Showing 21001 words to 24000 words out of 46235 words
Chapter 8 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
sai na sameta tana bacci, shine dalilin da yasa ban
tasheta ba.
Yana kokarin barin gurin yace." Yanzu zamu shirya tafiya insha Allah."
Kallo ta bishi da kallo tana mamakin maganarsa.
Rigar jikinsa ya cire ya zauna kusa da ita tare da kokarin cire mata rigar jikinta.
Ido ta bud'e cikin alamun bacci take kallonsa. sai ta fara kokarin tashi zaune.
Ya taimaka ta tashi burinsa kawai ya rabata da rigar saboda gumin da take.
Ha nashi tayi domin tsarguwa tayi ganinsa babu riga sai take tunanin wani abu zai yi mata.
Da ya fuskanci haka sai ya girgiza mata kai da fadin." Babu abunda zanyi miki ki cire rigar
saboda zafi.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara kokarin tashi........hanyar fita ta nufa ya bita da kallon
mamaki!
Bandaki ta shiga ta kama ruwa kafin ta fito ta daura alwala.
Uwale ta fito daga kicin hannuna rike da farantin silba da kwanukan abinci a jere, ta kalleta da
fadin." Kin tashi kenan."
Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba ta fara kokarin kar'bar kayan abincin.
Ta janye da fadin." A'a ki bar shi na k'arasa lada na mana."
Murmushi tayi tana kallonta, hakika matar nada kima da daraja a idonta.
Ta ajiye Tire din da fadin." Umaru ashe sai da ka tashi yarinyar nan .''
Yace." Uwale tashin shi yafi alkairi tayi sallah ta kuma ci abinci domin mu dauki hanya da wuri.
Tace." Tun dazu kake magana a 'boye me kake nufi ne."?
Yace." Uwale kiyi hakuri tare zan koma da ita."
Ta 'bata rai da fadin." Okey ta saka ka a d'aki ta nuna maka rashin yarda ta kenan."
Maganar tayi dai-dai da shigowarta dakin.
Itama Uwalen sai da ta fadi maganar sannan kuma tayi dakace.
Yace." Ko d'aya kawai nayi wani tunani ne, shiyasa na sanja shawara."
Ba tace komai ba ta kama hanya ta fita ranta a 'bace!
Tana idar da sallar ta kalleshi da fadin." Ka bari kawai zamu dawo tare dasu kayi tafiyarka.''
Yace." Saboda me? shin kin san damuwa da nake ciki kuwa."?
Tace." Kayi hakuri ka danne damuwarka duka kwana nawa za muyi zamu dawo."
Shuru kawai yayi mata a ransa sam beso hakan ba dan dai sun fi karfinsa ne.
Tare suka ci abincin sai jifanta yake da wani irin kallo na mussaman wanda ya kashe mata jiki
babu shakka akan ga'ba yake tana jin tsoron suyi abun kunya.
Aikuwa dai abunda yake shirin faruwa kenan, dan fafur! yaki tafiya lokacin yayi kwanciyarsa
sai bayan da ya biya bukatarsa tukkuna! kunyar duniya ta isheta, ba ta iya wanka a lokacin ba
sai da ta tabbatar cewa duhu yayi sannan ta tsarkake jikinta ta gabatar da magariba da
isha'i......Lokacin shi kuma ya gama shirin tafiya.
Zuciyarta ce ta karye ta kasa kallonsa sai kokarin mayar da hawaye take.
Koda ya fuskanci halin da take ciki sai ya rungumeta yana rarrashinta......Yanzu bashi da
damuwa tunda ya kawar da abunda ke damunsa.
Sosai ta b'oye damuwarta duk dan kada Uwalen ta fahimci wani abu ta saki jikinta sosai! suka
dinga hira a tsakaninsu. Har take tambayar Hamra'u, nan take sheda mata cewa ta tafi gidansu
a can zata kwana.
Allah sarki Uwale mace mai karamci da kanta ta gyara mata shimfida sabon zanin gado ta
shimfida akan gadon katifar audigar dake shimfide akan gadon karfenta irin na mutan da , ta
kunna mata turaran wata na tsinke! dakin ya dinga kamshi mai dadi, bata kwanta ba sai da tayi
wanka tukkuna ta sanya wata doguwar riga cotton mai tausa sai tasa hula da yake duk tayi
gurizin abinda zata bukata....Sosai taji dadin kasancewarta a d'akin, tayi kwanciyarta kan
lallausar katifa iskar hadari na kad'a labulan dakin.
Mijinta kawai take gani a lokacin da idonta yake lumshe, ta kira wayarsa ba adadi taki shiga da
alama gidan bashi da network ko kad'an ! gabadaya ta shiga damuwa, muryarsa kawai take
bukatar saurara a kunnanta.
*Ayi hakuri da rashin posting akan lokaci wallahi kanwata ce za tayi sauka al'kur'ani Gobeí ½í¹í ¼í¿»*
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*105&106*
To shima nashi 'bangaran abinda yake faruwa kenan, domin tun bayan ya sauka gida yake
kiran wayarta abun ya gagara, da ta fara shiga sai ta katse ya kira ya kai sau goma bai samu
biyan bukata ba, sai kawai ya ajiye wayar ranshi gabadaya a 'bace yaso kafin ya kwanta yaji
lafiyarta da ta babynsa dake kwance a cikinta, haka kawai yake tausaya mata, ya san duk wani
abu da take daurewa take akan ta nuna masa kaunar 'yan uwansa, kuma abunda tayi ya siya
mata kima da daraja a idonsa, ya sake jin sonta ya k'aru a zuciyarsa.
Da tunaninta ya kwana ya kuma tashi dashi, wannan dalilin ne yasa yana dawowa daga
massalaci ya dauki wayarsa ya kunna, ya fara laluben number ta, cikin ikon Allah sai ta kira shi,
a jiyar zuciya ya sauke mai sanyi kafin ya sanya wayar a kunnansa da sallama a bakinsa.
Ta amsa a sanyaye tana dan gyara kwanciyarta, yace." My GIMBIYA fatan kin tashi lafiya ya
kwanan bakunta."?
Tace."Lafiya alhamdullihi na kwana da tunaninka da kewarka rashin kwanciya a kirjinka ya janyo
min ciwon jiki."
Ya lumshe ido yana jin wani feeling na taso masa yace." Me yasa ki ka takura kanki lallai sai kin
kwana umm? saboda na san hakan zai faru ya sa na sauya shawara, yanzu na gamsu da
kaunar da kike a kaina da family na.
Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Nifa ba'a takure nake ba, domin yanayin garin ya
burgeni sosai da zamu dawo garin da zama da hakan yayi min dadi." Tafad'i hakane kawai ba
har can cikin zuciyarta ba.
Aikuwa yaji dadin maganar yace." Tunda yanayin garin yayi miki dadi zamu dinga zuwa hutu
ko? zan gina miki gida mai kyau."
Tayi 'yar dariya da fadin." Naji dadin hakan mijina."
Yace." Ya babyna ina fatan yana lafiya."?
A shagwabe tace." Jiya tun bayan da kuka gaisa dashi ya dameni da k'iriniya sai motsi yake
min."
Dariya yasa da fadin." Yana bukatar mu sake gaisawa sosai dan jiya baki sakar min jiki mun
gaisa yanda ya dace ba, amma ki bashi hakuri kafin mu had'u."
Itama dariyar take kafin tace." Aa ni babu ruwana idan kun had'u sai ka bashi hakuri dan da
alama yayi fushi tun wayewar gari beyi motsi ba."
Gabansa ya fad'i! da sauri yace." Beyi motsi ba fa ki kace."?
Ta dora hannunta a saman cikin tana shafawa kafin tace." Eh mana ya tattara a guri daya
kamar bashi da lafiya."
Gabad'aya yaji hankalinsa ya dawo garin yace." Ganin tafe insha Allah."
Da sauri tace." Laa da wasa fa nake maka."?
Ya 'bata rai da fadin." ZINAT an ta'ba wasa da lafiya ashe.'?
Jin yanda yayi maganar babu wasa yasa ta zama serious tace." Allah tsokanarka nake yanzu
haka ma motsi yake yaji muryarka."
Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Saboda kin ga na damu shiyasa zaki mayar dani shashasha
ko.''?
Kunshe baki tayi tana danne dariyar dake kokarin subce mata, tace." Kayi hakuri Darling."
"Um-um! naki hakurin." Cikin shagawaba yayi maganar.........Tace." Dan Allah fa."
Yace." Nayi amma kada ki sake min wannan wasa hankali na ya tashi wallahi."
Tace." To ba zan sake ba insha Allah.''
Yace." Uwale ta tashi."? tace." Eh tana kicin tana aiki."
Yace." Idan babu damuwa ki kai mata wayar mu gaisa."
Tace." To insha Allah bari na kai mata."
Cikin jin dadi yace." Allah yayi miki albarka."
Ta amsa da "Ameen tana kokarin tashi tsaye.
****
Hamra'u da kanta ta shirya abincin ta zuba cikin kwanuka masu kyau ta jera kan tire kafin ta nufi
bandaki a gurguje ta shiga wanka.
A lokacin ne mahaifiyarta Dayyiba ta samu damar aikata mugun nufin ta.
Ko kafin ma Hamra'un ta fito daga bandaki har ta sanya k'aramin d'anta ya dauki tiran dake
dauke da abincin sun fita a tare.
D'aya da rabi na rana Uwale na aiki a kicin Dayyiba tayi sallama a gidan.
Uwale ta amsa ta fito daga kicin din tana mata barka da zuwa, kai tsaye daki suka nufa.
Suka fara gaisawa tare da tambayar bayan rabuwa.....Dayyiba tace." Ai da wuri yau na gama
abinci nace bari nazo mu gaisa na kuma ga matar Umaru kin san dama ni ban ta'ba ganinta
ba."
Uwale tace." Allah sarki sannu da kokari Dayyiba har da wahala haka to mun gode sosai."
Tana murmushi tace." Babu komai Dambu ne na turara mata na san masu ciki da kwad'ayi
watakila yayi mata dadi."
Tace." Eh 'kwarai kuwa, bacci takeyi yanzu amma bari na leka na gani ko ta tashi."
Lokacin da ta shiga dakin zaune ta sameta a bakin gado tun bayan shigowar Dayyibar ta tashi
duk tana jin maganganunsu.
Tace." Ashe kin tashi dama mahaifiyar Hamra'u ce tazo ku gaisa ta kuma kawo miki abinci."
Tace."Allah sarki amma na gode sosai bari na fito mu gaisa."
Ta juya da fadin." To bari na sheda mata."
Shuru tayi tana nazarin al'amarin, mahaifiyar Hamra'u? ita sunan yarinyar ma bata kauna
ballantana wanda ya danganceta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi da k'yar! yunwa sai sasakar cikinta take, abun goge baki ta
dauko cikin kayanta.
Koda ta fito bata zauna ba tukkuna sai da ta wanko bakinta ta dauro alwala sannan ta dawo
dakin.
A nutse ta zauna kusa da Uwale ta kalli Dayyibar dake mata wani munafikin kallo tace." Ina
wuni fatan mun sameku lafiya."?
A firgice ta amsa da fadin." Lafiya lou muke ya mutan gida da can gurin manyan."
Tace." Duk suna nan lafiya lou."
Daga haka sai ta kawar da kanta tana nazari akan matar kamar mara gaskiya.
Uwale ta bud'e kwanunkan abincin da fadin." Dambu ne ko kina sha'awa."
Kamshi ya bugi hancinta Dambun ya hadu yaji gyada da zogale ga k'amshin man gyada ziryan
yana tashi...........Tunda take sau biyu kacal ta ta'ba cin irin wannan abincin, shima kuma irin na
shinkafa bana masara ba , wannan dalilin yasa gabadaya ta rikice yaron dake cikinta ya nuna
kwadayinsa akan abincin .
Ta kalli Dayyibar da fadin" Na gode sosai."
Tana washe baki ta amsa da babu komai dan nayi miki hidima kamar 'yar cikina kike."
Murmushi kawai tayi ta kalli Uwale da fadin." Nayi sha'awarsa.".
Uwale tasa dariya da fadin.'' Ai dole ni kaina ya bani sha'awa ballanatana ke da kike da lalura."
Dayyiba ta dinga dariyar farin ciki tace." Ai kin san Hamra'u ta gwane gurin iya abinci gargajiya
dama na turawan kowacce mace tana da baiwa, amma tabbas duk macan da ta iya girki zata
samu soyayyar mijinta.
Ba ita Zinat din ba har Uwale sai da taji babu dadi da maganar Dayyibar dan kamar maganar
tayi kama da habaici.
Babu dai wanda yayi magana a cikinsu, ta zuba mata a ma daidaicin plate. tayi bisimillah ta
fara ci a nutse ba ta tunanin komai a ranta.
Sosai dambun yayi mata dad'i, tas ta cinye wanda yake gabanta. a cikinta tana jin k'oshi amma
a bakinta ba ta gaji ba, haka dai tayi kawaici tasha ruwa.Uwale ke tambayarta, tace." A yanzu
dai ta koshi sai zuwa an jima tukkuna."
Dayyiba mahaifiyar Hamra'u zuciyarta fes! ta fita gidan, babban burinta cikin ya zube ko kuma
Gimbiyar ta galabaita.
Aikuwa dai jikinta ne ya mutu kasala ta dame ta, sai kawai taje ta kwanta tana ya mutse
fuskarta cikinta ne yake hautsinawa zuciyarta na tashi.
Minti ashirin da kwanciyarta ta tashi a gigice! sakamakon jin wani irin mahaukacin amai da yake
taso mata.
Bakin rariya ta gurfana ta dinga sheka aman tana rike kirji!
Uwale hankalinta ya tashi ganin mawuyacin halin da Gimbiyar ke ciki.
Ta rike ta tana mata sannu a lokacin kanta ya dinga juyawa tayi kwance a gurin tana mayar da
numfashi.
Uwale tace." Sannu ki daure ki tashi ki koma daki ki kwanta a can kinga nan akwai rana gaki a
bakin kwata a kwance."
Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, gabadaya ma bata cikin hayyacinta, tana jin yanda cikinta
yake kartawa! wannan karan ba amai takeji ba zawo! ne mai karfi yake kokarin kwace mata.
Kokarin tashi take domin shiga bandaki abun ya gagara domin gabadaya jikinta ya shika babu
kwari! duk yanda taso da ta daure ta kasa ba ta ma san lokacin da zawon ya kwace mata ba,
kawai sai tsuuuuuu! ta dinga jin fitarsa kamar an kwance famfo.
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! shine abinda Uwale take nanatawa.
(Cutar a mai da gudawa!) ya kama 'yar mutane! cutar dake saurin halaka mutum, hankali a
tashe ta nufi gidan Tasallah.
Suka shigo tare lokacin gudawar sai bin rariya take ita kuma tana kwance a gurin sai matagugu
take domin wani masifaffan ciwo cikinta yake mata.
Tasallah tayi salati tana sanar da Ubangiji kafin tayi azamar fita, gidanta ta koma da yake akwai
magungunan gargajiya da take aje dasu, ta daga karkashin gadon karfenta ta dauko ledar
maganar duk tayi kura da dauda! da yanar gizagizo ajikin ledar ta dauka ta fita.
Aje ledar tayi a gefe ta taimakawa Uwalen suka fara gyarata, idonta a lumshe yake amma duk
tana jin taretaran da suke da ita, ta riga ta mika wuya yanda take jin jiki bata tsammanin zata
rayu.
Jikinta suka wanke mata lokacin anyi sa'a Gudawar ta tsaigata da zuba.
Uwale tayi saurin dauko mata wasu kayan da wando da rigar nono suka sanya mata jikinta
mikar da ita sukayi kafafunta suka dinga kyarma! a daddafe suka shiga da ita daki.
Uwale ce ta shiga gyara gurin, ita kuma Tasallah sai da ta tsaftace hannuwanta, sannan ta
kwance ledar maganin data dauko ta fito dasu a daddaure! daka gani sun jima a ajiye, wuta ta
hura kafin ta wanke maganin tas ta zuba a tukunya tasa jar kanwa sannan ta d'ora a wuta.
Sai da ya tafasa sosai sannan ta sauke domin yasha iska.
To cikin ikon Allah da hukuncinsa tana shan wannan magani ta samu sassauci ciwon cikin da
yake damunta yayi sauki baccin wahala ya d'auketa.
Uwale ta kalli Tasallah da fadin." Sai yanzu hankalina ya kwanta Tasallah al'amarin nan ya
tsorata ni mutuka."
Tace." Dole ne, ni kaina ganin yarinyar a galabaice sai da na firgita kasancewar na san cewa
wannan cutar na saurin halaka mutum! Allah yasa akwai ajiyayyun magunguna kinga cikin ikon
Allah sunyi amfani "
Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Tasallah nifa ina zargin Dayyiba."
Shuru tayi tana kallonta da mamakin maganarta.
Tace." Tun bayan da yarinyar nan taci Dambun da Dayyibar ta kawo mata shikkenan ta rikice
shiyasa nake zargin ko da abunda tayi.
Tace." Uwale zato zunubi aka ce koda ya kasance gaskiya ne, ni kuma nafi tunanin ko sauyin
cima ne da ruwan sha, kin san hakan na iya janyo faruwar mummunar matsala.
Tace." Idan hakane me yasa jiya da taci abincina ta kwana lafiya? ruwa kuma ba irin wannan
muke sha yarinyar take sha ba, kafin mijinta ya tafi sai da ya siya mata ruwan roba gashi can a
daki kwali guda. gaskiya ina zargin Dayyiba.
Tasallah tayi murmushi da fadin." Hakan na iya faruwa amma kada kiyi gaggawar yanke
hukunci tukkuna.
Shigowar Hamra'u ne ya katse maganar, babu wanda ya nuna mata wani abu a fuska, ta zauna
suka gaisa, kafin ta kalli Uwale da fadin." Ummana ta kawo miki Dambu ko."?
Tace." Eh ta kawowa dai Gimbiya."
Ta dan 'bata rai da fadin." Ai naki ne kasancewar na san kina son Dambun masara