Showing 6001 words to 9000 words out of 46825 words

Chapter 3 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf

ajiyar zuciya wacce taso ta jefe shi cikin wani yanayi yayi saurin janye wayar
daga kunnashi, sai da ya daidaita nutsuwarsa sannan ya mayar da wayar kunnanshi da fadin."
Ke nake sauraro."


'Karamin tsaki taja za ta cigaba da magana ya katseta da fadin." Na tsani wannan da'bi'ar taki
ke kuma na fahimci abinda kika sa a gaba kenan rashin d'a'a da tarbiya, ayi miki magana kiyi
tsaki! to kada ki kuskura kizo gidana da wannan da'biar zaki sha wahala a hannuna."

Wani kuttun takaici yazo ya tsaya mata a wuya! wai gargadinta yake kamar wanda aka gaya
masa cewa tana san zama dashi al'amarin ya bata mamaki mutu'ka ta daure ta had'iye bacin
ran kafin tace." Magana nake so nayi da kai ni bakar magana nace ka gaya min ba saboda
haka ina so ka tsaya ka saurareni."

Ya kalli agogon dake kafe a dakin goma saura na dare dawowarsa kenan ya kwa'be kaya zai
shiga wanka ta kira shi, yace." Ni nafi ki Uzuri wanka zanyi yanzu naci abinci na kwanta domin
yau gabadaya a tsaye na yini ina bukatar hutu a halin yanzu saboda haka minti uku na baki
kiyi sauri ki fadi abinda ke tafe dake ina sauraranki.
Wata 'kwalla mai zafi ta ciko idonta, wai shin za tayi da wannan mutumin ne, wato bama shi
da cikkken lokacin da zai saurareta.

Hanci taja kamar ta fashe da kuka saboda tsabar bakin ciki da takaici tace." Matsalar kace
wannan, abinda nakeso na fada maka shine ni ba zan zauna gida d'aya da kowa ba, idan
wannan ne tunaninka sai ka sauya wani."


Ya jima yana jajanta maganar a cikin zuciyarsa kafin yace." A yanzu dai baki isa ki tsara min
yanda zanyi ba, ballanatana kuma kina k'arkashi iko na, kafin na san kowa a duniya Uwale na
sani, saboda haka akan ki dai ba zan rabu da ita ba Ina tare da ita, duk inda nasa 'kafa zata
ajiye tata, Idan kuma kina ganin zaki zo da gurin zama daga gidanku to ni zan baki fili ki dasa ki
zauna ke kad'ai, amma ni ina tare da Uwale muddun rai insha Allah."

Tace." Kana maganar nazo da gurin zama ai kasan nafi 'karfin wannan, kai ne matalauci ba'kon
arziki da har kake wani tutiya! da arzikin gomnati, to shikkenan tunda kana ganin ba za kayi
abinda nace ba, to kuwa kullum kana tare da bacin rai a cikin gidanka."
Bata jira jin ta bakinsa ba tayi saurin kashe wayar tana wani irin numfarfashi irin na b'acin rai!




*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[1/30, 6:24 PM] Matar Malam: *GJSR*
*47&48*
Cikin tsantsar 'bacin rai da damuwa ya samu gefen gado ya zauna yana auna maganganunta,
"Kai ne mataulaci ba'kon arziki wanda yake tutiya da arzikin gomnati to tunda ba zaka yi abunda
nace ba kullum zaka kasance cikin bacin rai." Wa'innan maganganun sune kawai suke masa
amsa kuwwa a kunne! babu shakkah auran wannan yarinyar bashi da fa'idah a gurinsa, Dole
abunda yake gudu babu makawa sai ya faru, tun kafin ta shigo gidansa ga irin furucin da take a
kansa da famliy nasa, Annabi SAW yace ku auri salihan mata masu hankali da tarbiya duk
wanda yake so ya gina zamantakewar auransa dole ya cire son zuciya gami da rudin duniya ya
nemi nagarta ya aura, yarinyar ta tara komai na hallita wanda zata iya ja ra'ayinsa amma ta
samu nakusu gurin mugun hali da rashin tarbiya, tana ta'kama da kudi da mulki da suffar jiki,
wannan dalilin yasa take ganin tafi karfin kowa babu wanda ya isa ya tursasata! dama haka

rayuwa take, ya jima yana addua akan Allah ya arzurta shi da mace tagari dalilin tsoro da
gujewa hallayarsu, hakan yasa be tsawwalawa rayuwarsa akansu ba duk da cewa yana da
bukatarsu amma bai bari hakan yayi tasiri a zuciyarsa da gangar jikinsa ba, ya cigaba dai da
addua da neman zabin Allah, sai gashi kuma Allah ya jarabceshi da auran yarinyar da
kwata-kwata tunaninsa be kai kanta ba, hakika kowane bawa yana tare da
jarrabawarsa...................babu shakka shigowar yarinyar rayuwarsa babban kalubane a
rayuwarsa tunda ya fahimci cewa shaid'aniya ce bata k'aunar zaman lafiya da kwanciyarsa
hankali, dole ya zage damtse a kanta ya nuna mata bambancin mace da namiji, babu ruwansa
da mulki da sarautarta domin basu ne a gabansa ba, mutukar an d'aura auran nan to dole ta
zauna karkashin ikonsa ko tana so ko bata so kuma ba zai yarda da shirme da shashanci ba,
kullum maganarta bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane to shine zai tabbatar mata da hakan
daga zarar ta shigo gidansa zai nuna mata cewa ita ba komai bace a gurinsa.

Da wannan tunanin ya shiga wankan yana sake jin tsanarta a cikin zuciyarsa duk wasu iskanci
da take masa bai ta'ba jin haushinta irin yau ba, in banda hauka da jahilci waye yayi mai kudi
da talaka idan ba Allah ba, maganar yana ci da gomnati ai halak yake ci ba sata yayi ba, to
duk wannan ma bai dameshi ba sosai akan yanda take kokarin kafa masa dokoki wannan
shine yafi 'bata masa rai! yana samun nutsuwa zai auri wacce zata kwantar masa da hankali
yayi rayuwar jin dadi da ita wannan shine shawarar da ya yanke.


*****
A cikin 'yan kwanakin da suka rage a daura auran gabadaya ta sauya tayi wani bal'in kayau na
mussaman fatar ta tamkar kasa harshe ka lashe domin kyau da taushi sai sheki take saboda
gyara na mussaman da Mamanta tasa ake mata, in ta zauna a guri kuwa har ta tashi kamshinta
yana gurin, tasha gyara ciki da waje, wanda yake janyo mata feelings sa'i da lokaci shiyasa
wani lokacin take fakar ido ta zubar da rabin maganin a toilet domin ita kadai ta san halin da
take shiga idan sha'awarta tashi,

Sosai ta jinjinawa mamanta ta kuma yaba da kokarinta a kanta, sai dai kash duk wannan
gyaran da ake har yanxu zuciyarta ta nan a kangare bata jin za taje gidan mijin nata da sigar
san zaman lafiya.


Asp ya kira wayarta suka gaisa a mutunce da yake yanzu ta saki jiki dashi dalilin matarsa aunty
Zeey kenan, suka dan ta'ba hira kafin ya shiga tsokanarta da fadin" Yau saura kwana biyu ki
zama amaryarmu ina fatan dai yanzu kun sansanta da mutumin naki."?


'Bata fuska tayi tace." Asp ka daina yi min maganar wannan mara kirkin abokin naka saboda ya
same ni a arha shine har ya samu damar kira na da *Matar ladan noma* to ka fada masa cewa
koda na shigo gidansa yayi kokarin samun zaman lafiya dani, idan ba haka ba wallahi sai na
hana shi kwanciyar hankali domin auranshi kaddara ne a tare dani, domin ni nafi karfinsa ni ba

matar k'ananun yara bace."

Maganganunta sun bashi haushi da dariya amma bai yarda yayi dariyar ba ya danne cikin
taushin murya yace." ZINATU wai me yasa ki ke haka ne? me kika dauki duniya? ita fa mace
duk isa da kasaitarta gidan mijinta shine mutuncinta, duk da bakya san abokina amma bai
cancanci haka daga gurinki ba, na tabbata cewa kece kika tunzurashi har ya kira ki da wannan
kalmar *Matar ladan noma* wanda ni kaina nasan ya fad'a ne domin ya 'bata miki rai amma
matan da za'a kira da irin wannan sunan kwata-kwata bakya cikinsu, ina mai tabbatar miki da
cewa abokina yana sonki, abunda yasa ki ka kasa gane kansa wannan dabi'un naki marasa
kyau! shi mutum ne wanda baya son raini ko kadan, yana da zafi! shiyasa bana so kije gidansa
da wannan dabi'un naki, don Allah kiyi hakuri ki dauka cewa auransa alkairi ne ki zauna lafiya
dashi da 'yan uwansa."


Baki ta ta'be da fadin.'' Asp ni ba zan yarda da wannan maganganun naka ba, kawai kana so ka
tsara ni ne idan ba haka ba yaushe zaka zo kana fada min cewa yana sona ai da yana sona ba
zai so bacin rai na ba, sannan duk abunda nace ina so sai yayi min amma tsakanina dashi
kullum ba'kar magana kafada masa cewa a shirye nake idan ya bukaci ya zauna lafiya dani
kansa, idan kuma tashin hankali yake bukata ashirye nake."

Da sauri ya tare ta da fadin." Mugun ji da mugun gani Allah ya tsare mu, bama neman tashin
hankali kullum alkairi muke nema ZINAT Abokina zuma ne (ga zaki ga harbi) duk da ban dade
tare dashi ba amma na karanci halayyansa tsaf, yana da saukin kai ga wanda ya fahimceshi
baya san tashin hankali zaku jima wani sa'bani bai shiga tsakaninku ba, mutukar ka kiyaye
abunda zai kawo muku samun sab'anin, ina so ki rike wannan don Allah na ro'ke ki, ki zauna
lafiya dashi kada ki bari shaid'an ya samu nasara a kanki.

Murmushin takaici tayi kafin tace." Ranka ya dad'e na rasa me yasa kake tsoron wannan abokin
naka kullum kai kenan gurin yi masa campaign kana kare shi to ni duk abunda zaka fada a
kansa ba zai sanya naji tsoronsa ba, ka fada masa cewa nafi karfin wannan b'akin kwallin da
yake rambad'awa a idanuwansa, kuma be isa ya firgitani ba."
Dariya yayi kafin ya girgiza kai da fadin." Kinga mu bar wannan maganar tunda kin kasa
fahintata, yanzu wane shirye-shirye kike yi game da hidimar biki."?


Baki ta ta'be ta yatsine fuska da fadin." Wane irin shirye-shirye sai kace wacce za tayi auran
so, ni babu wani shiri da nake kuma bana bukatar komai daga gurinku.

Yace." A haba dai gimbiya koda ba auran so bane yana da kyau ki d'an yi gyare-gyare domin ki
fita daban a cikin mutane kasancewarki amarya, wannan hakkinki ne, ki fadi ko nawa kike
bukata sai na tura miki yanzu."

Dariyar takaici tayi kafin tace." Ranka ya dade na fada maka fa duk campaign din da za kayi
masa wallahi baku isa ku sayi soyyayata ba, ka fada masa cewa har yanzu bai kai wannan
matsayin ba,har yaushe yayi arzikin da zai zo yayi wa mutane tutiya dashi."

Asp ransa ya b'aci da jin maganarta, Yace." Wai ke mai yasa kike hakane? ina yi miki kallon
mai ilimi amma kina aikata aiki irin na jahilai, Zinatu girman kai da izzah duk ba dabi'u ne
marasa kyau! don Allah ki daina sannan ki daina daukar kanki daban da mutane dukkaninmu
Allah ne ya hallice mu, shine kuma yayi mai kudi da talaka kuma shi yake bada mulki ga wanda
yaso ya kuma hana wanda yaso, kada kiyi mamaki Allah zai iya musayan miki rayuwa, ki zama
mak'askanciya wannan kadan kenan daga irin hukuncinsa, ki gane duniya dan Allah."

Shuru tayi da alama nasiharsa ta shige ta.

Ya sauke numfashi da fadin." Kin san Allah duk wannan kai da kawon da na keyi akan
wannan al'amari UMARU be sani ba, amma magana kadan sai kice ina masa campaign ai ba
sai munyi campaign ba tunda an riga an bamu kyauta wane campaign za muyi." Cikin zolaya
ya 'karashe maganar.
Ta kuwa fusata! da fadin." Ina ganin mutuncinka fa kada ka 'kara yi min irin wannan wasan."

Ya tsagaita dariyar da yake da fadin." Na daina ranki ya dade yanzu ake hukuma ce sai da
rarrashi duk da an bamu kyauta muna godiya domin mun san ba karan mu ne ya kai tsaiko ba,
dami a kala muka tsinta."


Ya mutse fuska tayi da fadin." Shikkenan ni zan kashe wayar sai an jima."

Yace." Ai bamu gama ba.

A k'agauce tace." Saura me kuma Asp idan kun kwantar da hankalinku saura 'yan kwana ki aka
kawo muku ni." Yace." Ni da kaina ma zanzo na dauke ki tunda kin san mutumin naki baya gari
yana gurin training ni ya bar wa wuka da nama."

Shuru tayi ba tace uffan ba.

Yace."Yanzu nawa kike bukata."? babu wasa yayi maganar.

Itama cikin rashin wasa tace." Bana bukatar ko kwabon ku."

Murmushi yay da fadin."Shikkenan tunda kin ce haka mu dai mun fita hakki dan kada watarana
ayi mana gori."

Cikin takaicinsa tace." Sai an jima kace ina gaishe da da k'awata."

Ba ta jira jin abinda zai ce ba ta kashe wayarta tana jan tsaki, gabadayansu haushinsu takeji,
magana d'aya da yayi itace ta tsaya mata a rai..........Inda yake cewa duk wannan abubuwan da
yake abokin nasa bai sani ba, ita ai ta dauka shine ya wakiltashi kafin yayi tafiyar yazo ya kafa
masa gwamnati a gurinta, tsaki mai tsayi taja kafin ta nufi toilet da bacin ran hakan a cikin
ranta.


Cikin baccin da ya fara daukarsa yaji alamun kira ya shigo wayarsa.

Hannu yasa yana laluban drowar da wayar ke kai.

Murmushi yay ganin mutumin shi ke kira.

Yasa wayar a kunnashi tare da sallama a bakinshi.

Daga daya bangaran Asp din ya amsa da fadin." Jarumi ya na jika wani iri ne ina fata dai
lafiya."?

Ya bude murya sosai da fadin." Lafiya lou wallahi bacci ne ya fara daukana kiran wayarka ya
tashe ni."

Yace."Okey yau kun dan samu hutu kenan."

Hamma! yayi kafin yace." Eh amma hutun duka na two hours shine dalilin da yasa na kwanta
domin na rage baccin dake idona.

Yace."Hakan yana da kyau mutumina, shin kana waya mutuniyar kuwa."?

Murmushi yay wanda ya tsaya iyakar fatar bakinsa ya fahimci wacce yake nufi shiyasa yayi
murmushin takaici.


Asp yace." Tunda naji wannan murmshin naka na san baka d'auki shawarata ba, UMARU na
fada maka fa dole a wannan ga'bar kai ka sauka kabi yarinyar a sannu a hankali kafin ta shigo
gidanka, idan ta shigo shine zaka nuna mata kai ne a sama da ita, har yanzu ka kasa gane
hallayar 'ya'ya mata, wallahi da ka dauki shawarata da tuntuni yarinyar nan ta bada kai bori ya
hau, na fada maka tana bukatar rarrashi da nuna kulawa mybe *Ilove you* wannan ka kasa
fad'a mata wanda ni nayi imanin da cewa abinda take bukata kenan."


Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Asp wannan yarinyar fa bahaguwace! kai ne har yanzu baka
fahimta ba kake ganin nuna kulawa ko kuma *I love you* zasu sanya ta daina rashin mutunc! a

haka take, haka Allah ya halliceta zan iya karyar mata da kaina domin samun soyayyarta ta
dizgani girmana ya zube a banza a wofi, ni bana wahalar da kaina a in da na san ba zan samu
biyan bukata ba.

Yace." Kai ne dai kake ganin haka, amma ni nayi imanin cewa kabi wannan matakin wallahi sai
ka sameta a hannu kuma ka gwada ka gani."


'Yar dariya yay da fadin." To shikkenan zanyi kokarin ganin nayi abinda kace duk yanda mukayi
da ita za kaji."

Yace."Yawwa haka nake so na ji yanzu nima muka gama waya da ita na kira ta domin jin
abunda take bukata na hidimar biki, tace bata bukatar komai daga gurinku kuma tace lallai na
sheda maka cewa duk irin campaign din daka turo ni gurinta to ba zaka samu abunda kake so
ba.
Dariya ya fashe da ita, ya dinga yi yana girgiza kai ya ma kasa magana saboda yanda dariyar
taci karfinsa.

Asp shima yana dariyar yace." Ai ban ta'ba ganin rigimmiyar yarinya irin wannan ba, amma na
fahimci nasiha tana ratsa ta wannan ma makami ne wanda ya cancanta ka rike hannu bibbiyu.


Dakatar da dariyar yayi da fadin." Asp maganar nan ta bani dariya da haushi wallahi amma dai
dariyar tafi yawa, lokacin da tace maka kana yi min campaign sai kace mata kai din
ubangidana ne kafi karfin kayi min fadanci ko wani aiki, amma na san da wuya ka iya mayar
mata da martani.
Yace."Ni da nake kokarin ganin an raya sunnah ma'aiki SAW yaushe zan dagula al'amarin ai
duk abunda tace dai-dai ne, amma ina kokarin ganin na nusar da ita idan tayi wani shirman."

Yace." Nagode sosai abokina, yanzu a wace matsaya kuka tsaya."?

Yace." Tunda tace bata bukatar komai namu shikkenan, amma na fada mata cewa kada daga
baya tazo da wata magana.

Yace." Kwarai kuwa tunda an fita hakkinta wannan shine sharadi."

Yace." To kaji yanda mu kayi da ita insha Allahu kuma za'a gabatar da komai cikin tsari amma
ya kake gani? shin a ranar da aka daura auran za'a daukota ko kuma sai washe garin ranar."?


'Dan 'bata fuska yayi da fadin.'' Aa ana d'aurawa ka d'auko ta, bana tsammanin ma mahaifinta

zai bari ta sake kwana a gidan mutukar an d'aura auran."

Yace." Okey to shikkenan hakan dama shine tsari mai kyau, insha Allah zanyi kokarin hakan ya
tabbata."

Yace." Godiya nake abokina Allah ya kara zumunci ya kuma bar abotar mu." Ya amsa da
"Amen ya rabb mutumina ka wuce aboki a gurina a matsayin dan uwa kake a gurina."
Cikin wani irin farin ciki yace." Haka kake a gurina wallahi jinka nake tamkar wanda muka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login