Showing 18001 words to 21000 words out of 46235 words

Chapter 7 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale

rirrik'eshi domin shiga dashi
cikin gidan.

Cikin uwar dakin Uwale Kawu Ado ya zaunar dashi, kafin ya fita ya sallami yaran nasa da har
yanzu ba su daina bushe-bushe da buga gangani ba, garin duk ya hautsine! sai kace wani
babban basarake ne ya sauka.


Da sauri- sauri yake sauke numfashi makogwaronsa sai suya yake, a maimakon yaji sha'awar
ruwan sanyi amma abun mamaki a lokacin babu abunda yake bukata face hayakin Sigari ko
shisha duk dai wanda ya samu.

Sai da ya dan samu nutsuwa tukkuna ya fito, aikuwa ya tarar tsakar gidan cike da mata 'yan
uwa da kuma abokanar arziki.

Kaf ya dube gurin babu ita babu dalilinta.

Gabansa ya fad'i! ya kalli Uwale da fadin." Ina Zinatu."?

Tace." Umaru ai kai zan tambaya ni da na barka tare da ita a mota."


Ba tare da ya sake wata magana ba ya kama hanyar fita......matan dake tsaitsaye a gurin sai
gaisheshi suke da kyar yake iya amsawa, gabadaya hankalinsa na gurinta.


Tunda ta hango fitowarsa daga gidab ta dauke kai tare da jan tsaki! cikin ranta take ayyana

wasu abubuwa a kansa.

Ya bud'e motar idanuwansu suka had'u! bai ta'ba jin kunyarta ba irin yau!

Yayi saurin janye idonsa yana dawurwura domin ya ma rasa me zai ce mata.

Ganin haka ya sanya kawai ta girgiza kanta ta fara kokarin fitowa daga motar. ya dauki
handbang d'inta ya rike yana gyara mata hijab din dake jikinta.

Cikin gajiya ta fito daga motar tana dudduba gurin.

Ya rufe motar da fadin.'' Muje ko."? Gaba yayi tabi bayansa kamar bata son taka 'kasa.

Handbag din ya mika mata da fadin." Ki shiga zan shigo yanzu."?

Kallonsa tayi na minti biyu kafin ta girgiza kai da fadin." Ni ba zan shiga ni ka d'ai ba."

Bai ce mata komai ba ya koma gurin motar ya bude ya dauko Shishar sa dake cikin kwali! ba ta
gane komeye ba amma tana ta kallonsa gami daso ta hasaso abunda yake cikin kwalin.


Ido ne yayi caaaaa! a kanta yayin da suka shiga gidan......Wa'inda basu santa ba tambaya
kawai suke "Wannan ce matar UMARU."? Uwale na basu amsa daidai da abunda suka
tambaya.

Ita dai kasa tsayuwa tayi kawai tabi bayansa dakin da taga ya shiga.

Hamra'u na dakin sai share-share take.......Yanayin dakin ya nuna nasa ne tun lokacin
samartaka duba da irin tarin kayan farauta da suka rataye a bagon dakin da kuma tarin
buhun-buhun magungunan gargajiya irin wanda yake bayarwa.


'Kura duk ta tashi a dakin sakamakon rashin gyaran da bai samu ba tsayin watannin da suka
wuce.

Taja ta tsaya bakin k'ofar tana mata wani irin kallo, wallahi bata ta'ba ganin mara zuciya irin ta
ba, kullum cikin bautar namijin da babu guarantee akansa.


Ganin yaki mata magana yasa ita ta magantu tace." Kin ga ya isa haka don Allah! mutumin da
ba zama yazo ba meye zaki damu kanki gurin gyara masa daki, ko kin manta yau zai tafi."

A sanyaye Hamra'un ta kalleshi wai ko zaiyi magana, Uffan bece ba shima so yake ta fita ya

samu sararin busa hayak'insa.

Jiki babu kwari tazo za ta wuce da tsintsinya a hannunta, hanya ta matsa mata har yanzu kallon
shashasha take mata, to idan ba haka ba akan me zata dinga wahalar da rayuwarta.


Ta fita daga d'akin ya fito da shishar ya fara tada hayaki!


Ta kalleshi da fadin." Ni ce marainiyar wayonka ko.''?

Ya kalleta tare daso tayi masa karin bayani.

Murmushin takaici tayi kafin tace." Ka b'oye ashararanci da kake a idon duniya saboda gudun
abun magana amma da yake ni ka mayar dani towon tushe baka jin kunyar aikata abu mara
kyau a gabana."


Ya fesar da hayakin dake bakinsa kafin yace." Kwalbar giya ki ka gani a hannuna."?

Tayi shuru tana kallonsa

Yace." Wannan da yake hannuna! bashi da lada ko zunubi! sanya kai ne ga wanda yake da
ra'ayi kuma bana sha sai irin haka ta faru, ko kin ta'ba tsintar karan Sigari a aljihun rigata."?


Ba tace komai ba tana dai ta nazari da tunani a kansa.


Yayi murmushi da fadin." Ko kin manta kalmar da take cewa (Mata sirrin miji) kece sirri na
kuma ina da ta tabbacin cewa duk rintsi duk wuya zaki rufa min asiri a kowane hali, akwai
bambanci sosai a tsakaninki da Hamra'u."


Maganganunsa suka kashe mata jiki, ta dinga kallonsa tana sake jin kaunarsa na ratsa sassan
jikinta.


Da hannu ya nuna mata kusa dashi da fadin." Zo ki zauna kusa dani sanyin idanuwana."

Murmushi tayi kafin ta nufi gurin ta zauna kusa dashi da fadin ." Dubi jikinka yanda ya 'baci!
kayi wani dukun-dukun! sam wannan rayuwar ba ta dace da kai ba."

Ya ajiye abunda ke hannunsa gabadaya ya mayar da hankalinsa kanta, yace." *ZINA* ina so ki
fahimci wani abu, wannan abun fa ya kai matakin da ba za'a iya raba ni dashi ba, ya riga ya
zama jiki da Jinina! duk sanda tsumin ya tashi bana iya sarrafa kaina, tun ina yaro nake shan
magungunan tauri! a cikin dabbobin da Allah ya hallita masu rai kad'an ne ban ci ba. nayi
gwagwarmaya da jinsi mutum da aljanu domin har so sukayi su bude min ido! ni ne ban bada
goyon baya amma duk da hakan wani lokacin idan sun so suna ziyartata muyi hira su tafi salin
alin ba tare da sun cutar dani ba.... babu tabbas akan aljani kuma ba'a yarda dasu amma ni
bana tsammanin cewar zasu cutar dani da duk wanda ya shafe ni, dalili musulmai ne kamar
yanda nake musulmi saboda haka ki kwantar da hankali kisa a ranki cewa ni ne abokin
rayuwarki."


Gabadaya jikinta ya mutu jin abinda yake fada........Dama ta jima tana zarginsa cewa bashi
kadai yake rayuwa ba akwai masu taimaka masa.

Ta rasa wane irin tunani za tayi a kansa.

Yace." Bayan sallar la'asar za mu tafi gida bana tsammanin barin ki a garin nan."

Wani bala'in dadi y rufe ta, amma bata nuna masa ba tace." Saboda me."?

Shu'umin kallo yayi mata kafin yace." Ba zan iya bacci ba yau saboda sha'awar dake damuna
kwana biyu kina fushi dani kin daina kwana a dakina."

Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Hannu yasa ya daga fuskarta, wanda yayi daidai da shigowar Hamra'u dakin tana sheda masa
ruwan wankan data dora masa yayi zafi."

Hankalinsa gabadaya yana kan matarsa ya amsa da" Okey to na gode kanwata."

A sanyaye ta saki labulan d'akin, zuciyarta kamar ta fashe sakamakon abunda ta gani a
tsakaninsu.



Yana fitowa daga wankan Uwake ke sheda masa cewa Kawunan sa suna son
ganinsa......Yace." Babu damuwa yanzu zai shirya yaje ya samesu.


Ya shiga dakin ya sameta a kwance saman katifarsa sai juye-juye take cikinta ne yake ciwo ga
yunwa na damunta.

Cikin kulawa yace." Zina akwai abunda ke damunki amma idan na tambayeki sai kice babu
komai."


Tana ya mutse fuska tace." Ciki na ne yake ciwo idan ba amai nayi ba to ba zan ji dadi ba.

Girgiza kansa yayi da fadin." Sannu Allah ya sawwake me kike bukata idan na fita na kawo miki
kin san muna da komai na gargajiya."

Tace." Goba da mangaro amma irin wa'inda basu nuna ba."

Yace." Shikkenan."? shuru tayi na minti biyu kafin tace." Meye ma sunan abun."?

'Yar dariya yayi kafin yace." Agwalima kuke ce masa ko."? tace." Yawwa dashi da kuma
Magarya."

Yace." An gama ranki ya dad'e! amma gyad'a marau-marau fa."

Dariya ya bata kafin tace." Ina so." Yace." To insha Allah zan kawo miki, ki kwanta ki huta
yanzu ni zanje gurin. Iyayana suna nema na.".

Tace." To babu damuwa a ce ina gaishesu." Yana kokarin fita ya amsa da zasuji insha Allah."


Yayi wa Uwale sallama lokacin tana kicin tana aikin soye-soye......da yake tana da irin kaji na
hausa wanda take kiwo a can baya, sai ta bar su a hannun Tasallah shine fa tasa aka yanka
mata guda biyar aka gyarasu tsaf ta kawo mata tare da duk abun bukata...




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malam😊: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga

ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*103&104*
Su biyu ya same su zaune a cikin rumfar kwanon dake k'ofar gidan Kawu Adon, a nutse ya cire
takalmansa kafin ya hau kan tabarmar ya zauna cikin girmamawa suka gaisa da juna tare da
tambayar bayan rabuwa.........Kawu Haruna yace." Bayan rabuwa sai alkairi Umaru abubuwa da
yawa sun faru masu dadi da marasa dadi sai godiyar Allah dama kuma haka duniyar take yau
da gobe duk na Allah ne."

Yace." K'warai hakane Kawu Amma naji dadin ganinku cikin koshin lafiya babu wata matsala
wannan ne dalilin da yasa hankalina ya kwanta sosai dan idan ba dole ba, babu yanda za'ayi
nayi nesa daku to kana taka Allah na tasa tabbas hukuncin da Allah ya zartar shine dai-dai."

Kawu Ado yace." Umaru mu ai hakan abun alfahari ne a gare mu, domin ka fita zakkah a cikin
mu, nasan yanzu da yawa wa'inda suke zagin ka a baya jikinsu yayi sanyi domin bahaushe
yace (Dan hakin daka raina shike tsone maka ido) kuma Ubangiji na saukar da ikonsa sai dai
kallo, shiyasa idan kaga wani yana aikata kuskure babbah ko yaro ta kafadi alkairi ko kuma kayi
shuru, jama'a da yawa sun kasa gane hakan, sai sanda Allah ya saukar da ikonsa tukkuna,
saboda haka ka daina damuwa wai dan kayi nesa damu hakan ne alkairi a gare mu bakidaya."

Cike da jin dadin maganar yace." Masha Allah Kawu Na gode kwarai da addua da kuma fatan
alkairi Allah ya kara girma."

Suka amsa da ''Ameen." kafin gurin ya dauki shuru na 'yan mintina.

Ya dan gyara zamansa da fadin." Uwale ce ke sheda min cewa kuna nema na."

Gyara zama yayi tare da gyaran murya kafin yace." Mak'asudin kiran akan wannan yarinya ne
Hamra'u! kwanakin baya mahaifinta ya sameni da maganar muka tattauna kuma ya fahimce ni
sosai amma na sheda masa cewa sai kazo tukkuna za'a tsayar da magana."


Yayi shuru yana nazarin maganar...sam! baya san gaggawa acikin al'amarinsa, amma yana
ganin dole ya amince musu dalili bashi da kwakwkwaran hujjar da zai bayar.

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ni kaina al'amarin yana damuna, kuma na san da yawa daga

cikin mutanan gari sun dauke ni kamar mara amana da cika alkawari! tabbas Allah ke tsarawa
bawa rayuwarsa amma a mafarki banyi tunanin auran wata mace bayan Hamra'u ba, akwai
abinda Allah yake nufi da faruwar hakan, saboda haka yau nake da niyyar komawa bakin aiki
amma zan bar komai a hannuku duk abunda ya kamata ayi na neman aure a tabbatar an
gabatar zan turo kudin hidima da sauransu idan yaso sai a tsayar da lokaci."


Gabadayansu farin ciki ya lullubesu dama babban burinsu ace yaron ya dawo gida yayi aure,
domin auran da yayi a baya sam bai kwanta musu a rai ba sai kuma gashi had'uwarsu ta farko
da sukayi da yarinyar ta nuna k'yama! a garesu wannan shine dalilin da yasa gabad'aya suka
d'ora mata karan tsana basa kaunarta ko kad'an.

Kawu Haruna yace." Allah yayi maka albarka Umaru yanda kayi mana biyayya Allah ya
azurtaka da yaran masu albarka, Allah ya jikan mahaifinka yayi masa gafara."

Ya amsa da "Ameen ya Allah Kawu Allah ya saka da alkairi."

Kawu Ado yace." Yanzu kai ya kamata ka tsayar da lokaci domin mu shedawa mahaifin
yarinyar."

Yayi jim! yana nazari kafin yace." Shekara guda yayi."

Kawu Haruna yace." Haba Umaru wane irin shekara kuma? me ka nema ka rasa da har zaka ja
lokaci haka."

Shuru kawai yayi yana kallonsa shi a ganinsa shekarar shine dai-dai lokacin matarsa ta haihu
hankalinsa zai fi kwanciya baya so yanzu ta samu labari matsala ta afku.

Kawu Adon yace." Kayi shuru kana tunani Umaru ka duba lamarin nan da kyau."


Yace." Kawu akwai dalilin da yasa nace a sa shekara guda domin iyalina na da juna biyu kasan
mata da kishi bana so wata matsalar ta biyo baya idan ta samu labari."


Kawu Haruna ya 'bata fuska tsanar yarinyar ta sake nunnukuwa a ransa yace." Umaru na
dauka ai tuntuni ka shedawa matarka tsakaninka da yarinyar nan Hamra'u, ai bai kamata kaja
bakinka kayi shuru ba tunda tilas ta san ba zata zauna ita kad'ai ba."


Ya tsirawa Kawun nasa ido yana mamakin furucinsa.....Idan ban da kaddara baya tsammanin
kara aure domin bai tashi da ra'ayin haka ba, mace daya ta isheshi rayuwa mutukar ta cika

abunda yake bukata, amma yanda ya tsara rayuwarsa ba haka Allah ya tsara masa ba,
wannan shine dalilin da yasa yake mamakin furucin kawun nasa.

Kawu Haruna yace." Wata shida za'a sanya shine dai-dai."

Yace." To shikkenan Kawu Babu damuwa Allah ya tabbatar mana da alkairi."

Gabad'aya suka amsa da "Ameen ya Allah."

Ya d'an gyara kafin yasa hannu cikin aljihu ya fito da kudi 'yan dubu-dubu saffi kar guda ashirin
ya ajiye gabansu da fadin.'' Ga wannan babu yawa bayan haka akwai kayan abinci a can gidan
Uwale idan na koma yanzu zan sanya yara sukai gida."

Suka dinga godiya suna shi masa albarka gabadaya bakinsu yaki rufuwa sai fatan alkairi suke
masa. sallama yayi musu kafin ya bar gurin cike da tararrabi da damuwar abunda zai biyo
baya.


Kawu Ado ya shiga gidansa bakinsa kamar gonar audiga.

Matarsa Taburni tana tsintar shinkafa ta kalleshi tana mamakin annushuwar da ya shigo dashi
gidan


Kusa da ita ya zauna da fadin." Kina da labarin zuwan Umaru ko."?

Tace." Eh na samu labari a bakin yara Allah yasa da alkairi yazo mana."


Ya fito da sabbin kudin ya ajiye a gabanta, ta dauka tana lissafawa ta kalleshi da fadin." Dubu
goma ne."


Yace." Kwarai kuwa haka ya bani ya kuma bawa Haruna sannan yace yanzu zai turo mana da
kayan abincin.


Ta washe baki da fadin." Kai masha Allah ashe yau za muyi miya da nama! mun gode sosai
Allah ya saka masa da alkairi."


Ya amsa da "Ameen yana tattara kan kudinsa yasa a aljihu da fadin." Bayan haka kuma mun
tsayar da magana wata shida masu zuwa za'a daura auransa da Hamra'u 'yar gidan 'kawarki

'Dayyiba.

Taburni ta rangad'a bud'a farin ciki kamar ya kasheta tace." Lallai Allah yayi aure da mara
kwabo! yanzu kuwa zan je na shedawa kawata halin da ake ciki."

Yace." Ai yanda na lura da yaron kamar yana tsoron matarsa ne idan ba haka ba mai zai sanya
yace sai ta haihu sannan za'ayi maganar aure a take a gurin Haruna ya nuna masa fushinsa.


Taburni ranta a bace tace."Au! ciki ne da matar tasa."?

Yace." 'Kwarai kuwa ciki ne da ita har yayi kwari mana."

Taja tsaki da fadin." Hegiyar yarinya mara mutunci ai duk sanda na tuna abunda tayi mana
sai raina ya 'baci! bana k'aunarta ko kad'an ."

Yace." Duk cikinmu babu mai k'aunarta! wannan ne dalilin da yasa muke so yayi auren cikin
gida domin mu samu wacce zata mutuntamu ta kuma daraja mu."

Tace." Wannan shine gaskiya, naji dadin faruwar wannan al'amarin, Allah kuma ya tabbatar da
alkairi." Ya amsa da "Ameen." Yana kokarin kishingida a gurin.

Ita kuwa da sauri ta tashi ta fara aikace-aikacen ta tana Allah-Allah ta kammala taje ta shedawa
'Kawarta albishir mai dadi.
Da wata iriyar kasala ya koma gidan, gabadaya kansa ya daure ya rasa wane irin tunani zai yi.

Bacci take sosai duk gumi ya ji'kata! da sauri ya dage labulan ya dora saman 'kofar dakin, kai
tsaye dakin Uwale ya nufa ya samo mafici ya fito wanda yayi dai-dai fitowarta daga kicin, ta
kalleshi da fadin." Har ka dawo."?

Yace." Eh yanzu nan na shigo Zinatu taci abinci."?

Tace." A'a ai bayan fitarka na leka dakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login