Showing 36001 words to 39000 words out of 46235 words
Chapter 13 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
magana tayi kawai ta sunkuyar da kanta sai so take ta tsayar da hawayen dake zuba
amma ya gagara! zubar hawayen shine samun zaman lafiyarta.
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta girgiza kai ta kama hanyar fita zuciyarta cike da tunanin
neman mafita.
Kishingide ta sameshi a dakin hutawarsa.
A nutse ta zauna kusa dashi kafin tace." Barka da hutu ranka ya dade."
Ya amsa da "Barka kadai Gimbiyar mata ya gida ina 'yar uwar taki.''? ya tambayeta Safara'u
saboda ya san abinda ya kawo ta gurinsa bayan ba girkinta bane tabbas itama Safara'un tana
tafe.
Tana kokarin magana Safah din tayi sallama, jikinta nannade da lifaya kwantankwancin ta jikin
Aysha.
Suka gaisa cikin girma da mutunta juna.
Zamansa ya gyara yana kallonsu daya bayan daya kafin yace." Labarin gizo a tambayi koki tun
kafin kuyi min bayanin abinda yake tafe daku na karanci hakan a fuskokinku. to ina jiran
shigowar Magajin sarki ne domin shi nakeso ya kira mijin yarinyar muji daga bakinsa."
Gimbiyar tasha kunu da fadin." Ranka ya dad'e wannan al'amarin fa bana wasa bane ya za'ayi
a matsayinka na mahaifin yarinyar nan ka wakilta wani ai sai ya kara rainawa mutane hankali
saboda haka kai ya cancanta kayi magana dashi."
Yace."Aysha ko bayan raina Abdullahi shine Magaji na, wannan dalilin ya sanya nasa shi a cikin
maganar domin yayi wa 'yar uwarsa wakilci, ita tazo da magana to amma yana da kyau shima
mijin nata aji daga bakinsa.
Tace." Wannan yaro fa bashi da kirki! ranka ya dade in banda wulakanci da ciki zai kori yarinya
me tayi masa haka da zafi."?
Yace." Ashe har kin manta halinta kenan? Aysha idan ke kin manta wacece Zinatu ni ban
mance ba, kada ki manta irin d'auki ba dadin da muka dinga yi da ita kafin ta amince da auran,
ko shakka ba nayi matsalar daga gurinta take.
Safah ta katse shi ta hanyar fadin." Kada kayi gaggawar yanke hukunci ranka ya dad'e! yanda
yarinyar nan ta zabge lokaci guda shine zai nuna mana cewa akwai matsalar da take faruwa a
tsakaninsu kuma taura d'aya bata taunuwa, bahaushe yace idan anbi ta b'arawo to abi ta mabi
sawu, dole shima nasa laifin saboda haka yana da kyau yazo gabanka ku tattauna domin
magana ta waya ba zata gamsar ba."
Yace." Wannan shawarar taki tayi Safara'u abinda za'ayi kenan. Insha Allah komai zai warware.
Magajin Sarki ne ya shigo da sallama a bakinsa.
Gabad'aya suka amsa. ya samu guri ya zauna kafin ya fara gaishe su......Maimartaba yace." Ka
kira Umaru mijin Zinatu kace masa ina san ganinsa idan ya samu dama."
Ya fito da waya domin bin umarni.
Daf da zata katse ya daga wayar............bai ma duba suna ba, sai da yayi masa bayanin kansa
sannan yace." Magaji afuwa don Allah ya mutan gida ina fatan kuna lafiya."
Yace." Kowa Lafiya lau dama Maimartaba ne ya bukaci ganinka idan ka samu dama."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Magaji ayi min afuwa ina da uzuri aiki zai kani Zamfara sai
dai idan na dawo.''
Ransa ya baci da jin abinda yake fada.......Yace." Okey to idan babu damuwa inaso na san
dalilin da ya sanya Zinatu zuwa gida."
Yayi jim yana nazarin maganar kafin yace." Babu wani 'kwakw'kwaran dalili nima kawai na dawo
gida na samu bata nan."
Yace." No! akwai dalili Goje sai dai idan ba zaka fada ba."
Murmushi yayi kafin yace."Ka tambaye mana ni dai na san lafiya lau muke zaune amma ina
tunanin kishi ne dalilin da ya sanya ta yanke wannan hukuncin."
Yace."Kishi kuma."?
Yace." Eh 'kwarai kuwa na 'kara aure kwana uku da suka wuce wannan shine abinda nake
tunani."
Yayi murmushi da fadin." Ni a ganina wannan kadai ba zai janyo har tazo gida ba ko ka manta
da lalurar da take tare da ita."? A dan kausashe! yayi maganar.
Shima ya fusata! yace." Magaji yarinyar nan fa bani na koreta ba, ita ta kori kanta, kuma
saboda ita ba zan fasa abinda nayi niyya ba, nasan kasan mata hudu Allah ya halasta min to
akan wata ba zan tauye rayuwata ba."
Ya girgiza kansa da fadin." Okey to babu damuwa Allah ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya.
Ya amsa da "Ameen ya Allah."
Cikin rashin dadi sukayi sallama da juna.
Da yake hands free yasa wayar duk suna jin abunda suka tattauna.
Yana kishingide bai ce komai ba.....Gimbiya Aysha kuwa sai fad'a take da fadin." Wannan auran
warwareshi shi yafi alkairi dama can ita al'amarin be kwanta mata ba, auran jahili wanda yayi
rayuwa a daji! bashi da fa'idah mutumin kauye akwai karancin ilimi ta tare dashi babu abunda
ba zai aikata ba."
Duk yana jin sababin da take bai ce komai ba har sai da ta gama tukkuna ya gyara zamanshi
kafin ya fara magana kamar haka.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*117&118*
"Aysha duk wannan maganganun da kike basu da tushe ballantana makama, wannan dalilin
kad'ai ba zai sanya mu kashewa yarinya aure ba, ba hujja bace, dole mu jirayi zuwansa kamar
yanda ya fada yana da uzuri to zamu saurare shi zuwa lokacin da zai kawo kansa."
'Bacin rai ya hana ta magana, kawai taja bakinta tayi shuru takaici tare da tausayin 'yar ta kadai
ke damun zuciyarta. Ganin yanda hankalinta ya tashi yasa Shafara'u kwantar mata da hankali
da tausasan kalamai masu sanyaya zuciya gami da sa tawakkali da dangana.
Yana kallonsu yayin da suke tattauna maganar so kaunar Safah na cigaba da bin kowane
'bargo na jikinsa, har yanzu tana nan da kyawun zuciya da kuma fahimta, a duk sanda Gimbiyar
tasa ta rikice ta tafka wani shirman yana alfahari da ita gurin ganin ta shawo kan matsalar da
duk ta shafe su baki d'aya.
****
A daran Asp ya kira wayarsa don da shima har yayi zuciya da abubuwan da yake masa na
rashin kyautawa, sai kuma yaga da cewar kiran wayarsa domin su tattauna akan maganar
yarinyar da aka bashi amanarta.
Dai-dai lokacin da ya fito daga wanka kiran ya shigo wayarsa.
Sai da ya mula tukkuna kafin ya daga wayar yayi salama babu cikakkiyar walwala a tare dashi.
Ya amsa shima babu sakewa kafin yace." I dan babu damuwa ina so mu tattauna muhimiyyar
magana."
Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace." Ba damuwa ina sauraranka."
Yace."Maganar dai akan Zinatu take duk da baka san na shiga cikin al'amarin amma ya zama
dole na shiga tunda amana ce a hannuna."
Ya danne 'bacin ransa kafin yace." Okey ina sauraranka."
Ya cigaba da cewa." Yanzu Umaru dai-dai kenan abinda kayi ka kyauta! har ka rufe idonka kaci
mutunci yarinya da juna biyu a tare da ita, 'bacin ran abinda kake har ya kai ta tattara kayanta ta
tafi gidansu, Umaru kai a ganinka hakan dacewa ne."?
Yace." Kaga Asp ni da hankali da tunani nake al'amurana, wannan matsalar data shafe ni ce
babu ruwanka da ita, maganar Zinatu ta tafi gidansu wannan matsalarta ce, idan tayi ra'ayi ta
dawo idan tana ganin zama a can yafi mata bani da damuwa."
Asp din ya fusata! da fadin." Kana da hankali kuwa Umaru shin ko ka manta waye mahaifin
yarinyar ne."?
Murmushin takaici yayi kafin yaja karamin tsaki da fadin." Shiyasa ai farkon magana ta da kai
nace ni da hankali da tunani nake tafiyar da al'amura na, mahaifin Zinatu shine Sarkin *KANO*
to sai me? bari kaji Asp Allah kadai shine abin tsoro ba wani mahaluki ba, kuma idan ka manta
bari na tuna maka dama can ban furta ina sonta ba, bani akayi to akan me zan damu kaina, sai
magana ta karshe da za muyi da kai dan naga ka damu da yarinyar nan da yawa baka kaunar
damuwarta yanzu ma zan sake maimaita maka cewa zan iya rabuwa da ita ka aura sai kuma
me."?
Asp jikinsa ya mutu murus! bakinsa ya mutu ya gaza furta kalma daya hakika ya bashi mamakin
da bai taba tunani ba. kawai sai ya kashe wayar ya ajiye a gefe ya shiga tunani akan
al'amarin......Tabbas akwai alamun tambaya wannan abun da abokin nasa yake bana masu
hankali da tunani bane.
***
Kamar wanda aka daukewa sha'awa haka ya zama surkududu! duk da yana ganin amaryarsa a
kusa dashi hakan bai sanya yayi sha'awarta ba, gashi nan dai zuciyarsa a kusa abu kadan
yake fusata shi .
Ta shigo dakin ta sameshi a kwance ya tsirawa rufin dakin ido......A sanyaye ta zauna a kusa
dashi da fadin." Yaya na."
Ya kalleta tare da kokarin tashi zaune.
Tace."Kayi hakuri kayi bikon matarka domin Uwale da gaske take akan kudirin data dauka. dan
naga tana yi min wani irin kallo, yanzu bata sakewa dani.
Yayi jim yana nazarin maganar kafin yace." Babu ruwanki a cikin wannan al'amarin kin gane
ko." Shuru tayi tana kallonsa, ya cigaba da cewa." Aiki zai kai ni Zamfara da yardar Allah gobe
da asubah zamu d'auki hanya, ki kula sosai gida kuma duk rintsi kada ki bari Uwale tasa kafa ta
fita daga gidan nan."
Ta marairaice fuska da fadin." Yaya na tafiya kuma nifa amarya ce zaka tafi ka barni."
Ya tsira mata ido yana kallo, sam abunda take bai burge shi sai ma mugun haushi da ta bashi.
tsaki! yaja dogo kafin yace " Tashi kije ki kwanta."
Ganin yanda ya murtuke fuskarsa! babu shiri ta tashi salo-salo ta fita daga dakin. ya koma ya
kwanta yana cigaba da tunanin rayuwa.
***
A 'bangaran Zinatu kuwa tunda taji yanda akayi da mijin nata, ta 'kara tsanarsa a cikin ranta,
cikinsa ma da take dauke dashi ta dora masa karan tsana tun kafin yazo duniya, dan dai yayi
kwari ne amma da duk wuya sai ta zubar dashi ta yar da kwallon mangwaro ta huta da 'kuda.
****
Tafiyarsu Umar din da sati biyu, Asp ya shirya zuwa *KANO* domin tattauna maganar da ta
shafi auran abokin nasa, ya kud'urce a ransa cewa kafin abokin nasa ya dawo daga bakin aiki
yayi masa kokari gurin ganin matarsa ta dawo dakinta.
Bahaushe yace." Kiwon mutum ake ba dabbah ba, wannan damar Commissioner ya samu ya
dinga bibibiyar al'amarin har dai ya fahimci abinda yake da akwai. dama yana bala'in jin haushin
kusancin dake tsakaninsu.
A ranar da Asp din ya tafi shi kuma ya samu damar kiran Umar din su gaisa kana sukayi
maganganun da ya shafi aikinsu, kafin ya shigo masa da maganar dake bakinsa Asp baya gari
yaje Kano ziyara.
Sai ya shiga tunanin abinda ya kai Asp garin Kano bayan bashi da wasu 'yan uwa a can, wani
sashe na zuciyarsa yace masa yaje gurin matarka ne.''
Wani irin bakin ciki ya turnukeshi tabbas ko shakka ba yayi abinda ya kai shi garin Kano kanan.
wato dai mutumin nan ba zai daina bibibiyar matarsa ba, lallai wannan karon dole ya tauna
tsakuwa dan aya taji tsoro!
Saboda haka yana sallama da Commissioner din bai jirayi komai ba ya nemi number Asp din,
sai kuma aka samu akasi domin shi Asp din yana ganin kiran yaki dauka saboda jikinsa ya
bashi ba alkairi bane.
Ya kirashi ya kai sau biyar bai daga ba.
Ya fusata! ya kira number ta, itama tayi shakulatun 'bangaro dashi yayi-yayi ya gaji tana kallo
bata daga ba. takaici yasa ya jefar da wayar ya turmutsa yatsun hannuwansa cikin sumar dake
kansa yana hargitsawa, jikinsa in banda karkarwa babu abinda yake.
Sai da yaci abinci tukkuna ya huta sannan Maimartaban ya zauna dashi domin tattauna
maganar da ta kawoshi garin.
Da yake dattijo ne mai halin girma bai nuna 'bacin ran akan abinda ya faru ba, sai ma dinga
kokarin dora laifin a kan 'yar tasa halin mutanan da kenan ma'ana (kaso naka duniya ta k'i shi)
ka qi naka duniya taso shi) Asp din ya bada hakuri sosai ya bukaci a bashi Zinatu din domin
tafiya da ita.
Ya jima yana nazarin maganar kafin ya kalleshi da fadin." Da izinin abokinka kake tafe ko kuma
dai kaine kake kokarin gyara al'amarin."?
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kwarai kuwa ranka ya dade kafin nazo nan sai da muka
tattauna maganar dashi, yace shi bai ce mata tazo gida ba sa'bani kawai suka samu ya dawo
gidan ya samu bata nan. dalilin da yasa kuma ba muzo tare ba, yaje *Ran gadi!* garin Zamfara
na san kana da labarin irin tashin hankali da yake faruwa a garin."
Yace." Tabbas muna da labarin irin rikicin da yake faruwa a garin, muna kuma rokon Allah ya
kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki daya.
Ya amsa da "Ameen ya Allah insha Allahu komai zai-dai ta za'a samu tsaro da kwanciyar
hankali mutukar an hadu da shuwagabbani nagari."
Yace." Wannan haka yake, samun shuwagabbani nagari a wannan zamanin yana wahala dole
muma mu dage da addua mu kuma gujewa abinda Allah baya so sai mu zauna lafiya.''
Asp ya risina cikin girmamawa yace ." Allah ya taimake ka kayi magana mai ma'ana yawancin
zagin shuwagabbanin da muke shine babbar matsala a gare mu, addua ya kamata muyi musu
domin Allah ya basu ikon aikata abinda ya dace to kaga dole mu kiyaye harshen mu mutukar
muna so mu zauna lafiya a k'asa."
To tsakanin Asp da Sarki Umaru sun tattauna maganganu masu muhimmanci wanda sai mai
hankali da tsinkaye ne zai fahimci inda suka dosa.
Da farko bijirewa tayi da taji maganar ita kam duk abinda za'ayi ba zata koma ba ta gama
auran har abadah.
Babu wanda bai shiga dakin ya rarrasheta ba amma fafur! taki karshe ma sai kawai ta kwanta
tana kuka ita ta gaji da wannan al'amari wane irin aure ne wannan mara 'yanci.
Da yake akwai kauna mai tsanani a tsakaninta da mahaifinta, koda ya shiga dakin rungumeshi
tayi tana kuka tace." Ni ba zan koma ba nafi bukatar rabuwa da auran saboda babu kwanciyar
hankali a cikinsa, tun farko sai da nayi tunanin hakan zata faru amma babu wanda ya fahimce
ni sai yanzu gashi abubuwa marasa dadi suna biyo baya ina ganin ko na koma babu abunda
zai sauya.
Jikinsa ne ya mutu a hankali ya zauna tare da zaunar da ita a kusa dashi, cikin laluma ya fara
kwantar mata da hankali, shi kansa baya san ta koma a yanzu yafi bukatarta a gabansa saboda
yana tausayawa halin da take ciki, hakika yaron ya bashi mamaki mutuka!
Ya rarrasheta sosai tare da sake bata umarni a karo na biyu, ya kuma tabbatar mata da cewa
shine na karshe wata matsalar ta sake faruwa a tsakaninta da mijinta to ba zai mata dole ba
amma dai a yanzu tayi masa alfarma ta koma dakinta.
Mahaifinta yafi karfin alfarma a gurinta, tabbas idan ta bijirewa bukatarsa ba zata ga da kyau ba,
dole ta sanya hakuri da dangana a zuciyarta, amma a can kasan zuciyarta ita kadai tasan
abinda damunta.
Albarka da addua da fatan alkari iyayenta sukayi mata insha Allahu kuma adduarsu ba zata fad'i
a kasa ba.
****
Koda suka isa gidan Uwale kasa 'boye farin cikinta tayi ita kuwa Hamra'u kamar wacce aka
aikowa da mala'ikan mutuwa! tayi kicin-kicin! idonta jawur kamar me shirin fashewa da kuka!
Uwale ta kalli Asp da fadin." Hakika samun irinka a wannan zamanin sai an tsananta binkice!
kai ba za'a kira ka da aboki ba domin ka wuce haka! kana tsaye akan Umaru da al'amuransa
Allah ya saka maka da alkairi ya biya ka da aljanna madawwamiya.
Ya amsa da "Ameen ya rabbi ai ba wani abu bane Uwale ban dauki Umar a matsayin aboki ba
kamar yanda ki ka fada dan uwana ne! wannan dalilin yasa hankalina ya tashi ganin yanda
abubuwa marasa kyau suke faruwa dashi. tabbas akwai abinda yake lullu'be kuma muna rokon
Allah yayi mana maganin ko menene.
Tace." Insha Allahu kuwa Ai babu abunda yafi karfin Ubangiji kai dai Allah ya saka maka da
alkairi."
Ya amsa