Showing 15001 words to 18000 words out of 46235 words
Chapter 6 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
uwansa ba.
Ya saba kiran wayarta idan ya samu saukin aiki amma a ranar sai ya share ta yana so ya nuna
mata kuskuranta
B'angaranta kuwa ba wai zuwa 'kauyen ne ba taso ba,cewar da yayi zata zauna tare dasu har
na tsayin wasu kwanaki shine abinda ya 'bata mata rai! gaskiya bata tunanin kwana a kauyen
'kafarta-'kafarsa.
Da taji shuru bai kira ta ba, sai ta kira shi, ya daga yana shan k'amshi.
Murmushi tayi kafin tace." Fushi kake ko darling."
Gyaran murya kafin yace." Fushi akan me? a halinki ai ba sabo bane a gurina."
A shagwabe tace." Au! mugun hali ne dani."?
Yayi shuru bai ce mata komai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye tace." Kayi hakuri ba wai bana so naje bane naji kayi maganar
kwanaki shine bana so."
Ya fusata! yace." Kin ga idan ma ba zakije ba kiyi zamanki okey." Kawai ya kashe wayarsa.
Ta dinga bin wayar da kallon mamaki! ita fa yanzu kwata-kwata bata bukatar abunda zai shiga
tsakaninsu, amma ta fahimci akan 'yan uwansa zai iya cin mutuncin kowa.
A'a! abu kamar wasa 'karamar magana na nema ta zama babba! fushi yake da ita sosai! dan
koda ya dawo daga gurin aikin bai shiga gurinta ba, ya gama duk abunda yake ya nufi
sashensu Uwale, zuciyarsa duk babu dadi.
Koda taji shuru bai shigo ba, sai ta yanke shawarar zuwa gurinsa, tunda zuwa yanzu ta san ya
dawo, ita sam ba taga abun fushi da 'bacin rai ba, bata gudin 'yan uwansa. halinsu ne kawai
abun gudu.
Koda ta shiga gurin nasa, Babu shi babu dalilinsa. amma akwai alamun ya dawo yayi wanka
sannan ga 'karamar wayarsa nan a saman drowar.
Kai tsaye gurinsu Uwale ta nufa domin tana da tabbacin yana can.
Abunda taci karo dashi ya kusa tarwatsa mata zuciya, amma sai ta jajurce! tayi kokarin danne
mugun kishin da yake taso mata.. tayi musu sallama.
Su biyu ne a falon, Uwale na daki domin gabatar da sallar magariba, shima dawowarsa kenan
daga massalancin, ya samu Hamra'un ta shirya masa lafiyayyan towon farar shinkafa da miyar
kubewa d'anya wacce taji bushashshen kifi da man shanu!
Ya dinga shi mata albarka domin yini cur bai ci abinci ba, tun breakfast din safe, b'acin ran da
ya fita dashi ya ha nashi cin wani abu.
Tana zaune durshan a gabansa bayan ta zuba masa abincin yana ci tana bashi labarai sai
dariya yake sai kace mata da miji.
A zabure! ta kalli bakin kofar! suka had'a ido, bahaushe yace (Mara gaskiya ko a ruwa gumi
yake) duk sai ta daburce! tayi gaggawar matsawa daga kusa dashi, shi kam ko gezau!
abincinsa kawai yake ci amma ya amsa sallamar bai dai kalleta ba.
Ta zauna kujarar dake kallonsa da fadin.'' Ranka ya dade ashe ka dawo."?
Ya dago kansa yana kallonta da mamakin sunansa da ta kira shi, sam bai mayi tunanin za tayi
masa magana ba, saboda ya san azabar kishinta.
Da yake Namijin duniya ne babu kunya yace." Eh na dawo kina raina yanzu nake maganarki a
zuciyata."
Taji kamar ta fada masa bakar magana! amma sai tayi shuru kawai tana masa wani irin kallo na
tuhuma!
Saurin sunkuyar da kansa yayi! duk dadin towon a bakinsa yaji ya fice masa daga rai!
Hamra'u kam! simi-simi ta kama hanyar d'akinta! tana ta wani kumbura fuska shigowar Gimbiyar
ya 'bata mata rai mutu'ka! domin ta katse mata jin dad'inta.
Ya kalleta da fadin." Ya zaki tafi baku gaisa ba.
Ya'ke tayi ta juya da fadin." Aunty Gimbiya ina wuni."?
Tace." Lafiya lou ina Uwale."? Kafin ma ta bata amsa Uwalen ta fito da carbi a hannunta, ganin
Gimbiyar yasa ta washe bakinta, sosai tayi farin cikin ganinta a zaune babban burin ta ace
Gimbiyar ta saki jikinta dasu.
Hamra'u kasa tsayuwa tayi a gurin da sauri ta shige dakinta, ranta idan yayi dubu ya ba'ci, ita
dai tana kishin yanda Uwale ke nuna kauna da kulawa akan Gimbiyar.
Cikin mutuncin da girmamawa suka gaisa da juna.
Ta kalleta da fadin." Ya jikin naki jiya Ai yake fada min kin 'kone a hannu har nake cewa zan
shiga na dubaki Allah bai bani iko ba."
Tace." Ai ba sosai na k'one ba, kuma tunda yayi min addua gurin ya bushe ya daina ma zafi."
Tace." Duk da haka dai ai kin tsallake tsautsayi! kin ma yi kokari abunda ba ka saba a kansa ba,
ai dole ka sha wahala."
Murmushi tayi amma ba tace komai ba.
Da farin ciki a maganarta tace." Mijinki ya sheda miki gobe za muje 'kauye ko "?
Fuska a sake ta amsa " Eh ya fad'a min Allah ya nuna mana goben lafiya."
Tace." Ameen ai yana da kyau kema ki saba da dangi shiyasa da yace shi ba zai kwana ba,
nace to ya zama dole ke ya barki tare damu domin 'yan uwa su sheda fuskarki ai riga an zama
d'aya."
Tace." Hakan yayi insha babu matsala ta b'angare na, ina tare daku."
Kallonta yayi yana mamakin furuncinta.
D'auke kanta tayi dan tunda suke maganarsu bata kalleshi ba saboda masifar haushinsa da
take ji.
Uwale sarkin hira da labarai na ban dariya ta dinga bata labarai irin na da! ta dinga dariya tana
mamakin kokari irin na mutan da! ace Mace ta haihu amma unguwar zoma ta fita yawan nama!
ita abun ma dariya ya dinga bata.
Ganin kamar sun manta dashi a gurin yasa ya tashi domin zuwa ya kwanta a gajiya yake tilis!
Ta kalleshi da fadin." Ya zaka tashi kuma."?
Yace." Eh mana to zaman me zanyi kun manta dani kuna hira bakwa sani a ciki zanje na
kwanta ne."
Dariya tayi irin ta tsaffi! kafin tace." To ai gwara ka kwanta ko ka tashi da wuri nima nafiso muyi
sammako."
Yana kokarin fita yace." Uwale ai ke yau bana tsammanin zaki iya bacci ."
Ta fashe da dariya da fadin." Me zai hana zanyi wanda ya sawwa'ka dai ai dole nayi zumudi
UMARU wata da watanni ba tare da 'yan uwa ba." Da al'ajabi ta k'arasa maganar.
Girgiza kansa kawai yayi kafin yace.'' Sai da safe kenan ya kalleta bata da niyyar tashi su
tafi......."A nan zaki kwana ne."?
Ya jefa mata tambayar hannunsa na rike da handle domin bude kofar.
A nutse ta mik'e ta kalli Uwalen da fadin." Sai Allah ya kaimu." Ta amsa da "To Allah ya tashe
mu lafiya Alla ya bamu alkairi."
Kusan a tare suka amsa kafin ya bude kofar ya fita ta bi bayansa.
Kowa sashensa ya nufa, bata tsammanin bin sa domin yanda zuciyarta take a tunzure! bata
tsammanin
zasu wanye lafiya. munufiki ne har yanzu akwai abunda yake 'boye mata.
Wanka tayi ta sanya kayan bacci tayi kwanciyarta tana tunanin irin hukuncin da za tayi masa
cikin ruwan sanyi, abu d'aya za tai masa ya shiga damuwa! shine ta hana shi kanta wannan
shine babban tashin hankalinsa, tabbas zai kawo kansa anan za ta fanshe in yaso yaje gurin
yarinyar ta bashi kanta, tunda yana zuwa yaci abincinta a boye.
Washe gari da wuri ta gama shirinta sosai ta had'a musu tsaraba cikin baggo, sai da ta shirya
tsaf sannan ta zauna domin karyawa.
Lokacin ya shigao cikin farar shadda kar! wando da riga iya gwiwa da wani irin tsadaddan aiki
a wuyan rigar da hannu. yayi kyau sosai rashin sanya hula shine yai masa cikas, da alama
bashi da ra'ayi ta sosai.
Ta kalleshi ta 'kara kallo, yana da kyau sosai sai yanzu take tantancewa dole mata su rikice a
kansa, itama tana masifar sonsa saboda yana da baiwar da ba kowane namiji ne ke dashi ba.
Abinda take rayawa a kansa shima irinsa ne a zuciyarsa, duk kwanan duniya 'kara sonta da
kaunarta yake a zuciyarsa.
Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta gaishe shi a sanyaye.
Babu yabo babu fallasa ya amsa yana gyara agogon sarkar dake hannunsa, yace." Har kin
shirya kenan."?
Shuru tai masa bata ce komai ba. ta cigaba da kurbar tea din dake gabanta.
Saboda neman magana sai ya kai hannu yana so ya dauke cup din.
Ta kalleshi da fadin." Ya haka kuma."?
Yace." So nake na sha."
Murmushi kawai tayi ta sakar masa cup din.....ya dauka ya kai bakinsa dai-dai bakinta ya
shanye tas!
Ta yunk'ura ta tashi daga gurin.
Ya bi bayanta da kallo a lokacin da take kokarin shiga dakin, yawu ya had'iye ya lumshe idonsa!
bayanta kad'ai ya isa ya gigita duk wani namiji lafiyayya dama mara lafiya.
Bayanta yabi jikinsa duk yayi la'asar! ya same ta tana kokarin nad'a lifaya a jikinta.
Yaje gurin da fadin." Bakya jin zafi zaki nad'a wannan bayan kayan dake jikinki." Yana maganar
yana ha nata abunda take.
Ta kalleshi da fadin." Zafi kuma."?
Kansa ya daga da fadin."Eh ana zafi a gari ko bakya jinsa ne."?
Ta san neman magana yake da ita kawai sai ta cire lifayar ta ajiye, hijab ta d'auko amma bece
komai ba. sai abun ya bata mamaki ganinta kamar a yanzu zai magana tunda a zahiri kamar
hijab din zai fi lifayar zafi, amma bece komai ba sai aukin kallonta yake gabadaya kwayar
idonsa ta sauya! ganin haka yasa da sauri ta kama hanyar fita tare da fadin." Wannan jakar
baggo din ka fito da ita kaya ne a ciki."
Da hannu ta nuna masa, yabi gurin da kallo kafin ma yayi magana ta fita daga dakin. Zazzafar
ajiyar zuciya sauke kafin yasa hannu ya dauki bakkon ya bi bayan ta da tunanin wani abu a
ransa.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukan
ki ya kare_
*GJSR*
*101&102*
Itace a kusa dashi, Uwale da Hamra'u kuma a baya a tsakaninsu suke hirar da ta shafe su, ita
dai tayi shuru tana dai jinsu, gabadaya tunaninta ya ta'allaka ne gurin ganin yanda za ta koyi
mu'amula da 'yan uwansa, a jikinta takejin kamar akwai abunda zai faru sakamakon zuwanta
garin.
Shi tunaninsa yasha bam-bam da wanda takeyi, domin shi kadai ya san halin damuwar da yake
ciki a halin yanzu sha'awa ce tafi damunsa, gashi yayi wa Uwale alkawari yana ganin da kamar
wuya alkawarin nan ya tabbata domin tare da matarsa zai tafi, saboda samun saukin abinda ke
damunsa.
Daga karshe dai shuru yayi musu ya daina sanya musu baki a hirar sai ya kasance su biyu
kadai suke magana a motar yanayinsu ya nuna d'okin kasancewa da 'yan uwansu.
Daf da za su shiga garin ya kalleta, yaga duk tayi wani iri sai ya mutse fuska take, da alama
akwai abunda ke damunta ta dai yi shuru ne kawai.
Sassauta murya yayi da fadin." Menene."?
Kallonshi tayi da gajiyayyun idanuwanta tace." Zuciyata ce take tashi!.
Yace." Saboda me."? shuru tai masa tana ganin ko ta fada masa dalili bai zama lallai ya yarda
ba."
Yace." Ba zaki magana ba."?
Ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi kafin tace." mybe tafiyar mota ne." Ta dan ja tsaki mtssw!
kafin ta cigaba da cewa ."idan ba yau ba din ba, bana tsammanin na ta'ba dogowar tafiya a
mota irin wannan."
Yayi shuru yana nazarin maganarta, kwarai hakan na iya faruwa idan anyi la'akari da irin gidan
da ta fito mostly masu kud'in nan ba sa jurar tafiyar mota 'karamar tafiya sai hau mata jirgi.
Yace."Sannu ai mun shigo garin da ikon Allah."
Ba tace masa komai ba kawai ta jingina kanta jikin kujera tana sauke numfashi sannu a hankali.
Uwale ce ta iya tofa albarkacin bakinta a kan maganar amma Hamra'u ta tafas! ba tace ba, sai
wani dauke kai take tana kumbura fuska.
Tunda suka shiga garin motar ta fara gargada tana ciccijewa sakamakon kwazazzabai da
ramuka! bayan wannan yara da almajirai suka dinga bin motar da gudu suna ihu!!!!!!!
Al'amarin ya daure mata kai mutu'ka! ashe lalacewar 'kauyen har ta kai haka? ko'ina ginin jar
kasa da wasu dirka-dirka bishiyon kuka da tsamiya had'e da mangaro gasu nan dai iri-iri! garin
cike da dabbobi barkatai yaransu da manyansu cikin 'kazanta abun dai sai godiyar Allah.
Uwale sai wangale Baki take tana d'agawa yaran dake bin motar hannu, a tunaninta suna
ganinta motar tintac ce ita take ganinsu amma su basa ganin na ciki, su dai farin cikinsu mota ta
shigo garin.
Can wani fili mai yalwa ya nufa domin gyara parking.....Lokacin gungun! yaransa suka durfafo
gurin suna bushe-bushe karnukan dake biye dasu na haushi gurin ya kacame! 'kura sai tashi
take!
Hankalinta ya tashi ganin haukan da yaran nasa suke! saboda haka yana gyara parking din ta
kalleshi lokacin jikinsa har ya fara tsuma! gumi na karyo masa! tace." Dan Allah kada ka biye
musu ina nufin kada kayi wannnan abun da kake bana so."
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya ciro hankici daga jikinsa gumin fuskarsa ya goge kafin ya
juya gurinsu Uwale lokacin tana ta kici-kicin bude kofar motar.
Ya mika hannu ya bude musu kofar suka fita........Karnukan suna hangoshi a motar sai suka
sake rikicewa! da haushi kokari suke iske in da yake, ta rintse idonta da karfi tace." Kada bari su
shigo ka rufe motar.
Gaggawar rufewa yayi yana kallonta jikinta sai karkarwa yake, 'kwalla ta cika kwarmin idonta,
yana daya daga cikin dalilan da yasa bata kaunar zuwa k'auyen! ta tsani ta bude ido tayi tozali
da k'azaman karnukan da idanuwansu ke cike da kwantsa.
Yace."Wai meye hakane? ki saki jikinki kina tare dani babu abunda za suyi miki."
Ta kalleshi hawayen bakin ciki na zuba tace." Ba zan fita a motar nan ba sai ka sallami wa'innan
'kazaman dasu da karnukansu bana san ganinsu.
Yaji haushin maganarta amma sai ya basar! kawai ya bud'e 'kofar ya fita.....aikuwa karnukan ne
suka dinga tsalle suna rungumeshi! akwai sabo mai tsanani a tsakaninsu. takaici da bakin ciki
ya ishe ta, kullum yana kiran kansa musulumi amma yana tu'ammali da karnuka wanda kowa ya
san hakan haramun ne a musulunci.
Alba ya kwance masa bakin wani kuttu dake cike da tsumi!!! sai kumfa yake!! ya kafa kansa ya
dinga kwankwad'a!! yana wata irin girgiza!
Gurin cika yayi manya da yara duk sun kewayeshi alamu dai sun nuna jama'ar garin suna
alfahari dashi.
Duk bada'kalar da take faruwa tana kallo, duk rokon da tayi masa hakan bai sa ya fasa abinda
yayi niyya ba, kafaffar wu'ka gayawa jini na wuce! ya kar'ba a hannun Alba tana walwali ya
fara dadurawa! a wuyansa! anci sa'a wannan karan bai cire rigarsa ba. ya kai minti goma
yana gurzawa wu'kar! kafin ya kurma! uban ihun! da ya sanya gurin amsawa! ya fara kai kawo
a gurin yana dukan kirjinsa!
Takaici yasa kawai ta sunkuyar da kanta 'kasa bata tsammanin zata iya cigaba da kallonsa yana
wannan halin.
Farar shaddar jikinsa ta rine! tayi jajawur! ta jike da gumiin jikinsa! hatta! da gashin kansa digar
da gumi! yake!
Kawu Ado ne yayi namijin tunkarar gurin da yake! yana kokarin rike hannunsa yana fizgewa! jin
karfi kawai yake yana wani tattaune bakinsa, su kuma yaran sai kara kambaba darajarsa suke
suna 'kara tayar masa da tsumin da yake jikinsa.
Maigari da jama'arsa suka 'karaso gurin domin suna zaune a fada labari ya samesu cewa
*GOJE!* ya shigo garin.
Maigarin ya samu nasarar isa gurin da yake......Kawu Ado ya rufa masa baya. dukkaninsu
*mubaya* (goyon baya) sukayi kafin ya sadadu! Maigari da Kawu Ado hannu na dukan hannu
í ½í²ªí ¼í¿»suke masa kirari! *Cau!! Sa'a dai!! Mai maganin wuka da kaho."!!* ire-iren wannan kirarin
suka dinga yi masa kafin su samu kansa! jagab! ji'ke da gumi suka