Showing 30001 words to 33000 words out of 46235 words

Chapter 11 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale

MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*111&112*
A kwance ya sameta bacci na shirin d'aukarta, ya zauna kusa da ita da fadin." Ki tashi ga
abinci na san akwai yunwa a tare dake."

Ta d'an muskuta da niyyar gyara kwanciyarta a ta'kaice tace." Bana jin yunwa."

Yayi kasa'ke yana kallonta kafin yace." Ban yarda ba kwayar idonki ta tabbatar min da cewa
akwai abinda ke damunki ko bayan haka ma ai ba ke kadai ce kike rayuwa ba, akwai wanda
yake bukatar kici abinci shima ya samu rabonsa.

Shuru kawai tayi masa ba ta da niyyar tashi ballanatana taci abincin.

Ya 'bata ransa da fadin." Na lura kina so mu sanya kafar wando guda, me yasa ki ke min haka
ne? ko dan kin ga na damu dake."

Uffan ba tace masa ba, asali ma idonta yana rufe sama-sama take jin sa.


Cikin zafin zuciya ya janye bargon dake rufe a jikinta murya a sama ya kira sunanta "Zinatu."

Ta bude ido tana kallonsa fuskarta babu fara'a ko kadan.

Yace." Na gaji da wasa da hankalin da kike min ki fito fili kiyi min bayanin dalilin da yasa kike
wannan abun ai ba haka muka rabu ba da juna ba.


Zaune ta mike tana kallonsa duk ya wani firgice! har gumi yake kamar babu Ac a dakin.

Zum'bura baki tayi ba tace komai ba ta fara kokarin komawa ta kwanta, da sauri ya rike
kafadarta ya hana ta kwanciyar in ban da rawa babu abunda jikinsa keyi, da alama baya son
b'acin ranta.


"Kina so ki jefa ni cikin damuwa ko? shin ko dai wani abu 'yan uwana sukayi miki wanda kike
hukuntani dashi."

Ta kalleshi tare da girgiza kanta kafin tace." Ko daya ni 'yan uwanka ba suyi min komai ba sai
alkairi saboda haka ba wannan ce matsala ta ba."

Da sauri yace." Menene matsalarki ki fada min zanyi miki magani."

Cikin ranta ta ayyana wani abu, ta kalleshi ba tare da ta auna maganar ba tace." Ka janye
maganar auran Hamra'u."


Ya tsira mata idanuwansa da suke a rikice! alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dashi,
yace." Wacece Hamra'u."?

Kallon mamaki take masa "Wacece Hamra'u."? wai tambayarta yake saboda ya raina mata
hankali.

Ganin tana masa kallon zargi yasa ya daburce kafin yace." Waye ya fad'a miki zan aure ta da
har kike wannan maganar."?


Tsaki taja kafin tace." Ba ka da gaskiya wallahi kuma ban san cewa kai munafiki bane sai yau
wato har ni kake tambaya wacece Hamra'u? yarinyar da kowa ya sanka da ita a gari shine zaka
raina min hankali.

Maganganunta sun 'bata masa rai mutuka! ya fusata! tare da nuna ta da hannu "Kin ga saurara
kada kiyi min rashin kunya ni kike kira da munafiki."?


Tace." Kana nad'e tabarmar kunya da hauka meye dan ka fada min dalilin zuwanka garin cewa
maganar auranka zaku tattauna har ka bada sadaki kun tsayar da magana to sai me don kayi

aure ko ka d'auka zan damu kaina a kan hakan namijin da ake so shi ake kishi a kansa."


Yaji wani mugun bakin ciki da jin kausasan kalamanta! ya dinga fesar da wani irin huci! yana
kallonta idonsa yayi jajawur! magana daya da tayi itace take sa hankakinsa ya tashi, (Namijin
da ake so shi ake kishi a kansa) wato wannan yana nuna masa cewar duk abinda zai yi yaje
yayi bata sonsa.

Ya tashi ya fita ya bar mata dakin domin zamansa zai iya haifar da kowace irin matsala mara
kyau.


Ba ta wani damu da yanayin da ya shiga ba, bacci tayi sosai babu wata damuwa a tare da ita,
ta riga ta san duk abinda yake raragefe ne da kame-kame.

Washe gari bai saurareta ba ya shirya ya fita da tarin bacin rai a tare dashi. Wanda har sai da
abokinsa ya fahimci cewa yana da damuwa domin kallo daya yayi masa ya sheda hakan, abota
ce ta gaskiya wannan dalilin yasa dukkaninsu suka fahimci junansu.

Ya kalleshi da fadin." UMARU kana da damuwa domin na ganta a cikin idanuwanka."


Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin." Zinatu ce damuwa ta Asp yarinyar nan idan ta
burkice na kan rasa gane kanta."

Asp din yace." Wani abu ne ya faru."?


Yace." Ta samu labarin tabbatuwar aurena da Hamra'u shikkenan take fushi jiya da k'yar na
rintsa wallahi."


Yace." Sai hakuri, amma dole ka fuskanci wannan matsalar, kai dai kawai kabi hanyoyi masu
kyau da zaka rarrasheta mussaman yanzu da take da juna biyu dole sai an bi komai sannu a
hankali."

Yace." Kana nufin nayi ta bin kanta ta nayi min yanda takeso, bana tsammanin yin hakan."

Yace." Aa ba haka nake nufi ba abinda nakeso ka fahinta shine kada ta dauki zafi kaima ka
dauka, ka kai zuciyarka nesa ka rarrasheta kada ka biye mata idan ka kwantar da kai ina mai
tabbatar maka da cewa fushin ba zai yi nisa ba."

Shuru kawai yayi yana nazarin maganar.......Wani sa'in shi kansa mamakin kansa yake idan
yana wani abu akan yarinyar ya rasa dalilin da ya sanya yake gudun bacin ranta, amma baya
so ya sakankance ta gane lagonshi ta raina shi. shi yasa wasu lokutan yake mata jan ido.


Da tarin yunwa da damuwa ya isa gidan. jiri da ciwon kai sun addaba masa! kai tsaye gurin
Uwale ya nufa ya samu abinci yaci ya kwanta yana hutawa.

Uwalen da kanta ta fuskanci bashi da lafiya....Tace." Ai ba kwanciya ya dace kayi ba asibiti za
kaje a dubaka shine abinda ya dace."


Idonsa a rufe yace." Kada ki damu ina so na huta tukkuna muna da likitoci na mussaman zan
kira daya daga ciki ya dubani."


Tace." To hakan shine dai-dai ai matar taka ma ai ta jima anan muna hira sai bayan la'asar ta
shiga gurinta.


Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Uwale me yasa kika shedawa yarinyar nan abunda yake
faruwa."?


Tace." Me yasa ba zan sheda mata ba Umaru ko kafiso mu tafi a haka ta samu labari a duniya
tayi mana kallon mutanan banza."


Yace." Ba nufina kenan ba, nafiso duk abinda zai faru a bari ta haihu tukkuna kinga tun bayan
dawowarmu babu kwanciyar hankali, na san kuma dalilin jin wannan maganar ne."


Tace." Umaru dole ne fa kayi hakuri da duk abunda zai biyo baya domin lusarin namiji baya
ta'ba iya zama da mace biyu uku ko hudu, ka zama jarumi jajurtacce! akan duk abinda zai faru,
bayan haka kuma ya zama dole ka jawa Hamra'u kunne ta kiyaye ta kuma sauya munanan
d'abi'un da take yi kishi ai ba hauka bane."

Ya kalleta da fadin." Me tayi Hamr'un."? Girgiza kanta tayi da fadin." Aa ni ba zan fada maka
komai ba, amma lallai ka ja mata kunne akan abubuwan da take aikatawa."


Ransa ya 'baci! idan ya fahimci maganar wato Hamra'u ta samu hanyar cin mutuncin matarsa

saboda tana da tabbacin cewa ta kusa zama dai-dai da ita, wannan shine tunanin da yake,
Hamra'u taki dawowa saboda akwai wani abu da tasan ta aikata na rashin kyautawa.
sosai yayi mamakin al'amarin beyi tsammanin cewa zai samu matsala da yarinyar ba, saboda
yana da tabbacin nutsuwa da hankalinta.


Sai wajejan goma da wani abu ya shiga gurinta, lokacin ma ita har taci abinci tayi shirin
kwanciya ba ta dai kwanta ba wayarta take dubawa.

Yayi sallama ya shiga dakin kamar mara laka a jikinsa.


Babu yabo babu fallasa ta amsa tana kallonsa har ya zauna kusa da ita.......Tace." Sannu ka
dawo lafiya."?

Wani sanyi ya sauka a zuciyarsa, sam bai tsammaci haka da gurinta ba.

Da kwarin gwiwa yace." Lafiya ya kika wuni ya babyna."?

Tayi shuru ba tace komai ba.

Ya sake matsawa jikinta yana nanik'arta. ba tace komai ba, amma gabadaya tsigar jikinta ta
tashi jinsa a kusa da ita yana nema ya haifar mata da matsala.


Ya sassauta murya da fadin." My love ki kalleni za muyi magana ta fahimta."

Ta jim na minti biyu kafin ta kalleshi. ya dinga sarrafa kwayoyin idonsa a kanta, gabadaya
jikinta ya mutu, dama abinda ya keso kenan.

Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya kafin ya lalubi hannunta ya rike cikin nashi, a hankali yace."
Hamra'u bake taci mutunci ba, ni taciwa mutunci kuma dole na nuna mata muhimmancinki kiyi
hakuri kinji ko."

Murmushin takaici tayi kafin tace." Waye yace maka Hamra'u taci mutunci na."?

Yace." Uwale ta sheda min abinda ya faru a tsakaninku kuma raina ya 'baci sosai wannan dalilin
yasa na yanke shawarar kiran wayarta a gabana ta baki hakuri."


Ta kalleshi tana so ta gazgata maganarsa, kamar gaske dai gashi nan yana mata dadin baki.

Ya fito da wayarsa ya nemi number Hamra'un.....cikin ikon Allah wayar ta shiga ba'a samu

matsalar network ba.

Bai wani saki fuska ba ya amsa gaisuwarta kafin ya dora da fadin." Hamra'u abinda ki kayi ban
ji dadi ba, kuma ba Gimbiya ki ka tozarta ba ni Umaru ki ka wulakanta sanin kanki ne cewa
mutanan garin *Kafur!* muna da karrama bako da mutuntashi me zai sanya ki wulakanta min
mata saboda kin ganta a mahaifarki."

Murya na rawa ta fara rantse-rantse da fadin." Ya saurara tayi masa bayani.....'Kin sauraranta
yayi yace." Mutukar kina so mu shirya da juna dole ki bata hakuri akan abinda ki kai mata
wannan ne kadai zai sanya na saurareki.

Sai kawai ta fashe da kuka da fadin." Wallahi ni ba zan bata hakuri ba, kuma duk wanda ya
fada maka cewa na tozarta ta Allah ya isa tsakanina dashi, ka tambayi Uwale itama idan zata
fad'i gaskiya ai a gabanta komai ya faru! sau biyu tana gaura min mari! a fuskata amma
saboda son zuciya za'a ce na bata hakuri! ni kam duk abunda za'ayi sai dai ayi ba zan bata
hakuri ba."


Yace." Ashe baki da mutunci dama."? Shuru gabanta sai bugawa yake! yace." Okey shikkenan
tunda haka ki ka za'ba zan baki mamaki." sai kawai ya kashe wayarsa yana jan tsaki!


Ta kalleshi da fadin." Nifa idan saboda ka faranta min rai kake wannan abun to ka daina, domin
hakan ba burge ni kayi ba...........koda yarinyar nan tayi min laifi na hukuntata tuntuni ka dai ja
mata kunne ta kiyaye! idan kuma taki za fuskanci b'acin rai."

Yace." Akan hakan zan iya janye auranta sai me."?

Tace." Duniya za tayi Alla wadai dakai! wane irin hallaci ne yarinyar ba tayi maka ba, ai samun
nutsuwarka ka aureta, ni bani da matsala domin ban san abinda Allah ya rufe a tsakaninku ba."

Yace." A da can baya ina sha'awar auranta saboda kyawawan halayenta amma yanzu duk ta
fice min rai saboda d'abi'un data sauya, bayan haka kuma mutukar ba zata zauna lafiya dake
ba, to kamar yanda na fada a farko zan iya janye auranta."

'Yar dariya tayi tare da girgiza kanta tace." To Allah ya rufa asiri ya tabbatar da alkairi ni dai duk
wanda ya nufe ni da sharri kansa zai koma."
daga wannan maganar ba ta sake cewa uffan ba, ta shige cikin bargo tana gyara lulluba, tashi
yayi ya fita, minti goma ya dawo dakin, ya kashe fitila kai tsaye gadon ya nufa ya kwanta kusa
da ita, kamar zai daure ya danne abinda ke cinsa, sai ya kasa ya matsa jikinta sosai yana
shanshana sassan jikinta, gabadaya ya rikice jikinsa sai rawa yake ya birkito ta rungumeta
yayi tsam a jikinsa yana kesses din fuskarta da wuyanta.

*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malam😊: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._


*113&114*
Da asubar fari 'Dayyiba ta fice daga gidanta da mummunan kudiri a zuciyarta. wani k'aramin
kauye ta yiwa tsinke anan take sanya ran biyan bukatar ta, to duk da sammakon da ta buga sai
da ta samu kusan mutum biyar suna zaune tsumayin fitowar wacce ta shiga zauran malamin.
Dayyiba ta kama layi ta zauna a kusa da wata mata hankalinta kaf yana kan hirar da suke da
abokiyar tafiyarta.

Magana suke tattaunawa akan abinda ya kawosu gurinsu bokan wacce tayi kamanceceniya da
wacce ta kawo ta, ta kalli matar da fadin." Nima abinda yake tafe dani kenan, ni abinda nakeso
ma a rabasu gabadaya ko kuma a haukatata ta shiga duniya."

Matar tace." Wannan duk mai sauki ne mutukar kin cika sharud'ai to bukatarki za ta biya."

Tace." A shirye nake bani da matsala duk abinda akace zanyi mutukar bukatata za ta biya."

Wannan shine 'karshen magana.......Fitowar matar dake ciki ya katse maganarsu, wacce take
kan layi tayi saurin shiga ita kuma wacce ta fito daga zauran ta tsaya tana musu sallama da
wani irin murmushi a fuskarta da alama akwai nasara a kan abunda tazo dashi gurin.

To d'aya bayan daya suke shiga har layi yazo kan Dayyiba ta shiga ta gurfana gabansa kafin
ma ta fara yi masa bayanin abinda yake tafe da ita yace." Kina tafe da aikin babban aljani
wanda yake da bukatar kafa hud'u ina fatan kin fahimta."

Gabanta yana faduwa tace." Malam har aikin nawa ya kai haka."?

Ya buga mata tsawa da fadin." Tashi ki fita ashe da sauran imani ta tare dake tunda kike
jayayya damu."

Tace." Ayi hakuri ranka ya dad'e ina neman alfarma na bada kafa biyu amma samuwar kafa
hud'u a gurina zai yi wuya."

Ya shiru yana kallon wani jan koko mai kurji-kurji cike da jini a ciki.

Ya kalleta da fadin." To dai gaki gashi nan yana kallonki sai kiyi masa bayani idan ya amince.

Gabanta na bugawa tace." Ubana idan zai yuwu zan bada rago mai koshin lafiya a taimaka
min."

Shuru gurin yayi bayan k'are maganarta, can kuma bokan ya kama wata girgiza farar kumfa na
fitowa daga bakinsa, ya kai minti goma haka kafin ya dawo hayyacinsa duk yayi wuri-wuri sai
uban gumi yake.

Ya kalleta da fadin.'' Kin ci sa'a yau yana cikin walwala ya kuma amince da maganarki, sauran
aikin kuma ya rage naki idan kika kuskure wani to aikin zai dawo kanki.

Cike da farin ciki tace." Na gode ranka ya dade zan kuma kiyaye da izinin ku."

Yace." Da daddare karfe biyu ki samu bakin kwatami (kazamar kwata) ki yanka ragon da
hannun hagu ki nayi kina zagin uwarki da ubanki."

Tace." To an gama ranka ya dade.......Ya siffan ta mata kalar ragon da ake bukata sannan ya
bata wata laya yace a gurin da ta zubda jinin zata binne.

Cike da farin ta dawo gida, kuma hankalinta bai kwanta ba sai da ta tabbatar ta samu kalar
ragon da aka bukata.

Karfe biyu na dare ta fito babu tsoro babu imani ta fara aiwatar da mummunan kudirinta tana
yanka ragon tana zagin uwarta da ubanta.........Ta gama ta haka rami da wukar hannunta ta
binne layar....kamar saukar aradu taji wata tsawa! "Tashi ki gusa daga gurin."! a gigice! ta
shige gida kafafunta na karkarwa.
Koda ta duba gurin da safe wayam! babu alamun anyi wani abu! hankalin ya kwanta ta koma
gida da tunanin abinda zai biyo baya.

A daran kwanan soyayya sukayi sai dai kuma gari yana waye wa suka tashi da bala'i da masifa!
kamar karnuka! ya nayi ta nayi a fusace! ta jefa masa kwalbar turare a goshinsa a take gurin ya
kumbura! shima ya fusata ya zazzabga mata maruka ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa
na wani tafasa! gabadaya hankalinsa yayi kan Hamra'u
Koda ya isa ofis din kasa samun nutsuwa yayi ya kasa aikata komai, kawai sai ya nufi ofis din
Asp yana sheda masa cewa zai tafi *'Kafur* 'Kauyensu.

Asp din yace." Allah yasa dai lafiya domin naga kamar baka hayyacinka.

Budar bakinsa yace." Daf yake da ya rabu da Zinatu saboda wasu dalilai.

Asp ya tsirawa goshinsa ido da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login