Showing 24001 words to 27000 words out of 46825 words

Chapter 9 - GOJE Book 2 By Binta Umar Abbale.pdf

mata komai ba, ta yun'kura ta tashi tsaye, kwandon abincin ta d'auka ta kama hanyar
fita, zuciyarta cike da takaici da haushinta.

Kallon banza tabi dashi, cikin zuciyarta tana raya wasu abubuwa akan yarinyar, tabbas akwai
alamun munafurci a tare da ita.

Gabad'aya ta riga ta saki jiki tana jiran abinci mai dadi da gamsarwa irin na jiya, wannan shine
dalilin da yasa koda Marakissiya ta tambayata abunda take bukata ta dakatar da ita da cewar
taje kawai tayi musu nasu, ita tana jiran wanda za'a kawo mata daga cikin gidan, sai kuma
yanzu taga a kasin haka, tsaki taja mai tsayi, sam bata tsammanin zata iya cin abincin
yarinyar domin bata yarda da tsabtarta ta ba.

Shigowar Uwale ne ya katse tunaninta, wannan karon a d'an sake ta amsa sallamarta, bata
kuma dauke idon ta ba har sai da ta k'araso inda take zaune.


Cikin damuwa tace." Zinatu me ya faru ne? Hamra'u ta kawo miki abinci kin kore ta dashi."


Numfashi ta sauke kafin tace." Babu komai kawai bana bukatar nata, nafi bukatar naki domin
wanda ki kawo min jiya yay min dadi sosai."


Ta 'bangale baki tana dariyar farin ciki tace."Shine dalili kenan to kada ki damu idan kinfi bukatar
nawa nayi miki alkawarin yi miki duk irin wanda kike so."

Murmushi tayi da fadin." Nagode sosai, me zaki min yanzu? amma dai ina bukatar kunun gyada
irin na jiya."

Tace." To kada ki damu yanzu zan je na dama miki bayan shi sai me kuma."?

Kallonta tayi cikin zuciyarta tana yaba kokarinta, a rayuwarta tana son mai sonta, lokaci guda
taji tsohowar ta kwanta mata a rai."

A sake tace." duk abunda ki kayi ina bukata, Ina yaba kokarin ki sosai koda yake dama girkin
tsaffi akwai dadi da gamsarwa."

Ta kyalkyala dariya da fadin." 'Kwarai haka maganarki take, ai mutanan da bamu da 'kyiwa da
ganda muna zama mu gyara abinci yanda zai gamsar, mijinki ma Umaru haka yake min irin
wannan sambatun."

Murmushi kawai tayi, bata iya cewa komai ba, har Uwalen ta fita daga falon, Ta girgiza kai da
fadin." Kakar sa mai kyawun hali, shi kam halinsa daban da sauran mutane.


Ganin Uwalan ta shigo cikin farin ciki da walwala ya sanya ta mamaki, ta bita da kallo a lokacin
da ta kama hanyar kicin, sai ta shiga nazari da tunanin abinda ya sanyata walwala da farin ciki
irin haka, dalili duk lokacin da zata shiga sashen Gimbiyar to babu shakka zata fito da bacin rai
amma yau sai aka samu sauyi.
Tana nan zaune tana saka wasikar jaki tsayin mintina arba'in Uwale ta fito daga kicin ta
kammala komai hannunta rike da kwandon abincin.

Ta dinga yi mata kallon mamaki! kafin ta bude baki da niyyar magana Uwalan ta riga ta da
fadin." Hamra'u kada kiyi wa al'amarin nan mummunan fahinta, domin ni dake da Zinatu duk
daya na dauke ku a zuciyata, bayan na shiga gurinta take sheda min cewa tafi bukatar ni nayi
mata abinda za taci saboda taji dadin wanda nayi mata jiya, don haka kada ki sanya a ranki
cewa domin ta tozartaki ta 'kyamaci abincinki."

Kasa magana tayi tsabar bacin rai da yanda zuciyarta take tururin zafi, zuwan gimbiyar gidan
yana barazana da rayuwarta domin abubuwan da Uwale take mata zasu iya sanyawa zuciyarta
ta buga......Tana can tana tunani Uwalen ta fita motsin kofa ne ya dawo da ita nutsuwarta.

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta mike ta nufi dakinta.

Tana shiga ta zauna gefan gado tare da daukar wayarta, kai tsaye number wayarsa nemo, a
wannan ga'bar dole itama tayi wani k'okorin domin samun cikar muradin ta, bata iya k'arya ba
amma tana ganin yau zata fara saboda abubuwan da Uwale da ita Gimbiyar suke mata a gidan
sun isheta.

Murya na rawa kamar me shirin fashewa da kuka duk ta sheda masa abunda yake faruwa bata

tsaya a haka ba, sai da ta kara gishiri kamar yanda ta tsara hakan a ranta.


Yace." Hamra'u banyi mamakin jin wannan al'amarin ba, domin duk abinda akace min yarinyar
ta aikata ba zan karyata ba, saboda dama can bata da tarbiya, to amma duk abinda za tayi ya
tsaya iyakacin kaina domin ni na ajiye ta a gidan, ba zan lamunci taci zarafin wata daga cikinku
ba, Mussaman Uwale da bani da kamarta a duniya , saboda haka kiyi hakuri idan na dawo
zanyi wa tufkar hanci, na roki alfarma a gurinki cewa duk irin rashin arzikin da za tayi miki kada
ki biye mata, ai kin fita nutsuwa da hankali da kuma ilimin addini, banda jahili babu wanda yake
da ta'kidin cin zarafin dan adam wanda Ubangiji ya karrama shi a cikin hallita, mulki! izzah! iko!
sune suke damunta da sannu ni zan sauke mata duk wani abu dake kanta."

Sassauta murya tayi cikin kissa gami da kokarin kar yaga laifinta tace." Insha Allahu zan kiyaye
duk abunda za tayi min koda zata zagi iyayena ne to ba zan tanka mata ba, zan bari ne har ka
dawo."

Yace." Yawwa nagode sosai my lov dina, maganar hidimar da Uwale take mata kada ki kara
magana akai ki kyaleta tunda tana ganin zata iya idan na dawo dole ta ajiye aikin ta zauna ta
huta."

Tace." To shikkenan Yaya na Allah ya dawo da kai lafiya."

Ya amsa da ameen ya Allah, kafin suyi sallama da juna.


******
Bayan kwana biyar da faruwar al'amarin, Asp ya kira ta a waya suka gaisa da juna ya
tambayata ko tana da matsala tace babu, sai yace." To masha Allah haka ake so, ai mutumin
naki yana kan hanya gobe mybe iwar haka ya sauka, ko da yake ma ai nasan ya fada miki
dawowar tasa.
Gabanta yana d'an faduwa Tace." Aa ni bai fada min ba." Kawai ta tsinci kanta da fadin."
Yaushe rabon ma da ya kira ni a waya."

Asp din ya shiga mamaki mutuka, kafin yace." Kinga kullum kuwa muna waya dashi kuma idan
na tambayashi cewa kuna waya sai yace min Eh amma kiyi hakuri kada ki damu mybe aiki ne
yay masa yawa.

Ta danne bacin ran dake taso mata tace." Ranka ya dade abokinka mak'aryaci ne, kuma bashi
da kirki wallahi, ai ya san abinda ya aikata dole ya kare kansa a gurinka.

Yace." ZINATU ki daina jifan sa da irin wannan kalaman mijinki ne fa a koda yaushe ya zama
magana mai kyau ce zata fito daga bakinki.

"Humm kawai ta iya cewa ranta idan yayi dubu ya baci Tace." Ba ka tambayi dalilin komai ba ka
nema ka dora min laifi idan nace maka kana tsoronsa sai kace ba haka bane."


Yar dariya yayi yace." Ai na san labarin gizo ba zai wuce na koki ba, shiyasa ban tambayi dalili
ba, amma dai ki fada min laifin da yay miki ina sauraranki."


Tace."Gabad'aya ya sanya an fita da kayan masarufin da masarautar mahaifina ta bashi, a
cewarsa yafi karfin komai baya bukatar taimakon wani, shine ni kuma nai mamakin hakan nace
har yaushe yayi arzikin da zai dinga yiwa mutane tutiya shin wai nawa ne ma albashinsa a
wata."?

Asp din ya dinga jinjina maganar a ransa, ba tun yau ba yasan da cewar yarinyar ga'buwa ce
zata iya farfada masa wannan maganganun.

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Aa kece dai ki ka fahimceshi a bai-bai amma ba nufinsa
kenan ba, domin mun jima da yin wannan maganar in da yake sheda min cewa akwashe
kayan a rabawa mabukata, ba wai don baya bukata ba, tunda akwai wa'inda suka fishi bukata
a raba musu sai a bar masa kadan, ni kaina yayi min kyautar wasu, nace A'a saboda nima
Allah ya rufa min asiri, wannan shine dalilinsa, amma ina fatan bakiyi masa rashin kunya ba."

Shuru tayi masa domin shi kansa a yanzu haushinsa takeji ganin har yanzu yaki hango laifin
abokin nasa .

Jin tayi shuru yasa ya gazgata zarginsa, yace." shikkenan shurunki ya bani amsa ba, kinga
kuwa duk wani abu da yay miki a yanzu ke kika janyo amma bari zan kira shi yanzu domin naji
komai daga bakinsa."

Still ba tace masa komai ba har ya gaji ya kashe wayarsa, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tare
da cire wayar daga kunnata. ta a jiye saman drowar, kwanciya tayi ta lumshe idonta kawai ta
shiga tunanin abinda zai faru a tsakaninsu idan ya dawo gidan.


Koda Asp din ya kira shi cikin mutumci da dattako suka gaisa kamar koda yashe, Asp din ya
tambayeshi yanayin aikin da kuma maganar dawowarshi gobe, yace." Na kammala komai cikin
nasara da sahalewar ubangiji kuma insha Allah gobe iwar haka na sauka da ikon Ubangiji.

Yace." Alhamdullhi masha Allah, mutumina na taya ka murna da samun cigaba a rayuwa Allah
kuma ya sauke ka lafiya."

Cikin farin ciki ya amsa da ameen ya Allah mutumin kirki nagode kwarai."

Yace." A babu komai fa abokina idan nai maka addua da fatan alkairi ai kamar kaina nayi wa sai
dai kuma hanzari ba gudu ba, yanzu-yanzu na gama waya da mutuniyarka."

Jin abinda yace yasa ya d'ora idonsa kan agogon dake kafe a dakin, goma da rabi na dare, sai
ya shiga mamakin dalilin da yasa ya kira ta acikin wannan daran, be yarda da abinda zuciyarsa
take raya masa ba, yace." ta kawo maka 'kara ta kenan."?

Murmushi yay da fadin." Kwarai kuwa UMARU a gaskiya idan baka sauya halinka ba zamu
'bata domin ni yanzu gabadaya na daina ganin laifin yarinyar nan laifinka nake gani."

Cike da mamaki yace." Wannan ya nuna min cewar kana goyon bayan duk iskancin da take."

Yace." Ba nufi na kenan ba, na san abinda take bata kyautawa, to amma ni nafi yarda da cewa
kaine kake janyo duk abunda yake faruwa me yasa ba zaka rarrasheta ba; me yasa ba zaka
dinga tausasa harshenka gurin yi mata kalami ba? nasha fada maka cewa mata wasu irin
hallita ne masu wuyar sha'ani amma daga ranar daka gane hallinsu to za kaji dadin zama dasu,
domin suna da dadin sha'ani da kuma saukin hali, me yasa kai baka daukar shawara ne."?


Asp yana da 'kima da daraja a idonsa, wannan shine dalilin da yasa ya dinga tausar zuciyarsa
kada ta tunzurashi aikata abinda zai janyo musu samun sa'bani da juna, bayan haka kuma
wannan gantafalfalar yarinyar bata isa ta shiga tsakaninsa da amininsa ba, hakuri ya bawa
zuciyarsa dake turari! gami da jin kishi-kishin Asp din domin haka kawai yake jin haushin
kyakykyawar fahintar dake tsakaninsa da yarinyar wanda hakan ya janyo yazo yana gaya
masa magana a kanta..........Ajiyar zuciya ya sauke da fadin."To Naji na dauki laifina domin a
yanzu yanda kake a tunzure ko nayi maka bayani ba zaka fahinta ba, okey komai zai yi dai-dai
kamar yanda kake so, zan kuma yi kokarin ganin na gyara kuskura na."


Asp din yace." Yawwa to ko kai fa mutumina, ni wallahi banga abin gudu a tattare da yarinyar
nan ba, a ganina kai da kanka zaka sauya mata hallaya kada ka manta kuma bata da kowa a
garin nan sai kai da family naka sai kuma mu da muke abokanan arziki."

A d'an tunzure yace." Asp maganar nan abar ta haka don Allah, nace naji na kar'bi laifi na zan
gyara kuma shikkenan ko."?

Yace." Shine abinda nake bukata a tare da kai, ka dawo gida naga sauyi daga gareka."

Shuru yay masa yana jin wani irin abu na sukan zuciyarsa, a duk sanda Asp din yake nuna
kulawarsa akan yarinyar yakan ji abun ya dame shi a ransa, sai yayi auziyya ya kori shaidan din
dake kusa dashi tukkuna yake samun sassauci, shi kansa be san me yasa yake tsananin kishin

yarinyar ba.





*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta
WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
[2/9, 7:01 AM] Matar Malam: _*GOJE!!🏹🐕â€í ¾í¶º*_
_*Ya dawo!! ga Akuya ga kura!! tofah! 'ka'ka-'kara-'ka'ka-tsara!! A yanzu ne labarin zai fara....!
Na jima ina rubuce-rubuce amma ban ta'ba rubuta littafin daya dauki hankalina irin wannan ba,
dalili littafin yazo da sabon salon da ba'a ta'ba yin irinshi ba, bahaushe yace yabon kai jahilci 😃
a wannan ga'bar dole na jinjinawa kaina gurin rubuta littafin farauta ba tare dana shirya hakan
ba, Tirk'ashi idan ana dara fidda uwa ake, shin wai ina labarin uban daba ne? ina nufin
(mashekin daji) wanda Ubana UMARU ya samu nasarar sare masa hannu guda🙊 akwai
badakala anan gaba.......GOJE🐕â€í ¾í¶ºí ¼í¿¹ ya dawo cike da nasarori masu yawa shin ya zaman auran
su zai kasance da 'yar rigimarshi wato GIMBIYA ZINATU, wanda Tun a daji suka fara son
junansu amma dukkaninsu sun 'ki gazgata cewa suna son junansu😃 to zamu ga yanda game
d'in nasu zai kasance tare da boyayyan masoyinta😃 shin a tsakanin waye zai saduda kowa
dai ba kanwar lasa bane..........! Domin samun damar shiga paid group....#500
0542382124.....Binta Umar gtbank. Idan kati za'a turo sai ayi min magana ta WhatsApp da
wannan number...... 07084653262......BINTA UMAR ABBALE🍒*_

*61&62*
*GJSR*
Wayewar garin ranar da zai dawo tun safe gidan ya fara cika da mutane yan uwa da abokan
arziki daga can garinsu, yaran shi ma kaf sun hallara, jiran saukar sa kawai suke, hayaniyarsu
har part d'inta, ta dinga mamakin al'amarin, Baraka ce take shaida mata cewa ai ba'ki akayi a
gidan, kuma da alamar su mutanan k'auye ne, jim tayi tana nazarin meye dalilin zuwansa,
wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita cewa sun zo tarar d'an uwansu ne, kasancewar a
cikinsu shike da kumbar susa shine dalilin da yasa suke tururubin zuwa gidanshi.

Tsaki taja a fili tace." Duk inda d'an kauye yake sai ya nuna halin dabbanci." Ta kalli Barakan
dake zaune a gefanta tace." Ki sheda musu cewar hayaniyarsu tayi yawa su rage."
Ta amsa kafin ta yun'kura ta mike kai tsaye hanyar fita ta nufa.

Da yake a 'bangaran da suke zaune ba'kin suka sauka, kai tsaye can ta nufa. aikuwa ta
samesu sunyi kaca-kaca da guri sunci abinci duk sun zubar sai dirkar lemon roba suke da sun
shanye sai su ajiye su dauki wani, lemo da ruwan kusan kwali biyar aka a je musu amma sun
shanye saura kadan. Sosai ta cika da mamakin yanda ta gansu mazan da mata sai hira suke suna shewa kowanne

rike da robar lemo a hannu.

Tayi musu sallama suka amsa tace." Dama sa'ko ne daga matar gidan wato Gimbiya Zinatu
tace na sheda muku cewa hayaniyarku tayi yawa ku tak'aita."

Sai suka hada baki gurin fadin." To shikkenan amma dai mutum da bakinsa ai ba za'a ha nashi
magana ba ko."?

Tace." Eh itama ba tace kuyi shuru ba cewa tayi ku rage hayaniya."

Wasu daga ciki suka amsa sauran kuwa shewa sukayi irin ta shakiyanci suka fara kuskus da
yawa daga cikinsu mutanan 'Dayyiba ne wato mahaifyar Hamra'u, domin ita bata samu damar
zuwa ba, sai ta tura wakilai domin dauko mata rahoto.

Tun kafin ya sauka ya samu labarin tarin jama'ar dake jiransa, sosai yay farin cikin hakan ya
kuma dinga Allah-Allah ya sauka domin haduwa da 'yan uwansa wanda bashi da kamarsu.


Uwale da kanta ta jagorance su duk yawan su maza da mata suka nufi sashen Gimbiyar.


Suka cika falon duk girmansa ko wanne sai zare ido yake da kalle-kalle falon ya dumame da
wani irin wari da tsami mara dadin ji!!

Marakissiya ce ta shiga ta shiga ta sheda mata cewa tana da baki.


Koda ta fito ta riske su jigum-jigum! a zaune ga tsami da hamami! ya cika mata falo, ranta yay
masifar b'aci, toshe hanci tai ba tare da tace musu komai ba ta juya da sauri ta koma
daki.................A gaggauce ta nufi toilet ta dinga kwara amai! wanda ta kasa tantance na
meye, ta dai fi zargin warin data sha'ka ne.
A galabaice ta fito ta zauna kan Sofa tana mayar da numfashi, ita kanta ba ta ji dadin faruwar
hakan ba, sai dai ba yanda za tayi ta iya zama a falon yana wannan uban warin!


Uwale kuwa kunyar duniya ce ta isheta ta kalle su suna zaune har yanzu sai dai akwai alamun
'bacin rai a tare da wasu mussaman Kawun sa wanda suke 'yan maza zir da mahaifinsa.

Ya kalleta da fadin." Uwale wannan yarinyar i ta ce matar UMARU."!

Tace." Eh ita ce kuyi hakuri da abunda ya faru.

Kawu Ado ya girgiza kansa rai a bace yace." Babu shakka albasa ba tayi halin ruwa, yanda
muke jin labarin mahaifinta a duniya mutum mai nagarta da dattako, bashi da nuna bambanci
ko 'kyama ga al'ummah! yana da kyauta da sakin fuska, kowa nasa ne, tabbas da yarinyar nan
ta gaji halin mahaifinta to da ba zata tozarta dan adam ba, amma babu komai. saboda nagartar
Mahaifinta za'a zauna da ita amma dole sai UMARU ya auri za'bin mu matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login