Showing 33001 words to 36000 words out of 46825 words
Chapter 12 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
tarin sha'awar da take damunta lokaci gudu yay mata magani ta hanyar
romancing kad'ai! tana bala'in san irin wannan soyayyar shiyasa ta gaza ha na shi aikatawa, a
ganinta hakan ba zai shafi rashin jituwarsu ba, mutukar zai dinga bata kulawa irin wannan zata
amince amma ba zata yarda da ya rabata da budurcinta ba, sai ya furta mata kalmar so da
bakinsa ta tabbatar da gaskiyar maganarsa, zata iya zama dashi saboda wannan dalilin.
Ya fito ya sameta tana ta sa'kawa da kwancewa, ya kalleta da fadin."Ina fatan dai Kin iya
wankan tsarki ko."?
Cike da mamaki ta kalleshi wace irin magana ce wannan......Cikin gatse tace "Ban iya ba."!
Ya girgiza kanshi da fadin." Ban yi mamaki ba." ya fada tare da kokarin barin gurin.
Kallon takaici take masa tana mamakin rainin hankalinsa, ko ya d'auka ita din jahila ce."
Tsaki mai tsayi taja tana hararar bayanshi lokacin da yake kokarin sanya jallabiya.
Sarai yaji lokacin da take tsakin amma bece mata komai ba ya lura kamar hakan dabi'arta ce.
*(Yawan Tsaki ba abun arziki bane ballanatana ga miji, mata don Allah mu kiyaye kada mu bari
bakinmu ya saba da jan tsaki)* Cigaba yayi da shirya jikinsa yana tunanin hanyoyin da zai bi
gurin sauya mata munanan d'abi'u
Zanin les d'inta ta d'aura ta yafa dankwalin a jikinta ta nufi toilet tana jin wani irin bacin rai da
damuwa a cikin ranta, abinda ya faru a tsakaninsu duk ya dameta.
Toilet din ya bita lokacin tana tsugune da ruwa a gabanta amma bata fara wankan ba.
Tsayuwarsa ya gyara har da rungume hannu a kirji ya zuba mata ido so yake ya gani shin ta iya
wankan tsarkin ko bata iya ba.
Daburcewa tayi ta dan harareshi da gefen ido da fadin." Wai meye haka zaka sani a gaba kana
kallona ko kuma abunda kayi ne be isheka ba."?
Be tanka mata ba har yanzu idonshi na kanta kuma bashi da niyyar fita.
Ta sauke ajiyar zuciya tsaki take so tayi amma tana jin tsoron abinda zai biyo ba, haka nan ba
yanda za tayi ta fara watsa ruwa a jikinta kafin ta dauki soso da sabulu.
Ganinshi tayi a gabanta.
Ta kalleshi kamar ta kurma ihu!! shin wai wane irin takurawa ne wannan.
Ruwan dake gabanta ya zubar ya had'a wani duk tana kallonshi, ya 'bata rai da fadin." Ba kiyi
dai-dai ba bari na nuna miki."
Taji kamar ta gallawa fuskarsa mari! saboda takaici, da 'kyar tace." To dama wa aka haifa da
iyawa kowa a duniya ya ko ya."
Yace." Kada kiyi min rashin kunya ranki zai 'baci yanzu."
Ta kalleshi taga yanda ya 'bata rai! dauke kanta tayi zuciyarta cike da takaici
Rigar jikinsa ya cire amma ya bar gajeran wando ya tsuguna kusa da ita da fadin." Kalle ni
nan."
Saboda babu yanda za tayi yasa ta juya tana kallonshi.........Yace.'' Da farko za kiyi niyyar irin
wankan da za kiyi a zucci ko a fili kafin ki ta'ba ruwa, ina so kiyi min niyyar wankan janaba da
bakinki."
Ta zumbura baki da fadin." Wani abu mukayi gagarimi! wanda lallai sai nayi wankan tsarki."?
Ya kalleta da mamaki a tare dashi yace." Okey kin raina abinda ya shiga tsakaninmu kenan."?
Shuru tayi tana dauke kanta.
Ya girgiza kai da fadin." Akwai karanci ilimin addini a tare dake wankan janaba ya wajaba a
kanki dalilin ruwan da kika fitar, ko zakiyi min musu baki fitar da komai ba."
Shuru tai ba tace komai ba.
Yace." Kinji dad'i har wani ruwa na mussaman ya fita daga jikinki a lokacin nutsuwarki ta dawo
daidai wannan shine dalilin da janyo miki wanka domin tsarkake jikinki wajibi ne wannan,
maziyi kadai zaki fitar ki wanke abinki kana ki cigaba da ibada da wannan kawai addini ya
yarda."
Jikinta yay sanyi domin ita tayi tunanin tunda romancing kawai sukayi ba za tayi wankan tsarki
ba sai da soso da sabulu............*(Hakan yana faruwa ga ma'aurata masu 'karanci ilmin addini
za suyi wassani a tsakaninsu har su gamsuwa amma kuma ba za suyi wankan tsarki ba
saboda suna tunanin kamar janaba bata hau kansu ba, wannan ba dai-dai bane mutukar wani
abu ya fita kuma an ji dadi an samu gamsuwa to janaba ta wajaba dole idan ana so ibadah ta
cika sai an wanke wannan janabar.*
*_(Nawaitu gusulul janabati-far'kul hadasul akbari-Wal-asgari_*) Za'a karanta sai uku kafin
ta'ba ruwa alwala za'a fara d'aurawa a jika kai jagab da ruwa sai an tabbatar ruwan ya ratsa
ko'ina sannan sai a tashi tsaye a fara wanke b'angaran dama a zuba ruwan a ko'ina kafin a tafi
b'angaran hagu nan ma haka za'ayi sai an tabbatar da cewa ko'ina ya wanku sannan.
Da kanshi yay mata wankan tsaf! besa wani abu a ransa ba ballanatana hankalinsa ya tashi! ita
kuwa sai no'kewa take tana jin wani iri da nauyin sa, kawai dan yafi karfinta ne.
Tsaf ya kammala ya cire towel ya mika mata, da sauri ta kar'ba ta daura.......Karami ya dauko
ya daura mata a saman gashinta da yake ta digar da ruwa. ba tace komai ba ta kama hanyar
fita, jikinta duk sanyaye........Zanin les din da dankwalin ya d'auka yabi bayanta dasu a
hannunsa....
*SAI ALLAH YA KAI MU MONDAY DA IKONSAí ½í¹í ¼í¿»*
*AYI HUTUN K'ARSHEN MAKO LAFIYA*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/13, 9:08 PM] Matar Malam: *67&68*
D'aya daga cikin dogwayen rigunanshi ya dauko mata sabuwa ya mika mata da fadin." Kisa a
jikinki kafin gari ya waye ko."
Kallonshi tayi da fadin." To ka bude min kofa kawai na tafi guri na meye amfanin kwana na a
dakinka." ? Da mamaki a tare dashi yace." Kece kike ganin kamar kwanan ki anan bashi da
amfani amma ni ina mai tabbatar miki da cewar kwananki a dakina zai janyo miki samun lada
a gurin Allah, wannan shine abinda nake miki sha'awa.
Shuru tayi tana auna maganarsa, yanda ta fahimta kamar yana so suyi zaman lafiya ga yanayin
yanda yake kawo mata 'kauli da ba'adi Allah yace Annabi yace ba da son ranta ba ta kar'bi
rigar ta ajiye a gefanta, shi kuma bed din ya hau yana gyara bedshirt din daya cukurkude.
Breziyyar ta dake saman gadon ya mika mata, tayi saurin kar'ba tare da dauke kanta.
Bacci ne a idonsa saboda haka yana gama gyara shimfidar gadon ya kwanta tare da rufe jikinsa
da bargo, rufe idonsa yay yana addua a cikin zuciyarsa.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, jiki babu kuzari ta dauki rigar tasa a jikinta ba tare da ta mayar
da breziyyar ba pant d'inta dama yana toilet anan ta cire ta ajiye saboda ya riga ya b'aci dole
sai an wanke.
Can nesa dashi ta kwanta da yake blanket din mai girma ne ya ishe su rufa ba tare da wani ya
takurawa dan uwansa ba.
Ya bude idonsa ya hangeta a can nesa dashi ta juya masa baya bece mata komai ba ya mayar
da idonsa ya rufe yana sauke ajiyar zuciya...........Ya riga ta bacci saboda yanayin gajiyar dake
tattare dashi, ta dinga jin saukar numfashisa cikin nutsuwa hakan ya sake tabbatar mata da
cewa bacci mai nauyi ya daukeshi. Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara kwanciyarta idonta ta rufe
tana addua a cikin zuciyarta cikin ikon Allah itama baccin ya d'auketa.
Da asubah shi ya tashe ta bayan ya shirya zuwa massalaci, sai da ya tabbatar ta tashi tukkuna
ya fita.
Tana idar da sallah, ta nemi kayanta ta mayar jikinta, ba ta jirayi dawowarsa ba ta kama hanyar
sashenta.
Su Kawu Ado A massalacin suka same shi saboda haka ana idar da sallah, gabadaya sai suka
nufi gidan a tare kowanne cikin walwala da farin ciki, kai tsaye sashen Uwale suka nufa domin
gaisawa a tsanake.
Sai da yayi musabaha da kowannesu ya dinga tambayarsu iyalinsu da sauran 'yan uwa da basu
samu damar zuwa ba, Kawu Ado yace." Kowa lafiya lau UMARU suna maka fatan alkari.
Cike da jin dadi yace." Nagode sosai Kawu amma zaku dan kwana biyu kafin ku tafi ko."
Yace." Aa yau zamu tafi saboda dukkaninmu muna da ayyuka, muna jiran rana ta fito tukkuna."
Yace." To babu laifi Kawu hakan yayi, Nagode kwarai da wannan karamacin."
Yace." Babu komai Umaru amma ina da muhimiyyar maganar da nake so mu tattauna a
tsakaninmu."
Ba tare da ya Kawo komai a ranshi ba yace." To babu damuwa Kawu Allah yasa alkairi ne."
Yana murmushi yace." Alkairi ne da ikon Allah."
Uwale ce ta fara fitowa daga dakin kafin sauran matan su biyo bayanta............Ganinsa a zaune
yasa farin ciki ya rufesu.
Samun guri sukayi suka zazzauna kafin a fara gaishe-gaishe.
Sosai yaji dadin ganin yan uwansa maza da mata ya dinga biyewa shirmansu yana dariya da
yake a cikinsu akwai wanda wasa yake a tsakaninsu sai tsokanarsa suke yana biye musu suna
dariya.
Hamra'u ce ta shirya musu abun karyawa har kala biyu, tazo ta sheda musu cewa ta
kammala.Kawu Ado ya dinga sanya mata albarka da irin dawaniyyar da take dasu tun bayan
saukarsu a gidan.
Shima Umar din yaji dadin hakan, domin da babu ita to tabbas za'a ji kunya idan akayi duba da
irin kalar matar gidan, wanda a tunaninsa nauyin kula da 'yan uwansa yana wuyanta.
Sashensa ya nufa domin barin su suka karya a tsanake.
Dama bai tsammaci samunta a sashen ba, ya kalli agogon dake kafe a dakin tara saura na
safe.......Jalliyar jikinsa ya cire ya zauna gefan gado daga shi sai gajeran wando.
Wayoyinsa dake ajiye kan bedside ya dauka duka ya kunnasu..............tarin messages da suke
kan wayar ya fara dubawa, kafin yaji shigowar wani messenge din a daya wayar.
Da sauri ya dauka domin yana tsammanin message din daga gurin ta ne dalili number ta ce
kawai akan wayar sai ta Asp
Aikuwa itace take bashi amsar text din sa na jiya.
_" FARUK Kayi hakuri tun jiya ka turo min sako babu replay sai yanzu, kada ka samu damuwa
nayi maka alkawarin kare maka kaina, kuma duk rintsi ba zan bari wani abu ya ratsa a
tsakaninmu ba ni taka ce har abada."_
Ya karanta text din ya kai sau biyar, yana nazari da tunanin kalamanta........Murmushi kawai yay
yana mamakin al'amarin, ba zata bari wani abu ya ratsa tsakaninsu ba, amma mai yasa jiya ta
kasa sarrafa kanta sai yanda yayi da ita, aka ce wai maza sun fi iya yaudara to yau ya 'karyata
wannan magana domin ga yaudara nan kiri-kiri yana gani, be yarda da soyayyar da takewa
boyayyan masoyin nata ba.....Ba tare da ya bata amsa ba ya ajiye wayar, ya cigaba da duba
mai muhimmancin.
A nutse ta shigo da sallama a bakinta, shuru falon, da alama yana daki, saman daninig ta ajiye
kwandon abincin dake hannuna.
Tayi jim! tana dan tunani kafin ta yanke shawarar buga kofar dakin nasa.
Yana jin bugun ya tsammaci yarinyar ce, be so hakan ba, saboda yana gujewa abunda ka iya
zuwa ya dawo.
Jallabiyarsa yasa kafin ya bude mata kofar.
Ya dan saki fuskarsa tare da kiran sunanta.
Farin cikin ganinsa ya cika mata zuciya, wani irin kallo tai masa kafin ta amsa da fadin." Barka
da asubah Farin cikin zuciyata." Ya amsa da "Barka dai fatan kin tashi lafiya."?
Ta dan girgiza kai da fadin." Lafiya lau amma kwana nayi ina mafarkin ka." Murmushi yayi yana
mata wani irin duba, kafin bakinsa ya subce gurin fadin." Nima haka da kyar na iya rintsawa
saboda tunaninki."
Taji wani irin sanyin dadi a ranta, tace." Nagode sosai masoyina ga abun kari na kawo maka,
sannan ina so na gyara maka dakin ka."
Yace." Okey to godiya nake my love Allah yay miki albarka."
Ta amsa da "Ameen tana kokarin shiga dakin ya bata hanya yana bin bayanta da kallo,
yarinyar tausayi take bashi mutuka, ta jima tana dawainiya dashi da kakarsa babu shakka idan
bai aureta ba yayi butulci, nagartaciyyar macace irin wacce take da wahalar samu, dole ya
cika muradin zuciyarsa.
Tana tsaka da karkad'e bedshirt din breziyya ta fad'o kasan kafafunta.........Gabanta ne yayi
mugun fad'uwa, lokaci guda kafafunta suka shiga karkarwa!
Jiki a mace ta tsirawa breziyyar ido tana tunanin wani abu..............Wato daga dawowarsa har
wata mu'amula ta shiga tsakaninsu? shin ina 'kiyayyar da sukewa junansu take? wasu zafafan
hawaye ne suka k'wace mata tana gogewa wasu na zubowa, wani mugun kishi ne ya dinga
yun'kuro mata, ta dinga ji kamar ta dora hannu aka ta dinga zabga ihu! ko ta taji sassaucin
abinda take ji a cikin ranta.
Sosai take kuka sai kace wacce uwarta ta mutu! mugun haushin gimbiyar take idan akwai
wacce ta tsana a duniya to itace.
Ta gama gyara dakin cikin halin ni 'yasu kafin ta kama hanyar toilet tana had'a hanya kamar
wata 'yar maye, Wai UMAR din ta masoyinta shine ya fara mu'amula da wata mace ba ita ba.
Tana shiga toilet din taci tuntunbe da pant a k'asan ties, da sauri ta janye kafarta, gabanta ne
ya tsananta fad'uwa, ta jingina jikin bango(garu) idonta kuri kan pant din tana ayyanawa
abubuwa da yawa a cikin ranta
Da tasan mugun ganin da za tayi kenan da ba tayi sha'awar shigowa dakin ba.
Wani nannauyen abu yazo ya tsaya mata a wuya, ganin pant da breziyya ya gama kashe
karsashinta, al'amarin ya bata mamaki mutuk'a sam bata kawo cewa wani abu zai shiga
tsakaninsu a kusa ba.
Kafarta tasa ta ture pant din, cikin rashin kuzari da kunar zuciya ta gyara toilet din ta fito
zuciyarta dankare da kishin gimbiyar ji take kamar taje ta shake mata wuya saboda yanda take
jin wani bala'in haushinta a cikin ranta.
Tana fitowa suka hada ido yana zaune a daining yana karyawa, kallonta yake yana mamakin
yanda idonta yayi ja! da alamun kuka a tare da ita
Kasa had'a ido tayi dashi ba tare da tace masa komai ba ta kama hanyar fita.
Cokalin dake hannunsa ya ajiye ya kira sunanta.
Tsayawa tayi amma bata juyo ba.
Yace."Me ya sami idonki sunyi jawur! domin ba haka kika shigo."
Kamar me jiran kiris sai kawai ta fashe da kuka kariris! al'amarin ya bashi mamaki mutuka gaya!
ya mike da niyyar zuwa inda take, a gaggauce ta bude kofa ta fita tana share hawaye.
Sai kawai yayi tsaye a tsakiyar falon yana mamakin al'amarin.
Da yake sun shagala da hira a tsakaninsu babu wanda ya lura da shigowarta sai Ladidi wacce
ta kasance 'yar uwa Dayyiba wato mahaifiyarta.............Itace ta lura da shigowarta.
Sai kawai ta tashi ta bi bayanta dakin, ta sameta tana kuka!
Zama tayi kusa da ita tana tambayarta, sai kawai ta rungumeta cikin kuka tace." Ladidi na rasa
ya zanyi da rayuwata Umaru yana wahalar da zuciyata gani nake kamar yaudarata yake tunda
ya auri 'yar sarauta ba zai aureni ba.
Hannu tasa tana share mata hawaye tace." Hamra'u mu ma tunanin da muke kenan, muna
ganin kamar wannan yaro wasa yake mana da hankali domin idan da wacce ya kamata ya aura
kece duba da irin hallacin da ki kayi masa, amma saboda rashin adalci lokaci guda muka samu
labarin auransa da 'yar sarki, da muka fito muna magana kakarsa ta goya masa baya cewa ai
bashi yarinyar akayi ba a son ranshi ba ya aureta ba idan gaskiya ne al'amarin me yasa ba'a
had'a auran a lokaci daya ba, kakarsa Uwale ba taso ya aureki ba domin da taso ya aureki da
tuntuni anyi angama idan ma haihuwa ce da tuni kin haihu, amma babu komai, akwai hanyoyin
da zamu bi domin biyan bukatarmu domin ba zamu bar wannan daular ta wuce mu ba."
Tana sauke ajiyar zuciya tace." Ladidi wannan al'amarin dole sai an nemi taimako don ganin
tabbatuwarsa ki shed'awa Inna ta duk abunda yake faruwa domin a yanzu babban burina naga
na mallaki Umar a matsayin mijina uban 'ya'yana."
Tace." Kada ki damu daga zarar mun isa gida zanje na sheda mata duk abunda yake faruwa
dole sai ta tashi a tsaye domin idan lamari irin wannan ya tunkari mutum ba zama zai yi ba
sai ya tashi ya nemi taimako daga gurin Malamai."
*(Subahanallahi Allah kasa mufi karfin zukatanmu, Allah kada kasa mu gaza gurin neman biyan
bukata a gurinka, Allah ka sanya mana imani a zuciyarmu*)
Yana kokarin fitowa daga part din shi Asp ya kira shi, ya sanya wayar a kunnanshi da sallama a
bakinsa, Asp ya amsa yana 'yar dariya shima dariyar yay kafin su gaisa cikin girmama juna,
Yace." Ya kwanan amarya."?
Murmushi yayi tare da d'an sosa gemunsa yace." Ta nan lafiya yanzu zan shiga gurinta yanzu."
Yace ." A'a ban gane ba, kana nufin kace min ba tare kuka kwana ba"?
Yace." Tare muka kwana da