Showing 39001 words to 42000 words out of 46235 words
Chapter 14 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
da "Ameen kafin yayi musu sallama ya tafi muhallinsa.
Hamra'u tayi zaune a daki tana sakawa da kwancewa, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta
dauki wayarta number sa ta kira.
Sai da ta kira sau uku ana hud'un ya daga! kafin ma tayi magana ya buga mata tsawa! dama
zuciyar a kusa take ana fagen daga!!
Jikinta ya shiga rawa! sai ta manta ma abinda za ta fad'a
Yace." Wai shin ke ban ha naki kira na bane? da kaina nace ki bari idan na samu isheshshen
lokaci zan kira ki me yake damunki ne."?
Hawaye masu zafi suka cika kwarmin idonta! kamar ta kashe wayar sai dai ta daure murya na
rawa tace ." Dama zan fada maka cewa Zinatu t.........! jin ta ambaci sunan wacce ya tsana!
yasa da gaggawa ya kashe wayarsa ba zai saurari karshen maganar ba ballantana ransa ya
'baci!
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*119&120*
Kasa daurewa tayi ba'kin cikin abinda yayi mata yasa ta kasa fita falon, nan ta kwanta kan gado
kuka mai cin rai ya k'wace mata, ita kam har yanzu ta kasa fahimtar inda ya dosa kullum babu
kyakykyawar mu'amula a tsakaninsu, ba dama tayi masa magana sai ya kyareta! ko ya
hantareta! gabad'aya ta kasa shawo kansa a lokacin da ba suyi aure ba ma yafi kulawa da ita,
yanzu kuwa da ya cancanta ace ya kula da ita hakan bai samu ba, wannan al'amarin yana
bala'in damunta.
Haka ta zama mujiya a cikinsu, dan gabad'aya sai ta tsargi kanta ta dinga ja da baya tana wani
abu irin abu na marasa gaskiya, Uwale kam tunda ta fahimci cewa ita da uwarta basu da
gaskiya sai kawai itama ta shata mata layi, ta daina sakar mata fuska a yanzu babu
kyakykyawar mu'amula a tsakaninsu. Tafi mayar da hankalinta kan Zinatu saboda tana tausayawa halin da take ciki, tunda ta dawo
take fama yau da lafiya gobe babu sai ya kasance kusan kullum Uwalen tana can sashen nata
domin debe mata kewa duk da cewa tana tare dasu Baraka amma kasancewar Uwalen a tare
da ita ya faranta mata rai mutuka. sha'kuwa mai kyau ta shiga tsakaninsu.
'Bangaran Hamra'u kuwa abin duniya ya isheta, kullum sai ta zubar da hawayen takaici gidan
kaf sun hade mata kai sun mayar da ita saniyar ware babu wanda yake yi da ita, sai ta fara
rama a tsaitsaye saboda damuwar da ta sanya a ranta dole itama tabi ayari mutukar tana so
tayi rayuwar farin ciki a gidan.
Sai ta dingi shiga sashen Gimbiyar, al'amarin da ya basu mamaki mutuka! amma basu nuna
mata komai ba, tun bata sakewa dasu har dai ta saba ta daina dari-dari domin ganin ta sauya
hali ya sanya Uwalen sassauta mata, wannan ya sanya hankalinta ya kwanta a gidan, ita ta
cigaba da yi wa Zinat din d'awainiya har wankin undis wani sa'in ita take wanke mata ta tsafe
mata kitson kanta kana ta kitsa mata sabo, idan kafafunta sun dameta da ciwo itake matsa
mata.
Abun dai har ya soma damun Zinat din saboda bata so wasu daga waje suga abunda yake
faruwa su d'ora ayar tambaya a kanta shiyasa tayi wani tunani akan al'amarin.
Da fara'a ta shiga ta sameta kan doguwar kujera a kwance tace." Aunty Gimbiya jikin ne ko
garin ina fata dai babu abunda ke damunki."?
Ta ya mutse fuska da fadin." Kinga wallahi tun safe na tashi da ciwon mara asibiti nake so muje
yanzu."
Tace." Eh lallai zuwa asibitin yana da muhimmanci bari na shedawa Uwale."
Tana kokarin tashi tace." Okey bari na shirya kafin ki dawo." Daki ta nufa tana cire kafa da kyar!
ciki wata biyar kacal yayi girma sai suddubaru iri-iri!
Uwale tace." To ko na shirya muje tare."? kai ta girgiza da fadin." Ki zauna kawai yanzu zamu
dawo." Tace." Shikkenan amma yana da kyau kafin ku tafi ki shedawa mijinku koda ta waya ne."
Tace." Uwale bana so na kira shi yayi min fad'a ki bari kawai mu tafi."
Tace." Aa dole ki fada masa hakkinsa ne."
A sanyaye tace." Shikkenan.
Cikin tararrabi da jin tsoro ta kira shi, akaci sa'a ya dauka bai kuma yi mata fada ba, su gaisa a
mutunce ya tambayeta gida tace." Kowa lafiya lau."
Shuru tayi tana nazarin maganar dake bakinta. tuntuni tasan baya kaunar tayi masa maganar
matarsa amma ya zama dole ta sheda masa abinda yake faruwa.
Yace." Hamrau ko da matsala ne."?
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Dama za muje asibiti ne da Aunty Gimbiya bata jin dadin
jikinta."
Yaja wani dogon tsaki da fadin." Ba da yawu na ba, kada ki kuskura kije ko'ina."
Ta bude baki kenan za tayi magana ya kashe wayarsa! ta tsirawa wayar hannunta ido tana
mamakin irin k'iyayyar da yake nunawa matarsa kamar wacce ta kashe masa uwa da uba.
A sanyaye ta fito daga dakin ta shedawa Uwale yanda sukayi......Cikin bacin rai! tace." Kamo
min wayar tasa muyi magana."
Koda ta kira shi yana kallo har ta katse bai dauka ba, ta dinga kira tana katsewa, kwata-kwata
yaki dauka.
Tace." Wallahi yaki daga wayar na kira ya kai sau bakwai.
Murmushin takaici tayi tana girgiza kai! hakika Dayyiba bata kyauta ba ta shiga tsakanin
ma'aurata ta sanya musu kiyayyar junansu.
Sosai fa take jin jiki dan koda ta shiga dakin da niyyar sauya kaya kasa komai tayi ta sake
kwanciya tana kiran sunan Allah, cikinta ne yake mata wani irin ciwo ga wani uban gumi da
take shar'bawa!
Cikin wannan halin ta shiga ta sameta, bahaushe yace ciwon 'ya mace na 'ya mace ne!
Hamra'u hankalinta ya tashi ganin yanda take murkususu! duk kiyayyar da take mata sai ta
nemeta ta rasa hankalinta ya tashi ta rasa wane irin taimako za tayi mata.
A hankali tace." Na shigo dan na sauya kaya amma na kasa saboda yanda ciwon cikin nan ya
dameni."
A sanyaye tace." Sannu yanzu ya za'ayi? Uwale tace." Lallai sai na kira maigidan na sheda
masa abinda yake faruwa, to koda na kira shin sai yace kada muje ko'ina."
Ta kalleta tana jin wani irin 'bacin a can cikin ranta, rintse idonta tayi tana tunanin yanda za tayi,
ta bud'e idon tare da kallonta tace." Kyaleshi kawai miko min wayata gata can saman mirror."
Da sauri ta mika mata wayar. ta lalubi number Asp da kyar ta iya sheda masa halin da take ciki.
Hankali a tashe yace." Insha Allahu zan turo Likita zai zo ya dubaki yanzu ya baki magani ba sai
kunje ko'ina ba tunda muna tare da kwararrun likitoci a cikin gidan.
Tace." To shikkenan nagode Allah ya saka da alkairi."
Ya amsa da" Ameen ya Allah." kafin ya kashe wayar ya fara laluben number Likitan da yake da
tabbaci a kansa.
To cikin ikon Allah tana shan magungunan da likitan ya d'ora ta akai ta samu sassauci a take
wahalallan bacci ya dauketa, duk ta rame na lokaci guda.
Asp yana tashi daga aiki bai nufi ko'ina ba sai gidan abokin nasa hankalinsa gabad'aya yana
kan yarinyar, sai da yaje ya dubata sannan hankalinsa ya kwanta mussaman da ya sameta a
zaune ta warware tana cin abinci.
Ya dubata sosai ya kuma bata shawarwari masu amfani kafin yayi mata sallama ya nufi
muhallinsa.
A daran ranar ya samu labarin duk abunda yake faruwa.
Koda yake ba labari ya samu ba, hotonan Likitan da ya dubata da hoton Asp da shigarsa da
fitarsa duk aka tura masa ta WhatsApp bashi da tabbaci akan wanda ya turo masa sa'kon asali
ma bashi da number.
Hankalinsa ya tashi ainun! Asp ya zame masa kadangaran bakin tulu, baya gari amma yana
shigar masa gida ba tare da izininsa ba, garadan maza suna karakaina a cikin gidansa har
cikin dakin matarsa.
Kansa ya dinga yi masa wani irin ciwo! tunaninsa gabadaya ta tafi gurin ganin ya samu hanyar
da warware matsalarsa, yanzu zargin cikin da yake jikin yarinyar yake, Asp ya wuce gona da iri
babu abunda ba zai aikata ba.
Cikin rashin tunani da gushewar hankali da tsinkaye ya kira Asp din yana wani irin huci! ya fara
surfa masa rashin mutunci! Asp din ya fusata! da karfi ya buga tevur din dake gabansa ya
mike tsaye da wayar a kunnansa yana fadin." Umaru ni kake kira fasiki! anya kana da hankali
kuwa ko dai ka fara shaye-shaye ne."?
Shima a fusace! yace." Bana shan komai! hankali kuma bani dashi mutuk'ar akan na zuba maka
ido kana abunda kaga kake so, nifa ba bagidaje bane da zaka dinga raina min hankali. kullum
kana bibiyar matata a gindi-agindi dole nayi zarginka, kaje ka dawo da ita ba tare da izinina ba,
bana gari kana zurga-zurga a cikin gidana, akan me ba zanyi zarginka ba."
"Ya isa haka."!! Da karfi yayi maganar jikinsa na wani irin karkawa.
Ya cigaba da cewa." Wallahi ban ta'ba tunanin da'kiki! bane kai sai yau! dole kayi wannan
tunanin saboda jahilcin da yake damunka, ka jima kana mummunan furuci a kaina har kana
danganta ni da matarka ta sunnah. to bari kaji kwata-kwata kai baka dace da wannan yarinyar
ba, wallahi dana san haka halinka yake da ba zan shige maka gaba har ka samu nasarar
auranta ba, babu damuwa kayi kuskuran sakinta ni kuma zan baka mamaki."! Bai jirayi
amsarsa ba kawai ya kashe wayarsa.
Wayar ya tsirawa ido yana kallo hankalinsa a tashe! wannan shine a dake ka a kuma hana ka
kuka, Asp ya shiga huriminsa amma saboda tsabar rashin tsoron Allah yana nad'e tabarmar
kunya da hauka.
A daran kasa rintsawa yayi koda yake dama can ba wani baccin arziki suke ba, kullum suna
tsakanin border suna kai kawo amma dai wani lokacin idan baccin yazo yi suke ba tare da
saninsu ba, domin shi bacci daban yake a cikin abinda Allah ya hallata mara sa rai.
Yana kallon wasu daga cikin abokan tafiyarsa suna bingirewa bacci na kwasar su, bai hanasu
ba kwai ya kyalesu su sarara shima ya samu damar nazari da tunanin hanyar warware
matsalarsa......Sai dai a gurin tunanin baccin dai da yake gudu yazo ya sace shi ba tare da yayi
tsammani ba.
Cikin baccin yayi mafarki da wani dattijon mutum da fararan kaya a jikinsa kansa nade da farin
rawani farin gemunsa ya kusa ta'ba kasa akwai wani zabgegen carbi a hannunsa. suffar
mutumin dai gashinan ba mutum ba ba kuma aljan ba.
Sunansa ya kira." UMARU."
Ya amsa da "Na'am."
Yace." Ni ne abokinka ina tare da kai tun kana cikin uwarka nima sunana UMARU ni musulmi
ne ina kuma taimakon bil'adam mussaman musulmai. ban ta'ba bayyana a gare ka ba sai yau
duba da ganin yanda al'amuranka suka lalace! me yasa kake sakaci da addua? a can baya
baka da wasa amma yanzu ka bari har ma'kiya sunyi tasiri a kanka."
Shuru kawai yayi yana kallon Dattijon.
Yace." Rufe idonka.
Kallonsa yayi nan ya hango k'wayoyin idon dattijon sunyi kama dana *ZAKI!* Ya zabura! da
sauri ya rufe idonsa.
Kamar al'amara ya ganshi gurfane bakin kwatami (kwata mara kyau) yana hake kasar gurin.
yana fito da layar! a zabure! ya bude idonsa yana duba hannunsa yaga layar sai ya fara
dube-dube a gurin, babu dattijon babu dalilinsa.
Ya dinga kiran sunan Allah yana tu'ajibun Al'amarin shin waye wannan dattijon daya
ziyarceshi.?
Ya sake duba layar dake rintse a hannunsa tunanin a inda ya ciro ta yake.....Kofar gidan Malam
Shafi'i." Zuciyarsa take tuna masa.
Tabbas hakane shin me hakan yake nufi? surkulle akayi maka aka shiga tsakaninka da iyalinka.
wannan karon ma zuciyarsa ta sake tunasar masa.
Sai kawai abubuwan da suka wuce suka dinga dawo masa daki-daki! jikinsa ya jike sharkaf da
gumi tsabar fargaba da tashin hankali.
Haka ya wayi gari cikin rashin karsashi da kwarin jiki, duk abunda yake daurewa kawai yake ya
rasa ma tunanin da zai yi.
Ya kira wayar Asp din sau curin masaki amma yaki dauka domin ya dauki fushi! dashi mai
tsanani.
Ya kira Hamra'u da fadin.'' Lallai ta kai wa Zinatu wayar yana so yayi magana da ita, dalili ya
kira wayarta itama taki dauka.
Rasa abinda yake damunta tayi ba dan ranta yaso ba ta kai wa Zinat din wayar ta sheda mata
abunda yake da akwai.
Tace." Kinga Hamra'u fita dan Allah bana san b'acin rai! kinzo da rawar jikinki watakila ba alkairi
bane a kiran nasa, saboda haka kije kawai bana bukata.
Jikinta babu kwari ta fita da wayar a hannunta tana tunanin irin masifar da zai mata.
Aikuwa dai rufeta yayi da bala'i yana nema ya d'ora mata laifi! takaici yasa kawai ta fashe da
kuka ta kashe wayar ba tare da ta cigaba da sauraransa ba kwanciya tayi ta dinga kuka tana
tunanin ya rayuwarta zata kasance a gidan, dan taga kamar hankalinsa ya dawo kan matarsa
watakila ita za ta zame musu 'yar aiki, gashinan sai walagigi suke da rayuwarta shi ya kyareta!
ya hantare! ta ita kuma ta aike ta shin wannan wane irin aurene mara 'yanci.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*121*
Ya kira wayar Asp yafi a 'kirga amma bai saurareshi ba, kawai sai ya yanke shawarar rabuwa
dashi ya mayar da hankalinsa guri daya amma can kasan zuciyarsa akwai tarin fargaba da
tashin hankali a dan'kare! domin duk abubuwan da suka faru a baya yana tunaninsu yana kuma
nazarin ya akayi hakan ta kasance. babu shakka yanzu ya fara hangen gaskiya akan mafarkin
da yayi cewa da akwai sanya hannun iyayen Hamra'u gurin 'bacewar tunaninsa, idan ba haka
ba ya akayi al'amura suka sauya, da hankalinsa da tunaninsa ba zai manta lokacin da yanke
hukuncin wata shida kafin a daura musu aure ba, amma ya akayi al'amura suka sauya, babban
abinda yafi damunsa yanda suka samu matsala da amininsa ya rasa dalilin da ya janyo hakan,
burinsa ace Asp din ya d'aga wayarsa sun tattauna maganar, amma ga dukkan alamu yayi fushi
dashi irin wanda bai ta faruwa a tsakaninsu ba.
Damuwar da yake ciki ta sanya masa rashin karsashi! da 'kwarin jiki duk abinda yake 'kok'ari
kawai yake amma gabadaya hankalinsa yana gida gurin iyalinsa mussaman ita Zinat din da
take tare da lalura.
Wani irin tashin hankali ne ya faru a daran ranar da suka gama shirye-shiryen tafiya gida.
Abinda ya faru shine, tun bayan zuwansu garin. 'yan ta'addan da suka damu garin ta'addanci
suka sauya dubara! domin tuntuni suna da labarinsa da irin jazaba da baiwar da Allah yayi
masa, sai duk suka watse suka sauya ma'boya, amma suna da labarin duk abinda yake faruwa
a garin.
Iya bakin kokari da binkice sunyi a garin basu kama wani mai laifi ba. wannan dalilin yasa suka