Showing 24001 words to 27000 words out of 69832 words

Chapter 9 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

946

damuwa Mama tace “tunani nake wakika biyo da temper nan naki
Rashida? Kap dangina babu mai fada masifa, fushi, taurin kai da kafiya irin naki, to maybe sai
dangin mahaifinki dan bangama saninasu ba abinki da yan Sarauta sunada yawa” tamau
Rashida ta daure fuska sai kawai ta tashi tace “Mama inaga harda kallan son da mutumin nan
yaga kinmai saisa ya wulakantaki, baki magana baki kawoshi ba after how many years Mama
you still remember mutanen da mutumin that hurt and destroyed life dinki” kallonta Mama tayi
tace “babanki yamin kirki abaya dudda ya wulakantanin amman hakan bazaisa na manta
kirkinshi ba” ayanda fuskan Rashida yayi da ace zata iya dukan Mama datayi akufule tace
“Allah karya dauramin son wani haka Mama cus inaaa! Mama you have no idea yanda na tsani
mutumin nan and duk randa na sami opportunity wlh I will hurt him sama da yanda yayi hurting
naki, bari nagama makaranta nazama wani abu saizan ya wulakantamini uwa!” Mama zata kara
magana Rashida ta tashi da sauri kawai tashige ciki Mama tai murmushi kawai tareda sauke
ijiyan zuciya.
***



Around 7 na safe yadawo daga masallaci wanda haka yakeyi daman before yayi bacci yatashi
10 ya shirya yaje fada by 11. Bacci yakoma adakin daya kwana ya kwanta, harya fara bacci yaji
hayaniya sama sama da alamun kuka, dan bude idanunshi kadan yayi trying yaji da gaske anan
side yaji kuka, knocking kofar dakin dayake ciki akayi saikuma yaji muryan Mom afadace tace
“open this door Riyad nasan kana jina” tashi yayi ahankali ya kunna wutan dakin yana mamakin
meya faru, yadauki jallabiya ya zura dan dagashi sai short yayi wajen kofan ahankali yabude

kofan Mami yagani ranta abace saikuma ya hango Haleema duke tsakiyan corridor tana kuka
sosai kaman an mata mutu har yanzu rigan baccin jiya ne ajikinta, yadai daure yace “good
morning Mom…” hannu Mom tadagamai ranta amasifan bace tace “hold greeting naka I don’t
want it Riyad” confusingly yake kallon Mom saikuma yakalli Haleema dake kuka sosai trying to
ask meya sameta kawai yaga Mom ta mikamai hannunta da karamin dankunne ke kai tace “a
ina kasamo wannan Riyad”? Kallon dan kunnen yayi harga Allah baigane dan kunnen bama
hakan yasa yace “Mom wat is this”? Cikin fushi sosai Mom tarufeshi da fada tace “nikake
tambaya wat is this? Matanka ta tsinci dan kunnen mace a aljihun rigan kayan dakasa jiya
kadawo very late kusan to 12 nadare” sai alokacin yama gane dan kunnen nan dayatake ne
akasa a office nashi dasauri yawani ma Haleema dake kuka kallo kai tsaye yace “kayana kika
duba kika bincika is that abinda kikeyi anytime kikazo this side?” Mami tace “look at me here
nine nazo nike magana dakai not Haleema” authoritatively tace “tell me, me dan kunnen mata
keyi a aljihun ka wanda bana matarka ba, mata kake bi yanzu Riyad? Me ka nema wajen
Haleematu karasa? Dan kunnen waye tell me now”? Tunda yake baitaba jin Mom ta batamai rai
irin na yau ba kanshi ya nuna yanama Mom wani irin kallo yace “Mom I’m your Son, kin sanni
sama da kowa a duniyan nan, Mom yanzu akazo aka cemiki ina neman mata bazaki iya
shedana ba? Do I look like ina neman Mata? Ni?” Harga Allah tun Riyad na yaro bai taso dason
Mata ba, ko kallonsu bayayi hasalima kunya suke bashi amman dai cikeda kafiya dason
nunama Haleema she own her Son tace “how do you want me to trust me bayan matarka taga
dan kunne akayan dakasa jiya and kadawo very late eh? Look at the way the poor thing is
crying” tanuna Haleematu dake wani irin mummunan kuka tace “ko kadan banso kayi hurting
yarinyar nan cus she’s a good gurl, tadaukeni mahaifiyarta, Babanta yataka rawan gani sosai
wajen zamanka sarki, he’s the one blocking all kulle kulle da akeyi yanzu daka zama sarki” “did I
ask him to do anything for me?” Riyad yayi maganan da karfi da saida Mom tabude idanunta
cikeda mamaki ta kalleshi, yau Riyad ya daga mata murya haka? Agaban matarshi, cikeda
mamaki tace “Nikake dayama Murya Riyad?” Cikin fushi sosai yace “Mom abinda kikemin is
totally wrong, sabida Haleema tace inabin mata saikizo ki yarda da maganan ta kinamin fada
agabanta baki san danki ba? You’re not allowing me to be the man in my marriage, nagaji I can’t
continue with this marriage because of Babanta kikasa ya nemamin sarki dagayau…….” da
sauri Haleematu ta taso tana kuka sosai afirgice kawai ta zube agabanshi tarike kafanshi tace
“dan Allah kayakuri wlh nasan bakabin mata bansan menakeyi ba danaga dan kunnen saisa
nakira Mom” fizge kafanshi yayi yakalli Mom yace “dagayau tell her bata babu this side I forbid
her from coming to my side, duk sanda nake bukatanta zan nemeta!” Rushewa da kuka sosai
Haleematou tayi takama kafan Mom tace “Mom do something, dan Allah kimai magana ya
yakuri, bazan karaba”
Yakalli yanda Haleema ke rokon Mom ya cije baki ya kalli Mom din dake kallonshi mamaki
yagama kasheta yace “and for your question Mom” sai kawai yadaga mata kafanshi yanuna
mata tafin kafan inda dan kunnen ya shiga yace “nataka dan kunnen nan akasa ya shigan min
kafa, na cire zan yarda ganin ina cikin premises kar wani yaje yataka yasa nasa a pocket with
the hope nafito i will trash it but I forgot” ya maida kafanshi ya ijiye yace “I don’t want the sarauta
ki nemo wani kibashi, I need a break” yana maganan yabi ta gefensu yawuce dagashi sai
jallabiyan jikinshi yanda ranshi yabaci ko waya bai daukaba Mom tajuya tabiyoshi dasauri ganin
ahaka zai fita tace “Riyad, Riyad” hannu yasa yabude kofa azuciye yafito key motar compound

nashi na wajen Munir hakan yasa yayi gate yafice fadawa zasumai kirari ya buga musu tsawa
“leave me alone!” Kawai yawuce fuuuuuuuu shi kadai yana tafiya a bala’in zuciye kawai yawuce
side din su Munir bude kofa yayi azuciye key daya hango akan table yawuce kaman zaki
yadauka daidai Ammi na lekowa daga kitchen ganin shi yadau key dinta ranshi abace yasa tai
shiru daidai yabude kofa yafice parking space nasu yaje yana danna key wani jeep yayi kara
motar Ammi ce direct yawuce yabude ya shiga yanda ya danna horn zakasan ba lafiya aka
budemai key yawuce yafita.


Kusan yaune rana na farko da Mom take ganin serious fushin Riyad haka, and for him to
provoke like this that means abinda yafadi gaskiya ne babu matan dayake nema, hankalinta
yatashi sosai, wayanta dake hannunta ta daga zata kirashi saitaga wayanshi akan gado kawai
cike da takaici takalli Haleema dake kuka tace “you are not sure of something akan wani dalili
da rashin hankali zaki tafka shirmen nan eh Halimatu? Jibi abinda kika jawo yanzu? Bakisan
idan mai hakuri yayi fushi yafi zama worst ba? Jibi yanda yafita ko wanka baiyiba bai dauki
wayanshi ba tsabagen bacinrai, sabida kinga dan kunne in this pocket mesa zaki assuming
mata yakebi”? Cikin kuka Halimatu tace “Mami kishi ne yarufeni I can’t share mijina with
anybody wlh, kiyakuri Mom kiyafemin dan Allah” dan tsukin takaici Mom tayi tace “naji is not
your fault nima daban biyemiki ba nasan waye Riyad, yana tashen samartaka ma beyi neman
mata ba sai yanzu, tashi kitafi side naki zansa azo agyara dakinshi lemme handle the situation”
Kama hannun Mom Haleema tayi tace “Mom kinsan baya tsallake maganan ki, please kice yayi
hakuri karyayi fushi dani koya chanzamin fuska” “naji tafi” Alkyabban tadauko tasaka tawuce
tafita daga side din, Mom itama tafito ta tafi sauro da idanu takira babban bafaden gate din
yataho da sauri ya zube yace “an gaida Mai Babban daki matan da darajanta yakai…..” Mom
bata bari ya karasa maganan ba cikin whispering yace “inada aiki for you Sarki baida lafiya
bazai iya fitowa ba shine abinda zaka sanar kaida yaranka bansan kowa yasan Sarki bayanan,
zakaga babban sakon tukuici kai haka” Gyadamata Kai yayi yace “angama me Babban daki”
juyawa Mom tayi takoma ciki takira Dr su kaman da gaske, kazo gida by 10 duba Riyad”.
**



1 dot tagama da hospital wanda a outpatient department group nasu yake tareda wani
consultant na pediatrics, she’s happy sosai yanda itada Bilal da crew dinsa na yanmata basa
group daya, salla tawuce tafarayi a masallaci sannan ta linke lab coat nata tasa a bagpack
tawuce tafito daga mosque din tagoya jakan abaya tasa takalmi tafito Keke napep ta tare zuwa
hotel, sauka tayi tabiyashi ta shiga ciki ko kallon receptionist wajen batayiba as usual changing
room tawuce tashiga cire kayan jikinta tayi ta saka dark blue dogon wandon da light blue shirt
mai botur tundaga kasan rigan har sama wajajen wuya, farin fatan jikinta ya haska kayan sosai
kaman dan ita akai uniform din, clean baby hijab nata farı ta dauka ta saka wanda yarufe mata
kirji sannan tasa takalminta, fitowa tayi zuwa office din Madam tai knocking akace mata ta
shigo, shiga tayi tace “good afternoon” “Afternoon Rashida oya ga card din jeki goge office din
maza maza, ki dauko kayan gyaran office din a store” karban katin tayi tace “okay” fitowa tayi

tawuce store tahada duka abubuwan dazatai amfani dashi sannan tawuce elevator zuwa 5th
floor tayi corridor office din, manna katin tayi kofan yayi kara sannan ta tura kofan ahankali
hakanan kawai taji gabanta yafadi ga office din yayi mahaukacin sanyi kaman kankara AC a
kunne, ahankali ta shiga tareda maida kofan tarufe cikin yar muryanta tace “wayyoo sanyi”
dasauri tawuce wajen kashe AC ta kashe tanabin office din da kallo alamun an shigo dama jiya
ance Oga yazo lokacin da zata tafi saisa ya shigo office dinshi kenan, a aljihunta tasa hannu ta
zaro yar wayanta ta makala earpiece din a kunnenta ta danna wakan Araina Grande mai suna
Into You, sannan takoma wajen kofa tadauko kayan ayyukanta tawuce bayi ta tara ruwa tafara
bin wakan tafito tadauki handglove black na aiki tazura a hannu tadauki brush din share kura
tafara aikinta tana waka……





Ko manager shi batasan yana nan ba babu wanda yasani sabida yanda yazo da jallabiya he
looks like normal guest yawuce direct elevator, tunda yazo yake kwance dazun nan ne ma ya
iya tashi yayi zuhur yakoma ya kwanta though ba bacci yakeba but ya lumshe idanu kawai
having moment of peace, tunda aka bude kofan office din aka shigo yaji, sai chan kuma yaji
murya mai bala’in zaki tace wayyoo sanyi, saikuma ga same muryan tafara waka tana aikace
aikace dake making sound, shi kadai yace “is she some sort of DJ ko wata Artist?” Cus
muryanta dadi bata missing ko harafi daya, kaman tana performing a stage, chan kuma kawai
saiya tashi zaune sabida ta kunna vacuum cleaner bayajin muryan nata da kyau kaman da,
karan vacuum cleaner yafi muryanta kara, ahankali yataso yataka zuwa wajen kofan hannunshi
yakai ahankali zai kama handle na kofan yabude kofan sai kawai yaji yafasa cus baimason
aganshi amman kuma saiya tsaya chak awajen yanajin the way she’s singing din cus takashe
machine din yanzu tana bin wakan Into your arms na Witty Lowry, God! Her voice is captivating
kawai yaji yakasa matsawa.



Daukan bucket na mop din tayi a hannu tarike vacuum cleaner shima a dayan hannun ta tako
zuwa gaban dakin sabida tagama da office sai uwardakan before wanke bayuka, juyar da
fusknata tayi tana ijiye vacuum cleaner akasa still holding on to the bucket na mop takai free
hand din tabude kofan ahankali fuskanta na kallon side din tana rera waka tadawo da hannun
tana kokarin daukan vacuum cleaner back danta shigo tunda tabude kofan…



Tunda tabude kofan yayi setting eyes nashi chak akanta yana kallonta tundaga kan pink crocs
din dake kafanta dayay finding nasu so funny, dogon dark blue wandonta dabai kamata ba at all
kusan ma yaso yamata yawa ya kalla, zuwa navy blue rigan dashi ma bai kamata ba zuwa farin
hijab din jikinta that looks extremely neat da side na face nata da he could see sajenta da dan

gashinta baki sidik daya leko, daidai tadaga vacuum cleaner ta juyo da kanta kawai taga dogon
farin mutum da farin jallabiya ajikinshi ya tsaya chak kaman gunki yazuba hannu a aljihun
jallabiyan yana kallonta batada tsoro but saida ta tsorata tayi baya da sauri ganin namiji hakan
yasa cord (wayan) vacuum cleaner ya kwasheta jikake timmm tafadi akasa ruwa mopping din
hannunta ya kware mata daga ciki zuwa wando, zaro ido tayi atsorace tace “wayyoo Allah na”
tai maza maza ta tashi tama rasa mezatayi arude tace “I am sorry” ganin kaman ba ghost bane
maybe shine me hotel din takai hannu tana kakkabe jikinta da cinyanta da sauri chan ta lura da
aljihuta ajike dasauri tace “Innalillahi wayana” hannu tasa a aljihun taciro wayanta ta cisge
earpiece din tashiga tattaba wayan baya haske tace “innalillahi Innalillahi” bude wayan tayi da
sauri taciro battery ta huhure wayan sannan tawuce table dagudu ta ijiye wayan awajen danya
bushe sannan tajuyo tama kasa kallonshi taduka tana daukan mop tace “sorry i will clean
everything yanzu” chak yake kallonta dan yana ganin full fuskanta ya ganeta the girl from the
airport! The feisty gurl! Yarinyar daya dade yana nema to reward her for saving his life….

GOGAN NAMU BATA GANESHI BA? KODAI IDONANE
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI


✍M SHAKUR


EPISODE 1️⃣2️⃣
Bucket na moping din tadauka da gudu tawuce bathroom na office din ta tara wani ruwa ta taho
da sauri jikinta duk rawa yake zata fara mopping ruwan kunfan kasan jikinta duk yana tsiyaya
kaman daga sama taji sassanyar muryanshi yace “stop!” Dasauri tadago manyan fararen
idanunta ta kalleshi, hada ido tasakeyi dashi for the second time da sauri ta dauke kai aranta
tace “sai shegen kallon mata mtsww” fitowa daga dakin yayi ahankali, cikeda tsantsan kulawa
yace “step aside” dasauri ta matsa gefe ga mamakinta sai kawai taga ya tsugunna yadauki
bucket na mop din ya matsar gefe da vacuum cleaner, yashiga nannade carpet din na tsakiyan
office din yadaga yadauka yawuce wajen kofa yabude yafitar dashi ya ijiye bakin kofan nan
yashigo yasameta tana kokari fara mopping wajen cikin kwantacciyan murya yace “go and
change” dan kallon daga kasan riganta har zuwa crocs na kafanta tayi dake tsiyaya tace “karka
damu I can do it banda wani uniform, zai bushe ai” yanda take kallon jikinta tana maganan yake
kallo with her voice dake piercing kunnuwa sabida dadinsu, calmly yace “go take them off kisa
kayan gida” kawai dan tasan office din mai hotel dinnan ne, sannan shita gani cikin offive din so
dole tai assuming shine mai hotel din banda haka data gayamai me ruwanshi da yanda zatai
aikinta yabarta tayi abinta tagama mana ha’a, sai gwadamata yanda zatayi yake, sai kawai
tawuce kofa batare datace komiba tana zare handglove din, tabude kofa tafita yabita da kallo
kafin kawai yazaga yazauna kan kujeranshi na office yayi shiru.



Changing room dinsu tawuce ta chanza kayan tasaka doguwan rigan atampanta brown ne da

milk just straight gown babu wani ado ajiki, dan kwalin kayan ta daura aka sannan ta zari
gyalenta brown ta yafa daya kara haskata hasken fatanta yayi bau aciki, ta kwashi kayan
bayinsu na staff ta shiga ta dauraye kayan ta wanke cinyanta da kafanta da takalmin tama
wanke fuskanta kawai gaba daya hakan yasa tai wani haske mai kyau dinnan na bayan ka
wanke fuska, tawuce baya ta shanya kayan sannan tafito tana tafiya da sauri sauri sabida
tasamu tai sauran ayyukanta tabar office dinshi, tashiga elevator zuwa 5th floor tawuce office
din kofan office din ta bude ahankali tashigo tunda ta bude office din ya kafamata ido, the first
time daya ganta uniform ne jikinta, yauma haka yanzu ne yafara ganinta da kayan gida, kasa
dauke idanunshi yayi akanta, ta taho direct cikin office din batare data kalli wajen dayake bama,
zubamata idanu yayi yana kara tantancewa itace dai wannan mara kunyan ta airport, bai cika
manta face ba idan yasan mutum, hade fuska tayi batacemai komiba dan jikinta yabata kallonta
ake, tadauki moping stick din tafara moping wajen ahankali tana gamawa tadan juyo ta kalleshi
karaf suka dake hada ido dauke kai tayi tace “zan iya shiga dakin na gyara”? “Yes” ya amsa
calmly hakan yasa kwai ta shiga ta sharo tai arranging bed din dataga ba’a gyare ba, ta wanke
bathroom din, kusan 5min tayi sannan tafito tawuce bayin nan office ta gyara shi in 3min sannan
tafito tai arranging abubuwan datai amfani dasu tafita dasu waje sannan tadawo tazo gaban
table dinshi tasa hannunta tana kwasan wayanta na wajen yanabin white long fingers dinta da
kallo that looks so feminine, ahankali yace “wat is your name?” Batare data kalleshi ba tace
“Rashida Almustapha” tana maganan tajuya dasauri zata wuce kaman daga sama yace “is your
back hurting you naga kin fadi tabaya”? “No it’s not” tabashi amsa atakaice tacigaba da tafiya da
sauri bataso yayi wani maganan kuma, hartakai kofa tasa hannu zata bude yace
“Rasheedahhh!” Wlh batasan meya faru ba hakanan gabanta yafadi chak ta tsaya takasa motsi
sabida yanda yakira sunanta, kawai she felt something strange in her dayasa dasauri tajuyo ta
kalleshi sake hada ido tayi dashi saikuma ta dauke kai tace “na’am” kusan 30secs yayi shiru
saichan ahankali yace “Thank You” Da sauri ta kalleshi zatace thank you for wat saikuma ta
tuna maybe na gyaran ne hakan yasa ta gyadamai kai kawai tama kasa magana sabida yanda
heart nata yafara racing tajuya tafito dasauri ta kwashi komi tawuce kasa ta maida komi store
tawuce taje dakunan dazata chanza duvet nasu takai washing machine takai sannan tahau
gyara Allah yasota bata hadu da Madam ba balle ta tambayeta ya akayi tasa kayan gida ba.



Wuraren 6 tafito daga hotel din sai fama take da wayanta dayaki kunnuwa sai cire battery tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login