Showing 45001 words to 46235 words out of 46235 words

Chapter 16 - GOJE Part 4 Complete Document by Binta Abbale

waya yafi sau biyar har kuka takeyi.

Tsigar jikinsa ta tashi, ido ya lumshe da fadin." Nima kukan zucci nake tsayin wata da wasu
kwanakin ban sata a idona ba mun rabu babu jituwa wallahi hankalina gabadaya yana kanta.

Asp din yana laluben number yace." Kamar ita kadai ka ajiye a gidan ko ka manta su biyu ne ga
Uwale ma babbar uwar gida."

Murmushi yayi bai iya cewa komai ba, hannu ya mika masa domin ya bashi wayar.


Yasa wayar a kunnanshi yayi dai-dai da maganarta......"Assalamu alaikum."

Idonsa ya lumshe wani irin yanayi na ziyartashi.

Gyaran murya yayi a nutse yace." Wa'alaikissalam Sirrina marufar asiri na."

Jin muryarsa a kunnanta ya sanya ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya a hankali tace."
Alhamdullihi jin muryarka a yanzu ya tabbatar min da cewa sauki ya samu a gareka ina rokon
Allah ya baka lafiya tare da sauran wa'inda suke kwance."

Ya amsa da "Ameen ya rabbi ya kike ya babyna dake tare dake."?

Hannu ta dora saman cikin da yayi wani irin girma tace.'' Babynka yana kewarka shima kullum
sai yayi kukan rashinka a kusa dashi."


Yace." Ki bashi hakuri kinji ko insha Allah ina nan zuwa gare ku baki d'aya sannan ina neman
afuwarki akan abubuwan da suka faru a baya.

Tayi dan murmushi da fadin." Na yafe maka nima ka yafe min."

Yace." Baki min komai ba my love ni ne mai laifi a gurinki amma naji dadi da ki kayi min afuwa

zan dawo mu cigaba da rayuwa mai kyau."

Tace." Allah ya yafe mana baki daya.

Ya amsa da Ameen kafin yace." Ina Uwale ki bata wayar mu gaisa."

Tace." Gata a kusa dani tare da Hamra'u."

Shuru yayi bece komai ba .

Ta mikawa Uwale wayar suka gaisa sosai tana jajanta masa.

Yace." Uwale ku kwantar da hankalinku na samu lafiya insha Allan zan dawo da kafafuna.

Tace." To Alhamdulillhi Allah ne abin godiya mutanan *Kafur!* ma duk sun ce ayi maka sannu
da jiki sai ka dawo gida zasu zo dubaka."


Yace." Na gode sosai Allah ya saka da alkairi."

Wayar ta mikawa Zinat din fuskarta yawalce da fara'a da jin dadin samuwar lafiyar jikinta nata.


Ta mikawa Hamra'u wayar dake zaune tayi jugum!

A sanyaye tace." Yaya na sannu ya jikin."?

Babu yabo babu fallasa ya amsa, iyayen yarinyar sun janyo mata tsana a gurinsa.


Daga haka babu wata kalma mai dadi kawai ya kashe wayarsa.

Idonta ya ciko da ruwan hawaye! tana so itama ya dinga gwada mata soyayya koda bata kai irin
wacce yake gwadawa Zinat din ba.


A sanyaye ta mika mata wayar jikinta babu kwari ta tashi ta shige daki ta kwanta abin duniya ya
isheta.

Zinat da Uwale kuwa yinin walwala da farin ciki sukayi sakamakon amsa adduarsu da Ubangiji
yayi babu shakka Allah maji rokon bawansa ne.

To bahaushe yace ." Rana dubu ta 'barawo rana guda ta me kaya.

*UBAN DABA!* ya samu nasarar shiga asibitin cikin shigar Dr Shu'aib likitan dake tsaye a kan
Umar din!

Yayi basaja sosai da yake Dr Shu'aib din gajere ne mai 'kiba shiyasa babu wanda yayi tunanin
cewa bashi bane, abinka da dare duk da akwai fitilu a asibitin hakan bai sa an ganeshi ba,kai
tsaye ya nufi d'akin da Umar din yake kwance!


A hankali ya mayar da kofar ya rufe.....Asp dake kwance a can saman kujera ya bude idonsa
sakamon jin motsin a dakin
Dama can bashi da nauyin bacci.

Ganinshi yasa ya koma ya kwanta dan beyi tunanin cewa wani ne daban ba. baccin ya sake
fizgarsa.

Da har ya tsorata amma ganin ya koma ya kwanta yasa ya sauke ajiyar zuciya.

Kai tsaye gadon da yake kwance ya nufa.


Isarsa ke da wuya ya b'ude idonsa!!

'Kwayar idonsa kawai ya kalla ya sheda waye a gabansa.


A zabure! yayi nufin tashi.......shi kuma da gaggawa ya rike masa wuya da kyau!!

Wata shegiyar igiya mai wasu k'ananun kososhi masu tsini! ya ciro daga can kasan aljihun
wandon dake jikinsa.

Kokarin d'aure masa wuya yake da igiyar abun ya gagara! domin dambe! suke sosai! duk da ya
sha'ke masa wuya! amma bai samu nasara a kansa ba.

Naushi! ya kaiwa hancinsa a take ya fashe ya fara zubar da jini. ya sake kawai fuskarka wawan
naushi! yayi tagaga! zai fadi! amma saboda taurin zuciya bai sakar masa wuya ba.


Gurnani! ya dinga yi yana buge-buge! da kyar yake janyo numfashi! ya galabaita sosai! saboda
dama can jikin babu 'kwari!

Kamar a mafarki ya dinga jin wani irin abu.

Ya bude ido da saurin gaske.

Abinda ya gani ya tayar masa da hankali shin mai yake faruwa a tsakaninsu.


Da sauri ya nufi gurin da fadin." Dr me yake faruwa ne."n

Juyowar da zai yi suka had'a ido! nan ya sheda ko waye! jikinsa ya shiga tsuma! ya zabura! zai
fita. kawai ya d'aga igiyar dake hannunsa ya kai masa duka da ita a fuska! aikam duk ta yanke
masa fuskarsa har kan idonsa ya rufe! idon jini ya 'bata fuska........Da kyau! yayi ihu!! da fadin."
Babu lafiya a daki mai lamba 21."
Kafin kice me hankalin kowa ya tashi duk likitocin dake aikin kwana suka fito tare da masu gadi.

Kai tsaye d'akin suka nufa.....Lokacin ana buga damben Maza! tsakanin mutum biyu. Asp na
kasa a kwance yana matagugu! rai a hannun Allah.

Sosai suke dambe!! irin na k'wanji da 'kwanji *UBAN DABA!* hannu guda gareshi amma ya
san makwantan mugunta!


Shi kuma da yake da rauni a jikinsa hakan bai sanya yayi rauni ba, ganin Asp a kwance! ya
tayar masa da hankali babu shakka yau sai yaga karshen mutumin nan mutu'kar yayi sanadin
abokinsa.


Ganin abinda yake faruwa ya tayar musu da hankali.

Duk yawansu aka rasa wanda ya iya zuwa gurin domin bada taimakonsa.

Su kansu sucurity din abun yafi 'karfinsu!


Gabadaya ya manta da wanda yake gogayya! shine fa mutumin nan da wu'ka! bata aiki a
kansa! amma ya dage yana wahalar da kansa sai kai masa sara da kaifaffar wukar dake
hannunsa burinsa kawai ya illatashi.

Ganin haka yasa yayi kwankwance ya murd'e! masa hannu ya kwace wu'kar!

Bai kuma jirayi komai ba ya soka masa ita wuyansa!!

A take ya fadi a gurin yana wani irin gurnani! jini ya dinga tsartuwa!

Zubewa a kusa dashi da wu'kar a hannunsa da karfi yace *." Ashahadu Allah ila ha'illalahu
-wa ashshahadu Anna Muhammadur-rasulullah.* fad'ar hakan keda wuya ya mi'ke cikin zafin
nama yaje ya fizgo k'aramar bindigar dake jikin rigar Asp dake rataye bai jira komai ba ya sai ta
a wuyansa.



*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi
sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar
gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login