Showing 27001 words to 30000 words out of 46235 words
Chapter 10 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*109&110*
Gidan ya rage saura ita kadai, sai ta shiga tunanin abubuwan da suke faruwa, jiya da daddare
kafin su kwanta Uwale tayi mata cikakken bayanin abunda yake tsakanin mijinta da yarinyar da
tuntuni ta d'ora zargi a kanta, tabbas koda Uwale ba tayi mata bayanin komai ba dama
tuntuni ta fahimci wani abu, duk da dai shi bai fad'a mata cewa akwai al'kawarin aure a
tsakaninsa da yarinyar ba, to ita yarinyar ta nuna mata alamu tun farkon fara had'uwarsu...Ba
zata ha nashi aure ba, domin a yanda Uwalen ke sheda mata yanda yarinyar tayi wahala a
kansa hakan ya sanya taji tausayinta, bayan haka kuma ta san duk daran dadewa bai zama
lallai ta zauna ita kadai ba, wannan ne dalilin da yasa ta tausayawa yarinar. wai akace son
maso wani koshin wagala! amma babu shakka ba zata lamunci munafurci da
kumbiya-kumbiya ba. domin tafiso duk abinda za'ayi a fada mata kada a munafurce ta, abu na
karshe kuwa dole ya jawa yarinyar kunne ta kiyayi shiga gonarta ko kuma yi mata rashin kunya
anan ne za'a samu matsala! domin mutukar yarinyar tace zata raina mata hankali to abu ne
mai sauki a gurinta ta cire blet ta zane mata jiki dashi, sai dai duk abunda zai faru ya faru.
To can gidan biki kuwa ya kacame! da hayaniya mata sun fi ashirin akan Uwale dake rabon
turaman atamfofi da mayafai da sabulai na wanka da wanki.
Da yawa wasu basu samu zanin ba, saboda yawansu, wasu kuma mayafai suka samu da
sabulai, duk wanda ta mik'awa sai tayi masa bayani cewa daga matar Umaru ne.
A cikin wa'inda suka samu kayan har da mutanan Dayyiba......sai suka silale suka nufi gidanta
domin kai mata rahoto.
Wasu kuwa gidan Uwalen suka nufa domin mika godiyarsu da kuma jin dadin alkairin da akayi
musu.
Hayaniyar shigowarsu gidan ya katse tunanin da take.
Ta fito tsakar gidan ta gan su da yawa a tsaye....ikon Allah har da masu durkusa mata, ta
jingina jikin bango (garu) tana amsa gaisuwarsu da fadin." Ku daina godiya haka babu komai an
zama daya.
D'aya daga cikinsu tace." Dole muyi godiya yarinyar kirki! domin bamu tsammaci haka daga
gurinki ba, dalili mun samu labari a bakin wasu daga cikin 'yan uwanmu cewa baki da kirki
mutuniyar banza ce ke da dai sauransu, sai gashi kinyi mana bazata mun gode sosai."
Murmushi kawai tayi kafin tace." Ba komai kun san mutum tara yake bai cika cif ba, kowa yana
kuskure a rayuwa, wa'inda na 'batawa rai a cikinku su yafe min tunda har Allah yasa na shiga
cikinku ai mun zama daya dama rashin sabo da juna ne."
Matar tace." Kwarai kuwa Gimbiya to mu dai muna bayanki insha Allah domin dai Dayyiba bata
da alkibula mai kyau! mu mutanan *KAFUR* muna sonki da kaunarki dan haka ki cire kokwanto
a ranki."
Tace." To na gode sosai Allah ya saka da alkairi."
Gabadaya suka amsa da ameen. kafin suyi mata sallama su fita....Itama cike da farin ciki da jin
dadi ta koma dakin ta kwanta, cikin zuciyarta take adduar Allah ya bata hakurin zama dasu,
tunda tana son mijinta babu abinda ba za tayi ba.
Dayyiba da labari ya iske ta kamar ta kurma ihu saboda bakin ciki, idonta ya ciko da ruwan
hawayen bakin ciki ta kalli Taburni da fadin." Amma dai kinji kunya wallahi Ashe amincin da
yake tsakaninmu na 'karya ne."?
Taburni tace." Kamar yaya ban gane ba."?
Ta zabga mata harara da fadin.'' Meye amfanin zuwa ki kar'bi turmin atamafa kamar baki ta'ba
daura zani ba."
Ta daga mata hannu da fadin." Kinga Dayyiba saurara! kawai saboda gudun bacin ranki ina
kallon alkairi sai na bar shi, kema kin san ba zai yuwu ba, zani da sabulai na samu ke ko dake
ko babu ke dole ina da rabo saboda matar Kawunsa ce to meye abin damuwa."
Dayyiba ta sanya gefan zani ta share guntun hawayen daya fara fitowa tace." Taburni ban san
ya zanyi ba akan wannan al'amari, wallahi idan Hamra'u ta samu shiga gidan Umaru buri na bai
wuce ace ta zama mowa ba, amma na san hakan ba zai yuwu ba sai na taka muhimiyyar rawa.
gashi bani da kudi a hannuna ballanatana naje a taimaka min."
Tace." Yanzu dai abu na farko da za fara shine janyo hankalinsa kan 'yarki, ma'ana ya daina
ganin kowa a gabansa sai ita, kafin ace ta shiga gidansa, sai kuma ayi musu farraku da
Uwargidansa.
Tace." Taburni bani da kudi wallahi, kuma kin san wannan harkar sai an ajiye kudi dole a zubar
da jini."
Taja tsaki da fadin." Ashe wasa ki ka dauki al'amarin, ai idan zakiyi yawo tsirara ba abun
damuwa bane mutu'kar bukatarki zata biya, ki sayar da gado da katifarki ai ba'a kanki aka fara
ba.
Tayi shuru tana nazarin maganar, tabbas hakan shine mafita domin idan ta tsaya kallon ruwa to
kwado ne zai yi mata 'kafa gwara ta tashi a tsaye.
Uwale ta kawo mata gurasa *(band'asho)í ½í¸ƒ* Kanawa mune gurasa Allah yasa akwai wa'inda
suka san meye ma'anar *(Band'asho)* Taji k'uli da man gyada mai kamshi gefe da kabeji da
sauran kayan had'i, sosai taji dadi gurasar taci ta k'oshi kafin tayi wanka ta shirya jikinta cikin
wani milk din les mai taushi da stones a jikinsa, sai ta dora alkyabba mai tafe da hula a jikinta,
ta sanya takalmi rufaffan takalmi irin nasarauta, sosai tayi kyau, kamshi turaranta duk ya cika
gidan.
Waje ta fito da wayar ta a hannunta.......ido yayi caaa! a kanta, itama kallonsu takeyi sunyi
rukuni-rukuni a gindin bishiya suna ta cin abinci babu kimtsi balle kamun kai.
Can gefe kuma amaryar ce da k'awayenta da ango da abokansa sun sanya katuwar redio a
tsakiyarsu kalangu sai tashi yake amarya da ango suna rawa ana lika musu 'yan biyar-biyar.
Abin ya burgeta ya bata dariya kai tsaye gurun ta nufa cikin yanayin tafiyarta.
Hamra'u tare da Zabbah dake can nesa suka hangeta tawagar 'yan matan garin sun rufeta a
lokacin da take tsakiyar amarya da ango tana manna musu 'yan dari biyar-biyar.......Ihu!!! da
kaya-kaya ya cika gurun!
Takaici ya hana Hamr'au karasawa gurin, ta juya a sukwane ta koma gida.....Ita kuwa Zabbah!
sai da ta k'arasa gurin, ta kutsa ta samu rabonta dan sai da ta tsira da dubu biyu.
Da wayarta ta dinga yi musu vedio sai hauka suke suna he da he kowa so yake tayi hoto dashi,
amarya da ango kuwa kamar su zuba ruwa a kasa su sha a tarihi ba a ta'ba biki irin nasu ba.
Hamra'u ta 'karaso gurin tana wani dauke kai! ita gata wacce ta fita zakkah a cikinsu, da ba a
san asalin balbela ba sai ace daga masar tazo .......Ta zuge jakar hannunta ta fito da kudi 'yan
dari -dari ta fara watsawa a gurin.........Wani abokin ango yayi saurin sanya wakar *Komai na
Babah yafi na yaro!* Zinat kuwa ganin haukan da yarinyar take ya sanya tayi gaggawar fita
daga gurin.
Ita kuwa Hamra'u sai wani jin kai take tana wani ya mutse fuska! Zabbah taja ta gefe da fadin."
Wannan wa'kar fa da Salmanu yasa dake yake, kinzo kina lika dari-dari ita kishiyar taki dari
biyar biyar ta dinga watsawa kuma ta watsa yafi dubu ashirin kinga nima na samu dubu biyu.
amma ke kina lika 'yan dari -dari sai wani jin kai kike."
Jikinta yayi sanyi ta kalleta da fadin." Kina nufin dama saboda naji haushi Salmanu yasa
wannan wa'kar!
Ta fashe da dariya da fadin." E mana ma'ana kiji haushi kema ki watsa musu kudi."
Ta girgiza kai da fadin.' Lallai Salmanu bashi da mutunci."
Tace." Hamra'u ni dai shawarar da zan baki shine kiyi hakuri ki kwantar da kanki ku zauna
lafiya, dan na fahimci matar nan kamar tana da saukin kai kuma ba zaki samu matsala da ita
ba, sannan kuma a zahiri ta fiki ta ko'ina kada kice zakiyi gasa da ita."
Tace." Idan na fahimce ki kina so kice na zauna nayi mata bauta ko."?
Ta girgiza kai da fadin " Aa ba haka nake nufi ba, ina nufin ki dai daina kishi a kanta dan naga
kin zafafa da yawa, baki da gashin wance dole ki zauna a matsayinki."
Ta girgiza kai da fadin." Ba zai yuwu ba Zabbah shekara sama da goma ina dauki ba dadi akan
biyan bu'kata na amma lokaci guda wata ta shiga rayuwata, wallahi ba zan iya daina kishi a
kanta ba, domin bana kaunarta na tsaneta! kuma zan iya komai akan ganin bayanta."
Zabbah ta dinga yi mata kallon mara hankali da tunani! itafa gabadaya rayuwar yanzu ta zama
wayo da dubara da kuma siyasa mutukar ka iya wannan zaka zauna lafiya, amma shikkenan
tunda tayi iya bakin kokari gurin ganin ta nusar da ita ta kasa fahimta zata kyaleta kawai taje
duk abinda za tayi rayuwarta ce.
Shida shaura ya sauka a garin.......Tun kafin ya fito a mota gurin ya hautsine! hayaniya da
ifece-iface! tare da haushin karnuka!
Saboda ba ta san ganin bacin rai yasa tayi gaggawar shiga gida, ta san mybe sai ya tsaya yayi
abinda ya saba.
Sai dai kuma bata jima da shiga gidan ba ya shigo cikin inform da alama daga gurin aiki yake.
Koda ya shiga gidan hankalinsa gabadaya yana kanta....ya rungumeta yana ta sumbutar
fuskarta. A lokacin su Uwale suka shigo gidan.
Uwale Hamra'u da Zabbah dake bayansu......Gabadaya jikin su ne yayi sanyi ganin irin
soyayyar da ake zabgawa a gurin, kamar zai cinyeta ya rike fuskarta sai so yake ya kama
bakinta tana kaucewa.
Gilmawar Uwale a gurin ita ta hankaltar dashi, ya sakar mata fuska yana sauke wani irin
numfashi.....Juyawar da zai yi yayi ido hudu da Hamra'u dake tsaye kamar wacce aka dasa,
gwiwarta tayi bala'in sanyi!
Ya d'an ji kunyarta amma da yake namijin duniya ne sai ya basar yace." Kanwata ina fata dai
kin shirya kin kuma yi sallama don yau zamu tafi."
Murya na rawa tace." Ni ba zan koma ba."
Ya kalleta da mamakin furucinta a tare dashi yace." Saboda me."?
Ba tace komai ba, kawai ta juya ta fita kawarta ta rufa mata baya.
Ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin al'amarin.
Ya dan juya in da take, wayam babu ita a gurin......bai kawo komai a ransa ba, ya cire takalman
dake kafarsa ya shiga dakin da sallama a bakinsa.
Gabadaya suna uwar dakin ita da Uwalen.
Kusa da ita ya zauna yana d'an satar kallonta a idonsa ya hango rama a tare da ita kwana uku
kacal ta sauya masa tayi haske sannan duk ta rame.
Uwale dake had'a kaya tace." Naji kuna magana da Hamra'u ko."
Yace." Eh wai me yake faruwa ne?
Murmushi takaici tayi kafin tace." Alkairi ne, amma tunda tace ba zata koma ba, sai ka kyaleta a
ranar da aka daura muku aure ai dole ta zauna a dakinta."
Gabansa ya fadi da jin maganar da Uwalen tayi zata tona masa asiri! be shirya sanar mata da
maganar yanzu ba, ya saci kallon fuskarta yaga babu abunda ya sauya a yanayin ta wayarta
ma take dubawa.
Ajiyar zuciya ya sauke cikin zuciyarsa yake addua Allah yasa ba taji maganar ba, duk da ya san
da kamar wuya hakan dan kyau Uwale ta fadi maganar.
Ya kalli agogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi har an fara kiran sallar magriba, yace."
Zan je nayi sallah mu gaisa da wanda ya dace kafin na dawo sai ku shirya."
Tace." Ai mu a shirye muke Umaru sallah kawai za muyi.
Yace." Uwale anya ba wani abu ne ya faru ba kuwa."?
Tace." Me ka gani kake wannan maganar.''?
Yace." Naga kamar kina Allah-Allah mu bar garin bayan kinyi alkawari cewa sai kinyi sati uku ko
hudu."
Shuru kawai tayi ba tace masa komai ba. Ya girgiza kai tare da mikewa tsaye. bahaushe yace
shuru ma magana ce, lallai akwai abinda ya faru bayan barin sa garin.
Uwale na idar da sallah ta kalleta da fadin.'' Kafin Umaru ya shigo zan dan shiga muyi sallama
mutane."
Tace."To shikkean ba komai idan ya shigo zan sheda masa.
Fitar ta keda wuya ya shigo gidan, yana haska dakin da wayar hannnsa, kan dadduma ya
sameta, ta idar da sallah amma bata tashi ba.
Ya zauna saman gadon karfen dake dakin yana kallonta.
Babu yabo babu fallasa ta juyo suka had'a ido taga yana mata wani irin kallo kafin yace." Zo
nan ki fada min abinda ya faru bayan tafiya ta."
Ta iske in da yake ya rike hannunta tare da zaunar da ita kusa dashi, gabadaya hankalinsa
yana kanta, yana jiran abinda za tace.
Tace." Kai me kake tunanin zai faru."? Shuru yayi be san me zai ce ba kawai yana ji a jikinsa
ne."
Tace." Kamar yanda Uwale ta fada maka alheri ne hakane, Allah ya sanya alkairi a tsakaninku.''
Ya rasa gane abinda take nufi......Ganin yana kallonta yasa tace." Ya aiki ina mutuminka Asp ina
fatan kuna lafiya.''?
Hannunta ya rike da fadin.'' Asp yana nan lafiya har ya bani sakon gaisuwarki amma da ba kiyi
maganarsa ba na manta, sai kuma ni da nake cikin matsala."
Tace." Matsala kuma.''?
Kai ya daga mata kamar karamin yaro.
Ta zuba masa ido tana kallonsa.
Hannunta dake cikin nasa ya fara kokarin cusawa k'asan mararshi.......Tsigar jikinta ta tashi da
sauri ta fizge hannun tana harararsa.
Ido jawur! yake kallonta, kafin yace." Kin gane matsalar ko."?
Tace." Kai kam baka da matsala sai wannan."?
Yace." Ina dasu amma wannan itace a kan gaba."
Ta'be bakinta kawai tayi ta d'auke kanta.
Duk ya rasa yanda zai yi baya so tana sha masa k'amshi! tabbas ya san da akwai wani abu a
kasa.
Ganin abinda take yasa ya kama kansa, yayi kokarin danne kwad'ayinsa, saisaita muryarsa yayi
kafin yace." Ina Uwale take ne."?
Ba tare da ta kalleshi ba tace." Ta fita domin yin sallama da mutane."
Ya mike ba tare da yace mata komai ba ya kama hanyar fita, kallo ta bishi dashi tana girgiza
kanta.
Bata yarda ta zauna kusa dashi ba, a kusa da Uwale tayi zamanta suna hira, shi kuwa kamar
maraya suka mayar dashi direba haushin hakan ya sanya bai sa musu baki a maganarsu ba,
sai dai sa'i da lokaci yana amsa waya jefi-jefi! a haka suka isa gidan kowa da abunda ya
dameshi.
A maimakon ya nufi side dinshi kawai sai ya bita nata, ta riga ta san bin diddigin da yake mata,
haka kawai ta tsinci kanta da jin haushinsa.
A nan yayi wanka ya kimtsa ya fita ya siyo musu abinci, sai da ya kaiwa Uwale nata sannan
yayi mata bankwana, koda ya fito kai tsaye sashen Gimbiyar ya nufa babu wani kuzarin kirki a
tare dashi.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI