Showing 12001 words to 15000 words out of 46235 words
Chapter 5 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
da lalurar da take tare da ita."? A dan kausashe! yayi maganar.
Shima ya fusata! yace." Magaji yarinyar nan fa bani na koreta ba, ita ta kori kanta, kuma
saboda ita ba zan fasa abinda nayi niyya ba, nasan kasan mata hudu Allah ya halasta min to
akan wata ba zan tauye rayuwata ba."
Ya girgiza kansa da fadin." Okey to babu damuwa Allah ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya.
Ya amsa da "Ameen ya Allah."
Cikin rashin dadi sukayi sallama da juna.
Da yake hands free yasa wayar duk suna jin abunda suka tattauna.
Yana kishingide bai ce komai ba.....Gimbiya Aysha kuwa sai fad'a take da fadin." Wannan auran
warwareshi shi yafi alkairi dama can ita al'amarin be kwanta mata ba, auran jahili wanda yayi
rayuwa a daji! bashi da fa'idah mutumin kauye akwai karancin ilimi ta tare dashi babu abunda
ba zai aikata ba."
Duk yana jin sababin da take bai ce komai ba har sai da ta gama tukkuna ya gyara zamanshi
kafin ya fara magana kamar haka.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*97&98*
Wani irin bacci sukayi mara dad'i sakamakon damuwar da suke ciki. da yake namiji ne shi
yakan iya danne damuwarsa ita kam ta kasa dannewa domin gabadaya jin kanta take a takure!
ita akan kin kanta tasan yun'kurin da tayi ba mai kyau ba ne, shiyasa take bala'in jin kunyar
hada id'o dashi!
Kwance ya sameta saman gado tun bayan sallar asubahi ta kwanta tana k'okarin gayyatar bacci
yaki zuwa babu shi ma gabad'aya a idonta tunani yafi yawa a tare da ita.
Ido ta tsira masa har ya k'araso bakin gadon, ya shirya tsaf da niyyar fita gurin aiki.
Babu yabo babu fallasa ya kalleta da fadin." kin tashi lafiya."?
A hankali ta amsa tana dan lumshe idonta.
Kallonta yake yana ayyana abubuwa da yawa a kanta, yanayin ta ya nuna kamar mara lafiya.
Ya daure zuciyarsa yace." Ko kina da damuwa ne."?
Zuciyarta ta karye hawaye naso ya zubo tana mayar dashi bata bukatar tayi masa kuka tunda
yana kiranta da shagwababbiya.
Shuru tayi ba tace masa komai ba. sai da ya sake maimata maganar sannan tace." Lafiya na
kalau."
Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin" Okey haka nake so ni zan fita amma idan kinji
wani guri nai miki ciwo ki kira ni a waya."
Ta kalleshi k'auna da sonsa na kara nunkuwa a zuciyarta, a jiyar zuciya ta sauke a hankali tace
" To."
Ya kama hanyar fita jikinsa duk babu dadi, yarinyar ta tsaye masa a rai.
"Haka zaka fita ba kayi breakfast ba."?
Maganarta ta katse masa hanzari. juyowa yayi yana kallonta.
Ta sunkuyar da kanta domin bata jurewa kallon kwayar idonsa.
" Kada ki damu zan samu abunda zan ci buri na ki tashi ki nemi abinci kici ko dan abunda ke
cikin ki idan kinyi min haka kin gama min komai."
Ta yun'kura ta tashi tana d'an ya mutse fuskarta.
Saurin kawar da kansa yayi sakamakon ganin zahirinta kayan bacci ne a jikinta wanda suka
fitar da wasu sassan na jikinta.
Yay gaggawar bude kofar dakin ya fita yana jin yanda jarumarsa ke motsi har ta fara yun'kuri!
al'amarin ya bashi mamaki mutuka! koda yake ba'a abun mamaki bane idan anyi la'akari da
kwanakin da ya dauka rabon da ya hada shinfida da ita.
Yana zama a ofis kiran wayar Maimartabar ya same shi.
Suka gaisa cikin mutunci da dattako.
Maimartaban yake sheda masa cewa suna da baki da misali sha biyu jirginsu zai sauka anan
filin jirgi na Katsinan.
Farin ciki yayi sosai ya dinga godiya tare da adduar Allah ya saukesu lafiya.
Sukayi sallama cikin girmama juna.
Cike da farin ciki ya kira wayar ta.
Fitowarta daga wanka kenan tayi saurin dauka tare da zama gefan gado.
Ya sheda mata abunda yake faruwa.
Jikinta a sanyaye tace." Me yasa ka sheda musu abunda yake tsakanimu.''? murya na rawa
take maganar
Yayi shuru yana nazarin maganarta.
Tace." Shikkenan na shiga uku ka janyo min bacin ran iyaye na."
Ya kwantar da murya da fadin." Ni fa ban fada musu maganar da wata manufa ba, na fada
musu ne domin su ta ya ni neman mafita, amma bana fatan ranar da zan shiga tsakaninki da
iyayenki."
Ta share hawayen saman fuskarta kawai ta kashe wayar saboda kukan da yake kokarin kufce
mata.
Sake kiran wayar yayi tana kallo tana ringing taki dauka, ita yanzu tashin hankalinta zuwan
Mahaifiyarta tasan bacin rai ne zai biyo ba.
Babu kuzari a tare da ita ta kimtsa jikinta, ta nemi kujera ta zauna tana duba agogo sha biyu ta
gota tasan yanzu mybe sun sauka .
Wayarta ta d'auka cike da fargaba ta kira mahaifiyarta.
Murya na rawa tace."Mommy ina wuni."?.
A dakile ta amsa gaisuwar.
Ta daure tace." Kun sauka ne."?
Gimbiyar tace." Eh sun sauka dan yanzu suka kira waya, babu ni 'Yar uwata ce sai yayyunki."
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sanyi a zuciyarta tasan SAFAH tana da sanyi rai ba kamar
mahaifiyarta ba.
Ta katse tunaninta da fadin.'' Kin kyauta abunda ki kayi ZINA kin janyo min zagi da cin mutunci
na gode." Ba ta jira amsarta ba, kawai ta kashe wayarta.
Ita kam shuru tayi da waya a hannunta gabadaya ta rasa ya za tayi da rayuwarta.
SAFAH tare da Hassana da Hussaina da Magajin sarki suka sauka a gidan......Farin cikin
ganinsu yasa ta fashe da kuka! ta dinga rungumesu duk ta rasa yanda za tayi saboda jin dadin
ganinsu.
Magajin Sarki yace." Ki samu nutsuwa haka zuwan mu gidanki baya nufin farin cikin ki. akwai
babban dalili ne ya kawo mu gidanki."
Ta nemi kan kujera ta zauna jikinta duk a sa'bule.
Ya fara yi mata fad'a tare da kawo mata ayoyin al'kur'ani da hadisai duk dai akan abunda ta
aikata mara kyau!
Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, dukkaninsu kowa ya tofa albarkacin bakinsa mussaman
SAFAH da ta dinga yi mata nasiha mai ratsa jiki anan ne ta zubar da hawaye, tana kukan tace."
Mammah dan Allah ku gafarce ni wallahi tsautsayi ne da son zuciya insha Allah ba zan sake
maimaita abu mai muni irin wannan ba.
Hassana tace." To Alhamdulillhi haka muke so muna rokon Allah ya sauke ki lafiya ya kuma
inganta duk abunda zaki haifa."
Gabadaya suka amsa da "Ameen." Kafin su fara yun'kurin tafiya.
Tace." Mammah har zaku tafi ni wallahi na dauka kwana za kuyi."
Magajin Sarki ya harareta da fadin." Sai kace mahaukata ko."?
Ta 'bata rai da fadin." Aunty Hassana don Allah ku zauna ku kwana mana."
Hussaina tace." Baki da hankali ZINA daga zuwa sai mu kwana ke a ganinki hakan yayi
dai-dai"?
Tace." To meye wallahi babu matsala kuna gani dai kowa da gurinsa to me zai dame ku."
SAFAH ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta da murmushi a fuskarta tace." Zinatu rigima
kin ga tashi kiyi mana Jagora cikin gidan mu gaisa dasu. ke kanki kin san abinda kike bukata ba
mai yuwu wa bane.
Cike da rashin dadi ta tashi ta shiga daki domin dauko mayafi, nan Aunty Hussana ta bita dakin
ta bata wata leda dake cike da turarukan wuta da humra masu kamshin gaske, sai kuma
kaninfari da yawa cikin wata leda a d'aure, tace mata ta jika cikin wani abu tana shan ruwan.
Godiya sosai tayi mata kafin su fito daga dakin a tare.
Uwale tsohuwa mai dattako! ta kar'be su hannu biyu tana ina a saka ina a sauke dasu.......Da
yake basa rabo da abinci ta sanya Hamra'u ta had'a musu abinci wanda zai gamsar dasu.
Haka nan suka saki jikinsu suka ci abinci wanda Hamra'u ta sarrafa sosai Allah yai mata baiwar
iya sarrafa abinci ko wane iri ne a zahiri suma sun yaba sosai kuma ci sun gamsu.
Itama ZINAT din taji dadin yanda aka karramasu ta saki jikinta tamkar akwai sabo a tsakaninsu,
har tana jan Hamra'un da hira, wanda hakan ya basu mamaki mutuka, to itama dai Hamra'un
saki tayi kamar wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninsu ba.
Tafiyarsu keda wuya ya kira wayarta yana tambayarta.
Tace." Ai har sun tafi."
Cike da mamaki yace." Sun tafi."?
Tace."Eh nima wallahi babu yanda banyi dasu ba su kwana amma sun tafi kamar ana korarsu."
Ya girgiza kai da rashin jin dadin hakan, yace." Me yasa da zasu tafi baki kira ni kin sheda min
ba, sai na bar duk abunda nake nazo mu gaisa."
Tayi shuru domin ba tasan me za tace ba.
Yace." Laifin duk naki ne Zina kwata-kwata banji dadin tafiyarsu ba naso mun gaisa da juna
sosai."
Tace." Kayi hakuri amma ai sun gaisa da Uwale har suka ci abinci a gurinta.
Yace." Hakan ma yayi amma Uwale daban ni daban."
Tace." Hakane kuma." Shuru ya ratsa tsakaninsu kafin tace." Daddare me kake bukatar ci."?
Kai tsaye yace." Towon dawa da miyar kuka."
Iya gaskiyar sa ya fadi maganar.
Amma sai ta kyalkyale da dariya da fadin." Towon dawa! gaskiya ni ban iya ba."
Yace." Aikuwa ki koya domin shine favorite d'ina mussaman dumame towo ko wane iri ne ina
sonsa.
Tace." To shikkenan kada ka damu yau ma da kaina zan maka abincin insha Allah."
Yace."Okey da can bake kike ba kenan."?
Da sauri ta gyara maganarta tace." Ni ce mana ina nufin yau na mussaman zanyi maka towon
da kake so.
Yace." Idan da akwai matsala ki zauna ki huta kin san baki da koshin lafiya."
Murmushi tayi da fadin." Naji sauki ai ina bukatar samun ladan aure."
Murmushi jin dadi yayi yana juyi kan kujerarsa yace." Shikkenan yau da daddare za muyi hira
kenan."
Tana 'yar dariya tace." Sosai irin wacce ba mu ta'ba yin irinta ba."
Yace." Alhamdulillhi na gode Allah da ya bani ke a matsayin matata."
Tace." Nima haka amma dai ka yafe min laifi na ko."?
Ya gyara zamansa da fadin.'' Na yafe miki kuma da ikon Allah zan d'aga miki ki shiga aljanna
Bakya laifi a guri na GIMBIYATA."
Tace." Na gode *Mazan Fama!* Allah ya barmu tare." ya amsa da "Ameen wani irin farin ciki
na ziyartarsa.
Aikuwa kamar yanda tayi masa alkawari, da kanta ta shiga kicin din, ta sanya Marakisiyya ta
harhad'a mata komai wanda zata bukata, yau abunda bata ta'ba yi ba zata kwatanta.
Ita kad'ai a kicin din tana gwagwarmaya! duk ta jigata, sai gumi take abunka da wanda bai saba
ba.
Akayi rud'e kalau! aka rufe ruf! sannan aka shiga had'a miya, tayi dubarar silala naman da
albasa da kayan 'kamshi amma bai wani dahu sosai ba, ta zuba su daddawa da kayan miyan
data murza a gireta, ta zuba uban farin mai tamkar me shirin yin jar miya.........Can rud'en dake
rufe ya fara za'bal'bala kafin kice me murfin tukunyar yayo sama talgen ya fara kumfa yana
zuba saman gas din, da sauri take k'okarin cire murfin aikuwa ta 'kone a hannu!! baya ta
matsa tana ihu!! taje ta kwance famfo tana wanke talgen daya kona ta. kuka ne kawai ba tayi
ba fatar hannunta tayi jajawur! ido jawur! ta fita daga kicin.
Ta zauna kan kujera tana mayar da numfashi..........A'a abu kamar wasa hannu ya fara tashi!
ga wani irin zafi da yake mata......kira ta kwalawa Marakisiyya tace mata maza taje ta k'arasa
ita tayi abunda zata iya.
Tashi tayi ta shiga d'aki ta kwanta, tana jinyar hannunta.
Daf da zai shigo gidan ya kira wayarta, ta daga su gaisa yana tambayarta jikinta, tace." Lafiya
amma garin yi maka towo na k'ona hannu.
Yace." Subahanallahi garin ya hakan ya faru."?
A shagwabe tace." Talgen ne ya dinga zuba naje bude tukunya ya zubo min a hannu."
Yaji duk wani iri a jikinsa yace." Sannu my love amma ba sosai bane ko."?
Tace."Eh ba sosai ba amma har ya tashi sai ciwo yake min."
Yace." Yi hakuri kinji bari yanzu zanzo nai miki addua insha zaki ji sauki."
A sanyaye tace." Okey my darling na gode sai ka shigo." kashe wayar yayi yana Allah-Allah ya
isa gidan.
Wanka tayi ta kimtsa domin bata so ya shigo ya sameta babu ado, tunda tasan yana san haka
shiyasa ta mayar da hankali gurin yi masa ado da kwalliya na kece raini.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*99&100*
Wani sanyi ne ya ziyarceshi yayin da yayi tozali da ita a hakimce tayi ado irin wanda yake
bala'in burgeshi, in ban da kamshi babu abunda take........Gabadaya wata irin kasala ta rufeshi
tsananin sha'awarta ya sake kamashi, shi dai yana bala'in son kamshin jikinta.
Kusa da ita ya zauna ya jifanta da wani irin kallo, ta marairace fuska tana kallonsa kafin tayi
masa barka da zuwa.
Ya dubi hannun da ya kone! tsigar jikinsa ta tashi, a hankali ya rike hannun ya fara tofa mata
addua ya gama ya kalleta cike da kulawa yace." Ke zanyi wa sannu duba da irin tsautsayin da
kika samu ta dalili na, tunda kika sheda min hankalina ya tashi ina Allah-Allah na iso gida naga
halin da kike ciki, amma abun mamaki sai na sameki cikin koshin lafiya kinyi ado da kwalliya irin
wanda nakeso ina mai tabbatar miki da cewar ina alfaharin kasancerki a matsayin matata."
Murmushi tayi tare da jin dadin kalamansa, dama kuma babban burinta bai wuce ace ta siye
zuciyarsa kaf ya daina ganin ko wace mace a gabansa ba sai ita, ta lura yana da sau'kin kai!
kuma ta fahimci ya kamu da tsananin sonta wannan abin alfahari ne a gurinta.
*****
Da safe kafin ya fita gurin aiki yake sheda mata tafiyar da za suyi, sam ba tayi tunanin cewa har
da ita za'ayi tafiyar ba, sai da taji yana fadin." Za ku kwana biyu a k'auyen domin kisan 'yan
uwana suma su sheda ki sosa.''
Sai ta kasa 'boye bacin ranta! ta dan 'bata fuska tana kallonsa.
Ya fuskanci ba tayi na'am da tafiyar ba, ransa bai masa dadi ba.
Ganin taki yin magana ya sanya ya tashi da niyyar fita.
Ta kalleshi a lokacin da yake gyara f-cap din kansa. da kyar tace." Sai ka dawo."
A dakile ya amsa ya kama hanyar fita zuciyarsa duk babu dadi, sam bai ji dadin abinda tai masa
ba, ya lura har yanzu ba ta k'aunar a halinsa, a ganinsa duk soyayyar da take nuna masa a
banza take, mutukar ba zata kaunaci yan