Showing 42001 words to 45000 words out of 46235 words

Chapter 15 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale


shirya tafiya domin hakan ma nasara ce, ace zuwansu garin ya tsorata masu laifin sun gudu
saboda rashin yarda da kai.

Ashe lamfo sukayi. a daran ranar suka saka musu bom! gurin da suke ya kama da
wuta!.........Mutum shida suka kone kurmus! wasu suka jikkata! tashin hankali kenan! wannan
al'amarin ya dunguzuma shi! shima bom din wurgi yayi dashi can wata nahiya.
Cikin mawuyacin hali yake lalube da hannunsa so yake ya tashi zaune amma inaa! jikinsa yayi
nauyi wasu guraran duk sun 'kone! ya kira sunanan Allah da k'arfin gaske! kafin yayi kalmar
shahada! ya zabura! ya mike tsaye! yana wani irin ihu!!! da gurnani!!

Abinda ya tsorata su kenan dama sunyi lamfo a ma'boyarsu! duk sai suka gigice! suka fara
fitowa wasu na gudu wasu kuma na harbinsa da bindiga.

Basu samu nasarar samunsa ba, saboda yafiso da dabaru!!

Shi din dai Allah ya bawa nasara ya harbe kafafun mutum biyar sukayi kwance a gurin suna jan
jiki da ihu!!

Sauran suka ranta a na kare! duk da haka bai fasa sakar musu bullet ba, sai da ya sake samun
mutum biyu suka zube a gurin.


Hayaki! da zafin wuta ne kawai yake tashi a gurin.

Jini da sassan jikin dan Adam dole ya firgita wanda bai saba gani ba.


Ya dinga bin 'yan uwansa yana dubawa wasu da rai wasu babu wasu sunyi daga-daga! naman
jikinsu ya tarwatse!


Kuka ya dinga yi da hawaye yana kiran sunan Allah! a fili. wannan wane irin tashin hankali ne!


Wannan al'amarin da ya faru ya tashi hankali kowa ba mazauna garin ba kawai duk wani mai
kishin musulunci da kishin 'kasa dole ya jajantawa kansa zubar jini a Najeria ya zama kamar

zubar ruwan famfo.

A galabaice aka nufi asibiti dashi da sauran wa'inda suke raye.

'Yan jarida mane ma labarai basu samu cikakken bayanin da suke bukata ba, dalili shi wanda
zai musu bayanin baya hayyacinsa, sai dai sun d'auki rahoton gurin da abin ya faru, kuma sun
samu nasarar daukar hotonsa a lokacin da ake kokarin sanyashi a cikin motar asibiti, sannan
suka kutsa suka dauki hotonan masu laifin da aka samu nasara a kansu.
To kafin kice kwabo labari ya cika 'kasa baki d'aya
*GOJE!* wannan mafaraucin mutumin da ya kasance Jami'in tsaron dake garin katsina ya
samu nasara akan 'yan ta'addan da suka addabi garin Zamfara! sai dai yana da muhimmanci
mutanan Zamfara da 'kasa gabadaya su dage da addua akan Allah ya tashi kad'arsa! saboda
yana cikin tsaka mai wuya dashi da abokanan tafiyarsa dalilin tashin bom da 'yan ta'addan
sukayi ya k'ona wasu daga cikinsu kuma sun rigamu gidan gaskiya, yanzu haka dai *UMARU
wanda kuka fi Sani GOJE!* Yana kwance a babban asibitin garin Zamfara domin ceto
rayuwarsa."
wannan rahotanin da ke yawo gidajen television redio tare da wayoyin mutane .


Tashin hankalin da Asp ya shiga yafi gaban a kwantatashi! kaf headquarter 'yan sandan suna
cikin tsananin tashin hankali da damuwa sakamakon abinda ya faru da ma'aikatansu
mussaman shi Umar din da suke alfahari dashi........mutum daya ne zuciyarsa babu alkairi
domin shi bai so al'amarin ya tsaya a haka ba, amma a zahiri ya jajanta kuma shine ya
jagorancesu tafiyar zuwa can garin domin duba marasa lafiyan.


Idan kuka ga yanda hankalin iyalinsa ya tashi sai kun tausaya musu. Zinatu tsayuwa ta
gagareta! kafafunta sai karkarwa suke! tun lokacin da taga mijin nata a tv an nuna shi kan
wani gado irin na asibiti kamar matacce hankalinta ya tashi, kuka ta fashe dashi tana kiran
innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!! shikkenan mun zama marayu!
Kuka gabadaya gidan aka rasa mai rarrashin wani dan Uwale ma kasa daurewa tayi abunka da
mutan k'auye sai sambatu takeyi tana share hawaye.


Zinat kasa zaman gidan tayi tasa hijab ta fice. kai tsaye gidan Asp ta nufa.

Lokacin bai jima da dawowa ba wanka ya shiga domin shiryawa tafiya.

Kukan da yaji a falon ne yasa cikin gaggawa ya fito.

Ya sameta sai rusa kuka take Madam ta rungumeta tana rarrashi itama Nabila dake zaune a

gefe hawaye take sharewa.

Ya sassauta murya da fadin." Kuyi hakuri addua za kuyi musu Allah ya basu lafiya.

Jage-jage da hawaye a fuskarta take kallonsa da k'yar ta iya cewa." Ranka ya dade kuna 'boye
mana wani abu amma a jikina nake ji mijina ya mutu."


Ya girgiza kai da fadin" Zinat da mijinki ya mutu da yanzu gawarsa ta iso gida yana nan a raye
amma ba zan boye miki ba yana bukatar adduarki."


Tana shashshekar kuka tace." Don Allah kayi hakuri ka tafi dani gurinsa inaso na ganshi mu
yafewa junanmu."


Tausayinta ya rufeshi yace." Insha Allah zai dawo gida da rai da lafiya ku cigaba da rayuwa. kiyi
hakuri tafiya dake ba zai yuwu ba tunda bani kadai bane amma insha Allahu idan mun isa zan
kira ki a waya ki dubashi.

A sanyaye tace." Rayuwata ta kare idan na rasa mijina ina sonshi bana so ya mutu barni amma
mutuwa dole ce."!!


Wasu hawaye masu zafi suka zubo a fuskar Madam dauriyarta ta k'are sakamakon tausayin
yarinyar.


Shima zuciyarsa ce ta karye kawai sai yayi gaggawar shigewa daki yana kiran sunan Allah a
zuciyarsa, a gurguje ya shirya ya fita ta can kofar waje domin baya so yazo fita tausayin
yarinyar ya sashi zubar da hawaye.


Isar su keda wuya Allah ya kar'bi rayuwar mutum biyu daga cikin wa'inda suke kwance! Asp
dai kasa hakuri yayi ya fara share hawaye ganin tashin hankali da masifa mutuwa dole ce
amma irin wannan akwai tausayi da tayar da hankali.
Gawarwakin aka had'a guri guda kafin asa a motar da zata kaisu gida.

A daran suka juya amma banda Asp domin cewa yayi ba zai tafi ba tukkuna sai yaga abinda
hali yayi, gabadaya ya cire tsammani da samuwar abokin nasa.


Commissioner bai ce masa komai ba kawai ya rabu dashi amma akwai abinda ya kud'ire a

ransa!


Da asubah bayan ya idar da sallah yaje ya zauna kusa dashi yana kallonshi cikin zuciyarsa
yake masa adduar samun sassauci.

Likita ya shigo dakin, suka gaisa kafin ya k'arasa bakin gadon yana dubashi.

Ya kalli Asp din da fadin ." Insha Allah yau din za'ayi masa aikin wannan 'kunar dake
kafafuwansa za'a cire fatar gabad'aya a wanke gurin. kana a sanya magani."


Yace." Dr amma bayan wannan babu wata matsala ko ina nufin babu wani abu daya nakasa a
tare dashi.

Yace." Bana tsammanin hakan gaskiya tension ne yayi masa yawa da kuma fargaba amma
insha Allah zai tashi da tunaninsa wannan shine iyakar binkicen da mukayi a kansa.

Yace." To Alhamdullhi Allah ya bashi lafiya, su kuma wanda suka rasu Allah ya yafe musu ya
kuma kar'bi shahadarsu."

Likitan ya amsa da Ameen ya rabbi kafin ya gama duddubashi ya fita daga dakin.


Misalin tara da rabi Governor garin katsina tare da mu'karrabansa suka sauka a gidan
gomnatin garin.

Tare da governor Zamfara suka isa asibitin domin duba marasa lafiyan.

Lokacin ya tashi kuma cikin hayaccinsa kamar yanda Likitan ya fad'a! sai dai ya gaza furta
kalma daya sakamakon nazari da tunanin abunda ya faru.

Shi kansa Asp din gajiya yayi da magana yayi shuru da bakinsa farin cikinsa dai ya tashi cikin
nutsuwa babu buge-buge!


Shigar su keda wuya ya bisu da wani irin kallo yana girgiza kansa gabad'aya haushinsu yake ji
Malam me za'ayi da mulki bala'i ne ga wanda ya san hakan!


Asp ya mi'ke tsaye yana musu barka da zuwa.

Suka samu kujeru suka zauna hankalinsu gabadaya yana kansa alhini da damuwa ya bayyana

a fuskokinsu da alama dai ko a cikin shuwagabbanin suna da imani.

Kafin ma wani yayi magana a cikinsu shi ya mangantu....Asp yayi mamakin hakan mutu'ka!


"Rashin tsaro da rashin tsoron Allah da son duniya da mulki shine babbar asara! ga duk wani
shugaba."

Duk suba zuba masa ido jin maganar da yake.

Ya cigaba da cewa."
Lokacin da kake ya'kin neman za'be! idonka ya rufe ka tara talakawa kayi musu al'kawaririka
kan cewa idan sun mara maka baya zaka tallefesu zaka basu aikinyi za kuma ka taimaki k'asa
baki daya."


"Mulki ya zama abun rububi da kokawa! saboda samun jin dadin duniya, kayi rantsuwa da Allah
da al'kur'ani kan cewa zakayi adalci daga bisani idan bukatarka ta biya sai ka mance da komai
ka fara gina rayuwarka ka auri kyawawan mata ka ajiye a gida kaci mai kyau! kasha mai kyau!
ka kwanta a mai kyau! ka sanya suttura mai kyau! kayi facaka da kudi! ka nemi duk macen da
kake bukata ka tura yaranka kasashen waje suyi karatu, ka tara kudi a banki ka sayi gidaje
gonaki ka gina gidajen mai kayi duk wata bukatar rayuwarka ka manta da talakawa da
nauyinsu yake wuyanka wannan shine al'kawarin daka kayi wa Allah."?


D'akin yayi tsit! babu wanda yace uffan.

Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa........."Talauci yayi yawa a duniya saboda
zalincin shuwagabbani mai yasa matasa ba zasu shiga wani mummunan hali ba."?

"Sace-sace fyad'e harkokin Daba gami da sara suka sun zama ruwan dare shin menene ya
jawo hakan? idan akwai son zuciya irin na mutum to akwai sanya hannun gwamnati.

Akwai matasan da suke da degree takardunsu sunyi kyau amma ba'a daukesu aiki ba, an dauki
wanda yake takardar secondary aiki a halin yanzu sai kana da hanya zaka samu, mahukunta da
shuwagabbi basa bin doka kowa kansa ya sani yaya rayuwarsa za tayi kyau ya ingata
iyalinsa......Idan haka ake mulki Allah yayi mana tsakani dashi."

*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malam😊: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._





*122*
Governor Nuhu Bamalli ya sauke zazzafar ajiyar zuciya bayan kare maganganun Umar din
yace." Umaru ba zamu musanta maganarka ba, domin duk abinda ka fada gaskiya ne, mulki a
yanzu ya zama Innalillahi wa'ina wa'ina ilaihi raji'un! amma inaso ka sani cewa ba duka aka taru
a ka zama daya ba, da yawa akwai masu gaskiya ma'ana masu kwatantawa mulki irin na
Annabi Muhammad SAW da sahabansa, amma mafi akasari dai marasa tsoron Allah a ciki sunfi
yawa, sannan kuma bahaushe yace." Idan anbi ta barawo to abi ta mabi sawu! ina nufin ba
shuwagabbani kadai suke da laifi ba, har da jama'ar gari! rashin yiwa shugaba addua bai dace
ba, kana kuma zagin shugaba da cin mutuncinsa bai kyautu ba, Umaru wata masifar da kanmu
muke janyota idan Allah ya jarrabemu da masifa sai kuma mu dauki laifi mu dorawa
shuwagabbani. akwai masu aikata manyan laifukan da Allah ya haramta, Zina tayi yawa a
duniya uwa uba lud'u da madigo da suka zama gama gari wannan babban masifa ce zata iya
janyo mana fushin ubangiji. duk abinda muke aikatawa na rashin gaskiya Allah ya na kallonmu
kuma muna cin albarkacin Annabi Muhammad SAW ne da babu albarkasa da tuni Allah ya kifar
damu, saboda haka kayi hakuri dole ranka ya baci kuma duk sharhin da kayi mana babu
wanda ya bata mana rai, maganarka gaskiya ce, kasan da cewa muna alfahari dakai a Najeria
da zamu samu jarumai irinka to babu shakka Najeria zata gyaru za'a samu sauyin rayuwa fiye
da yanda muke tunani, kayi hakuri ka cigaba da bada gudumawarka mu bamu isa mu biyaka
ba, amma ka ajiye a ranka cewa zakaje lahira ka tarar da aikin alkairin da kayi, Allah ya
Ubangiji ya baka lafiya ya kuma kare ka a duk inda zaka shiga, muna rokon Ubangiji Allah ya
bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki d'aya."

Gabadaya suka amsa da Ameeen ya Allah."

To a takaice dai yini guda abinda ya kasance kenan.

Manya k'asa 'yan kasuwa da manyan 'yan siyasa masu sarauta suna sauka a garin domin
dubashi. Sarki Umaru mahaifin matarsa tare da 'yan uwanshi a washe garin ranar suka sauka a
garin. kai tsaye babban asibitin suka nufa domin dubashi.

Lokacin da suka isa asibitin yana bacci bayan an gamai masa aikin k'unar jikinsa Asp na kusa
dashi a zaune.

Maimartaba tare da mukarrabansa suka samu guri suka zauna cikin alhini da damuwa.

Ganin Takawaran nasa a kwance magashiyan jiki duk a 'kone ya tayar masa da hankali
mutu'ka! ya tausaya masa sosai kana yayi masa addua tare da fatan samun sauki da
ramgwame.

Har suka shirya tafiya bai tashi ba, Sarkin yace a kyaleshi kada a tashe shi tunda sun dubashi
a haka babu matsala.


Har bakin mota Asp ya rakasu yana godiya cikin girma da mutunta juna suka rabu.


Sarkin da kansa ya sanya Magaji ya kira masa Zinat a waya.

Koda suka gaisa sai ya shiga shaida mata abinda yake da akwai.

Kasa hakuri tayi hawayen da take dannewa suka subce tace." Ranka ya dade ya jikin nasa ina
fatan ya tashi kun gaisa da juna."?

Yace." Alhamdullhi yaji sauki ki kwantar da hankali ki kuma kiyi masa addua domin adduarki
tana da muhimmanci a tare dashi.

Tasa hannu ta share hawayen dake zuba tace." Bana iya bacci kullum addua nake masa Allah
ya tashi kafadarsa nace ina san zuwa domin na dubashi Asp ya hana."


Yace." Zinatu kada ki janyowa kanki wata matsalar, kinga kema ba cikakkiyar lafiya gareki ba.
ki barwa Allah al'amarin sannan kuma zuwanki bashi zai bashi lafiya ba, watakila akwai abinda
yake nufi da hakan dan haka ki samu nutsuwa ki kuma tsananta da yiwa mijinki addua."

A sanyaye tace." To insha Allahu Na gode a gaishe min dasu Mommy. " Yace." Za suji da kyau."

wayar ya kashe zuciyarsa cike da tausayin yarinyar.


Koda ya tashi daga baccin Asp yake sheda masa zuwa surukin nasa sai duk yaji rashin dadi.

Yace." Me yasa baka tasheni ba naso mu gaisa na nemi afuwar abubuwan da suka faru.

Yace." Shi da kansa ya hana a tasheka sosai ya dubaka ya kuma jajanta al'amarin, dattijon yayi
adduo'i masu muhimmanci a garemu baki daya."


Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ranka ya dade wallahi har kunyar na hada ido nake dakai
saboda irin abubuwa marasa kyau da suka faru tsakanina da kai wallahi duk abunda ya faru
bana hayyacina don Allah kayi hakuri ka gafarceni."


Murmushi yayi da fadin." Umaru abubuwan da suka faru tsakanina da kai ban daukesu wata
tsiya ba, domin dana k'ullace ka da ba zanzo inda kake har na kula da kai ba, ni kaina sai da
na zargin hakan saboda nafi kowa sanin halinka, wasu abubuwan da aikata akwai alamun
tambaya a ciki to amma Alhamdullhi tunda ka gane gaskiya kuma dawo nutsuwarka wannan
shine farin cikinmu."


Yace." Na gode abokina Allah ya bar abota domin Allah, amma ina zargin wani abu dangane da
al'amarin sai dai na kasa yarda da hakan."

Yace." Me kake tunani."?

Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace." Idan ban manta ba kwanakin da suka wuce da kaina na
sheda maka cewa wata shida na tsayar domin daurin aurena da Hamra'u."


Yace." Eh kwarai kuwa hakane amma nayi mamakin yanda akayi ka sauya shawara akayi abun
cikin gaggawa."


Murmushin takaici yayi kafin yace."Iyayen yarinyar basu da kirki sun jefe ni sun juyar min da
hankali domin biyan bukatarsu na rasa abinda suke nufi da hakan, ko da ba suyi surkulle a
kaina ba ni na amince cewar zan auri 'yarsu to wane irin rashin Imani ne zasu juyar min da
tunanina su mayar dani kamar zautacce."

Yace ." Gaskiya basu kyauta ba wallahi ban san me yasa wasu mutanan suka yarda da asiri ba,

to meye amfanin hakan da sukayi tunda gashi tun ba'aje ko'ina ba aikin da sukayi ya lalace."


Ya girgiza kai da fadin." Cikin mafarki da taimakon wani bawan Allah naje na lalata aikin.

Ya dinga kallonsa yana mamakin maganarsa......Murmushi yayi ya bagarar da maganar ta
hanyar fadin .'' Tunda na warware sosai sai ka kira min matata mu gaisa ko hankalinta ya
kwanta."


Yace." Kasan kuwa ta dameni kullum sai ta kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login