Showing 12001 words to 15000 words out of 46825 words
Chapter 5 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
kokarin kashe wayar take yayi
saurin fadin." 'Karfe nawa ma za'a daura auran."?
A kufule! tace."Ban sani ba."!! Kashe wayar tayi tana tsaki sai numfarfashi take na takaici da
'bacin rai!
Dariya yay mai yawa kafin ya ajiye wayar ya nufi toilet cikin wani irin farin ciki wanda ya jima be
tsinci kansa a ciki ba.
*'DAURIN AURAN* Ya samu halartar manyan mutane sarakai 'yan kasuwa da manyan 'yan
siyasa daga kowace jaha, daurin auran yayi albarka da yawa daga cikin mutanan da suka
halarci daurin auran sunyi mamakin rashin halartar angon, sai dai Asp beyi kasa a gwiwa ba
gurin sheda musu halin da ake ciki, hakan yasa wa'inda ba su sheda da UMAR din ba suka
sheda dashi da jamurtarsa amma mafi akasari jama'a sun san shi a hoto da kuma gidajen
television................ Asp bai samu kansa ba sai da ya tabbatar da cewa yasa jama'ar da suka
samu damar hallatar daurin a auran a mota, da yawa daga cikinsu 'yan uwan UMAR din ne da
suka dinga turereniya gurin zuwa daurin auran. wanda aka daura a garin KANO a fadar
maimartaba Sarkin gari..
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/1, 11:07 PM] Matar Malam: _Ina muku tallan group dina mai suna_
*MAR'ATUSSALIHA*
*Wanda na bude shi wata shida da suka wuce a lokacin 1k ne kudin register, yanzu saboda
yanayi na rayuwa yasa na mayar dashi #500 za kiyi register domin kasancewarki cikin group
din, matan aure da zawarawan dake shirin aure da 'yan mata masu shirin aure ku nake da
bukatar kuyi rigstar domin k'aruwarmu baki d'aya, akwai sirri da amana a tsakaninmu, duk wata
matsalar dake damunki ki sameni ta pravite insha Allah zan baki shawarwari wanda zasu
taimaka miki domin gyara kanki da zamantakewar auranki, 'yar uwa kiyi register da group din
MAR'ATUSSALIHA Insha Allah zaki samu mafita.......ga duk wacce take da bukatar biyan kudin
0542382124....Binta umar gtbank sai ki tura kudin ta wannan account din ki tura min sheda ta
wannan number... 07084653262*
*51&52*
Fitowarsa daga wanka yayi dai-dai da shigowar kira a wayarsa, koda ya dauki wayar ya duba
sai yay murmushi domin ganin sunan wanda yake tsammani a fuskar wayar
Yasa wayar a kunnanshi tare da sallama a bakinsa.
Daga daya bangaran Asp ya sauke ajiyar zuciya da fadin."Alhamdulillhi komai ya kammala an
daura aure cikin farin ciki da mutunta juna kowa ya kasance cikin walwala da farin ciki, bayan
haka daurin auran ya samu halartar manya mutane daga kowane sassah na kasar nan, anyi
taro an tashi lafiya duk jama'ar da suka samu damar halartar daurin auran daga b'angaran ka
kama daga 'yan uwa da abokan arziki da kuma yaran ka yanzu haka suna kan hanyarsu ta
komawa gidajensu da ikon Allah, muna rokon Allah ya bada zaman lafiya a cikin wannan auran
sannan ya mayar da kowa gidansa lafiya."
Numfashi ya sauke bayan k'are maganar Asp din yace." Na rasa da wane baki zan mika godiya
ta a gare ka, hakika ka cika mutum wanda ya tara duk wasu abubuwan da ake da bukatar
mutumin 'kwarai ya kasance, wallahi wayewar yau haka kawai na tsinci kaina wani irin farin ciki
wanda na kasa tantance ko na menene? bana gari ina wata uwa duniya ka tsaya min akan
muhimmin al'amarin da cancanta ace ni nake tsaye a kansa, Asp da izinin Allah ba zan baka
kunya ba, yanda ka tsaya kai da fata kaga tabbatuwar al'amarin nan, to nima nayi maka
alkawari zanyi iyakar bakin kokarina gurin ganin na zauna lafiya da yarinyar nan, kafi karfin
komai a gurina, duk irin kin al'amarin nan da nake tunda ka shiga cikinsa dole nayi mubaya da
kai da abunda kake so nagode sosai da sosai Allah ya saka da alkairi ya bar mana zumunci."
Murmushi yay da fadin." Haba babu komai wannan ba wani abun damuwa bane, dama ni fatana
ka yarda ka amince dari bisa dari da wannan auran, domin haka kawai nake maka sha'awar
auran yarinyar duk da a zahiri kai ka nuna cewa ba irinta kake da bukata ba, wannan dalilin ba
zai ha naka nan gaba ka auri wacce zuciyarka take so ba tunda kana da damar hakan, nagode
sosai da yanda kake mutuntani kana kar'bar shawarwarina daga karshe nake sake yi maka
fatan alkairi da samun zuria dayyiba."
Cikin jin dadi ya amsa da ameeen ya rabbi Allah ya saka da alkairi mutumina."
Cikin zolaya yace."Yanzu zan shiga cikin gidan domin samun dauko maka hoton amaryar taka
ko baka da bukatar hakan."?
Hannu yasa ya dan sosa sumar kanshi kafin yayi dan murmushi irin wanda ya saba, yace." Ina
da bukata mana, ba kaji bahaushe yace."Amarya ko tabuzuzu ce tana rike da kambutan sarauta
ba to ballantana ita wannan *GIMBIYA* ce mai lasisi wallahi haka kawai naji ina so nayi tozali
da ita."
Asp ya kyalkyala da dariya da fadin." Allah mutumina ai dama ni na san duk wannan abun da
kake iya fatar baki ne kana son yarinyar nan kawai ba zaka fito fili ka nuna ba."
Shima yana dariyar yace."Haka dai kake hasashe amma ni yar hanzu bana jin sonta a cikin
zuciyata."
Yace."Okey to shikkenan mu bar wannan maganar amma ni na san akwai ranar da tarihi zai
maimaita kansa."
Shuru yay bece komai ba har yanzu da kyakykyawan murmushi a fuskarsa sai wani sosa
sumar kanshi yake kamar wani mara gaskiya.
Asp din yace."Zan kashe waya zuwa an jima zaka ji ni."
Yace."Okey to shikkenan babu damuwa sai na jika din." Sallama sukayi da juna kafin kowa ya
kashe wayarsa.
To a can gidan Uwale kuwa hayaniya ce kawai take tashi tun bayan dawowar mazan daga gurin
daurin aure suka taru a gidan tare da sauran 'yan uwansu mata kowa na fadin albarkacin
bakinsa.
Da yawa daga cikinsu sun ji dadin kasancewar al'amarin, amma kuma akwai wa'inda suke
ganin kamar hakan cin fuska ne da kuma rashin adalci idan akayi duba da irin halarcin da
Hamra'u tayi masa bai cancanta ace saboda yayi arziki ya samu duniya ya juya mata baya ba,
ita ya kamata ace ya fara aure kafin wata mace.
Uwale da yake tana da hankali da tsinkaye ta dinga nusar dasu domin su fahimci cewa shi
UMAR din bashi da laifi domin yarinyar bashi akayi ba wai don yayi arziki zai guji auran ita
Hamra'un ba, kuma ya tabbatar mata da cewar zai auri ita Hamraun a matsayin matarsa ta
biyu...........Duk da wannan bayanin da tayi musu hakan besa hankalinsu ya kwanta ba domin
ita mahaifiyar Hamra'un ma kasa zama tayi a gidan rai a bace ta tattara 'ya'yanta suka
tafi........'Bangaran Ita Hamra'un, abun babu dadi domin tun waye war garin ranar take kuka duk
ta tsangwami kanta da kanta gani take kamar bukatarta ba zata biya ba , haka kawai take
tsoron hada kishi da 'yar sarautar tun ganin farko da tayi mata jikinta yay sanyi! 'Kawarta
Zabbah da tazo ta sake rikirkita ta da cewar had'a kishi da 'ya'yan sarauta bala'i ne domin basa
barin kishiyarsu ta zauna lafiya babu wanda be san gidan sarauta da asire-asire ba, saboda
haka dole itama sai ta tashi a tsaye mutukar tana so bukatarta ta biya.
'Bangaran uwar Hamra'un ma maganar da suke tattaunawa kenan da yar uwanta, inda suke
zuga ta kan cewa lallai dole ta tashi a tsaye domin ganin 'yarta ta auri UMARU idan ya kama
tabi malamai a kansa ba damuwa bace tunda duk wani abu da akayi masa shi ya janyo dalilin
rashin adalcin da yayi musu, idan ba haka ba mai zai sanya yaje ya auri wata bayan kowa ya
san abinda yake tsakaninsa da Hamra'u, ta bauta masa sosai ta kori duk masu neman auranta
akansa, ta zauna zaman jiransa, rana tsaka saboda yayi arziki zai je ya auri 'yar sarauta, ya
wulakanta yarinyar da tayi masa halarci, wannan dalilin yasa suke zugata kan cewa lallai ta
nemi taimako a gurin malamai domin janyo hankalinsa, idan kuma ta zauna to tana ganin daula
da jin dadi zasu wuce 'yarta wacce akayi gwagwarmar tare da ita.
Sosai Dayyiba mahaifiyar Hamra'u ta dauki hudubar 'yan uwanta tasa a zuciyarta cewa gobe
zakara ne zai bata sa'a yo ita da take a cikin garin Katsina to me zai gagareta, akwai malamai
iri-iri wa'inda zasu taimaka mata, duk asirin da ake fadi cewa gidan sarauta suna dashi, to ita ta
dauki alwashin bugawa dasu.
Tofah!!!í ¾í´”
*****
Yayi ta tsumayin Asp din shuru be turo masa hotonan ba, agogon dake daure a hannunsa ya
duba awa biyu kenan da wayarsu, ko wane irin hoto ne yaci ace an dauka ya turo masa haka
kawai ya 'kagauta ya kalli kwalliyar amaryar tasa.
Number sa ya nemo ya kira cike daso ya daga wayar, sai duk 'kagautarsa bai samu abunda
yake so ba, domin wayar haka ta k'araci 'burari Asp din be daga ba.
'Karamin tsaki yaja tare da dan ya mutse fuskarsa, ya ga alama fa zuciyarsa ta nema ta takura
masa.
Ajiya wayar yayi, ya dauki d'ayar dake saman drowar yana kunnawa ya shiga WhatsApp
number tace kawai data Asp a layin.
Ya duba status Asp ya dora hotonan daurin auran........Jama'a birjik babu masaka tsinke
harabar gidan sarautar cike da jama'a, murmushi kawai yake yana cigaba da duba status
din.......... Kowa ya halarci daurin auran a cikin abokan aikinsa da 'yan uwansa da kuma yaransa
su Alba da sauransu. hoton karshe shine Maimartaba Omar tare da maigirma Governor katsina
wato Nasiru Alkanawi dashi Asp din da kuma mutuminshi abokin fad'ansa wato Commissioner
of police wato Murtala Kabiru, serving din hoton yay a ajiye a gallery hoton yayi masa kyau
sosai.
Yana k'okarin sauka sak'on ta ya shigo, da sauri ya shiga yana dubawa hotonta ne kusan goma
ta turo masa.
Ya dinga duba hotonan d'aya bayan d'aya yana jin wani bala'in kishi na sukan zuciyarsa.
A zahiri dai shi ta turowa hotonan, amma a cikin rashin sanin ta, sai kawai ya tsinci kansa da
jin haushin kansa da kuma kishin kansa da kansa.
A zahiri shi ya kamata ace ta turowa hotonan a matsayinsa na miji a gareta. amma ta turawa
wani wanda bata da tabbas a kansa, wannan ya nuna masa cewa zata iya aikata komai bayan
da auransa a kanta.
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dauki daya daga cikin hoton nan data turo masa yay
magana a kansa.
"Wannan hoton yayi kyau sosai my love kallonki a yanzu ya jefe ni cikin wani hali mai wuyar
fassaruwa, gabadaya kin gama kashe min jikina ina jin sha'awar kasancewa dake a halin
yanzu, my lov ina kishin wannan mijin naki kada ki bari ya kusanceki ballantana wata mu'amula
ta shiga tsakaninku, ki rike min amanar kanki."
Koda ya tura mata sakon be sauka ba har sai data ta duba, ba tace masa komai ba sai emoji
data tura masa mai dauke da alamar kuka da ban hakuri.....Daga haka sai kawai ta sauka,
Cikin jin haushin abinda tayi ya kashe wayar ya ajiye yana nazari da tunani akan al'amarinta.
Kiran sallar la'asar ne ya katse tunaninshi, da sauri ya tashi ya nufi toliet domin daura alwala.
koda ya fito daga bandakin kai tsaye masjid ya nufa wanda yake cikin barrack din da suke
zaune........Da yawa daga cikinsu arna ne musulman cikinsu kadan ne, amma duk da hakan
akwai kyakykyawar alaka a tsakaninsu domin tsayin kwanakin da yayi tare dasu bai ta'ba
samun matsala da kowa ba.
Bayan fitowarsu daga masjid din Adewale abokin aikinsa wanda ta su tazo daya ya tsare shi da
hira, hakan ya zauna ya biye masa yana ta bashi labarin ban dariya cikin harshan turanci yake
magana domin hausar tashi bata fita sosai.
Kwanakin da yayi a cikinsu gami fa cud'anyarsa dasu yasa kwakwalwarsa ta kara bud'ewa
dama can sama-sama yana jin turacin amma ba kamar yanzu ba, ya na ji sosai kuma idan ta
kama yana sauya harshe yayi magana tamkar wanda ya jima a cikinsa.
Adewale mutum ne mai barkwanci shiyasa tasu tazo d'aya duk sanda basu da aiki sukan zauna
guri daya yay ta sauraran shiremansa yay ta kyalkyala dariya kamar bashi ba.
Kiran Asp ne ya shigo wayarsa yasa a kunne tare da sallama Asp din yace."Ka duba tuntuni na
tura maka sakon."
Yace."Okey to ina godiya sosai naje sallah shine dalili." Yace."Ba damuwa yanzu Ina
shirye-shiryen d'auko hanya amma ina tsammanin jirgi zamu bi."
Yace." Saboda me? zaku bi jirgi ina Kano ina Katsina ? da har sai kun shiga jirgi."
Yace." Wannan amaryar tamu ai daban take da sauran mata, idan da akwai abunda yafi jirgi to
a ciki zan kawo maka ita har Katsina."
Yayi yar dariya da fadin." Kana d'aurewa karya gindi wallahi, amarya babu ango a kusa ina
tausaya mata kwanan kad'aici."
Asp din yay dariya sosai kafin yace."Ka fara tausayawa kanka kafin ka tausaya mata
dukkaninku ababan tausayi ne."
'Yar dariya yay irin wacce ya saba da fadin'' Na yarda da maganarka amma ka mi'ka min sak'on
gaisuwata a gurinta ka sheda mata cewa daga yau ta fara lissafin dawowata."
Yace."Wannan kuma aikin ka ne, domin saura kadan na kammala nawa, sauran kuma ya rage
naka."
Kokarin magana yake Asp din ya kashe wayar
Ya cire wayar daga kunnansa yana murmushin da har yanzu ya rasa na menene.
Yana duba hoton nan Adewale ya leko da kansa.
Da sauri ya janye wayar don haka kawai yake jin kishin wani ya ga kwalliyarta.........duk da
hakan sai da ya hangota, ya kyakyala da dariya yana sake le'ka kansa da fadin."Oga wannan
yarinyar fa tana da kyau sosai ina san 'bakar mace domin tana da wani sirri na daban."
Wani irin kallo yay masa mai kama da harara kafin yaja karamin tsaki yasa wayar gaban aljihun
rigarsa ya mike da fadin." Kai matsala ta dakai shiririta haka kawai daga ganin matar mutane
kace kana so Adewale kana da son mata wallahi."
Yace."Ai sune jin dadin duniyar Oga hahahaha." Ya k'arashe maganar cikin dariya.
Girgixa kai kawai yay yana kallonsa da tarin takaicin shirmen da yake yace." Ni zan shiga ciki
na huta kafin magriba domin naga alamar yau shirmen naka yafi na kullum."
Shima tashi yay da fadin." Nima ina da uzuri yanzu zanje na gabatar sai mun hadu da daddare."
Hannu ya daga masa kawai, yana kallonsa yayin da yake kokarin barin gurin.
Kansa kawai ya girgiza kafin shima ya bar gurin cike da so ya samu zama a nutse domin samun
damar kallon hotonan amaryar tashi a tsanake.
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/2, 11:06 PM] Matar Malam: _Ina muku tallan group dina mai suna_
*MAR'ATUSSALIHA*
*Wanda na bude shi wata shida da suka wuce a lokacin 1k ne kudin register, yanzu saboda
yanayi na rayuwa yasa na mayar dashi #500 za kiyi register domin kasancewarki cikin group
din, matan aure da zawarawan dake shirin aure da 'yan mata masu shirin aure ku nake da
bukatar kuyi rigstar domin k'aruwarmu baki d'aya, akwai sirri da amana a tsakaninmu, duk wata
matsalar dake damunki ki sameni ta pravite insha Allah zan baki shawarwari wanda zasu
taimaka miki domin gyara kanki da zamantakewar auranki, 'yar uwa kiyi register da group din
MAR'ATUSSALIHA Insha Allah zaki samu mafita.......ga duk wacce take da bukatar biyan kudin
0542382124....Binta umar gtbank sai ki tura kudin ta wannan account din ki tura min sheda ta
wannan number... 07084653262*
*53&54*
Pictures din data tura masa a rashin sanin shi ta turawa, sun bambamta da wanda Asp din ya
turo masa a yanzu, wanda ta tura masa a yanzu tayi ado sosai sa'banin wanda ta tura masa
adon da tayi bai kai na yanzu ba, les din ne dai a jikinta amma kamar yafi na dazu kyau da
kudi, riga da siket ne dinkin ya karbi jikinta sosai tai kyau tai ado da gold wuya da hannu sai tai
amfani da set din jaka da takalmi da mayafi iri daya, mayafin a gefen kafada ta ajiyeshi, duk
jikinta a waje breast dinta sun matse a cikin rigar don har sun dan fito daga sama, kishin hakan
ya dinga sukan zuciyarsa ya cigaba da kallon hotonan wanda duk rabinsu ita da 'yan uwanta ne
maza da mata sai kuma wanda Asp din ya shiga akayi musu ita dashi, shi kansa Asp din
haushi ya bashi ya dinga jin kishinsa a ranshi, ganin yanda ya tsaya daf da ita bayan duk ga
tsaraicinta nan a waje a maimakon yay mata magana ta yafa mayafinta tunda dai su 'yan uwan
nata basu san abunda ya dace ba, shima sai yabi sahun su suna abunda bai dace
ba........'Karamin tsaki yaja ya cigaba da duba hotonan yana kokarin danne abunda ke cin
zuciyarsa.
hoton ta ida Sakina shine ya dauki hankalinsa, kallon fuskar Sakinar da shigar dake jikinta shi
kadai ya nuna masa zahirin ta, duk rashin arzikin dinkin