


Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Babu ruwanka da rashin ibada ta ko kuma kai ne kake bada
aljanna."


Ya girgiza kai da fadin.'' Ba ni bane amma hakkin kulawa dake yana hannuna mutukar kinyi
wasarere da addini da ibadarki to babu shakka nima ina da kamasho
"(zunubi)

Da gefan ido ta kalleshi har yanzu da sauran jin haushinsa a zuciyarta............Kawai saboda
tana so ya kyaleta yasa ta bashi amsa da fadin." Tun asubah nai sallah sai na kwanta okey
abinda kake so kaji kenan."

Yace." Eh abinda nake so na tabbatar kenan saboda haka kiyi duk wani uzurinki ina jiranki za
muyi magana." Hanya ya nuna mata da hannu alamun ta wuce.

Ba tace komai ba ta ratse shi ta wuce tana tunanin abinda yake tafe dashi.


Wanka tayi ta fito ta shirya tayi komai a kan idonsa, hakika ya shiga tashin hankali sosai amma
da yake yana iya sarrafa kansa beyi yunkurin yi mata wani abu saboda ba abunda ya shigo
dashi kenan ba.


Tana gyara daurin dankwalinta, ya cimma inda take, ta mirror ta ganshi a tsaye a
bayanta...........Gyara daurin dankwalin da ba tayi ba kenan ta fara kokarin barin gurin.

'Kungunta ya riko ya dan janyota jikinsa, ta kalleshi da mamakin abinda yake a fuskarta.


Dankwalin ya fara kokarin daura mata kawai ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah.

Sai da ya daura mata tsaf! sannan ya kai ta gaban mirror domin taga ni.

Sosai tayi mamakin yanda ya iya daura dankwali kamar mace, daurin yay mata kyau sosai, ta

dan saki fuskarta amma bata iya yi masa godiya ba, juyowa tayi kawai taji ta a jikinsa, da yake
yana daf da ita.

Ya dan rungumeta na second kafin ya cire ta daga jikinsa hannunta ya rike suka samu gurin
zama.


Yanda yake kula da ita yasa jikinta ya mutu, abinda take bukata kenan dama, wasa take da
yatsun hannuwanta tana sauraran maganarsa.


"Me yasa baki da sirri? me yasa zaki kira Asp a waya ki kai masa 'korafi akan abunda bai taka
kara ya karya ba, Zinatu mai yasa kullum kike daukata a matsayin macuci azzalimi, ko kina
tunanin Asp din ya fi ni sonki shiyasa kika fi yarda dashi a kaina, tsayin kwanakin ki a gidan nan
mai nayi miki na cutarwa, ko don na gyara miki kuskuranki shine kike ganin kamar ina cutarki."

Fashewa tayi da kuka ta daga masa hannu da fadin." Kaga baka da bakin da za kayi min wata
magana a yanzu, ka dauko ni daga gaban iyayena kazo kana kuntatawa rayuwata, me yasa kai
baka da uzuri a rayuwa, duk abunda na fada ai ba 'karya bane kuma kai ma ka san gaskiya
amma kake takewa, Asp kuma da kake magana a kansa dole na kira shi domin na sheda masa
abunda ke faruwa, saboda a gurinsa kadai nake samun sassauci."

Zuciyarsa ta cunkushe da tsananin bacin rai da takaicin kalamanta, hakan ya nuna masa cewa
Asp din ya fishi matsayi a zuciyarta.


Yayi namijin kokarin danne masifaffan kishin dake taso masa kafin yace.''Kina nufin Asp din ya
fini iya kalamai kenan."?


Ba ta iya munafurci da kumbiya-kumbiya ba, wannan dalilin yasa take zaune lafiya, ta kalleshi
da fadin." Eh shi baya zagi na duk abunda zanyi yana kokarin nusar dani cikin saukin kai,
amma kai kullum cikin aibata ni kake har ka iya fitar da hannu ka tsinka min mari! shin kai kad'ai
ne kake da 'yan uwa? nima ba daga sama na fad'o ba."

Yace." Wannan ne dalilin da yasa kika kira shi a waya kenan."?

"Eh shine dalili."

Ya girgiza kai da fadin.'' Okey bari nai miki magana ta 'karshe cewa duk sanda wani sa'bani ya
gifta a tsakaninmu ki ka sake kiran sa a waya wallahi tallahi kinji na rantse da Allah sai na

kwace wayar hannunki wannan shine hukuncinki."

Kallonsa tayi da mamakin furucinsa a tare da ita.

Ganin yanda fuskarsa take a murtuke yasa ta gazgata cewa zai aikata abinda ya fada, kawai
sai ta dauke kanta daga kansa tana zumbura baki.

Ya cigaba da cewa." Tun da muke abotarmu wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakanin mu ba sai ta
dalilinki, to ina so na sheda miki cewa ke baki isa ki shiga tsakaninmu ba dole na dauki mataki a
kanki idan yaso sai kiji dadin kirana da macuci da hujjah."!

Ita dai ba tace masa komai ba, har ya 'karaci fad'ansa ya tashi ya fita bata tanka masa ba.

Fitarsa daga dakin da kamar minti biyar Marakisiyya ta shigo, suka gaisa kafin ta sheda mata
cewa ta shirya mata abun kari.

A ya mutse ta kalleta da fadin." Marakisiyya yanzu bana sha'awar komai sai funkaso saboda
haka kije can sashen masu gidan ki basu uzuri na."

Tace." Shikkenan an gama ranki shi dade.'' Da sauri ta tashi ta fita domin isar da sa'kon uwar
dakin nata.


Hamra'u ce ta shirya masa abin kari mai kyau! ta kuma yi ado da kwalliya tamkar wata amarya,
bayan ta hada masa komai sai ta zauna a gabansa tana bashi labarai irin na ban dariya, yana
break fast din yana sauraranta sosai yake jin dadin abincinta da labaran da take bashi fuskarsa
sake sai murmushi yake.........Ita kuwa farin ciki mara misaltuwa ya cika zuciyarta dama babban
burinta kenan tasa farin ciki a zuciyarsa ta kuma janye hankalinsa, don dai kada ta wuce gona
da iri ne amma da tuni ta bashi abincin a baki.


Cikin wannan halin Marakisiyya ta shiga ta samesu.

Ita kanta sai da taji wani iri a zuciyarta, haushin Hamra'un ya rufe ta a ganinta hakan kamar bai
dace ba.

Gabadaya hankalinsu ya koma kanta, daga can gefe ta tsuguna kafin ta fadi abunda yake tafe
da ita.

Yayi jim! na minti biyu kafin yace." Okey babu damuwa je ki sheda mata cewa za'ayi mata
abunda take bukata."

Hamra'u ta kalleshi da mamakin furucinsa, idan bata manta ba, a kwanakin baya da bakinsa

yake cewa zai dauki mataki akan matar tasa amma shine yanzu ya kar'bi Uzurin ta, to ita dai
gaskiya ba za tayi mata bauta ba idan ma tunaninsa kenan.

Bayan fitar Marakisiyyar ya kalleta da fadin." Kin ji Uzurin 'yar uwarki ko."?

Ta d'anyi murmushi da fadin." Eh naji yaya na."

Yace."Kiyi hakuri ki shiga kicin ki mata abunda take bukata kafin komai ya daidaita."

Ta d'an sauke munafukar ajiyar zuciya kafin tace." Yaya na ban iya funkaso ba domin wancan
lokacin ma Uwale ce tayi mata ni idan nayi lalacewa yake."

Yace."Ayya! kinga yanzu kuma Uwale bata jin dadin amma bari na kammala na sheda mata ko
zata iya shiga kicin din."

Ranta ya 'baci jin maganarsa, wato uzurin matarsa har yafi rashin lafiyar kakarsa......Tai shuru
bata sake wata magana ba, da kansa ya dan fahimci wani abu amma bai kawo cewa kishi ne ya
ha nata bin umarninsa ba.


A kwance ya samu Uwalen tana bacci, baya tsammanin zai tashe ta, don haka sai kawai ya fito
daga dakin, ya kama hanyar fita, hankalinsa gabadaya yana kan gimbiyar ganin har sha daya ta
gota bata ci abinci ba.


Ganin yana kokarin fita yasa da sauri tace."Yaya na akwai fa maganar da nake so mu yi."
hannu kawai ya daga mata da fadin." Idan na shigo da daddare zamu tattauna." bai jira
amsarta ba ya kama hanya ya fice.

Ta ciji yatsa cike da bak'in kishi a zuciyarta ta kwashe kayan karin kicin ta nufa ta wasu irin
tunane-tunane a zuciyarta.


Shigarsa dakin besa ta dago kai ta kalleshi ba, hankalinta gabadaya yana kan wayarta hira
suke da Sakina tana bata labarin irin rayuwar bakin ciki da take a gidan auran nata.

Maganarsa ce ta dauki hankalinta ta daga kai ta kalleshi........"Kin tura baiwar ki kina bukatar
funkaso ko."?

Ta gyada kai alamun E......Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Uwale ba ta jin dadi ita kuma
Hamra'u tace bata iya ba me yasa ba zaki sanya hadiman ki suyi miki ba."

Ta dan ja numfashi kafin tace." Kawai nafi bukatar na gurin Uwalen yayi min dadi a wancan

lokaci amma ko da wasa kada kasa wata banzar bazara k'azama tayi min abinda zan ci domin
ban amince da hakan ba."

Ya dinga auna maganganun ta a cikin ranshi yace." Wacece banzar bazara kuma."?

Ba tare da ta kalleshi ba tace." Kafi ni sanin ta ka fad'a mata cewa duk abubuwan da take
aikatawa ina da labari amma idan na tashi yi mata hukunci ba za taji da kyau ba."

Maganar ta bashi dariya amma beyi ba, ya kalleta da fadin." Magana muke akan abincin da za
kici babu ruwana da banzar bazarar da kike magana ni bukata ta a yanzu kici abinci."


Kai tsaye tace." A bani abunda nake bukata mana."

Ya kai minti biyu yana kallonta kafin ya juya ya fita, ta bishi da kallon takaici! tsaki taja tana sake
jin haushinsa a zuciyarta a ganinta duk shine ya bawa yarinyar dama shiyasa take abunda take
so, Marakisiyya duk ta sheda mata abunda ta gani da idonta, za kuma ta dauki mataki a kansu
ba'ki d'aya."



*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/18, 12:09 PM] Matar Malam: *GJ*
*73&74*
Yana jin kunyar kiran Asp a waya saboda abunda ya faru a tsakaninsu, yana kuma tunanin
yanda za'ayi yarinyar ta samu abunda take bukata, bashi da ra'ayin yawace-yawacen gidan
abinci, wannan dalilin yasa yake tunanin kiran abokin nasa koda irin taimakon da zai masa, shi
a kankin kansa ya san hakan bai dace ba cewa da abinci da duk abun bukata a gidansa amma
ya tafi wani gidan barar abinci, babu shakka ba komai ne ya janyo masa hakan ba face rashin
samun nagartaciyyar mace. wacce bata kiyaye cikinta ba ballanatana ta kiyaye nasa da nauyin
yake a kanta.

Ajiyar zuciya ya sauke ya yanke shawarar kiran Asp din yayi......Suka gaisa da juna kamar wani
abu bai faru a tsakaninsu ba, cikinsu kowanne yay kokarin danne abun a ransa.

Cike da jin nauyi yake sheda masa Uzurinsa.

Asp din yay murmushi da fadin." Haba ai wannan ba'a abun damuwa bane abokina bari na kira
Madam a waya yanzu na sheda mata."

Yace." Godiya nake mutumin kirki Allah ya saka da alkairi."

Yana 'yar dariya yace." Umaru bana san yawan godiyar da kake min ai tuntuni na fada maka
cewa ni da kai mun zama daya saboda haka don Allah ka daina yawan yi min godiya idan wani
abu ya ratsa a tsakaninmu."

Murmushi kawai yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login