Showing 24001 words to 27000 words out of 46235 words
Chapter 9 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale
yasa na
tashi da wuri nayi miki, ko kafin na fito daga wanka na samu Ummana bata gidan wai ashe
anan tazo."
Tace." To Na gode sosai Allah yayi miki albarka."
Tasallah na 'yar dariya tace." Hamra'u kenan to menene dan kishiyarki taci ai abun burgewa ne
"
Zumbura bakinta tayi tana ya mutse fuska.......Dukkaninsu babu wanda yaji dadin abinda tayi,
kiri-kiri take nuna kishinta a fili.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/26, 9:56 PM] Matar Malamí ½í¸Š: _Akwai ingantaccan maganiní ¼í¼´í ¼í¼´ gyaran nono na hausa, ga
wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin
karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin
yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu
cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga
ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki,
bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya
muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin
ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita
kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*107&108*
Sai gefin magariba ta tashi daga baccin daya d'auketa, jiki babu kuzari ta tashi zaune da sunan
Allah a bakinta, shiru tayi tana tunanin irin wuyar da tasha a d'azu, tabbas da kwananta ya 'kare
babu wanda ya isa ya hana Allah zartar da Allah ikonsa, sam ba tayi tsammanin cewar zata
sake wata rayuwar ba, duba da irin siradin data tsallake, a mai da gudawa ba karamin cuta
bane, yanzu ma gabad'aya bata jin dadin jikinta, duk yayi laushi akwai bukatar karin ruwa a
tare da ita.
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta fara kokarin sauka daga gadon, kira ya shigo wayarta dake
saman gadon, ta dauka tana dubawa, a kalla ya kira yafi sau ashirin tana bacci, tausayinsa ya
rufe ta, tasan yana can a dame kamar yanda take a takure! ko kuma jikinsa ne yake fada masa
cewa akwai matsala.
Ta daga wayar cike da so taji muryarsa, network yayi tsiya dan sai magana take masa amma
shi ba yaji.....Ta kashe wayar ta sake kira anan ma ba babu biyan bukata, kamar zata fashe da
kuka ta ajiye wayar takaici duk ya isheta.
Uwale ta shigo dakin, ganinta a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya tace." Kin tashi ko ya jikin
naki."?
Tayi kokarin danne damuwarta ta amsa da fadin." Naji sauki sosai na gode."
Tace." Haba ai babu godiya a tsakaninmu Gimbiya Allah dai ya kiyaye gaba."
Ta amsa da "Ameen ya Allah."
A sanyaye tace." Amma don Allah ina neman alfarma a gurin ki."
Cike da mamaki take kallon matar wace irin alfarma ce."?
Tace."Don Allah kada ki fad'awa mijinki abunda ya faru kinji ko."?
Murmushi kawai tayi kafin tace." Insha Allah kada ki damu ba zan fad'a masa ba."
Tace." To na gode sosai.''
Har ta juya zata fita daga dakin ta dakatar da ita....."Ina bukatar nayi wanka jikina bana jin
dadinsa."
Tace." Ai dole! amma kiyi hakuri ayi sallah tukkuna bari na dora miki ruwan zafi sai ki gasa
jikinki."
Tace." To shikkenan hakan yayi." Uwale ta fita daga dakin tana godiya ga Allah ganin yanda ya
gajarta musu wahala.
Cikin ikon Allah ta na yin wanka jikinta ya warware ta zauna taci abinci zuciyarta fes domin ba
tayi tunanin cewa wai abincin da taci dazu ne ya janyo mata matsala ba, itama tafi tunanin
cewa ko sauyin yanayin gari da sauransu.
Ta kalli Uwale da fadin." Ina so nayi waya amma gidan nan bashi da network yana bada
matsala."
Tace." To yanzu ya za'ayi kin ga yanayin gidajen namu ginin da ne babu tsayin katanga a daki
ga zurfi.
Tace." Zan fita waje ko Allah zai sa a dace."
Tace." To shikkenan babu damuwa.
Can wani fili ta nufa, duk da dare ne hakan bai hana gane ta ba, ido yayi caaa! a kanta, yara da
manya masu wuce wa.
Ita dai bata damu ba bukatar ta, ta samu wayar masoyinta.
Bugu daya ta shiga ya daga, abun mamaki tar taji muryarsa babu gargada.
Ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke kafin tace " Darling ya kake? ina fatan kana cikin koshin
lafiya."
Yace." Kin san hakan ba zata samu ba, ZINAT me yasa baki d'aga wayata akan lokaci ba."
Tace." Ba laifi na bane network ne babu a garin, nima na damu da kai sosai wannan dalilin yasa
na fito waje wani fili duk dan naji muryarka."
Yace." Yanzu kina nufin ba'a cikin gida kike ba."?
Tace." Eh ai cikin gidan na fad'a maka babu network mai kyau.
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ki koma gida bana san tsayuwar ki a gurin nan."
Tace." Haba babu fa abunda zai faru duk ga jama'a nan suna kai kawo a gurin."
Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin wani abu a ransa, jiya kwana yayi yana munanan
mafarkai a kanta, amma yasan babu wani mahalukin da ya isa ya cutar da ita face Allah ya
mayar masa da sharrin kansa.
Hamra'u da k'awarta Zabbah suka hangota a tsaye da waya a kunne.
Hamra'u tace." Zabbah ga mutsiyaciyar can."
Zabbah ta kalli gurin da fadin." To me ya fito da ita a wannan daran ita ba 'yar gari ba."
Tace." Waya ta take na san kuma da masoyina take, yau sai naci mutuncinta in yaso duk
abinda zai faru ya faru."
Zabbah ta rike hannunta da fadin." Hamra'u kada fa ki aikata abunda zai janyo miki matsala ki bi
komai a sannu a hankali."
Ta fizge hannunta da fadin." Zabbah ni kad'ai na san irin b'akin cikin da wannan matar ta k'unsa
min, ai magana ta 'kare tunda manya sun shiga maganar har an tsayar da ranar daurin aure."
Hannunta ta fizge ta durfafi gurin da Gimbiyar take tsaye....Zabbah ta rufa mata baya.
Tace." Darling zan shiga na kwanta sai da safe." Daga d'aya b'angaran yace." Okey Allah ya
tashe mu lafiya amma ki mika min gaisuwa gurin babyna kafin mu had'u."
Tana murmushi tace." Zai ji da kyau! amma shima yayi kewarka sosai.
Yace." Haka nake so ai duk sanda muka had'u zamu gaisa sosai ki bashi hakuri."
Cikin shagwaba tace." 'Daya babyn naka ma yana bukatarka fa."
Ya lumshe ido tsigar jikinsa na tashi! ya gane abinda take nufi shiyasa gabadaya kasala ta
rufeshi yana bala'in son yanayin shagwabarta.
Yace." Wannan babyn yayi min laifi ki sheda masa cewa idan muka had'u zan hukuntashi da
kyau."!
Ta fashe da dariya da fadin." Ba ruwana amma na yarda duk sanda kuka ka had'u kayi masa
hukuncin da ya dace."
Yana sake release a kujera yace." Zan kuwa cire masa kai shine hukuncin da zanyi."
Maganar ta bata kunya sosai tana 'yar dariya tace." Ni dai sai da safe."
Yace." Dole ki gudu mana kin san halin da ki ka jefa ni ciki kuwa."?
A sanyaye tace." Kayi hakuri gobe ka dauki azimi."
Yace." Azimin dole kada kiyi tsammanin gani na gobe kuma idan nazo komai rigimarki tare
zamu tafi."
Tace." Ai gobe ne bikin idan kazo sai mu tafi shikkenan."
Yace."Okey Allah ya kaimu amma mybe shigowar dare zanyi.
Tace." To idan hakane kawai ka bari sai jibi da wuri sai ka shig.......maganar ta katse sakamakon
zuwansu Hamra'u gurun.
Ta kashe wayar tana kallonsu.
A wulakance tace." Munafukar Allah ta ala to duk asirin da kuke Allah ya karya alkadarinki, ina
so ki san cewa baki isa ki hana abinda Allah ya hukunta ba."
Cike da mamakin maganarta tace." Ke wannan wace irin magana ce."?
Da yatsa ta nuna ta kamar zata tsone mata ido tace." Hamra'u ta UMARU ce shekara da
shekaru ina nufin ke baki isa ki shiga tsakanin masoya ba."
Sai abun ya bata dariya amma ba tayi ba ta dake ta sha kunu da fadin." Kin san ni nafi karfin
kiyi min rashin kunya ko."?
Aikuwa sai ta fusata! ta sake nuna ta da hannu da fadin." Ke asuwa kuma? ko kin dauka kina
da mutunci a garin nan, to bari kiji dake da kare! baku da maraba domin bama 'kaunarki, kuma
ki kwana da shirin wata shida kacal ya rage a daura min aure da mijinki sai kiyi duk abinda za
kiyi."
Ranta ya 'baci sosai da irin fitsarar da yarinyar take mata, kawai sai ta girgiza kai ta kama
hanya domin barin gurun.......Tace." Matar cushe bata daraja."!!
A fusace! ta juyo ta wanke fuskarta da mari wanda sanya ta ganin gilmawar taurari! ta dafe
gurin cikin kad'uwa da mamaki take kallonta.
Ta nuna ta da hannu tana so tayi magana, amma tsabar b'acin rai ya ha nata furta komai,
kawai ta girgiza kai a gaggauce ta bar gurin, zuciyarta kamar ta fashe saboda tsananin bacin
rai!
Zabbah ta kalleta da fadin." Ko babu komai kin sha mari! wallahi Hamra'u baki da wayo har
yanzu."
Ido jawur! take kallonta kafin tace." Kin san Allah Zabbah! sai na rama mari na don kutumar
ubanta tazo cikin garinmu ta mare ni, wallahi ba zan yarda ba." Fizge hannunta tayi ta nufi cikin
gidan.
Zabbah ta bita da kallon takaici tana girgiza kai kwata-kwata Hamra'u bata da wayo wallahi,
kishi hauka take, ai idan itace ba zata fito da kishinta a fili kowa ya fahimta ba, amma ita duk
inda ta zauna maganar kenan, tayi ta zagin Gimbiyar
Kai tsaye da ta shiga gidan kanta ta nufa gadan-gadan! mari ta kai mata, tayi saurin kaucewa
ta mari iska!! ta tsaya tana numfarfashi idonta cike da ruwan hawaye take fadin." Wallahi baki
isa ki mare ni na kyale ki ba, sai na rama." Ta sake mika hannu da niyyar marin ta, kafin tayi
aune! taji saukar wani lafiyayyan marin a fuskarta!
Uwale hankali a tashe! ta shiga tsakaninsu tana tambayar ba'asi.
Gimbiyar ranta a 'bace tayi mata bayanin duk abinda yake faruwa.
Uwale ta kalli Hamra'u da fuskar bacin rai tace." Amma wallahi kinji kunya Hamra'u kin 'bata
wayonki ban ta'ba tunanin haka zuciyarki take ba sai yau."
Sai kawai ta fashe da kuka takaici biyu ya dameta, na farko tasha marika masu zafi daga gurin
Gimbiyar, gashi bata samu sararin ramawa ba ana fada mata bakar magana, dama ba tun yau
ba ta gane cewa Uwalen tafi kaunar Gimbiyar a kanta.
Bakin ciki da takaici ya ha nata magana kawai ta kada kanta ta kama hanyar fita tana share
hawaye.
Zabbah dake tsaye a tsakar gida tabi bayanta tana rarrashinta.....''Yanzu idan Umar din yaji
abinda ki kayi wa matarsa kina tsammanin zai kalleki da mutunci? Hamra'u shifa yaki dan
zamba ne me yasa zaki 'bata rawar ki da tsalle."
Ta daga mata hannu da fadin." Kin ga Zabbah na gaji da jin wannan maganar taki, domin ta
kunan hagu take fita, kin san Allah sai na saubata matar nan! sai ta gwammace kida da karatu."
Zabbah tace." Yawwa to dama tuntuni ta wannan hanyar ki ka biyo yafi sauki idan kin bi ta
karkashin kasa babu wanda zai fahimce ki, amma kin zauna kina hauka haba Hamra'u!
Mugun tsaki taja mai tsayi fuuuuuuu! ta shiga gidansu ba tare da tayi mata sallama ba, girgiza
kanta tayi itama ta kama hanyar gidansu cike da mamakin al'amarin.
Malam Shafi'i yana dawowa Dayyiba ta shirya masa karya da gaskiya cewa yana da kyau yaje
har gidan Uwalen ya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro domin ba zai yuwu ace 'yar uwar tasa
tana fifita wata a kan jininsa ba.
Aikuwa ya dauki zugar matarsa domin ransa ya baci da jin abinda 'yar uwarshi ciki daya tayi
wato tana fifita wata a kan 'yarsa
Har gida yaje ya sameta ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sai kumfar baki yake yana
sakin kausasan maganganu wanda duk wani mai hankali ya auna maganar ya san habaici ne.
Tana daga cikin daki duk ta na jin abinda yake faruwa....Uwalen na share hawaye tace." Shafi'i
na gode da cin mutunci matarka ta zuga ka kazo har gida kaci mutuncina cikinmu daya da kai,
baka duba furfurata ba, ka tsaya a kaina kana fada min magana babu komai na gode."
Yace." Ai gaskiya na fada miki Uwale ki gyara kuskuranki, kafin ki k'aunaci kowa Hamra'u ya
kamata ki nunawa kauna da kulawa, amma a karon banza kin watsar da zumunci saboda
kwadayi kin kama wata mara tarbiya kina mata ladabi a gabanki ta fitar da hannu ta tsinkawa
yarinya mari ki kasa daukar mataki, karshe ma ki ka mayar da laifin kanta, wannan ba adalci
bane."
Ta sanya gefan zani ta goge ragowar hawayen da ya rage tace." Tabbas da na san wannan
bacin ran zan samu da nayi zamana banzo ba, Shafi'i ban ta'ba tunanin akwai ranar da za tazo
ka tsaya a gabana ka nayi min rashin kunya ba."
Yace." Duk abinda nayi miki ke kika janyo idan kina son zumuncinmu ya cigaba da gudana to
kiyi gaggawar sanya albarka a cikin auran Umaru da Hamra'u! domin da kin so da tuni Umaru
ya auri yarinyar nan idan da rabo a kusa ma da tuni ta haihu."
Tayi shuru ta kasa magana tsabar bacin rai!
Shi kuwa rigarsa ya buge ya fita daga gidan ransa a bace.
Tana daga cikin dakin take jin sautin kukanta, tausayinta ya rufeta,duk akan ta nuna kulawa da
ita ne yasa aka zo har gida aka sanya ta zubar da hawaye......ita kuwa zata bawa mara da
kunya. taji wani kwarin gwiwa a tare da ita.
A nutse ta zauna a kusa da ita tare da dafa kafad'arta.
Ta kalleta a sanyaye da fadin." Kiyi hakuri abinda akayi miki kinji ko."
Girgiza kanta tayi da guntun murmushi a fuskarta tace." Uwale ke zan bawa hakuri nasan
dalilina dan uwanki yazo har gida yaci miki mutunci iya son ransa, kuma cikin maganganunsa
na fahimci abunda yake nufi. Ban hana Umar Auran Hamra'u ba, nima kaddara ce ta had'a ni
dashi ashe shine uban 'ya'yana ban sani ba, Amma wallahi kaf tunanina bai ta'ba kawowa cewa
zan aureshi ba ballantana har na fuskanci matsala irin wannan, wallahi na amince ya auri
yarinyar nan mutukar shine kwanciyar hankalinku gabadaya.
Uwalan ta dinga kallonta tana mamakin furucinta, sam ba tayi tsammanin cewa tana da sauki
kai irin haka ba, yarinyar nada nagarta sai mu'amula ta had'aku sannan zaka fahimta.
****
Washe gari da sassafe ta fita wajen gidan domin samun network......Lokacin jama'a basu fara
kai kawo ba, ta kira shi yana shirin fita.
Cike da farin ciki ya daga wayar ''Farin ciki na kin tashi lafiya."?
Ta amsa babu yabo babu fallasa kafin ta d'ora da fadin." Za kazo yau din."?
Yace." Eh insha Allah, ina fatan lafiya.''? ba tace masa komai ba, kawai ta kashe wayarta ta
koma gidan.
Ta samu Uwale ta fito da shirin shiga gidan Tasallah........Tace." Na fita ne nayi waya da
maigidanki yace yana kan hanya insha Allah."
Tace."Allah ya kawoshi lafiya da dai nayi niyyar mu zauna mu kwana biyu amma saboda
abubuwan da suke faruwa na rashin dadi gwara mu tafi shi yafi alkairi."
Murmushi tayi wanda ya tsaya iyakacin fatar bakinta, tace." Wancan kayan dake cikin baggo na
tsaraba ne ya kamata tunda zaki shiga cikin jama'a ki tafi dasu."
Tace." Kina nufin akwai wasu kayan da ki kazo dasu."?
Tace." Eh suna can dakin." tafada tana nuna dakin Umar din da yake dake rufe.
Uwale kasa magana tayi saboda mamakin mutunci da karamcin yarinyar, tana da kyawun
zuciya tana kuma da kyauta da alkairi hakan kamar a jinin jikinta yake.....Ta kalleta da fadin."
Sannu da kokari, Allah ya saka da alkairi amma yana da kyau muje tare dake sai ki basu da
hannunki.
Tayi jim tana nazarin maganar kafin ta girgiza kai da fadin." Babu komai Uwale ni dake duk daya
ne kawai ki basu a matsayin kece ki ka kawo musu babu komai."
Tace." Aa ba za'ayi haka ba, idan ma ba za kije ba babu damuwa amma tabbas da sunanki zan
bada kayan."
Tayi murmushi da fadin." To hakan ma yayi ni zan shiga na kwanta Allah ya sanya alkairi." Ta
amsa da ameen tana kokarin bude dakin Umar din domin fito da kayan.
*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da