Showing 15001 words to 18000 words out of 46825 words

Chapter 6 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf

dake jikin Zinat din yafi na ita Sakinar
mutunci, domin gabadaya wuyar rigar dake jikin Sakinar net ne nonowanta duk sun fito gashi
rigar ta matseta sosai ba mayafin arziki a jikinta sai wani uban gashin doki da tayi ado dashi,
gabadaya kamar ba 'yar musulmai ba..........Murmushin dake kan fuskokinsu shine ya nuna
masa cewa da akwai kusanci mai kyau a tsakaninisu domin hannuwasu ma a rike yake dana
juna.........Gabadaya yarinyar bata kwanta masa a rai ba, ba tare da ya gama kallon hotonan
ba, ya kashe wayar ya ajiye saman drowar haushi duk ishe shi.



Koda Asp din ya kira shi domin ya shada masa cewa suna jirgi shi da amaryar tasa, sharrin
zuciya sai kawai ya tsinci kansa da jin wani iri a ranshi, sai da yayi namijin kokari kafin ya iya
yi masa godiya, Asp din yaji muryarsa a dakile, yace."Mutumina ya akayi ne naji ka wani iri."?

Ya dan yi gyaran murya da kokarin kawar da abunda yake ransa yace." Normal ba matsala
idan kun sauka ka kira ni yanzu ina dan uzuri ne."

Yace."Okey to shikkenan ko na baka amaryar ne.''?

Girgixa kai yay da fadin." Aa bar ta kawai zan kira ta an jima idan ta huta." Yanda yake jin
haushinta ya san ba zasu wanye lafiya ba, shiyasa ya fadi haka.

Wayar ya kashe ya ajiye saman drowr ya tsirawa kasan kafet ido.

Alamu sun nuna yana son yarinyar nan, domin da baya sonta ba zai damu kansa har ya dinga
kishi a kanta ba.

Asp yafi karfin komai a gurinsa, kuma ya sheda cewa ba zai ci amanarsa ba, amma yana
mamakin yanda zuciyarsa take raya masa wasu munanan abubuwa akan Asp din wanda yayi

imani da cewa hakan ba zata faru ba, auziyya yayi a fili tare da korar shaidan din da yake so
lallai sai ya nuna masa aibun abokin nasa.


Hadiman ta wato masu yi mata hidima tare da motocin kayan garar da akai mata sune suka fara
sauka, duk girman store din sai da yay kadan gurin daukar kayan garar, babu abunda babu na
dangin ci da sha, da store din ya cika sai kawai aka jibge ragowar kayan abincin a harabar
gidan.
Asp sai da ya tabbatar da cewa komai ya kammala amarya na dakinta sannan hankalinsa ya
kwanta ya godewa Allah kafin ya kira wayarsa ya sheda masa duk abunda yake faruwa.

Yace."Asp nifa ban bukaci komai a gurinsu ba, me zai sanya akawo min abinci ina dashi ai ba
wai ina bukata bane."

Yace."Al'ada ce kawai kada ka damu ba wai dan ka gaza ko don baka dashi sukayi maka haka
ba alkairi ne kawai."


Yace."Idan za suyi ai sai ayi dai-dai gwargwado amma ace har mota goma ta kayan abinci me
zanyi dasu mybe ma kafin azo kan wani ya lalace kawai ka diba iya wanda kake bukata, sauran
kuma zanyi magana da Uwale domin ta bawa wanda ya dace."

Yace."Hakan da kayi yayi dai-dai, amma ni kam babu abunda zan dauka acikin wannan kayan,
akwai mabukatan da suke nema su ya kamata a rabawa.

Yace."Shikkenan tunda kace haka idan akwai masu bukata a bangaran ka sai ka basu duk
abunda ya dace."

Yace."Okey babu damuwa zan duba insha Allahu.

Godiya yayi masa sosai tare da ban gajiya kafin suyi sallama da junansu.


Tun bayan fitar Asp din daga gidan, take bin dakin da kallo, duk iya hangenta bata hango
abunda zata kushe a dakin ba, daga bedroom din har falon komai na kasar waje ne, kuma
tsarin yayi mata babu abunda zata nema komai a kwai wanda zata bukata, toilet biyu d'aya a
uwar daki d'aya kuma a falon, sai kicin dake can gefe a dai cikin falon, koda ta duba kicin din
shima a shirye yake da komai na bukatar yau da gobe, hakan yayi mata dadi dama bata
bukatar wani ya shiga sabgarta a gidan idan ba hadimanta ba.

Ta gama duba ko'ina ta koma bedroom din ta zauna gefen gado tare da zabga tagumi, to yanzu
fa wata sabuwar rayuwa za tayi tare da wasu sabbanin mutanan da bata san ya hallinsu yake

ba, koda yake a shirye take da kowa duk wanda ya bukaci zaman lafiya da ita bata da matsala
amma ba zata yarda da raini daga gurin kowa ba ciki kuwa harda wanda yayi dalilin zuwanta
gidan.


Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin akan irin zaman da za tayi da bagidajen mijin nata. Tsaki
taja mai tsayi ta girgiza kai a fili tace." Idan yaso mu zauna lafia zamu zauna idan kuma yazo
da tsiya to gidan ya tarar domin ba zan yarda da rainin hankali ba." Kamar dashi take maganar
sai girgiza k'afafu take.
Kiran wayarsa ne ya katse tunaninta, data duba taga shine sai taki d'aga wayar har sai da ta
katse.

Uzuri yay mata dan be kawo cewa iskanci ne ya ha nata daga masa waya ba.

A karo na biyu sai da ta kusa katsewa ta daga, ciki ciki tai sallama.

Be damu da abunda take ba ya amsa mata da fadin." Ya kike? ya kuma hidima da jama'a."?

Shuru tai ba tace masa komai ba.

Yace."Kin yi shuru ko baki da magana dani."?

Ta dan ya mutse fuska da fadin." Umm! yanzu bacci na keji okay sai da safe." Kokarin kashe
wayar take yay saurin fadin." Kada ki kashe waya ina da magana dake."

Ta fasa kashe wayar da fadin "Ina jin ka."

Jim yay kafin yace." Kina ina yanzu."? tambayar da yay mata kenan

Tace."Wace irin tambaya ce wannan."?

Dan murmushi yay kafin yace." Ke dai ki bani amsar tambayata."

Tsaki tayi niyyar ja, sai kuma ta fasa tace."Abokinka ya kamata ka tambaya ai."

Yace." Tun dazu nake kiran wayarsa bata shiga shine dalili.

Tace." Okey to gani yanzu a cikin gidanka zaune daki."

Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Alhamdulillhi dama abunda nake so naji kenan daga bakinki."

Numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Da bakin ki yanzu kike sheda min cewa kina cikin

gidana zaune a daki a matsayin matata ta sunnah, bana gari anyi komai an gama duk ta dalilin
jajurcewar abokina wanda ya tsaya min a cikin al'amara na, Asp hankalinsa bai kwanta ba sai
da ya tabbatar da cewa kin zama mallakina bayan haka kuma be samu nutsuwa ba sai da ya
tabbatar da cewa ya kawo ki har cikin dakinki ya ajiyeki kamar yanda ki ka sheda min a yanzu.

Ina so ki san cewa ni mutum ne mai tsananin kishi akan abuna, duk da ga yanda akayi wannan
auran namu cewa bana so bakya so hakan ba zai sa na zuba miki ido kiyi abunda ki ke so
ba.........Katse shi tayi ta hanyar fadin." Me kake nufi ne."? Yace ." Alkairi nake nufi dake."?
Shuru tai ba tace masa komai ba amma ya fara kai ta karshe........Ya cigaba da cewa." Yanzu
sabuwar rayuwa zakiyi domin aure ba wasan yara bane. Ki kiyaye mu'amula da wanda bai dace
ba, kada kiyi mamakin cewa ina can wani gari amma labarin halin da kike ciki zai sameni har
lokacin dawowata gida, ki goge number duk wanda kika san cewa ba muharramin ki bane kafin
na dawo, sannan ban yarda kije ko'ina ba, akwai securities da zasu sheda min shigarki da
kuma fitarki. idan kina da wata Matsala kina iya shedawa Asp domin dashi kadai na yarda
bayan shi ban yarda wata magana ta shiga tsakaninki da ma'aikatan gidan nan ba, wannan
shine abunda nake so ki rike a ranki kuma kiyi aiki da umarni na."


Wani bacin rai ne ya tsaya mata a wuya jin yanda yake mata magana cikin isa da gadara kamar
wani ubanta, koda yake tunda aka daura auran iyaye da kakanni ke mata nasiha cewa tabi
mijinta sau da kafa domin tunda ta riga ta bar hannun iyayenta to basu da hakki mai karfi a
kanta kamar yanda mijinta yake da hakki a kanta, dole ne ta bishi ta kuma bi umarninsa, yi nayi
bari na bari wannan sune irin nasihohin da aka dinga yi mata kafin kawo ta dakin mijin nata shi
kansa Maimartaba fada yay mata sosai akan biyayyar aure...............Ita kuma sai take ganin
kamar wannan shine dalilin da yasa su mazan suke nuna izzah! da gadara! akan matayensu
saboda wannan damar da Allah ya basu, gashi dai ita ko kwana daya ba tayi ba a gidan ya
fara kafa mata sharud'ai bayan ma baya garin amma yana nuna mata isa da mulki saboda
kawai yana wasu tunane- tunane marasa kyau a kanta, Ajiyar zuciya ta sauke tare da kokarin
danne bacin ranta tace." To i dan ka gama maganar ka zan kashe wayata.''

Ashe maganar banza take domin tuntuni ya kashe wayarsa ya bar ta da tata a kunne sai kace
shashasha.

Cire wayar daga kunnanta yayi dai-dai da zubar hawaye da take kokarin dannewa.

Ta jefar da wayar saman gado ta dafe kanta da duk hannuwa biyun kukan takaici ne ya kufce
mata!

Hakika an kassara mata rayuwa tunda har aka had'ata aure da bagidajen namiji wanda bai iya
lallashi da lallami mace ba, kullum bakar magana ce take shiga tsakaninsu, ya za'ayi ta iya
zaman aure dashi a haka, burin ta a rayuwa ta auri namijin da ya iya soyayya da kula da mace
sai gashi ta b'ige da auran bahagon mutum wanda ya rako maza duniya.

Ta jima tana share hawayen takaici kafin ta cire kayan jikinta ta nufi bandaki domin watsa ruwa
a jikinta.

Lokacin da ta fito yayi dai-dai da shigowar Uwale dakin, suna hada ido sai tayi saurin kawar da
kanta tana ya mutse fuskarta, kai tsaye dressing mirror ta nufa.

Uwale jikinta yay sanyi domin ta lura da irin kallon banzan da tayi mata.

Ta nuna kamar ba ta gani ba da 'yar fara'a tace."Sannu yarinyar arziki dama na shigo ne na
dubaki sannan na tambayeki ko da akwai abunda ki ke bukata, ga dai abinci can a falo ajiye
miki."

Uwale tafi minti biyar da gama maganar amma ko kallonta ba tayi ba ballantana ta samu damar
bata amsa, sai kawai ta juya jikinta a sanyaye ta bude dakin ta fita tana mamakin rashin
tarbiyar yarinyar.

Tana fita taja tsaki ta cigaba da shafa mai a fatar jikinta daga shi har kakar tasa haushinsu
takeji.

A sanyaye ta zauna kan kujera jikinta duk babu karsashi.

Hamra'u ta kalleta da fadin." Uwale ya naga kin dawo da jiki a sa'bule."?

'Yar dariya tayi da fadin." Aa ba wani abu ne ai Gimbiyar tayi bacci lokacin dana shiga gurin
nata."
Cikin rashin so ta bayyana mata abunda ya faru ta k'arasa maganar.

Tai 'yar dariya da fadin." Uwale kenan, jikina na bani akwai wani abu da ya faru amma tunda
kina boye min shikkenan."

Da sauri tace." Ke 'yar nan me zai faru kuma idan ba alkairi ba? ni babu wani abu da yarinyar
nan tayi min koda na shiga na sameta tana bacci sai kawai na fito nace idan Allah ya kaimu da
safe sai mu gaisa da juna kawai kuma sai ki zargi wani abu."

Yanda take magana da son kare Gimbiyar sai ranta ya baci kishi yasa ta ta'be baki tare da
mikewa da fadin." Ni zan shiga na kwanta sai da safe."
Ta bita da kallon nazari kafin tace."Allah ya tashemu lafiya." Da sauri ta bar gurin ranta a
masifar b'ace, Ta rasa gane mai yake damun Uwale, tunda Gimbiyar ta sauka a gidan ta rasa
nutsuwarta sai kai kawo take tsakanin kicin da falo da kanta ta shirya mata abinci mai dadi irin
na tsofaffin hannu, duk tana zaune tana kallonta tana rawar jiki ta dauki abincin domin ta kai
mata, sai gashi kuma ta dawo da jiki a sab'ule, tabbas wani abun ne ya faru amma wai sai take
'boyewa mata kome menene dalilin hakan oho! ita kam tayi alkawari cewa ba 'yar sarauta ba

ko wacece ita wallahi tayi rantsuwa cewar ba zata bauta mata ba, tunda dai ba zaman ta take a
gidan ba, itama Uwalen itace ta d'orawa kanta wahala amma ita kam duk rintsi ba zata yarda
ayi haka da ita ba.




*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/4, 3:24 PM] Matar Malam: *55&56*
Kayan bacci masu taushi ta sanya a jikinta, babu wani kuzarin kirki a tattare da ita, ta kwanta
kan gado tare da jan bargo ta rufe jikinta. Ido ta rintse bacci kawai ta keso tayi ko ta samu
saukin 'bacin ran da ya addabeta a zuciyarta, amma duk yanda taso ta gayyaci baccin yaki
zuwa, idonta tar mazai! har yanzu tana tunanin kausasan kalamansa a kanta, a mafarki bata
ta'ba tunanin cewa za tayi irin wannan auran ba, duba da yanda ta dinga katantanwa da tarin
maza masu mulki da mukamai daban-daban wanda suka mace a soyayyarta. Tabbas
maganar Sakina gaskiya ne in da take cewa a lokacin da kake dama ya kamata ka dama, idan
ba haka ba, to wanki hula zai kai ka ga dare, yanzu wa gari ya waya gashinan ta 'bige da auran
namijin da bata ra'ayinsa...........Idonta a lumshe take wannan tunanin tana kuma hasaso fuskar
b'oyayyan masoyinta wanda take jin bala'in sonsa a cikin zuciyarta saboda soyyarsa da kuma
iya kalamansa, shi kad'ai ne a yanxu zai kawar mata da b'acin ran dake damunta, amma kuma
haka kawai a zuciyarta take jin tsoron kiran wayarsa. zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta dan
gyara kwanciya tana takure jikinta guri guda kamar me jin sanyi koda yake hakan nan ta tsinci
kanta cikin wannan halin duk sanda za ta kwanta bacci ta dinga juye-juye kenan kafin baccin
ya dauketa sai an ja dogon lokaci tukkuna, daga nan kuma sai ta dingi mafarkai barkatai! masu
kyau da marasa kyau har sai garin Allah ya waye tukkuna, za ta tashi cikin tsananin sha'awa
domin duk yawanci mafarkan akan sex ta keyi alhalin sam bata kwanciya da abun a ranta,
wannan dalilin yasa tayi alkawarin cewa duk magungunan matan da Aunty's dinta sukayi mata
guzurinsa ba zata sha ko daya ba domin ta riga ta d'ora zarginta kan cewa duk magungunan
data dubga dalili, saboda da can ba haka take ba, duk yawan shekarunta bata ta'ba mafarkin
wani da namiji ba sai gashi kullum idan ta kwanta sai tayi mafarki gata dumu-dumu da namiji
suna sex yana biya mata bukata.


Bargon dake rufe a jikinta ta sake gyarawa kafin k'ira ya shigo wayarta dake saman bedside,
cike da mamaki ta dauki wayar tana dubawa ashe bata kashe ba ta kwanta.


Sunan 'boyayyan masoyi ne yake yawo kan fuskar wayar.

Gabanta ya dinga faduwa ta shiga nazari da tunani akan ta daga wayarsa ko kada ta

daga..........*"Ki goge duk number wanda ki kasan ba muharramin ki bane kafin na dawo, kada
kiyi mamakin cewa duk halin da kike ciki zan samu labari saboda haka ki kiyaye kuma kibi
umarnina."* Manganganunsa suka fad'o mata a rai, ta tsirawa fuskar wayar do tana kallo har ta
katse.

Ya sake kira still dai bata daga ba, sai bin dakin take da kallo tana tunanin ko da akwai wata
na'ura da ya daura a dakin domin ganin duk motsinta..............haka kawai take jin tsoron ya
kamata da wani laifi mussaman irin wannan ba wai don tana tsoronsa ba, yanda ta lura dashi
kamar shima yana zargin ta irin yanda wasu daga cikin jama'ar gari suke mata abunda ta tsana
kenan a zarge ta akan fasikanci, wannan shine dalilin da yasa take jin tsoron daga wayar
boyayyan masoyin nata.......Sai kawai ta yanke shawarar shiga whasp ta duba ko ya ajiye mata
sako.


WhatsApp ya shiga domin har yanzu ya kasa yarda da abinda zuciyarsa take raya masa a kan
yarinyar zai cigaba da gwadata har sai ya fahimci in da ta dosa.


Yaji dadin ganinta a online sai ya tura mata sako kamar haka.

_My love me yasa baki daga waya ta ba."_?

Ta bashi amsa kamar haka"

_Ai ba muyi da kai cewa zaka dinga kiran waya ta ba, idan hakan ma ta kama cewa nayi ka
bari ni zan kira ka, to mai zai sanya ka kira ni a irin wannan lokacin."_


Yace."
_My love menene a ciki don na kira ki na debe miki kewa, na san da cewa angon naki baya
gari shiyasa nake so na debe miki kewarsa._

Emoji ta tura masa na mamakin maganarsa.

Yace." _Kin san irin son da nake miki ne yasa nake bin diddigin duk abinda ya shafe ki mijin
baya gari yana gurin training ko ba haka bane."?_

Murmushi takaici tayi kafin ta tura masa da amsa.

_"Eh hakane maganar ka amma nayi mamakin yanda akayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login