Showing 9001 words to 12000 words out of 46235 words
Chapter 4 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
ta k'oshi, ido jawur! ta fito daga sashen, sai sukayi kicubus da Hamra'un
tayi wanka tayi ado sosai sai kamshin turare take.....kallon banza tayi mata kafin taja tsaki ta
shige ta bar ta a gurin.
Girgiza kanta kawai tayi ta nufi gurin Uwale domin jin k:arshen labarin.
Ta sameta a zaune fuskarta akwai alamun damuwa.
Suka gaisa sama-sama kowa da abinda ya dameshi a zuciya.
Uwalen ce ta fara magana kamar haka......"Zinatu kiyi hakuri kinji ko, na san wannan abun
shiryayye ne amma babu komai duk auran da ba'a gina shi ta hanyar Allah da Annabi ba, baya
zuwa ko'ina kiyi hakuri da duk abinda za ki gani."
Tace."Uwale me yake faruwa ne? naga yarinyar nan Hamra'u sai shige da fice take a gidan,
shin yaushe ma ta dawo? kuma naji kina maganar aure, ban san me yasa ba tun jiya muke
rigima da mijina na rasa abinda nayi masa."
Murmushi takaici tayi kafin ta shiga warware mata abinda yake da akwai, tace." Ni kaina ban
sani ba, sai yanzu da ita Hamra'un take sheda min cewa jiya da magariba aka daura auran shi
Umar din da kansa yaje garin akayi komai a ka gama to kinji abinda yake faruwa.
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." To saboda kawai zaiyi aure sai ya zama tamkar
mahaukaci! gabadaya fa tsakanin jiya da yau ya fice daga hayyacinsa.
Tace." Ni kaina yau kwana biyu kenan rabon daya shigo mu gaisa da duk rintsi yakan shigo idan
zai fita, sannan kuma idan ya dawo ma zai shigo ya dubani. wannan dalilin yasa nake zargin
wani abu akan al'amarin.
Tace." Uwale idan da matsala ni zan tattara kayana na tafi gida hankalina sai yafi kwanciya
bana san tashin hankali."
Ta kwantar da kai da fadin." Kada ki yanke wannan hukuncin Zinatu ki cigaba da hakuri duk
abinda mijinki yake baya hayyacinsa. Asiri akayi masa."
Ido ta tsira mata tana mamakin maganar ASIRI to waye zai yi musu ASIRI irin wannan.
A tare suka shigo falon, duk suka zuba musu ido suna kallo....Ita Hamra'un kicin ta nufa, shi
kuma ya zauna kusa da Uwale suna gaisawa.
Babu yabo babu fallasa ta amsa sai kallonsa take tana mamakinsa.........Ya dan duba agogon
hannunsa da fadin." Uwale sai ki kaji sabon al'amari ko."?
Tace." Eh abun ya bani mamaki Umaru ya akayi ka sauya shawara."?
Kai tsaye yace." Hakan ne samun kwanciyar hankalina domin bana samun nutsuwa a tare da
wacce nake rayuwa da ita.
Tace." Wannan maganar sam bata dace ba Umaru me yasa zaka sanja hali zaka kawo rashi
zaman lafiya a gidanka."
Yace." Uwale ki bar wannan maganar don Allah nifa dama can dole akayi min yanzu ne na auri
zabin raina."
Ta fusata! zuciyarta na tafasa! tace." Yanzu ma ba'ayi maka dole ba ka *SAKE NI MANA."!*
Innalillahi wa'inna ilahi raji'un! abinda Uwale take nanatawa kenan, lallai Dayyiba bata da Imani
tana so ta raba sunnar ma'aiki.
Ta sake maimaita maganar kamar sabuwar mahaukaciya.....*"KA SAKE!* ni idan ka cika dan
halak ne kai." Jikinta har karkarwa yake ta mike tsaye tana so taje gurin da yake zaune.
Ya mike a zabure! da fadin" Kada ki kuskura kizo nan sai kakkarya miki 'kafafu." yana gwada
yanda zaiyi da hannunsa.......Ba ta tsorata ba ta 'karasa da fadin." Gani dama tun jiya kake duka
na ka karya ni kaga abinda zai faru."
Ya daga hannu da niyyar zabga mata mari Uwale ta rike hannun tana kuka take fadin." Wannan
wane irin tashin hankali ne Umaru anya ba za kayi wa kanka fad'a ba."
Hawaye masu zafi suna gudana a saman fuskarta tace." Uwale ki kyaleshi ya aikata abinda yayi
niyya dama ai ba yau bane farko.
Tace." Aa ba za'ayi haka ba Zinatu kiyi hakuri ki koma gurinki insha Allah komai zai daidaita."
Hanci ta shaka kafin ta girgiza kanta ta juya da sassarfa ta fita daga falon.
Ya koma yana zauna yana wani irin nishi, sai gumi yake kamar wanda yayi 'yar
tsere......Hamra'u dake tsaye da fulas din shayi a hannunta ranta ya 'baci ganin abinda takeso
bai faru ba, jikinta a sanyaye taje ta ajiye fulas din kan daining ta koma kicin domin fito da
sauran kayan breakfast din.
Ta shiga sashenta ta sanya Baraka ta hada mata kayanta gida zasu tafi .
Ta zaune gefan gado jikinta sai rawa yake ta nemi number Asp murya a dashe suka gaisa,
tace." Zan tafi gidanmu ranka ya dade bahaushe yace." Ta inda aka hau ta nan ake sauka."
Da sauri yace." Zinatu idan na isa dake kada ki kuskura kije ko'ina kinji abinda nace miki ko."?
Kashe wayarta tayi bata tsammanin zata tsaya jiran wani abu.
Wanka tayi a gurguje! ta shirya, ta umarci hadimanta suka shirya.......Direban dake dawainiya
da gidan ya daukesu a mota suka dauki hanyar *KANO*
Minti ashirin da tafiyarsu Asp ya shiga gidan, kai tsaye sashenta ya nufa........ya tarar ko'ina a
rufe! hankalinsa a tashe ya nemi number wayarta a kashe.
Hannu na rawa ya kira abokin nasa yana ganin kiran yaki d'auka idan akwai wanda ya tsana a
duniya yake jin haushinsa Asp din ne.
Yayi ta kiran wayarsa yaki dagawa, sai ya hakura ya shiga har gurin Uwale suka gaisa, anan ne
ta san da cewar Zinat din bata gidan.
Tafi Asp din shiga tashin hankali, lallai babu shakka a wannan karan dole ta tauna tsakuwa dan
aya taji tsoro.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:55 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*115&116*
Suna shirin tashi daga aiki mai girma Commissioner ya same shi a ofis, cikin girmamawa ya
mika masa hannu suka gaisa kafin." Yace." Tunda naga mai girma da kansa to na san babban
al'amari ne."
Murmushi yayi kafin yace." K'warai kuwa Umaru wani aiki ne ya taso sai naga da cewar kaja
tawaga ma'ana ka zama jagora a tafiyar."
Yace." Insha Allah zan bayar da gudummawata.
Wata takarda ya fito da ita yana masa bayani cewa za suje *ran gadi* Zamfara saboda rashin
kwanciyar hankalin da suke fama dashi.....za su hadu da jami'an tsaron garin domin kawo
karshen ta'addancin da yake faruwa. gwamnatin garin tare da jami'an tsaron can suka bukaci
wannan taimakon daga gurinsu domin suna sa ran idan ya shiga cikin al'amarin za'a samu
maslaha."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.'' Ranka ya dade babu matsala yaushe ne tafiyar."?
Yace." Idan Allah ya kaimu gobe amma da Asubah zaku dauki hanya."
Yace." To Allah ya kaimu lafiya, amma me yasa ba'a za'ayi tafiyar da Asp ba."?
Girgiza kansa yayi da fadin." Akwai dalili shi akwai muhimman ayyukan da zamu gabatar tare
dashi."
Ya mika masa hannu da fadin." Allah yasa mu dace." Ya amsa da ameen ya rabbi.
Sallama sukayi cikin mutunci da girmama juna. tun lokacin da Commissioner ya fahimci cewa
Umar din ba irin mutanan da ake nuna su da yatsa bane ya kiyaye abinda zai kawo musu
samun matsala domin ya fahimci cewar Umar din yana da babban matsayi a government
house bayan haka kuma manya 'kasa suna ji dashi, domin shi kansa shugaban k'asa yana
alfahari dashi saboda yana taka muhimmiyar rawa gurin dakile harkokin ta'addanci a kasa baki
daya.
A maimakon ya kira Asp ya sheda masa abinda yake faruwa sai kawai yaja bakinsa yayi shuru
haka kawai yake jin wani irin haushinsa da kiyayyarsa a zuciyarsa duk wanda ya danganci
yarinyar haushinsa yake ji.
Asp ya samu labari a bakin Commissioner dole sai da sa hannunsa komai zai tafi dai-dai, koda
yaga abokin nasa ne zai jagoranci tafiyar sai yayi mamaki mutuka amma bai nuna a fuskarsa ba
saboda baya so wani ya fahimci cewa akwai sa'bani a tsakaninsu.
Ya isa gida cikin tarin gajiya da damuwa da rashin walwala duniyar gabadaya tayi masa zafi ya
rasa wane irin tunani zai yi.
Ya samu Uwale ta had'a kayanta tsaf tana jiran shigowarsa, ganinsa sai kawai ta fashe da
kuka! kariris!
Hankalinsa ya tashi ainun! domin ko kadan baya kaunar damuwarta.
Ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, amma fafur! taki tayi shuru! ya kalli Hamra'u da tayi
tsuru-tsuru! alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, yace." Me yake faruwa ne shin
me kukayi mata."?
Tace." Wallahi nima ban sani ba tun dazu nake tambayarta tayi shuru sai share hawaye take
wai *'Kafur!* za ta tafi."
Ya kalleta da fadin." Wane irin *'Kafur* kuma? ai na dau'ka ko sati uku baki da zuwa ba, ko
wani ne ya mutu a can."?
Tace." Umaru zama a tare da kai bashi da amfani tunda ban isa na saka ba kuma ban isa na ha
naka ba, to zanyi tafiya ta k'auye zamana a can yafi alkairi."
Yace." Me nayi miki wanda ya janyo wannan maganar."
Tace." Akan abunda kake Umaru shin ko ka samu ta'bin hankali ne."?
Yace." Lafiyata lau na san dai duk kina wannan maganganun akan Zinatu, gabadaya ni yanzu
bana ra'ayin zama da ita.
Tace." Shine dalilin da yasa ka koreta dada gidanka.?
Babu wata damuwa a tare dashi yace." Aa ni ban kore ta ba, ita ta kori kanta."
Tace." To shikkenan tunda kace haka mutukar kana bukatar zama tare dani kaje kayi bikon
matarka."
Yace." Uwale ni yanzu muhimiyyar tafiya ce a gabana gobe insha Allah, sai dai idan na dawo."
Shuru tayi kafin tace." Umaru baka kyauta ba wallahi jiya abokinka yazo gidan nan hankalinsa
a tashe, a bakinsa na samu labari cewa yarinyar bata gidan.
Yace." Kina nufin Asp yazo gidan nan bayan na fita."?
Tace." Eh yazo kuma yayi min cikakken bayani akan abunda yake faruwa tsakaninka da
matarka, gabadaya kaine baka da gaskiya Umaru me yasa ba zaka tausaya mata ba duba da
juna biyun da take tare dashi."
Yayi shuru zuciyarsa nayi masa wani irin zafi! Asp ya samu damar da har yake shigo masa gida
ba tare da izininsa ba, har ya samu damar da zai dinga bibiyar abunda ya shafi iyalinsa, shi ai
ba yayi masa wannan katsalandan din, ya kamata a wannan karan ya nuna masa kuskuransa.
Hamra'u ta had'a masa ruwan wanka yayi ya samu sassauci amma kadan domin shi kadai ya
san irin bakin cikin dake cin zuciyarsa.
Ya sanya jallabiya da gajeran wando ya fito falo fuskar nan a murtuke!
Ita kuwa Amarya ta rangad'a ado sai kamshin turare take mai dad'i da tayar da sha'awa.
Yana zama gurin cin abinci ta isa gurin cikin kwarkwasa da karairaya ta hada masa abincin ta
zauna kujerar dake fuskantarsa tana murmushi take bashi labarai irin na jan hankali.
Shi dai uffan bece ba abincinsa kawai yake ci, abinda ya dame shi ne a gabansa.
A gabanta ya kira wayar Zinatu. koda ta duba taga shine sai ta ajiye wayar........Lokacin
mahaifiyarta ta shiga dakin ta samu kiran ya sake shigowa a karo na biyu.
Ta kalleta cikin tausayi da jin kai irin na uwa, tace." Ki daga wayar mana."
Murya a dashe! tace." Shine fa."
Tace." To sai me? ki daga kiji abinda yake tafe dashi."
Kamar ba taso ta daga wayar tasa a kunne can kasan makoshi tayi sallama!
Gyaran murya yayi kafin yace." Na dawo na samu labarin kin tafi gidanku shin me kike nufi da
aikata hakan."?
Shuru tayi ta gaza furta komai.
Yace." Ke nake sauraro ko kin gaji kamar yanda nima na gaji."?
Hanci taja kafin tace." Bani da lokacin tsayawa na saurarin wannan mayaudariyar muryartaka
duk hukuncin daka yanke dai-dai ne a guri na."
Kawai ta katse wayar ta ajiye. wasu zafafan! hawaye suka kwace mata! ya cuceta ya dirka mata
ciki yana mata iskancin da ransa yake so.
Uwar ma kamar ta fashe da kuka saboda da takaici. kaf rayuwar yarinyar kwatankwacin
rayuwarta ne! tausayinta duk ya isheta, ta sassauta murya da fadin." Kiyi hakuri ki kwantar da
hankalinki insha Allah zamu tattauna maganar da mahaifinki idan auran ba zai yuwu ba a rabu
shi yafi alkairi."
Da sauri tace."Mammah ni kaina nafi bukatar rabuwar, babban takaici na wannan cikin da nake
dauke dashi."
Tace." Wannan kuma sai ki barwa Allah, domin shi ya barwa kansa sanin abinda yake boye,
kawai kiyi fatan rabuwa dashi lafiya."
Kasa magana tayi kawai ta sunkuyar da kanta sai so take ta tsayar da hawayen dake zuba
amma ya gagara! zubar hawayen shine samun zaman lafiyarta.
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta girgiza kai ta kama hanyar fita zuciyarta cike da tunanin
neman mafita.
Kishingide ta sameshi a dakin hutawarsa.
A nutse ta zauna kusa dashi kafin tace." Barka da hutu ranka ya dade."
Ya amsa da "Barka kadai Gimbiyar mata ya gida ina 'yar uwar taki.''? ya tambayeta Safara'u
saboda ya san abinda ya kawo ta gurinsa bayan ba girkinta bane tabbas itama Safara'un tana
tafe.
Tana kokarin magana Safah din tayi sallama, jikinta nannade da lifaya kwantankwancin ta jikin
Aysha.
Suka gaisa cikin girma da mutunta juna.
Zamansa ya gyara yana kallonsu daya bayan daya kafin yace." Labarin gizo a tambayi koki tun
kafin kuyi min bayanin abinda yake tafe daku na karanci hakan a fuskokinku. to ina jiran
shigowar Magajin sarki ne domin shi nakeso ya kira mijin yarinyar muji daga bakinsa."
Gimbiyar tasha kunu da fadin." Ranka ya dad'e wannan al'amarin fa bana wasa bane ya za'ayi
a matsayinka na mahaifin yarinyar nan ka wakilta wani ai sai ya kara rainawa mutane hankali
saboda haka kai ya cancanta kayi magana dashi."
Yace."Aysha ko bayan raina Abdullahi shine Magaji na, wannan dalilin ya sanya nasa shi a cikin
maganar domin yayi wa 'yar uwarsa wakilci, ita tazo da magana to amma yana da kyau shima
mijin nata aji daga bakinsa.
Tace." Wannan yaro fa bashi da kirki! ranka ya dade in banda wulakanci da ciki zai kori yarinya
me tayi masa haka da zafi."?
Yace." Ashe har kin manta halinta kenan? Aysha idan ke kin manta wacece Zinatu ni ban
mance ba, kada ki manta irin d'auki ba dadin da muka dinga yi da ita kafin ta amince da auran,
ko shakka ba nayi matsalar daga gurinta take.
Safah ta katse shi ta hanyar fadin." Kada kayi gaggawar yanke hukunci ranka ya dad'e! yanda
yarinyar nan ta zabge lokaci guda shine zai nuna mana cewa akwai matsalar da take faruwa a
tsakaninsu kuma taura d'aya bata taunuwa, bahaushe yace idan anbi ta b'arawo to abi ta mabi
sawu, dole shima nasa laifin saboda haka yana da kyau yazo gabanka ku tattauna domin
magana ta waya ba zata gamsar ba."
Yace." Wannan shawarar taki tayi Safara'u abinda za'ayi kenan. Insha Allah komai zai warware.
Magajin Sarki ne ya shigo da sallama a bakinsa.
Gabad'aya suka amsa. ya samu guri ya zauna kafin ya fara gaishe su......Maimartaba yace." Ka
kira Umaru mijin Zinatu kace masa ina san ganinsa idan ya samu dama."
Ya fito da waya domin bin umarni.
Daf da zata katse ya daga wayar............bai ma duba suna ba, sai da yayi masa bayanin kansa
sannan yace." Magaji afuwa don Allah ya mutan gida ina fatan kuna lafiya."
Yace." Kowa Lafiya lau dama Maimartaba ne ya bukaci ganinka idan ka samu dama."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Magaji ayi min afuwa ina da uzuri aiki zai kani Zamfara sai
dai idan na dawo.''
Ransa ya baci da jin abinda yake fada.......Yace." Okey to idan babu damuwa inaso na san
dalilin da ya sanya Zinatu zuwa gida."
Yayi jim yana nazarin maganar kafin yace." Babu wani 'kwakw'kwaran dalili nima kawai na dawo
gida na samu bata nan."
Yace." No! akwai dalili Goje sai dai idan ba zaka fada ba."
Murmushi yayi kafin yace."Ka tambaye mana ni dai na san lafiya lau muke zaune amma ina
tunanin kishi ne dalilin da ya sanya ta yanke wannan hukuncin."
Yace."Kishi kuma."?
Yace." Eh 'kwarai kuwa na 'kara aure kwana uku da suka wuce wannan shine abinda nake
tunani."
Yayi murmushi da fadin." Ni a ganina wannan kadai ba zai janyo har tazo gida ba ko ka manta