Showing 27001 words to 30000 words out of 69832 words

Chapter 10 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

953


maidawa take sabida ya kunnu yaki kunnuwa, ga jakanta goye abayanta. “Hi Rashy” Aisha
receptionist dake night zuwanta kenan tai waving nata tana murmushi awkwardly tadaga
hannunta saikuma ta maida ta gyada mata kai kawai tawuce tafito waje tana hure huren waya,
Munir da Riyad na tsaye awaje wannan karan ya chanza kaya zuwa jumper na milk yadi suna
magan kaman daga sama ya hangota tafito tana hura wayanta, yanda hankalinshi da attention
nashi yatafi wajenta saida Munir yajuya dasauri dan yaga meyake kallo haka ganin wacce yake
kallo wacce kallo daya yamata she looks like worker nasu not guest yasa yace “who is she?”
Batare daya dauke kanshi daga kallonta ba yace “my savior” dasauri Munir yadauke kanshi
daga kallonta ya kalleshi dasauri yace “kaman ya your savior?” Yana kallonta yace “the girl that
saved me from those goons a airport” dasauri Munir yajuya ya kalleta yace “wow the clearner

damuka dade muna nema wat a small world ashe anan hotel namu take aiki, but did you tell
her”? Girgixamai kai yayi daidai tasha kwanan layin yadauke kanshi yace “No bangayamata”
Munir yace “why?” mota yashiga yace “bata ganeni ba” tada motan Munir yayi yace “ai da saika
gayamata, How will you reward her yanzu?” Kai tsaye yace “I will ask her kome takeso arayuwa
i will grant her any wish take da shi she’s part of the reason I’m alive today” murmushi Munir
yayi yace “wat got you so angry today?” Yatsine fuska yayi yace “I don’t wanna talk about it”
ahankali Munir yace “to mutafi gida? Mom tasa an sanar bakada lafiya just to manage situation
din harda kiran Dr, tace na tabbatar mun dawo gida tare” hannunshi yasa yasauke glass na
window ya lumshe idanu bai sake cewa komi ba, ganin baison magana yasa yace “azumi saura
7days fa bakai approving fund na kayan abincin daza’a rabama al umma da ma’aikatan ka ba”
dan ijiyan zuciya yayi yace “i forgot bani file din da pen lemme sign” ahankali Munir yace “bari
mukai i will give u yana file dake back seat.
JOIN GROUP DANAKE POSTING

https://chat.whatsapp.com/Ckm5Bo7CcqR1NYkgT0HEvR
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI



✍M SHAKUR


EPISODE 1️⃣3️⃣

Gida tashiga around magrib agurguje tai alwala tashigo ciki Mama nakan dadduma hakan yasa
ta tsaya kusada ita ta kabbatar sallan.

Tana idarwa cikeda damuwa tace “Mama ruwa yashiga wayana taki aiki wlh” tai maganan tana
jawo jakanta taciro wayan cikeda damuwa itama Mama tace “garin yaya meya sameta?” Cikin
damuwa tana kara huhhure wayan tace “faduwa nayi ruwa ya kwaromin shine ruwan yataba har
wayan” dasauri Mama tasa hannu ta karbi wayan itama tana huhhura duk wani huji na wayan ta
maida battery din kozata kunnu amman bata kunnu ba hakan yasa ta tashi tawuce chan wajen
yan kayan abincinsu tabude ledan shinkafa tasa wayan ta zuba shinkafa akai tace “bari mugani
kozata kunnu idan bata kunnu ba saina tattara kudin dake wajena kije ki sayo wata wayan
dashi, kina bukatan waya kodan school, Allah kiyaye bakiji ciwo bako”? Gyadama Mama kai tayi
tace “banji ciwo ba” Mama tace “to ai mun gode Allah tashi kiyo wanka kici abinci” dasauri tace
“Mama girki kikayi”? Gyadamata kai tayi tace “eh nayi shinkafa da wake da mai sa yaji”
murmushi tayi tace “Mama banace ki dena girki ba” ture mata hanci Mama tayi tace “to banji
maganan ki ba Anty Rashida” kwashewa da dariya tayi hakan bakaramin dadi yama Mama ba
ganinta duk cikin damuwa sabida wayan tasan lissafi take ta yanda zata taba kudin saving
dinsu tasai waya dashi kafin takara samin wani kudin fa, rashin lafiyan Mama fa, abinci fa, kudin
wuta fa, tasan duk abinda take tunani kenan ganin tayi dariya yasa hankali ta ya kwanta, cikin
shagwaba tace “kai Mama nine Anty Rashida” Mama ta kama haba tace “yooo ai hakane,

Mama karki kaza, karki kaza, kullum command kike bani yarnan kinga ai kinzama Anty
Rashidan” sake bushewa da dariya tayi kawai saita kwanto jikin Mama tace “Mama stoppp wlh
ni ba Anty Rashida bane, Mama ina hanaki ne fa sabida karki fadi, kinga kinada yawan ganin
jiri, kınada migraine kuma, Mama I have to take care of you gwara namiki komi ko ruwan
dazakisha na ijiye kusa dake sabida karki wahala wajen daukowa” tabe baki Mama tayi
tadagata daga jikinta tace “jeki wanka kizo kici abinci” tashi tayi ba musu ta rage kayan jikinta
tadaura zani ta kwashe kayan da lab coat da kayan Mama data cire yau dasafe tafito saida ta
fara wankesu tsaf ta shanya sannan tawuce bayi tai wanka tadawo Mama tabata abincin ci tayi
bawani sosai ba batawani cin abinci abin yabi jikinta sannan takai kwanon waje ta kuskure baki
ta dawo tahau salla kusa da Mama tana idarwa ta kwanta awajen ko 2min ba’ayiba tafara
minshari Mama tai shiru tana kallonta sai kawai tasa hannu tadauki feet dinta ta daura kan
cinyanta dudda uban tafiya akasa datakeyi bata da kaushi kafanta still looks very fine ga nails
dinta farare kal masu kyau, ahankali take massaging kafafun ayanda ta gyara kwanciya kasan
tanajin dadin tausan Mama is just looking at her babu salloli biyar dazatayi arana da zatakai
goshinta kasa dabazatama Rashida addu’a ba, banda kiyamun Layli datakeyi kullum, kullum
addu’an ta shine Allah yakawo ma diyarta karshen wahalan nan Rashida ita ke ciyar da ita,
itace cinta shanta suturanta magungunanta da komi na rayuwan su Rashida ke nema, babu
yanda zatayi ne dan batama da karfin aikin ne da itace zata fita ta nemawa diyarta abinci da
komi ba diyarta tayi ba, kullum addu’an ta is Allah ya tsare yarinyar ya tsare imaninta kar wata
rana tagaji da aikin wahalan nan tace zata shiga duniya tabi maza dan shine hanya mafi sauki
da akebi asami kudi, addu’anta koda yaushe shine Allah yabata ikon kammala wannan karatun
likitan, kowani shekara da hayya hayya take tara kudin school fees nata na last year bai musu
wani wahala ba sabida tasami aikin hotel din nan ana biyan ta dubu 50k duk wata a nan ta
tattara tabiya, fatanta shine Allah sa wannan shekaran na biyar kar kudin makarantan yayi yawa
dubada yanda aka kakkara kudin makarantu, hawaye ta share ahankali daya zubo mata bata
taba sanin dan Uwanta na jini zai iya juya mata bayaba sabida wannan cutan dudda da ranshi
da lafiyanshi, bata da kowa sai Rashida, yau shekaru ashirin da uku kenan tana wannan
wahalan tun Rashida na cikinta, ta haifo yarinya cikin wahala ta tashi cikin wahala sannan itama
tana rayuwan wahala, batabama yarta komiba sai wahala, babu wanda ya yarda ya auri
Rashida, ga yanda yar karaman yarinya ke aiki kaman namiji wata kalan uwace ita, hawaye ne
suka kara zubo mata sai kawai ta jinginar da kanyon a bango takalli sama murya chan kasa that
is very weak tace “Ya Allah idan mutuwata shine mafi alkhairi agareni dakuma y’ata, idan
mutuwata zai cireta daga cikin wahalan nan datake ciki Allah ka kasheni, ka aurar da Rashida
gidan dazata huta, karufama Rashida asiri, ka lullubeta cikin nimarka Ya Allah.
Tadade ahaka yawanci tana boyema Rashida damuwanta da dama sabida kar yarinyar takasa
karatu idan kanaso kaga Rashida ta birkice tarasa sukuni to Mama tace kaza namata ciwo tuni
yarinyar zata rude, damuwa, tunani ga constant ciwon kai koda yaushe shiyafi damunta, saisa
kullum tane asibiti BP ta is high, magungunan BP nema ke cinye musu kudi cus maganin HIV
free ake bata a clinic dinsu.



Ganin yanda bacci ya shigeta yasa bata tadataba tabarta tai baccin anan kan dadduma.

Wuraren 5 Mama ta tadata da kyar ta tashi wanda hakan daman is daily battle nasu, gyaran
gidan tayı tasa takai Mama tai wanka tai salla tazo ta dumama shinkafa da waken sannan tama
Mama tuwo sunada miya daman kafin ta shirya cikin bakin abaya da stones nashi yagama fita
tass but dudda haka ya mugun mata kyau abunka da fara tazo taje wajen wayanta taciro daga
shinkafan tasa battery ta kunna amman still yaki kawowa Mama tace “bai kawo ba?” Gyadama
Mama Kai tayi ahankali, dasauri Mama tazo karban wayan tayi tace “kodai ba chaji ne” tawuce
wajen chazanta dake bango ta makala kusan 3min bai dauka ba, ahankali Mama ta tashi tace
“bari nabaki dubu talatin din nan saiki sayo wata wayan kawai” dasauri tace “a’a Mama ki adana
talatin din nan, bari zan kaita wajen yan waya a gyaramin zasu iya gyaramin” badan Mama taso
ba dan wayan tariga tagama tsufa dukta farfashe tace “to shikenan bari na baki kudin gyaran”
sip tabude taciro wani leda ta kirgo 5k tabata karba tayi sannan tayafa gyalenta tace “bye
Mama” har zaure Mama tarakota tace “adawo lpy” dayake 9 ake fara clinic dinsu hakan yasa
taje shagon Maman kuwa tayi aiki ta karbi 2k dinta sannan tawuce shan wajen gyara takai
wayan ganin zai dauki lokaci tace “zata dawo da yamma” tashiga keke sai hospital nasu.

she’s not really doing much a consulting room take zama attached to consultant din da aka
assigning nata to him yana duba yara marasa lafiya yana tambayanta me aganinta take tunanin
is diagnosis din tafadi, kokuma yace wani investigation yakamata ayima yaron tafado sunayen
series of test da za’ayi ganin how brilliant d girl is tsohon likitan yace “i will comfortably leave the
office for you tommorow” gyadamai kai tayi dan she hardly smile outside, haka dai tagama by 1
tawuce mosque tai salla ta linke labcoat tasa a bag sannan tafito tashiga keke sai hotel.





Yau tadanyi latti sabida traffic sai around 2:30 tashigo hotel din ko kallon mutanen dake
reception da lobby gabaki daya batayi ba da sauri sauri tawuce changing room nasu kofa
tabude ahankali, ma’aikatan su tagani gudu uku a lobby suna chanza kaya da kallo suka bita
batace musu kala ba tawuce locker dinta tasa password dinta tabude, daya daga cikinsu ne taja
tsaki tace “mutum sai fadin dai, nagadai da mutum dan wani ne dabaizo hotel neman aikin
shara da wanke bayi ba, tundadai duk ansan juna menene na jijji dakai kaman diyar wasu” ?
Sauran biyun ne suka kwashe da dariya daya tace “dadine dake Hussy baki hadiye abu aciki”
parking gashinta tashiga yi da ribbon tace “eh mana kullum fuskan mutum amurtuke ana fadin
rai ana daga shoulder kaman yar shugaban kasa amman shine akazo aikin wanke bayi a hotel”
wani irin buga marfin locker Rashida tayi saida yayi kara pammm!Tajuyo tai facing Hussy direct
cikin zafin rai tace “dani kike maganganun nan?” Wani banzan shakiyin kallo Hussy tamata dan
tadade tanajin haushin Rashida wai ace ma’aikata nawa a hotel din nan yarinya bata kula kowa,
kuma kai kasauke kanka ka kulata taki kulaka back, bama wannan yafi bata mata rai ba yanda
take nuna bamatasan anyi hallita irinsu a wajen ba ko ka kulata ita bazata kulakaba sai bakin

taurin kai, jibidai yanzu datazo tasamesu ko Hi bazata iya gayamusu ba? Amman basu isheta
kallo ba, cikeda tsana tace “naga dai ban kira suna ba, amman duk wanda ya tsargu dashi
nake” wani irin kallo Rashida tamata kaman taci ubanta saikuma ta tuna nan wajen aikin tane,
da kudin aikin wajen nan zata biya school fees and other things bari kawai ta barta today is her
lucky day, sai kawai tajuya tasa hannu zata dauki uniform nata batare data kara magana ba,
cikeda neman fada Hussy tai wani shewa tace “jakan ta tsorata” juyowa Rashida tayi da mugun
zafin rai batai wata wata ba ta fizgo gaban rigan Hussy ta kifa mata mari a fuska ihu jikake
tasss! Hussy tayi ihu ta chakume gaban rigan Rashida tace ni kika mara”? Sai dambe, dukanta
Rashida take bana wasaba har gyalenta na fadi kasa bakin gashinta datai parking donut mai
bala’in kyau ya bayyana, sauran yammatan biyu na kallo sunajin dadi ganin suna dakan juna
dudda Rashida nacin uban Hussy amman kallon fada da dadi yake sukaki rabasu, ganin jini
Rashida tafasa bakin Hussy yasa daya cikinsu ta tsorata tace “baruwana kar ayi kisan kai
agabana” dasauri tabude kofa tafita da gudu dayan ma tabiyota hango Madam sukayi a lobby
tana magana da receptionist kafin sukai wajen ma sukai ihu. “Madam ana fada” daidai lokacin
Munir da Riyad na shigowa yana shaye da brown jumper yasa brown shade a idanunshi na CK
dayamai kyau sosai, arude dayan tace “Ma come oo harda blood everywhere!” ganin Riyad
yasa Madam tace “Sir welcome wai ana fada I don’t even know with who lemme handle it”
tawuce jin yasa Munir yace “let’s intervene” Munir yayi gaba Riyad yabiyosu abaya yana tafiya
one one a kasaitance, da gudu Madam ta shiga dakin tai ihu “what is this”? Ganin blood har
wuyan Hussy, Rashida bama tasan an shigo bama Munir yashigo dakin daidai Riyad na isowa
chak ya tsaya wajen kofan batare daya shigo ciki ba yana kallon su, jan Rashida Madam ta
shigayi da karfi gaske ganin yanda take dukan Hussy, sauran yan aikin suna banbare hannunta
daga jikin Hussy sunajan Hussy da bakinta yayi jina jina da jini harda hanci baya suka kwasheta
da kyar daga hannun Rashida, Madam data rike Rashida cikin tsananin bacin rai tace “fighting
awajen aiki are you too Mad? Rashida wat is this why did you beat her up like this?” Itafa idan
tana fushi bata gane kowa, kabar da hannun Madam tayi daga jikinta a haukace kaman ba
Rashida ba cus ranta yabaci tace “dalla sakeni kekuma Malama” tajuya zata closet nata cikeda
taurin kai duka ma’aikatan har Munir saida yakalli Rashida yasake kara kallonta jin abinda ta
gayama Madam, Hussy dake haki an riketa tace “Ma kinga halinta ko saisa all worker ke
cemata psycho, kolomental ce wlh, mahaukaciya ce very weird girl, shegiya yar shaye shaye,
an gayamiki bamusan asalinki bane, uwarta nada HIV!” Chak Rashida dake tafiya ta tsaya
kaman kankara, ihu Hussy tayi ganin ta tsaya chak da tafiyan datakeyi that means maganan ya
shigeta tace “ai duk munsan sirrin ta Ma, harnan akazo tundaga layinsu aka gayamana we
should be careful with her tanada HIV Mamanta ma nadashi, bamu gayamiki ba Madam sabida
karki koreta cus munsan she needs this job for her virus drugs da Mamanta, amman shine zata
kama dukana ba ban mata komiba bayan tanada wacce tafi chanchanta adaka islamically
agida, diyar fasika kawai!” Wani irin juyowa da Rashida tayi zaka dauka zakanya ce ta taho da
gudu tareta Madam tayi tace “where do you think you’re going” wani irin hankada Madam
Rashida tayi saida Munir yatare Madan da sauri dan inda tafadi wlh saita karye, Hussy na ganin
haka ta wuce da gudu tabi gefen Riyad ta gudu tafice da gudu Rashida ta taho itama tsabagen
fushi ko ganin gabanta batayi ahankali Riyad yadaga kafanshi yashigo ya tare kofan yayi
blocking nata, hakan yasa ta dago jajayen idanunta takalleshi adake cikin tsananin fushi da
zuciya tace “ka tashin mini daga hanya” Madam da Munir ya daga kyar tace “it seems da gaske

yarinyar nan is mad, call security namu and call the police” yana kallonta ta glass batare daya
dauke idanunshi daga kallonta ba yace “don’t call anybody” cikin kumfan zuciya kaman zata
fashe tai wani irin ihu tace “nace ka tashinmini daga hanya” strictly yace “you’re not going
anywhere!” Wlh ayanda zuciya ke daukanta kaman ta dagashi ta yar takeji kawai tasan batada
karfin ne, yanda hannayenta ke rawa da jikinta yasa kawai ta juya fuuuu tawuce dan bence din
dake wajen ta zauna tai folding hands dinta akirji duk yan dakin kallonta suke she’s shaking, sai
alokacin yakalli Munir yace “get first aid box go and attend to that girl, yakalli Madam da sauran
yar aikin dake kallon Rashida da mamaki kaman yau suka fara ganinta yace “ku wuce kutafi”
cikeda mamaki Madam tana kallonta tace “this is your last day here” duk wucewa sukayi suka
fita yarage Riyad kadai dake tsaye awajen kofan dan kwalinta dake kasan dakin ya kalla
ahankali ya shigo ya duka gently yadauka dusting nashi yayi sannan yataho inda take zaune
kanta akasa tayi folding hands a kirji ahankali ya yafa gyalen akanta.



Dago kanta tayi tazubamai jajayen rinannun idanunta yanda yara masu taurin kan nan sukeyi
tace “ina ruwanka dani? Wayace katabamin gyale na? Wat is your business with me? Nabar
aikin naku dagayau nima, bazan kara aiki inda wata ta kira Mamana…….” Saita kasa karasa
maganan sabida yanda abin ya tsayamata awuya saikawai tajuya mai baya da sauri takai
hannunta ta sharce hawayen daya soma zubomata, data sharce da wani yasake zubowa sunki
tsayawa yakai almost 1min yana kallonta sannan yajuya ahankali yafice tareda maida kofan
yarufe kaman jira take fashewa tayi da kuka haryafara tafiya yajuyo sautin kukanta chak ya
tsaya har shesheka takeyi yakai kusan 1min ahaka sannan yabar wajen, kusan 5min tayi tana
kuka sannan ta goge fuskanta tass ta tashi tawuce drawer ta ta shiga kwashe yan small small
tarakacen datake dashi awajen uniform nasu tabar musu sannan ta goya jakan abaya ta tsaya
takara goge fuskanta tass bazaka gane tai kuka ba unless u look into her eyes tafito sai kallonta
ake a reception amman ko kallonsu batayiba ta wuce tafita ta tafiyanta gida.


JOIN MY WATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/Ckm5Bo7CcqR1NYkgT0HEvR
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI


✍M SHAKUR


EPISODE 1️⃣4️⃣

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/ChfonTBUkdg8q2KIWCSk46 Assalamu alaikum. my name is
Faredah Haruna Mamuda the founder of REEDAH'S EMPIRE, i base in kaduna state we are
your number one home appliances no (SCAM ZONE) we are 100% legit all our items are from

Lagos,Egypt,Turkey and cortonor we do delivery nationwide thanks u'll


Wuraren 3 Mama na zaune tsakar gida tana gyaran shinkafa ta kunna radio ta ijiye gefenta
saman tabarma tana sauraro taji an turo kofa an shigo hakan yasa ta kafa ido taga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login