Showing 3001 words to 6000 words out of 46825 words
Chapter 2 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
abokinsa zai aura ce, dalilin da yasa ya tsaya akan al'amarin shi abokin nasa baya gari yayi
tafiya shiyasa ya tsaya masa akan al'amarin auransa." Wannan bayanin da yayi mata yasa ta
kwantar da hankali amma da tayi tunanin ko yaudararta zaiyi.
Tun ranar da aka kai wa Uwale kayan lefen domin tasa albarka, Hamra'u ta shiga tashin
hankali mai tsananin gaske, domin kasa zaman falon tayi ta shiga daki ta rufe kofa ta dinga
rafsa ihu! bakin ciki da bakin kishi kamar ya kasheta.
Uwale ta shiga dakin ta sameta cikin mummunan yanayi, ta zauna tana rarrashinta gabadaya
itama zuciyarta ta karye da al'amarin anya kuwa UMARU ba yaudararsu yake ba? a tunaninsu
duk shine ya fitar da kudi masu nauyi aka had'a lefan, al'amarin dai duka bai musu dadi ba, ace
ayi ta abu d'aya sai kace cin k'wan makauniya.
Tana kuka tace."Ashe Uwale har dake za'a had'a baki a tozarta ni! me nayi miki kika tsanani
har ki ka bada goyon bayan auro wata bayan gani, kin san kuma tsayin shekarun dana dauka
ina jiransa, me yasa zaku ci amanata."
Hawayen tausayinta ta share kafin tace." Hamra'u ashe duk abunda yake faruwa UMARU be
fada miki ba.?
Ta girgiza kai da fadin." Ni be fada min komai ba kuma kema ai be kamata ki 'boye min ba,
yana da kyau duk abunda yake faruwa ki sanar dani nasan matsayina."
Tace."Hamra'u kada ki zarge ni ko kuma kiga laifina akan wannan al'amari, wallahi ni kaina ban
san da maganar ba sai ana i gobe zai yi tafiyar nan yake sheda min halin da ake ciki, kuma ya
tabbatar min da cewa wannan auran da zaiyi ba zai hana ya aureki ba, al'amarin ne yazo a
k'urace shiyasa kuma kinga mahaifin yarinyar nan babban mutum ne wannan shine dalilin da
yasa beyi jayayya dashi ba, a yanda na fahimtashi shima Auran zeyi shine saboda ganin
mutuncin mahaifin yarinyar saboda haka ki kwantar da hankali UMARU ya tabbatar min da
cewa kece za'bin sa kuma zai aureki da ikon Allah."
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sassauci a cikin zuciyarta, idan ta fahimci maganganun Uwale
suna nuna mata cewar zai yarinyar ne saboda mahaifinta, ba wai dan yana sonta ba, wannan
dalilin shi kad'ai sanya zuciyarta yin sanyi, amma dai duk da hakan ba zata hakura ba sai ta
sake jin matsayinta a gurinsa.
******
Tsakanin Madam da Aunty Zeey amaryarta basa shiri sosai fad'a suke da juna, dalilin da yasa
ma kenan basa iya haduwa guri daya domin mutukar suka hadu to sai sa'ba ni ya gifta a
tsakaninsu, kuma ba kowa ke janyo rikicin ba sai Aunt Zeey maca ce mai bala'in kishi da ganin
ido, ta tsani Madam da 'ya'yanta don dai ita ma Madam din a tsaye take shiyasa take shakkarta
amma dai duk da haka idan sa'bani ya gifta a tsakaninsu sai sun buga, duk da ita Madam din
tana kokarin ganin ta kama girma da mutuncinta.
To wannan dalilin yasa Asp din be gayyaci ita Aunty Zeey gurin zuwa kai kayan lefen ba, sai
kawai ya bukaci mutane biyu daga b'angaran Uwale da wasu daga cikin 'yan uwansa da ita
Madam din da Nabila yace suje su kad'ai ya isa.
Hakan yayi wa Aunt Zeey din ciwo, domin ita babban burinta ta 'kulla abota da amaryar tunda
taji an ce 'yar sarauta ce take san k'awance da ita dama kuma tana kishi akan cewa duk matan
abokan mijin nasu kawayen madam ne, wannan dalilin yasa takeso tayi kwace Zinat din domin
samun abokiyar shawara.
Kasa hakuri tayi da abunda yayi mata ta kira shi a waya tana masa 'korafi akan me yasa zai
mata haka, ai itama matarsa ce me yasa komai zai faru Madam ce a kan gaba ita gaskiya ta
gaji da wannan abu, da yake yasan halinta sai ya rarrasheta da fadin shi beyi hakan da wata
manufa ba, amma tunda ya fahimci tana so tayi abota da amaryar to idan ya dawo zai bata
number ta sai su dinga gaisawa, hakan yayi mata dadi sosai tayi masa fatan dawowa lafiya.
Babu wanda be yaba da kayan lefen ba, domin 'karshen isa da kasaitar mace kenan, kaya ne
da aka kashe iyayen kudi gurin had'awa tun daga kan kayan shafe-shafe har kan under wears
babu na Najeria takalma da jakkunansu sunfi kala ashirin, bayan manya manya atamfofi da
lesuka da iyayen shaddudi da goyayen riguna na waje da mayafai masu asalin kyau da tsada,
fashion na sarkoki kam ba zasu lissafu ba bayan gold din dake cikin akwatinsu set uku, kaya
tamkar za'a bude sabon kanti..................Kowa ya yaba da kayan amma ban da ita, bata fito ta
nuna hakan a zahiri ba, sai dai har hazar yau da kayan sukayi kwana uku a gidan ba ta duba
taga meye a ciki ba, tana kallon dai 'yan uwanta suka d'ibar mata wasu daga ciki zasu bayar a
dinka mata, shuru kawai tayi saboda bata so tayi wata magana su samu sa'ba ni da juna, suna
ta murna da farin ciki gefe guda kuma suna shirye-shiryen yanda za'a gudanar da shagalin biki,
ita dai ido ne nata duk abunda sukayi daidai ne, ta danne komai a ranta taki ta nuna musu
zahirin abinda yake cikin zuciyarta.
Aunty Zeey sarkin shishshigi da iya waje sai da ta san yanda tayi ta samu shiga a gurinta, ta
waya suka k'ulla abota, kullum sai sun gaisa da juna, wani sa'in har ita aunty Zeey din take dan
bata labarin wasu abubuwan da suka shafeta da mijinta da kuma kishiyarta.......Tayi ta mamakin
al'amarin, wani lokacin idan taji tana zagin Madam da 'ya'yanta ta kanyi mamaki! Tace." Ni kam
kinga na zauna da matar amma ban ta'ba ganin mugun halinta ba.
'Kwafa take da fadin." Don ba kishiyarki bace shiyasa amma ki san irin zaman da za kiyi da ita
kuma kada ki dinga sakin jiki kina fad'a mata sirinki."
Dariya ta kanyi a duk lokacin da sukayi irin wannan maganar ta kanyi mamakin yanda mata
suke kishi akan namiji ita kam duk irin so da kaunar da takewa namiji ba zata lalace guri kishi a
kansa ba, a ganinta kishin da ake a kansu shine yake sawa suna iskanci yanda ransu yake so,
shiyasa ita da namiji babu mutunci.
Aunty Zeey ita ta maye gurbin aminiyarta Sakina wacce ta tafi yawan siyasa sai dai duk
abunda yake faruwa tana samun labari daga bakin k'awar tata, tana sa ran dawowarta kafin
d'aurin auran.
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[1/29, 10:25 PM] Matar Malam: í ¼í½’
*45&46*
Hamra'u duk irin bayanin da Uwale tayi mata besa ta hakura ba ta kwantar da hankalinta ba,
mugun kishin Zinatu take, gabadaya ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, gani take
mutukar ya auri 'yar sarauta to maganar auranta dashi zai sha ruwa, da ta gaji da wasiwahsi
da zuciyarta sai kawa ta yanke shawarar kiran wayarsa domin taji a matsayinta a gurinsa duk
da cewa tunda ya tafi tsayin sati biyu da kwanaki goma be nema ta ba ballantana ya kira
wayarta yaji ya take. Sai dai sa'i da lokaci ya kan kira Uwale su gaisa itama ba kullum ba, ita
Uwalen ke bata sak'on gaisuwarsa gare ta, gashi kullum kara sonsa take da kishinsa, sam ta
tsani wata mace ta kusance shi, gashi daj shine da bakinsa ya furta cewa yana sonta zai
aureta amma duk wasu hanyoyi na nuna kauna da so da kulawa baya nuna mata, yanda ta
lura kamar yafi bawa aikinsa muhimmanci a kanta.
Ta kira wayar tasa gabanta na dan fad'uwa! dalili bata san irin kar'bar da zai yi mata ba.
Koda yaga kiran nata beyi mamaki ba, sai da ya fita daga cikin jama'a sannan ya samu sararin
amsawa.
Murya a sanyaye ta gaisheshi tana langwab'ewa! ya amsa cikin kulawa da fadin." Ina fatan duk
kuna nan lafiya aiki ya hana ni samun sukunin kiran wayar ku mu gaisa, ina fata dai kina
samun sakon gaisuwata a gurin Uwale."?
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke murya na rawa tace." Eh tana fada min a duk sanda ku kayi
waya, amma yaya na me yasa ni ba za ka kira waya ta domin mu gaisa ba sai dai ka bada
sa'ko."
Rashin abun fad'a yasa yace." Bana samun lokaci ne kullum cikin aiki nake wannan shine dalili
amma kada ki damu har yanzu kina nan a cikin zuciyata."
Girgiza kanta tayi da fadin." Ina kokwanto akan maganar ka domin na samu labarin duk abunda
yake faruwa wanda ka boye min zaka auri 'yar sarauta wannan ne dalilin da yasa kake kokarin
ka juya min baya."
K'aramin tsaki yaja ya dan girgiza kai da fadin." Idan wannan ne tunaninki to ki daina domin ni
ba a haka nake ba, aurena da Zinatu Allah ne ya kaddara! ban ta'ba tunanin had'uwa da ita ba,
ballanatana har naji sha'awar auranta a raina, mahaifinta ne ya bani ita dalilin taimakon da nayi
mata, babban mutum ne mai mutunci da dattako wannan dalilin yasa na kar'bi auranta domin
yafi karfin alfarma a gurina."
Cikin jin sassauci sakamakon maganganunsa tace." To shikkenan ni yanzu na kira kane domin
naji matsayina a gurinka."
Kansa ya dafe cikin rashin san damuwa yace." Wai shin Hamra'u sau nawa ki ke so kin san
yaya matsayinki yake a guri na? na fada miki cewa ina sonki kuma ina da bukatar auranki
saboda na yaba sa kyawawan halayenki wannan shine babban dalilin daya ja ra'ayi a kan ki,
duk wasu kyale-kyale basa burgeni nagarta nake nema, amma duk da wannan bayanin da nayi
miki na fahimceki kina kokwanto aikana shin me kike nufi ne."?
Dan murmushi tayi kafin ta kwantar da murya da fadin." Kayi hakuri Yayana bana nufin komai
sai alkairi, na fahimce ka kuma na amince da maganarka amma don Allah ka dinga nuna min
kulawa sannan kuma tun kafin amaryar taka ta shigo gidanka ka sheda mata maganata domin
ta san da zamana a zuciyarka."
Maganarta ta bashi haushi da mamaki! Yace." Okey kina so ki tsara min yanda zanyi kenan."?
Yanda yayi maganar cikin shan mur yasa tayi saurin fadin." Aa ba nufina kenan ba."
Yace." Idan ba haka kike nufi ba menene na damun kanki? alamu sun nuna akwai wani abu da
yake zuciyarki game da ita Amaryar tawa, kin gane ko bana so ki fito da kishinki tun yanzu yin
hakan zai janyo mana samun sa'bani dake, bana son tashin hankali a gidana kiyi kokarin ganin
kin kiyaye faruwar wata matsala.''
A sanyaye ta bashi hakuri da fadin'' Zata kiyaye insha Allah, zuciyarsa babu dadi yayi mata
sallama ya kashe wayarsa ya koma cikin mutane domin cigaba da abunda yake gabansa.
*****
A can masarautar kuwa komai yana tafiya kan tsari wata hatsaniya bata 'kara tashi ba, sosai
Ta samu daidaito da zaman lafiya da 'yan uwanta, kowa yana kokarin faranta mata rai, kuma
Komai na bukatar rayuwa an tanadar mata har da bayi wanda za taje dasu gidan mijin nata
domin su bauta mata maza biyu mata biyu.
'Bangaran gyaran jiki kuwa har gajiya tayi domin kullum da kalar maganin da zata sha,
al'amarin da ya janyo mata mugun ciwon mara wanda take kwana dashi ta tashi dashi ga wani
ruwa da take zubarwa wanda ta riga ta fahimci ko na menene, haka nan take hakuri domin
samun farin cikin mahaifiyarta tasan idan ta bijire to za'a ji kansu abunda bata fata kenan
babban burinta ta samu ta rabu da ita lafiya.
Ya kasance yau saura sati daya daurin auran Sakina tazo gidan suka rufe kofa suna tattauna
maganar, tace." Kawata ni kuwa zan so ganin wannan mutumin da ya samu wannan gara'basa
shiyasa fa mutum in yana da dama a hannunsa ya dama tun kafin wankin hula ya kaishi ga
dare, don Allah dube ki sankaceciya son kowa kin wanda ya rasa baki da kirar Allah wadai kin
tara duk wani abu da ake bukata wanda ya kamata a ce kin kasance matar daya daga cikin
shuwagabbanin kasa amma zaki kare a auran wani dan kauye bagidaje mafarauci wanda yake
ci a karkashin gwamnati wallahi wannan al'amarin sam beyi min dadi ba."
Ido cike da 'kwallah tace." Ya zanyi Sakina dole nayi hakuri nayi biyyaya na zauna da mutumin
nan domin hakan shine kwanciyar hankalina wallahi nasan idan na bijire wa wannan al'amarin
iyayena suna iya tsine min albarka, Sakina baki ga yanda suke 'kaunarsa ba, haka mutumin
yake da masifar kwarjini da shiga zuciyar duk wanda mu'amula ta had'asu........Kai tsaye ni ba
zan kushe hallitarsa ba domin kyakykwa ne sosai gashi da kirar maza bashi da makusa fa,
domin duk wani abu da mace take nema a gurin namiji ya mallaka hausawa suka juma'ar da za
tayi kyau tun daga labara ake ganeta, kin ga dai ban san zahirin sa ba amma jarumtarsa ke
nuna min cewa shi din ba rago bane zai iya daukewa mace dukkanin bukatarta, amma hakan
besa naji ina sonshi ba, dalili shi ba abokin burmi na bane, naso an kyaleni na za'bi daidai dani
na aura amma shi kaf family nasa mutanan k'auye ne matalauta, shima din akwai gidadanci da
'kauyanci a tare dashi wannan dalilin da yasa na tsaneshi! nake jin kunya a danganta shi dani
a matsayin mijina, bayan haka bashi da wata makusa a suffar sa."
Tsaki taja da fadin." Wallahi kin bani haushi sai maganar suffa kike suffarsa ta banza da wofi,
me za kiyi da suffarsa ai yanzu ba'a duba wannan, gabadaya mata sun gane sunyi wayo yanzu
basa yarda su kai kansu gidan wahala, ni nan da ki gan ni ba zan ta'ba yarda na auri talaka ba
wallahi mai kudin gaske zan aura koda kuwa ya kasance tsoho tukuf babu ruwana da tsufansa
kudinsa nake bukata ya fadi ya mutu na samu rabona, idan kuma bukatar namiji ta kamani na
fita na samu wanda zai biya min bukata, abunda duk gasu nan mazan da kudi ko babu zasu
gamsar dake amma duk kin damu mutane da maganar suffa da kyau, nan gaba kadan ina
kyautata zaton kyawunsa ne zai rinjayeki ."
Girgiza kai tayi da fadin." Baki fahimci magana ta bane shiyasa kike ganin kamar nan gaba zai
iya jan ra'ayi na, kawai dai ina fada miki abinda yake zuciyata ne."
Tabe baki tayi da fadin" Ke nifa ban yarda ma dake ba wallahi anya kuwa babu soyayya
ba'kauyen nan a cikin zuciyarki, ni dai nasan mutumin da kake qi ba zaka zauna kana
kwarzanta shi ba."
Cikin takaici da jin haushin maganarta tace." Sakina mu bar maganar nan haka kada ki 'bata
min rai, tunda dai kin kasa fahimtata shikkenan bana so mu rabu da bacin ran juna."
'Yar dariya tayi da fadin.'' Kada kiyi fushi k'awata tsokanarki nake yi amma don Allah bari nai
miki wata tambaya."
Ba tare da tace komai ba ta zuba mata ido tana sauraranta.
Tace." Shin wanda za'a aura miki din mutumin wane gari ne."?
Jim tayi tana tunani kafin tace."Mutumin Katsina ne cikin wani karamin kauye dake karamar
hukumar malunfashi, duk wani binkice daya cancanta Maimartaba yayi akansa da iyayenshi
basu da wani aibu kaf family nasu mutanan kirki ne, sai talauci da yayi musu katutu! kaf d'insu
matalauta ne asalin sana'ar mahaifin shi korar jakai, yanda Maimartaba yake fada mana shi
kansa Umar din be taso da mahaifiyarsa ba sai kakarsa wannan shine abinda na sani.
Tace."Okay yanzu dai idan na fahimta can k'auyen zai kai ki ya ajiye."?
Girgiza kai tayi da fadin." Aa na fada miki yanzu yana aiki a karkashin gomnati a matsayin
jami'in tsaro, ya samu daukaka sosai dalilin jarumtarsa wannan dalilin yasa gomnatin mallaka
masa gida tare da abubuwan more rayuwa yana nan tare da kakarsa a gidan.
Murmushi tayi da fadin." Akwai hanyoyi masu sauki da za kiyi amfani dasu ki cuzgunawa
rayuwarsa, ki hana shi jin dadi, sannan ki hana shi zaman lafiya, ni zan zan baki shawarwari
masu kyau yanda za kiyi ki ha nashi kwanciyar hankali dashi da kakar tasa."
Ajiyar zuciya ta sauke cikin jin sasauci tace." Nagode sosai k'awata.
A daran ranar ta sake kiran wayarsa tun bayan kiran da tayi masa ya d'ankara mata magana
mai zafi, to wannan karon a shirye take dashi tayi alkawari kan cewa duk cin mutuncin da yayi
mata sai ta rama.
Koda yaga kiran nata beyi kasa a gwiwa ba ya amsa cikin muryarsa mai cike da amo!!
Ji tayi ta daburce sakamakon jin sautin maganarsa a kunnuwanta, da sauri ta aro jarumta kafin
ta fara magana cikin Izzah! da isa! tace." Kana jina dai ko."?
Ya maimaita maganar a fili da mamakin yanda take masa maganar gatsar kamar uwarsa.
Be tanka mata ba kuma be kashe wayar ba.
Ta sauke zazzafar