Showing 27001 words to 30000 words out of 46825 words

Chapter 10 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf

da zata girmama
ta kuma mutunta mu."

Gabad'aya suka amsa da fadin." 'Kwarai wannan hukuncin shine dai-dai Kawu."

Ya mi'ke tare da basu Umarnin tashi su fita, gabadaya har ita Uwalen suka fita duk jikinsu a
sa'bule.

Kai tsaye sashen Uwalan suka nufa kowanne da b'acin rai a fuskarsa, ganinsu a sa'bule babu
karsashi! ya sanya Hamra'u murmushi dama ai ta san za'a yi haka, da kamar ta hana Uwale
jagorantarsu saboda ta san hali, to amma hakan ma babu laifi sun ga halinta a zahiri a gaba sai
su kiyaye.
To Asp da kanshi ya d'auko daga airport kai tsaye Headquarter 'yan sandan suka nufa, nan ya
tarar da yanda abokan aikinshi da wakilan manyan manyan 'yan siyasan da sukayi dafifi gurin
taron shi, yaji dadin hakan sosai, ya saki fuska yana gaisawa da kowa, sai fatan alkairin suke
masa yana amsawa da farin ciki a tare dashi, a zahiri yana ganin 'kauna tun daga kan abokan
aiki da kuma jama'ar gari.

A takaice suka tattauna da Commissioner kafin ya bashi hutu na sati daya, Asp yace." Ranka
shi dade ango ne fa, ya kamata a bashi hutun wata guda ya huta sosai ya kuma ci angoncin sa
a tsanake." Cike da barkwanci yake maganar.

Yana 'yar dariya ya kalleshi da fadin." *GOJE* kaji abinda abokinka yake cewa."

Murmushi yayi yana kallon Asp din yace." Hutun wata daya yay min yawa sai kace mace na
dingi zama a gida, ranka ya dade sati daya ya ishe ni."

Asp din yace." Okey shikkenan tunda kace haka amma nasan nan gaba da kanka zaka nemi
hutun."

Dariya kawai yayi sam bai bawa maganar muhimanci ba, a ganinsa babu yanda za'ayi ya dauki
hutu na wata saboda wata mace.

Cike da wasa da dariya sukayi sallama da commissioner din wanda yayi kokarin danne bacin
ransa, domin ya tsani wannan kusancin dake tsakaninsu.


Tun a mota Asp din ya kira ta ya sheda mata cewa ta shirya kar'bar angonta gashin suna tare

yanzu iso gidan."

Gabanta ne ya shiga fad'uwa, ta tashi zaune tana sa'ke-sa'ke, ba wai tsoron haduwa take dashi
ba, kawai a jikinta takejin kamar akwai abinda zai faruwa a tsakaninta dashi.

Wanka tayi ta cancand'a ado turaruka masu dadin kamshi ta fesa a jikinta.

Sai dai tana fitowa falon tayi saurin toshe hancin ta, har yanzu akwai sauran wari da hamamin
mutanan 'kauyen.


Baraka ta 'kwalawa kira da suke kicin suna aiki.......ta fito da sauri tare da risinawa, har yanzu
hannunta na toshe da hancinta tace" Ki san duk dubarar da za kiyi wannan warin ya fitar min
a falo." Tana gama maganarta ta koma cikin dakin.

Baraka ta dinga bunka turaran wuta sako da loko na falon tana hadawa da air freshener da
turaran tsinke, amma ina warin daban kamshin turaran ma daban.

Motar tana parking yaran shi, da suke dakon! isowarsa suka mike tare da karnukansu! kafin
kice kwabo gurin ya kacame! da bushe-bushe! gami da gangi mai taken sunansa!

Fitowarsa daga motar ta sanya karnukan wani irin haushi!! gabad'aya suka cika gurin kafin su
zagaye shi sai koke-koke suke suna shanshana rigar jikinsa, da alama sun jima
kewarsa...........

Gabad'aya jikinsa ne ya rikice! kafin kice kwabo gumi ya fara yanko masa daga kowace
kusurwa ta jikinsa! ganin haka ya sanya yaran nashi cigaba da bushe-bushen suna masa kirari
irin wanda suke masa.


Rigar jikinsa ya fara kokarin cirewa, Asp ya zuba masa ido yana mamakin abinda yake shirin
faruwa...........Har singlet din dake ciki be bari ba duk ya cire ya mi'ka masa tare da rigar.

Ya kar'ba kawai yana kallon ikon Allah...................Ya kalli gabas! yamma! kudu! a rewa! kafin
ya kurma wani irin ihu!!! wanda ya jima beyi irinshi ba, aikuwa gurin gabadaya sai da ya
amsa!!! Ihun! sai da ya ziyarci cikin gidajen mutanan dake Barack din, Uwale ta zabura! ta mike
tsaye da fadin.'' UMARU ya sauka domin ga alama nan.........Mazan ne suka fara turareniyar
fita, su kuma matan suka cigaba da tsumayin shigowarsa.


Gabad'aya jikinsa ya bud'e Damtsan hannuwansa suka wani kumbura! jijiyoyi rad'od'o!! Sai
wani irin motsi suke. tsigar jikinsa duk ta mike! gumi sai karyo masa yake daga kowace ga'ba
ta jikinsa. ihun!! yake kafin ya fara yi wa kanshi kirari kamar haka.............!

*" Namiji uban maza!! UMARU! Uban UMARU! d'aga Tanimu, Kandagarki kurmar dutse mugun
makaganri sai kure! Naci dubu sai ceto! nayi tawa kuma nayi ta wasu! Ni ne K'adangaran
bakin tulu mai maganin wani Takadiri! guguwa! maganin barazana! Namiji a cikin maza!
UMARU mai masoya gabas! yamma! kudu! a rewa!!" Yana wani irin nishi yake kirarin tare da
dadura! wuka! a kowane sassah na jikinsa.*

Tun sa'ilin da ya fara ifece-ifecen! Asp din ya fito da wayarsa ya fara masa vedio sosai abun ya
bashi sha'awa, ya dinga masa vedio da hotona a lokacin da yake kai kawo a gurin yana ciccije!
baki tare da gurzar jikinsa da kaifaffar wu'kar! da ya fizga a jikin yaron shi Alba.

Kawu Ado ne ya k'araso gurin da 'kyar ya samu nasarar rike hannunsa, sai ya fara kwantar
masa da hankali yana shafa kirjinsa dake cike da gargasa...........Ya dinga sauka a hankali a
hankali amma har yanzu numfashinsa bai dai-dai ta ba.

Asp yayi serving din duk abunda ya d'auka ya mayar da wayar ajihunsa, in da suke ya nufa, a
hankali yasa hannu ya kar'bi kaifaffar wukar dake hannunsa, ya mik'awa Alban tare da bashi
umarnin mayar da ita gidanta.

Numfashi da huci kawai yake fesarwa gabad'aya hancinsa duk ya bude gumi shar'ban a
saman karan hancin, Asp din ya fara kokarin mayar masa da rigarsa, ya daga masa hannu
alamun ya bari.

Kawu Ado yace." Kyaleshi ya sarara tukkuna ai duk ranar da tsumin ya tashi mu kan rasa gane
kanshi

Yace." Okey to idan hakane kuwa yana bukatar hutu bari kawai mu shiga dashi cikin gidan."

Kawu Adon yace." Hakan shine maslaha.

Duk yana jin su tsabar rashin nutsuwa ya ha nashi magana, babu abunda yake bukata a yanzu
sai haya'ki walau na Shisha ko na Sigari.


Jiki a masifar sanyaye ta saki labulan ta samu gefen gado ta zauna tana jin wani fad'uwar gaba!
duk badakalar da take faruwa faru a kan idonta, domin itama tana jin azababben ihun! ta
zabura! ta mike tsaye da farko gigicewa tayi ta shiga neman ma'boya domin ba ta manta irin
kicimilin wahalar da tasha a daji ba, jin ihun!! yana kara karfi had'e da sambatu yasa ta gazgata
cewa shine ya sauka a gidan.
Gabanta na wani irin bugawa taje ta zuge window da kyar ta d'age lalube, duk da akwai tazara
mai tsayi hakan be ha nata hango cibad'idi'n da yake faruwa a gurin ba.

Mamaki take sosai akan al'amarin sa, wane irin mutum ne mai taurin kai wanda wuk'a duk kaifin
ta bata yanka shi, haka fa ya dinga yi a daji, ta dinga kuka domin ita a ganinta wannan

kaikkafar wukar a take za tayi kisa amma ko gezau! idan yana dadurawa jikinsa har wani tsalle
yake, gabadaya yanzu al'amarinsa tsoro yake bata.


Asp ne ya shiga dashi dakinsa ko'ina tsaf tsaf kamshi sai tashi yake wannan duk aikin Hamra'u
ne, domin tun bayan tafiyarsa ba ta bar aikinta ba, duk bayan kwana uku take shigowa ta gyara
ko'ina tasa turare.


Ya kalleshi da jajayen idanuwansa da suka rine sakamakon tashin tsumin jikinsa........"Bani
Sigari." Ya fada tare da mika masa hannu.......Da yake Asp din ma ya dan busawa sa'i da lokaci
shiyasa baya rabo da ita a jikinsa ko a motarsa sai ya shiga laluban jikinsa, babu ko kara d'aya,
da sauri ya fita domin duba masa a cikin mota.
Kasa hakuri yay ya mike ya fara binkice dakin, *Shisha* ya dauka ya zauna kasan kafet ya
fara tada hayaki, Asp ya shigo ya samu dakin ya turnuke bece masa komai ba ya zauna
gefansa yana kallonsa.


Sai da ya tabbatar da cewar ya sha'ki hayakin ya ishe shi sannan ya ajiye, yana fesar da
wanda yay saura a bakinsa.

Asp din ya kalleshi da fadin." Yanzu dai na tabbatar da cewar ka samu relief kamar yanda kake
bukata."

Shuru yay na minti biyu kafin yace." Alhamdulillhi wanka zanyi na huta domin bana
tsammamin zama da kowa a yanzu sai Allah ya kaimu gobe."

Yace." Hakan yana da kyau, yanda kayi wannan gumurzun nima zan so ka huta ka samu
nutsuwa kafin wani abu ya biyo ba......Ya mike tsaye da fadin." Bari na shedawa Gimbiya cewa
tazo ta had'a maka ruwan wanka ko."? Yana yar dariya ya kare maganar.

Kallonshi kawai yay yana mamakin furucinsa, shima Asp din be sake wata magana ba, ya
kama hanyar fita yana amsa kiran da akayi masa a waya.

Duk da ya damu yin wankan amma sai ya kasa tashi domin yaje yayi, kawai ya zauna jiran
zuwan yarinyar kamar yanda Asp din yace, amma shi a jikinshi yana ganin kamar hakan ba zai
yiwu ba, kawai dai ya biyewa san zuciyarsa ne.




*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta

WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/10, 4:06 PM] Matar Malam: *GSUR*
*63&64*



*ROMANTIC🙈*
Da 'kyar da jibin goshi Asp din ta shawo kanta har ta yarda da zuwa sashen angon
nata.........Asp din ya cigaba da kwantar da murya yana rarrashinta tare da bata tabbacin cewa
shi angon nata ne yake bukatarta a kusa dashi yana kuma da kyau taje ta kula dashi kamar
yanda sauran mata suke yi.
Ta kalleshi cikin rashin walwala tace." Ai shi ya kamata yazo guri na bani zan kai kaina ba,
kamar yanda ka fada idan ya damu dani to ya tako kafarsa yazo inda nake."

Ya 'bata rai da fadin." Zinatu idan baki min wannan alfarmar ba to babu shakka zamu 'bata
zanyi fushi dake irin wanda ban ta'ba yi ba, Zinatu kwata-kwata bana sonki da wannan dabi'un
kullum so nake ki zama mace ta gari, bayan haka kuma shima nai masa magana akan
abunda yake aikatawa ya kar'bi laifinsa domin da bakina da nasa yayi min alkawarin gyara
kuskuransa, saboda haka kema ki ajiye duk wata kiyayya da kike masa ki zauna lafiya dashi.

Jikinta ne yayi sanyi ganin yanda ransa ya ba'ci! Tabbas mutumin ya cancanta da komai
saboda mutumci da kuma hallacinsa, wannan dalilin ne ya sanya ta amince da Uzurinsa amma
ba dan ranta yaso ba.

Tunda suka doshi sashen gabanta yake wani irin faduwa ta rasa meye dalili.

Suka tsaya bakin kofar ya kalleta da fadin." Bisimillah ki shiga yana ciki ni dama munyi sallama
dashi zan wuce gida yanzu."

Shuru kawai tai tana kallonsa.


Had'e fuskarsa yayi don kada ta kawo wasa yasa hannu ya bude mata kofar falon, da hannu
yayi mata alamar ta shiga.


Wata irin ajiyar zuciya ta sauke! kafin ta dan girgiza kai, saboda gudun bacin ransa zata shiga
a ganinta ai shi ya kamata ace yazo gurinta, amma Asp yafi karfin alfarma a gurinta.

Tana shiga ya mayar da kofar ya rufe.........Ta tsaya bakin kofar falon tana bin ko'ina da kallo,
shuru kamar baya ciki ko'ina tsaf-tsaf! kamshi mai dadi sai tashi yake.

Ta jima a tsaye a bakin kofar falon tana sa'kawa da kwancewa kafin ta yanke shawarar da
zuciyarta take ba ta.

Tana kokarin bude kofar domin fita, gyaran muryarsa ya dakatar da ita.

Kasa juyowa tayi ballanatana taga halin da yake ciki.

Asp din ne ya kira shi a waya yace ya fito falo ga amaryarsa ya kawo masa, beyi kasa a gwiwa
ba ya fito sai kuma ya hange ta ita kadai tana kokarin fita.

Murmushi kawai yay yanzu ya fahimci manufar abokin nashi.

Kai tsaye gurin da take ya nufa, yana isa yasa hannunsa a kafad'arta.

Gabanta ya fadi tare da tashin tsigar jiki, wani irin rawa jikinta ya shiga yi.

Ya d'an juyo da ita domin su fuskanci juna.

Sosai tayi namijin kokarin kallonshi........wanda har yanzu babu riga a jikinsa sai dogon wandon
uniform na
d'in shi.
Rintse ido tayi gabanta na cigaba da fad'uwa, rayuwarsu a daji ce ta fad'o mata a rai.

Hannunshi ya d'auke daga kan fad'arta ya lalubi hannunta guda ya rike a nashi, Cikin taushin
murya yace." Amaryata."

Gwiwarta ta dinga rawa bata tsammanci haka daga gurinshi ba, ta dauka za su cigaba da
rigima kamar yanda suka saba a waya sai kuma taga akasin haka, koda yake a cikin
maganganun Asp ya sheda mata cewa abokin nasa zai gyara kuskuransa.

Zuciyarta ce tai rauni! ta kasa hasala komai tana kallo ya ja hannunta har cikin dakinshi ya
zaunar da ita gefan gado......Kafin yace." Abokina yace dani wai ya kawo min ke domin kiyi min
tausa! ki kuma hada min ruwan wanka ni nace kam *wane mutum!* ai idan tausar ce ni ya
cancanta nayi miki a matsayinki na gimbiya kuma amarya ko ba haka bane."
Kallonshi tayi tana mamakinsa, kamar bashi ne wannan masifaffan ba mai ba'kar maganar
tsiya.

Kafin ta ankara taji saukar hannunshi saman bakinta, tayi saurin kawar da kanta, bata yarda ta
sake kallonshi ba, abun nasa kamar yana kokarin wuce gona da iri.

Ganin yanda tayi rauni da yawa! yasa ya rabu da ita ya shige toilet din ya bar ta da mugun

mamakinsa.

Tana nan zaune ya fito daure da babban towel a jikinsa da wani karami a hannunsa yana goge
kanshi.

Ido suka had'a kawai ya sakar mata murmushi wanda yay masa bala'in kyau. dimples a
kumatunsa sai kace mace..............*"GIMBIYA TA.* Ta ji wani iri a tare da ita, tana bala'in jin
dadin ya kira ta da wannan sunan kamar a bakinsa aka kirkira.

Kusa da ita ya zauna da man shafawa a hannunsa.......Saurin janyewa tayi saboda kusancin
nasu yayi tsanani har yanzu mamakin al'amarin take mutum sai kace aljani, koda yake dama
dasu yake tu'ammali.


Da wayo da wayo sai da ya sake nani'karta ya mika mata man shafawar da fadin." Ki sha min a
baya na duk da na san nayi tsaurin ido amma ina neman alfarma."


Ta kalleshi a karo na farko da tayi magana tun bayan shigowarta............."Da can waye yake
shafa maka, nima da kaina nake shafa abina don haka kai ma sai kayi dubara ka shafa
abunka."

Ya sake kusantar jikinta sosai yace." Ni nake shafa abina yanzu ganinki a zaune a kusa dani
yasa nake miki sha'awar samun lada daga yau duk wani hidima da zakiyi min Allah zai baki lada
mai yawa kuma zan d'aga miki 'kafa ki shiga aljanna da ikon Allah."


Gabadaya ya gama kashe mata jikinta, ta dinga kallonsa tana tunanin wasu abubuwa a kanshi.

Man shafawar ya mi'ka mata da ido yay mata nuni.

A sanyaye ta kar'ba ta lakato a hannunta tana mutsikawa, ta rasa ma yanda tayi ta kai hannu
jikinsa, sai mutsika man take a tafin hannunta.

Hannunta ya kama ya dora a kan cinyarsa da fadin." Tunda ba zaki iya shafa min a baya na ba,
shafa min anan."


Da sauri ta cire hannunta tana galla masa harara!
Zumbura baki tayi da fadin." Ni wallahi ka takura min, abinda banyi niyya ba."

Yace." Ba kya san shiga aljanna madawwamiya ko."?

Shiru tai tana cigaba da mutsika man a hannunta duk ta zama wata iri sakamakon abinda yake
tsiro dashi, banbarakawai!

Ganin taki tayi abinda yake so yasa ya kyaleta yana nazari da tunanin hanya ta biyu da zai
bullo mata.


Tsaf ya shafe jikinsa da mai dama neman fitina ne kamar yanda ta fada da can waye yake shafa
masa.

Ba ta sake kallonsa ba har ya gama shiryawa yana fesa turare, kira ya shigo wayarsa.

Ya dauki wayar yana dubawa.

Gefan da take zaune ya kalla akayi katari suka had'a ido! bece komai ba ya janye idonsa tare
dasa wayar a kunnashi.

"Hamra'u ke za'ayi wa bangajiya ai na samu sashena tsaf yana kamshi mai dadi na kuma ga
daining cike da abinci iri-iri sannu kokari nagode sosai." da wannan maganar ya fara.

Jin ya ambaci sunan yarinyar yasa tai saurin kallonshi, wayarsa yake hankalinsa kwance ga
wani murmushi na mussaman a fuskarsa.

Mugun haushinsa ya turnuketa shin wai me yake nufi ne.?

"Bana bukatar komai Hamra'u hutu kawai nake bukata kuyi hakuri da safe zan shigo mu gaisa
sosai gaisuwata dake ta mussaman ce."

Daga daya bangaran tace."Shikkenan Yaya na, amma zan so nayi tozali da kyakykyawar
fuskarka dawowarka ta sanya ni farin ciki da wuya yau na iya rintsawa."

Farin ciki ya cika masa zuciya, a rayuwarsa yana masifar son kulawa da soyayya da kuma iya
kalami ta inda yarinyar ta siye zuciyarsa kenan.

Yana 'yar dariya yace."Ki kwanta kiyi barci zan zo miki a mafarki kar ki damu akwai amana a
tsakanin mu."

Be ji amsarta sakamakon jin bugun kofa kafin yai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login