Showing 36001 words to 39000 words out of 46825 words
Chapter 13 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf
asubah ta gudu."
'Yar dariya yay da fadin." Taji maza kenan shiyasa ta tsere kai kuma ai kayi gaggawa."
Dariya yay kafin yace." Kai fa kake min fada na gyara kuskurana kuma nayi mata kalamai na
soyayya ta bada kai a garin hakan na kasa daurewa kawai na ragewa kaina zafi."
Cike da jin dadin faruwar al'amarin yace." Alhamdulillhi nayi farin ciki da jin hakan, wannan
shine mataki na farko da zai sa ku sasanta kanku, Allah ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba."
Ya amsa da "ameen suma ameen mutumin kirki nagode kwarai da karamci." Yace." Babu komai
Umar mun riga mun zama daya da juna idan ka shiga ka mika min gaisuwa gurin amaryar."
Yace." Za taji insha Allah." Sallama sukayi cikin mutunci da mutuntawa.
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/16, 3:25 PM] Matar Malam: *69&70*
Tun lokacin da Kawu Ado ya fara magana yake girgiza kai yana mamakin al'amarin, koda yake
ba abin mamaki bane idan akayi duba da irin rashin tarbiyar yarinyar, zagi da cin mutumcin
d'an adam abune mai sauki a gurinta, sosai ransa ya 'baci da irin tozarcin da tayi wa 'yan
uwansa dama abinda yake gudu kenan, yana k'aunar family nasa gaba da baya duk talaucinsu
da rashin wayewar su shi ba zai k'yamace su ba tunda sune k'ashin bayan samar dashi,
sannan tare dasu yayi rayuwa saboda haka ba zai zama wani abu a duniya ya wofintar dasu ba,
dole ya nuna mata muhimmancin 'yan uwansa domin a gaba ta kiyaye.
Kawu Ado ya sauke numfashi da fadin." Saboda haka Umaru mu ba zamu ce ka rabu da
yarinyar nan ba, taci albarkacin mahaifinta, amma tilas ka auri wacce tasan kima da mutunci da
darajar mu, ina nufin yarinyar nan Hamra'u itace wacce ya dace ka aura tun kafin zuwan
wannan al'amari, saboda haka wannan ba shawara nake baka ba umarni ne a matsayina na
wanda ya isa ya fada maka magana kaji, idan kuma ban isa ba to sai na cire hannuna daga
kanka."
Ajiyar zuciya mai zafi ya sauke kafin yace." Kawu ka isa ka zartar da ko wane irin hukunci a
kaina domin a yanzu bani da kowa sai kai sai kuma Uwale tare da sauran 'yan uwana ina
alfahari daku mutuka, kuma ya zama dole na sanya kafar wando guda ga duk wanda yayi nufin
tozarta ku, kamar yanda ka bani umarnin auran Hamra'u dama da wannan aniyar a cikin
zuciyata, domin na jima ina son yarinyar itama tana sona, ba tun yau ba yarinyar take
dawainiya dani, ta sadaukar da rayuwarta kaf a kaina, sannan kuma tayi min hallacin da ba
zan ta'ba mantawa dashi ba, mutukar na cika dan halak dole na saka mata da alkairi, auranta
kad'ai shine sakayyar da ya cancanta nayi mata, saboda haka Kawu kayi hakuri da wannan abu
da ya faru hakika banji dadi ba kuma zanyi wa tufkar hanci insha Allah abu makamancin
wannan ba zai sake faruwa ba."
Kawu Ado yace." To Alhamdulillhi naji dadin wannan magana, kuma nayi farin ciki daka
mutuntani tare da sauran 'yan uwanka, haka ya kamata d'a na halak ya kasance duk rintsi kada
ya k'yamaci asali da tushen sa domin duk abun da ya zama a duniya bai isa ya canzawa towo
suna ba, saboda haka wannan kalaman naka sun faranta min rai mutuka da gaske, Allah yayi
maka albarka ya kuma kare ka daga sharrin masu sharri."
Ya amsa tare da jin dadin irin adduoin da yake masa.
Gabad'ayansu har Uwalen ya tattarasu suka nufi sashen Gimbiyar, da yawa daga cikinsu
hakan be musu dadi ba, saboda tsira da mutuncinsu, koda suke 'yan kauye ai mutane ne kamar
kowa me zai sanya a dinga k'yamatar su har idan suka zo guri a dinga toshe hanci, wannan
shine abinda yafi 'bata musu rai.
Suka cika falon taf don wasu ma a tsaitsaye suka tsaya saboda babu gurin zama, ya kallesu da
fadin." Ku dan saurari fitowa ta yanzu." suka hada baki gurin amsawa.
Koda ya shiga dakin bacci ya same ta tana yi ga airpix a cikin kunnanta wayar kuma na saman
kirjinta..........'Karamar riga ce a jikinta mai karamin hannu gabadaya jikinta a waje mussaman
cinyoyinta, tsigar jikinsa tana tashi ya 'karasa kusa da ita, ya daidai ta nutsuwarsa, kafin ya fara
kiran sunanta.
Shuru bata motsa ba bacci take sosai.
Yasa hannu ya cire airpix din kafin ya bude muryarsa da kiran sunanta.....*"ZINATU."*
Bata motsa ba ballanatana ta san shigowarsa dakin.
Ya zauna kusa da ita yana jan kafarta.........Ya jima yana jijjigata kafin ta bude ido da mayen
bacci a tare da ita take ganinsa dishi-dishi, ya sake jan kafarta da fadin." Ki tashi wane irin
bacci ne haka saboda rashin hankali kuma kin sanya airpix a kunne kina bacci dashi.
Ta bude idonta sosai tare da kokarin tashi.
Kawar da kanshi yayi sakamakon hango pant d'in ta, rigar da ita gwara babu domin abunda ta
rufe kad'an ne a jikinta.
Tashi tai ta kama hanyar toilet sassan jikinta na wani irin rawa sakamakon rashin sutturar arziki
da babu a jikinta.
Ajiyar zuciya ya sauke bayan shigar ta toilet din ya cigaba da dabarar danne k'ulafucinsa.
Jin shuru bata fito ba ya tabbar masa da wanka take, tsaki yaja ya tsaya kofar toilet din da fadin.
" Malama kiyi ki fito akwai jama'ar da suke jiran ki.
Jin abinda yace yasa ta kudiri aniyar 'bata masa rai domin dai ta riga ta san jama'ar basu wuce
mutanan k'auye 'yan uwansa masu wari da hamami!
Koda ta gama wankan kin fitowa tayi tai zamanta a toilet din tana saka wasikar jaki, tayi hakan
ne domin ta bata masa rai bayan haka kuma tana gujewa kanta sha'kar wari! wanda ka iya
janyo mata tashin zuciya.
Buga kofar yay da karfin gaske! ya bude murya da fadin." Ke! wai ba zaki fito ba ne."'?
Tsaki! taja ta mike tana zumbura baki da gunguni ta bude kofar, suka hada ido, ganin yanda
idonsa yayi jawur yasa gabanta fad'uwa, tai saurin ra'be shi ta wuce tana jin shakkar sa a
zuciyarta.
Ya bita da wani irin kallo kafin ya girgiza kanshi ya bita har dressing mirror din da take zaune.
Tana shafa mai tana sauraran maganganunshi.
"Duk irin rashin mutuncin da ki kayi wa 'yan uwana na samu labari! ki saurareni da kyau! domin
ki kiyaye abunda kan iya kawo rashin jituwa a tsakaninmu, zan iya hakuri da duk abunda za kiyi
amma ba zan iya kawar da kaina gurin ganin kinci zarafin iyaye da kakanni na ba, bani da
kowa sama dasu, domin su sukayi min duk wani gata har na girma na kai munzali, wallahi na
rantse miki da Allah akan su, babu abunda ba zan aikata ba, saboda ni na san kima da
mutuncin iyayena, mutukar kina so mu zauna lafiya to dole ki mutunta min su ki kuma darajasu."
Ko gezau! duk maganganusa ba su isa su hana ta fadin gaskiya ba, ta kalleshi da fadin.'' Ina
so a fada min abunda nai musu wanda ya sanya ka zuwa ka tsaya a kaina kana kalubalanta ai
na dauka sai mutum yay laifi za'a tuhumeshi."?
Yaga kamar ta raina masa hankali da jan ido yace." Zaki 'karyata maganarsu ne? wanda ya
tabbatar min da abinda ki ka 'aikata ba zai miki 'kaharu ba idan yayi miki k'arya yayi wa? ki
kiyaye nifa."? jikinsa na tsuma! ya ke maganar.
Man shafawa ta dan lakato tana mutsikawa a hannuwanta kafin tace." Sai kaje ka tambayi shi
wanda ya fada maka cewa naci mutuncinsu idan sharri nai musu, mai zai sanya su shigo in da
nake suna wari! da tsamin hammata."!!
Hankalinta kwance take maganar domin bata tsammanin cewa hukuncin mai tsauri zai bi ta
kanta ba.........Wani bahagon mari yayi mata da bayan hannunsa, wanda ya sanya ji da ganinta
daukewa na wucin gadi.
Kai ta sunkuyar kasa tana mamakin al'amarin! ita ya Mara akan wasu gigidadawa!! wani katon
bakin ciki yazo ya tsaya mata a wuya.
Yana tsaya a kanta yana surfa mata bala'i tare da jajjada mata muhimmacin mutanan da take
rainawa har tana fadin duk maganar da ta ga dama a kansu.
Ta danne kukan da yake kokarin kufce mata tace." Ko zaka ce 'karya nake sai na fadi gaskiya
domin kai kanka wari kake ballanatana su, na fad'a din."
Hannu yasa ya gwa'be bakin! zafi ya hanata karasa maganar dake bakinta............Ido ta zuba
masa ganin yanda fatar goshinsa duk ta tattare sai wani irin gumi yake kamar ba sanyi safiya
ba.
Yanda yake rawar jiki yana kai kawo a kanta yasa ta tsorata, babu yanda ta iya haka ta shirya
jikinta, ya nuna mata hanyar fita da hannunsa, ba tace komai ba tayi gaba zuciyarta na wani
irin zafi! tsaki mai tsayi yaja kafin yabi bayanta.
ZINATU ba tayi musu 'karya ba da gaske take tsami da wari suke shima ya san haka ya kuma ji
warin a hancinsa amma saboda rashin gaskiya ya take.
Rashin gurin zama yasa taja ta tsaya a bakin kofa, ta daure zuciyarta da fadin." Ina
kwananku."?
Wasu daga ciki sun amsa wasu kuma sukayi mata kallon uku saura kwata *Yo a fad'awa
mutumin k'auye iyashegeí ½í¸…*
Bata damu da hakan domin ba sune a gabanta ba burinta taje ta amayar da aman da yake taso
mata.
Jinsa kawai take yana mata bayaninsu da nuna mata muhimmanci su a tare dashi, yawu ya
cika mata baki, duk ta rasa yanda za tayi, itama a karan kanta bata san abinda take sai dai don
ba yanda za tayi ne.
Duk irin dauke kan da take yana lure da ita, ransa idan yay dubu ya baci! ya daure ya cigaba da
cewa.
" Kada kiyi tunanin don kin fito daga gidan sarauta kinfi wasu kima da daraja! to ina so ki san
cewa babu wanda yafi wani a wannan duniyar face wanda yafi bautawa Allah, duk daya muke a
gurinsa, kuma shi yayi na burni yayi na kauye, kana kuma shi yayi mai kudi yayi talaka, yayi
sarki yayi bafade, mulki talauci arziki duk shi yake bayarwa ga wanda yaso, saboda haka ni
'yan uwana sun fi min komai a duniyar nan don haka ba zan lamunci kici zarafinsu ba, ina so ki
rike wannan, ki zauna a matsayinki na matata, suma su zauna a matsayinsu na jinina wannan
shine abinda nake so ki rike kuma kiyi aiki dashi."
Uffan bata iya cewa ba to yaushe ma ta samu sararin maganar bakinta cike da yawu.
Tana kallonsu suka tashi daya bayan daya suka dinga fita, falon ya rage su biyu, harararsa tayi
kafin ta bude daki ta shige kai tsaye toilet ta nufa ta zubar da yawun bakinta, tsugunawa tayi
zuciyarta na cigaba da hantsilawa......Dole dai sai da tayi aman sannan ta samu sassauci.
Tana fitowa ta samu Baraka tana gyara dakin
Kan Sofa ta kwanta tana mayar da numfashi tace." Baraka don Allah kiyi kokari a falon nan
wannan wari duk ya fice kinji ko."
Tace." To ranki ya dade insha Allah bari na gama gyara miki dakin."
Kai ta girgiza kafin ta rufe idonta tana kukan zucci! wai dangin mijin da take aure sune kucakai
masu warin daud'a daddawa da tsamin hammata! wannan al'amari yana daure mata kai, a
mafarki ba ta'ba tsammanin cewa za ta auri d'an 'kauye ba.
Hamra'u a ranar da al'amarin ya faru kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki taji
dadin yanda ya nuna mata muhimmancinsu bayan haka kuma tayi farin ciki sosai da
maganarsu ta karshe da Kawu Ado, domin kafin su tafi sai da ya jaddada mata cewa ta kwantar
da hankalinta UMARU zai aureta da ikon Ubangiji, wannan shine abinda sanya farin cikinta kara
nununkuwa.
Sosai ta dauki fushi dashi saboda abunda yay mata yayi masifar 'bata mata rai, da farko tayi
tunanin zama dashi saboda salon soyayyarsa amma yanda yake kambaba darajar 'yan uwansa
yasa duk taji ya fice daga zuciyarta, tunaninta ya za'ayi ta samu namiji wanda yay daidai da
rayuwata wanda kuma ya iya love irin nashi.
'Bangaranshi bai damu da shan k'amshin da take masa ba, domun shi a ganinshi bai ga abun
'bacin rai da daukar gaba ba, kuskure tayi wanda ya cancanta da ayi mata gyara akai shiyasa
ya tsaya kai da fata ya nuna mata kuskuranta saboda a cikin zuciyarsa ya kudirci zaman lafiya
da ita, saboda baya so famliy nasa su tsaneta saboda mugun halinta, shi zai iya jure duk
abunda za tayi masa amma ba zai yarda taci zarafin wani nasa ba.
Haka suka cigaba da zama tsayin kwanaki uku wata mu'amular arziki bata sake hadasu ba
kowa yana gurinshi, sai dai shi da safe yana shiga ya dubata, ta shuka masa tsiya idan bata so
ba, wani sa'in kuma a lalace zata amsa masa magana, kyaleta kawai yake ya nufi gurin Uwale
a can yake zama yaci abinci suyi hira, wanda hakan yay bala'in farantawa Hamra'u rai, cikin
zuciyarta ta dinga jin dadin yanda masoyin nata yake mu'amula da ita, a cikin kwanaki wata irin
shakuwa sukayi, gabadaya ta siye zuciyarsa da kyawawan halayenta wanda suke mutukar
burgeshi, a cikin ransa yake jin ina ma ace Gimbiyarsa ce take da wannan kyawawan halayen.
Asp ya kira shi a waya da muryar bacin rai yace." Umaru me yake faruwa ne? yanzu mu kayi
waya da mutuniyar a maimakon ta sheda min abunda ya had'a ku kawai sai ta fashe da kuka."
Ranshi ya d'an 'baci, a zuciyarsa baya son yawan kiran da Asp din yake mata, ya danne 'bacin
ransa da fadin." Ita ce ta kira ka ko kaina ka kira ta."?
Yace." Itace ta kira ni, da kyar muka gaisa kafin ta fashe min da kuka."
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Asp kuskure tayi na gyara mata shine take fushi dani tsayin
kwana uku bata saurarata to akan me zan damu kaina a kanta."
Yace." Idan ba damuwa ina so na san kuskuran ko akwai shawarar da zan iya bayarwa."
*Ina jin dadin comments dinkuí ¾íµ°í ¾íµ°*
*Sai dai ayi hakuri a kar'bi labarin a yanda yake, kada kuce lallai sai anyi muku yanda kuke so,
labarin yana dauke da darrusa daban-daban, ku cigaba da bina sannu a hankali domin samun
isar da sakon dana d'aukoí ½í¸Š*
*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*
*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/17, 7:51 AM] Matar Malam: *71&72*
Ajiyar zuciya ya d'an sauke kafin yace." Laifi tayi min wanda ya cancanta da ko wane irin
hukunci, to amma tunda ka bukaci sanin abinda ta aikata ba zan boye maka ba domin kai ma
ka taya ni nuna mata kuskuranta."
Cikin nutsuwa duk ya sheda masa abinda ta aikata bayan zuwan 'yan uwansa gidan.
Girgiza kai kawai yake yana sauraranshi har ya gama yi masa bayani ya sauke ajiyar zuciya
yana jimanta al'amarin, ko da yake ba abun mamaki bane yarinyar zata iya aikata abinda yafi
haka amma shi bai ji dadin yanda abokin nasa ya fifita 'yan uwansa akanta ba, ita ta sheda
masa cewa ya tozartata ya wulakantata a gabansu harda duka da mari wannan dalilin ne
yasa hankalinsa ya tashi mutuka! bayan mijinta to shine mutum na biyu wanda aka bawa
amanar ta, dole idan wani abu makamancin wannan ya faru yayi kokarin ganin an samu
maslaha.
Ya dan ja numfashi kafin." Yace." Gaskiya abinda ta aikata bata kyauta ba, domin ita gaskiya
duk inda take dole a fada, abokina iyaye sun wuce wasa! dalili kenan da yasa kowane d'a
nagari yake kokarin kare mutuncinsu, babu yanda za'ayi kana kallo wani ya ci zarafin iyayenka
ka 'kyaleshi, ban ga laifinka ba, amma kuma kamar hukuncin da dauka bai kyautu ba Umaru
kada ka manta cewa yarinyar nan amana ce a hannunmu bata da kowa a garin nan face kai da
kuma 'yan uwanka, sai kuma ni da iyalina, Umaru duka babu shi a cikin sharadin aure don
Allah ka kiyaye ka daina saurin hannu, domin hukuncin duka baya shirya mutum nasiha gami
da nunawa mutum kuskuransa shine ke sanya mutum ya shiryu ya kuma gane hanya mai
kyau."
Murmushin takaici yayi kafin yay kokarin danne b'acin ran dake taso masa yace." Duk naji
bayaninka Asp amma me yasa da farko ka nuna kamar ba kasan abinda yake faruwa ba."?
Yace." Saboda kawai ina so naji bayani daga bakinka, tabbas abinda ta sheda min gaskiya ne
tunda gashi baka 'karya ta ba, ka doke ta a gaban 'yan uwanka wannan ba dai-dai bane."
Asp yana da 'kima da mutunci a idonsa, dalili kenan da ya sanya ya kasa d'aukar mataki
akansa, amma da babu wannan darajar da tuni sunyi uwaka! ubanka! domin