Showing 6001 words to 9000 words out of 69832 words

Chapter 3 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

947

duka duka bazata wuce 40 ba but
she looks kaman wacce ta tsufa, tana zaune kan dadduma tanajan charbi, ijiye kayan hannunta
Rasheeda tayi saikuma tai tagumi tana leka fuskan Mama tace “Mama kiyi sauri kigama kimin
sannu da zuwa niii” tafadi a shagwabe, hannu Ammi tasa ta shafe addu’an datakeyi sannan

tajuyo kawai saita kama kunnenta ta saman hijabin jikinta tace “dan kaniyanki ba alwala
yakamata kiyo ba kizo kiyi salla ba” dariya sosai tayi tana yarfe hannu tace “wayyooo kunnina
Mama zai cire” sakin kunnin Mama tayi tana murmushi looking so happy tace “imaza to jekiyo
alwala kafin lokacin magrib yafice baki salla ba” tashi tayi tafito tsakar gida alwala tayi tadawo
tai salla kusada Mama sannan tadauki jakanta tabude taciro kudin tasa a hannun Mama tace
“Maman Miwa tabiyani, hotel din nan gobe suma zasu biyani kuma manager tace nakawo
zanen tagani idan na iya sosai zasu saya” karban kudin Mama tayi tana kallo tana murmushi
Rashida tashiga fito da abincin tace “nabiya nabawa Abdul kudinshi Mama ga abinci Maman
Miwa tace nakawo miki” bubbude komi tayi ta tashi tafita dasauri tadauko ruwa a bowl tadawo
tazauna takama hannun Ammi tasa aruwan tace “wanke hannun muci” wanke hannunta Ammi
tayi ta ijiye kudin agefe ta gutsuro tuwon instead takai bakinta bakin Rasheeda takai dasauri
Rasheeda tace “Ammi ke kici” ahankali tace “ni naci abinci namana shinkafa, keko nasan tun
safe bakici abinci ba banda karin dakikayi ko kinci wani abu”? Hadiye tuwon bakinta tayı tana
fikifiki da ido most of the time idan tana aiki mantawa da abinci take, hararanta Ammi tayi tace
“bude bakin, kidena wasa da abinci kinji Doctor” gyadama Ammi kai tayi tana murmushi Ammi
nasa mata tuwo abaki tace “ko biscuit ne buy and eat kinji” sake gyadamata kai tayi, haka Ammi
tadinga feeding nata kuma sosai taci ita bama tasan takusan cinye tuwon ba saida takalli
takeaway dasauri tace “Ammi nacinye miki tuwon” murmushi tayi tace “haka nakeso dama
Doctor” tass tacinye tuwon Ammi kuma taci shinkafan ba sosai ba dan batajin yunwa, sannan ta
tashi taje tayo wanka da alwala tareda Mama sukai salla ta shiga tattara yan kwanukan zata
wanke Mama tace “kibarshi jekiyi zanen ki zanyi wanke wanken” dasauri tace “Mama ni kidaina
aiki, bayawa yanzun nan zanyi nagama zanyi zanen” kafin Mama tai magana tafice daga dakin
biyota Mama tayi dudda haka tana wankewa Mama na dauraye wa suka gama suka dawo daki
tayata Mama tayi ta kwaso board na zanen da colors nata da pen ta zuzzuba tafara zanen
kome takeso Mama na mikamata suna cikinyi aka dauke wuta torch light Mama tadauka ta
kunna Rasheeda tai murmushi tacigaba dayi sai wajajen 12 tagama tabarsu su bushe gobe
zata sasu acikin frame, zama tayi anan danta huta kafin suje su kwanta sai bacci itakuma
Mama na tattare brushes din tana dauraye mata su aruwa, munsharin ta da Mama taji yasa
tajuyo takalleta ganin yanda take baccin azaune kanta na lilo.


KINASON MAGANA DANI M SHAKUR??? CLICK ON THIS LINK AND CHAT ME UP
wa.me/+2347012181461
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI



✍M SHAKUR

JOIN INTIMACY CLASS TODAY WITH JUST 5k MY PEOPLE LEMME TEACH YOU YANDA
AKE HAVING AMAZING LOVE MAKING DA YALLABAI! YANDA AKE ENJOYING SEX! YANDA
ZAKI TASHI KANSA KIKUMA KWANTAR MAI DA HANKALI.
YANDA ZAKI KWANKWANCE KAN MEGIDA DA MAGANAN BANZA

I AM THE BEST IDAN DAI HARKAN KARATUN NAN NE A HAUSANCE�

Kimin magana a watsapp +2347012181461






EPISODE 4️⃣


She just wished all this ayyukan wahalan da suffering da yarinyarta yar karama keyi just to take
care of her itane keyi mutane bazasu gane rahama ne Allah yamaka lafiya sannan yabaka
karfin nema ba gashi tana neman wannan karfin ita tafita tayo aiki ta kula da diyarta daya tak a
duniya tarasa, Rasheeda ce zuwa ayyukan shara da wanke bayuka, da wanke wanke just to get
paid suci abinci ga school duk ita kadai dan yanzu ma suna hutun school, yarinyarta batasan
menene dadin rayuwa ba tunda ta taso sai wahala, Rashida doesn’t deserve to be born like this,
ta zaman ma yarta bakin tabo arayuwanta waye zai taba auren Rashida yanzu? Ko anzo ma
gulman yan anguwan nan koransu suke, babu kalan sherin da ba’a musu, kowace budurwa irin
Rashida nada kawaye ita batadashi kota fara kawance iyayen yaran zasu raba abotan sabida
ansan diyar mai HIv ce, yar fasika ne gantalalliya dan haka babu iyayen dakeson yaransu suyi
mu’amala da yarta, hawaye masu dumi ne suka gangaro daga idanunta dasauri takai hannunta
ta share fuskan tass tareda sauke ijiyan zuciya ahankali tace “Allah na yarda ka kasheni da
ciwon nan, Kama karomin cuta daban daban duk na yarda, amman Ya Allah kabama diyata
farin ciki arayuwanta, Ya Allah ka kawomata karshen wahalan nan, Ya Allah idan mutuwata zai
zamto abinda zaisa Rashidana tadena aikin wahalhalun nan just to take care of me Ya Allah ka
dauki raina dudda banson na barta, Ya Allah spare my daughter this harsh way of living and
take me instead” tasake share hawayen dasuka zubomata sai kawai tadaura kasan rigan
atampanta kan fuskanta tai shiru takai 2min ahaka sannan ta mike taje inda take tallabota tayi
tace “Raudah oya muje ki kwanta” ina batamasan anayiba baccin yayi nisa gajiya kuma kesata
baccin kaman tamutun nan, kamata Mama tasakeyi tace “tashi muje kinji Rish-rish din Mama”
Mama tai maganan tana dagata da kyar ina bamata iya tafiya kaman matatta, kakkamata Mama
tayi tasata ajikinta tana tafiya da ita ahankali tanajan kafa kaman irin wacce tasha giya tai tatil
din nan, uwar dakin babu komi banda wata yar katifa datake a gyare akasa sai kuma manyan
ganamasgo guda biyu na kaya sai dan rio na kayan kwalliya da wasu kodaddun hodon makeup
da gorunan turaren humra suke ciki saikuma wata benci haka da littafai ne cike na school akai
saikuma lab coat da aka makala a nail na bango jikin aljihun an rubuta Dr Rash ajiki Mama ta
kwantar da ita ahankali.


Karfe 4:30 daidai tabude idanunta adduan tashi daga bacci tayi sannan takalli Mama wacce

taganta kan dadduma idan da sabo ta saba agurguje ta tashi waje taje tahura wuta tadaura
ruwan wanka sannan tashare tsakar gidan taje ta wanko bayi ta watsa ruwan sanyi ita tafito tai
alwala tazo ruwan yayi zafi tahadama Mama a bucket tadawo daki dan kaita bayin dan
kafafunta na bala’in damunta tace “Mama muje kiyi wanka” tana rike da Mama har bayi Mama
tace “karki jirani jeki salla” batai musu ba salla taje tayi sannan tafito ta daura tuwo a wuta ta
kwashe kayan da Mama tasa sharp sharp ta wanke ta shanya tasake wucewa hanyar bayi
tadawo da Mama dakin dahar ta gyara tafita waje takarasa tuwo tai miya tazuba komi a kula
takawo daki sannan ta shirya cikin wani dogon rigan abaya baki wanda stones din duk sun
ciccire tadau gyalen zata yana kenan ta tuna jiya saitahau dariya Mama dake shafa mai tace
“ke lafiyanki kike dariya ke kadai?” Dasauri tajuyo ta taho wajen Mama tace “Mama wani dan
gayun mutumi nasa a bola na zuzzubamai shara bakiga yanda yake makyarkyata ba kaman da
zinare aka yishi ba kasa ba” yanda take murmushi tana dariya yasa Mama tace “wa kikasa a
bola Doctor?” Dan tsagaita murmushin tayi tabama Mama labari kunnenta Mama taja tace
“Rauda wai mesa bakiji ne inda sun kasheki ke fa dakike musu rashin kunya ina kikeso nasa
raina why mesa you are always putting yourself in trouble ne eh? Mesa bakiji wai kin dauka
wani karfi gareki wai sabida wani baitaba chasaki ba ko” kaman zatai kuka tace “Mama yakuri to
kisaki kunnena” sakejan kunnenta Mama tayi dudda bada karfi sosai ba tace “saina cireshi
duka, wai mesa bakiji eh? Why wat if wani abu yasameki?” Ganin yanda takeyi da fuska kaman
zatai kuka alamun jan kunnen namata zafi yasa Mama tasaki kunnen ahankali saikuma takama
kafadanta cikeda damuwa sosai tace “Doctor kinason duk idan kin fita yanzu hankalina yadena
kwanciya ne?” Dasauri ta girgizakai, ahankali Mama tace “to yimin alkawari u will not put kanki
in any trouble again” murmushi tayi tace “I promise Mama bazan karaba” ijiyan zuciya kawai
Mama tasauke dan tasan is impossible cus Rashida and trouble are besties, tashi tayi tawuce
takarasa shiryawa ta yana gyalen akanshi ta kwashi uniforms nata tasa ajakan ta sannan
tazauna tahada zanen tasaka musu frames Mama sai kallonta take kawai saida tagama tass
sanan tazo kusada Mama lokacin 7 daidai tace “Mama maganin safe” tadauko magani bama
Mama maganin tayi sannan tacire yar wayanta daga chaji tadauki earpiece dinta tace “Mama
bari inje” cikin kudin data kawo jiya Mama tazare 1k tace “ga wannan kihau abin hawa kidena
tafiya da kafa hotel din nan da nisa” dasauri ta girgiza kai tace “Mama ki ijiye duk nazuwa asibiti
ne next week ni dakafata zan taka ai ba nisa ko ciwon kai kikaji ki kirani zanbar kome nakeyi na
dawo zanyi aiki a hotel har karfe daya biyu yau ba airport zandaiga alert, sai karfe 4 ina wajen
Maman miwa bye Mama na” dasauri Mama tace “to baxaki daure ko Lipton kisha ba tunda baki
iyacin abinci dasafe” dukowa tayi ta rungume Mama tace “Mama zanyi latti ne nakai zansha a
hotel din ai ana bamu coffee da biscuit bye Mama kinji” ta shafa fuskan Mama tana kallonta
saikuma ta manna ma Mama kiss a goshi tace “Mama kinyi kyau wlh atampan nan zaki bani ita”
dan maketa kadan Mama tayi tace “ba Dr yace kidena min irin abubuwan nan ba saina
shafamiki ciwo” haderai Rashida tayi sosai tai sauri zata tashi hakan yasa Mama tarike mata
hannu tace “zo to fushi kikayi banso kibar gida da fushi yakuri bazan kara miki maganan ba”
hawaye idanunta suka tara saikuma tahadiye hawayen saikawai ta rungume Mama tsamtsam
kaman yar yarinya tace “Mama ko duka ciwon duniya kikedashi ni zan fiso su dawo kaina ke
naganki lafiyanki kalau, Mama kome kika dawo ko menene ajikinki you will always be Mama na
nikadai, koda zan samu I don’t mind ni ko mutuwa yazo nafiso mu mutu tare ma” dasauri Mama
ta daki bakinta tace “bazaki mutu yanzu ba sainaga yaranki jikokina” turobaki tayi tasaki Mama

tace “Mama ni banson maganan nan I hate maza to the core bazan taba aure ba, dana auri miji
irin wanda kika aura danni ba Babana bane gwara na mutu ahaka banyi aure ba,
matsiyac…….” “Doctor!” Mama takirata azafaffe hakan yasa tai shiru tadauke fuska, ahankali
Mama tace “karki kuskura ki zagi Babanki” kallon Mama tayi irin why are you still protecting him
sai kawai tayi hanyar fita daga uwar dakan cikin sanyin murya Mama tace “he’s your father”
jakanta tadauka ta goya tace “Mama he’s not my father ko sunanshi dakikasa nake amfani da
dan babu yanda zanyi ba, Mama na tsani mutumin nan and I hate all men naduniya, nidai
mudaina maganan banmasan maisa kikemin maganan maza ba to mezasumin? Akwai wani
hanyar neman kudi daban iyaba? Mama namafi mazan karfi laaaa nama manta ban daga karfe
ba yau” tajuya dasauri zata fita daga dakin Mama tace “kika daga karfen nan saina mammakeki
wlh waike namiji ne yau naga bala’i a hannun yarinyar nan” dariya Rashida tayi ta tsaya daga
bakin kofa tana kallon Mama tace “Mama bakiga saisa babu me kawomin raini ba sabida ansan
inada karfi Mama dan Allah kibari nadaga kinji Mama 2mins” da hannu Mama ta nunata tace
“wlh zanci kaniyanki, sokike ki mummurde ki koma namiji? Wannan harkan karfen wlh bazan
yarda dashi ba jira nake rannan lahadi idan Lawali yazo ince yatafi dashi” dasauri Rauda tace
“wlh Mama karki bayarmin da abuna da kyar nasamu mutanen garejin nan suka saidamin da
abin nan dubu uku” baki Mama tabude tace “yanzu bakisa dubu uku kin sayi sutura ba sai karfe
kikaje kika saya agareji tafi aiki ki dawo zaki gamu dani wlh agidan nan” dariya tayi sosai
saikuma ta buga kafa tace “to kice bazaki bayarba wlh Mama kowa kikaba sai naje na karbo
abuna kota katanga ne saina haura” haba Mama tarike tace “to wani daban zan bamawa ba
Lawal ba sai inga idan tsafi zakiyi ki gane wana bamawa, wuce kitafi” tace “bye Mama na,
Mamana kyakkyawa mai gashi, Mama haryau gashina yaki kamo naki narasa maisa” kaman jira
Mama take tace “sabida kin soma daga karfe ne saisa” dariya Rashida tayi harda kama ciki tace
“laaaa Mama wlh wannan zuki tamallo ne” baki Mama tasaki tace “ni Mamanki ke karya
Doctor”? Dan sosa kai tayi kaman mara gaskiya tace “uhnnn” kwapa Mama tayi tace “wuce
kitafi zan gamu dake kika dawo ai anan zakizo ki sameni” nokekai tayi tana danne dariya
tawuce tafita Mama itama tai murmushi ta daga murya daganan daki tace “ayi addu’a dai kafin
afita daga gida Allah bada sa’a” tsayawa tayi tai addu’a sannan tabude kofa tafita abinta tana
rike da frames na artwork datayi guda uku ga jaka abayanta she’s just a young lady da kana
ganinta kaga strong, bright hardworking young lady, Nisan daga gidansu zuwa hotel din kusan
tafiyan awa daya cur tabar gida bakwai takai hotel din by 8, Babban hadadden hotel ne shima
gyare gyaran daki take da da bayika su wata wata suke biyanta 30k office na wajen da uniform
nasu taje ta chanza kayanta taciro uniform din tana sawa Riga da wando ne tana kokarin saka
karamin farin hijabinta wata tashigo dakin hakan yasa dasauri tajuyo hada ido sukayi da
yarinyar tana ganin gashinta tace “Innalillahi Rashida kinasa attachment ne”? Dan zaro manyan
idanunta Rashida tayi dan bama tasan gashinta ya warware ba hannunta yarinyar tadaura kan
gashinta bakin kirin gashi da sulbi ga tsayi sosai tace “wlh gashin kine Woww Rashida hala ku
ba yan Nigeria bane” fizge gashinta Rashida tayi kaman fada tashiga parking tace “kada ki kara
tabani” baki yarinyan tasaki tace “ohhh nidai bantaba ganin masifaffiya irinki ba daga na yabi
gashinki Rashida sai fada” saka hijabinta tayi tace “aiki kikazo yi ko yabon gashi”? Tana
maganan ta kwashi frames din tabar wajen yarinyar tabita da kallo har cikin ranta tanason tai
kawance da Rashida but Rashida irin mutanen nan ne mafadata and too protective is as if
batason mutane su shigo space nata because she don’t wanna get hurt oho, u can’t

complement her, u can’t say anything to her fada but batada neman tsokana, bata shiga mutane
ba ruwanta da kowa itadai tazo tayi aikin datazo yi lokacin tafiya nayi ta tafi ko minti daya bata
karawa.

Sosai manager ke kallon zanen saikuma ta kalli Rashida tace “anya kene kikai zanen nan kodai
satowa kikayi”? Zaro manyan idanunta tayi tace “tunda nake bantaba sata arayuwana ba idan
baki yarda ninayi ba bani paper da pen da color namiki exactly irinshi agabanki” murmushi
manager tayi takalli abin saikuma tace “zan saya akan 10k each sannan ki dingayi kina
kawomin ko guda nawa ne zan saya” bakaramin dadi Rashida tajiba dudda zanen zane ne da
har 100k zaa iya saya awani waje but bata damuba 10k is huge 30k ta kirgo tabata sosai
Rashida taji dadi bata taba sanin zata iya saida zanenta ba kaman fa wasa taji ana maganan
sayan frames tace ta iya manager tace takawo tagani jibi anbata 30k akan guda uku anatse
tace “nagode Ma Allah kara arziki” dan tabe baki matan tayi tace “tafi kifara aikin ki” wucewa tayi
tafita manager ta kalli frame din tace “zan gayawa Oga 150k each nasaya wayyooo this girl is
talented bata sani ba inhar Oga yasosu zance muyi ma all rooms na hotel namu nabama
yarinyar tamin I will be fucking billionaire nabata 10k each ni na karbi 150k for each awajen Oga
wow look at her work”.


FOLLOW ME ON TIKTOK AND CATCH UP WTH ME


https://www.tiktok.com/@mshakurr?_t=8m0Y3PbS2GD&_r=1
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI


✍M SHAKUR

RUN TO HABISHMA GROUP NOW KUZABI SU BREZIYA DA PANTUNA DA KAYAN BACCI
DAKUKE SO KUCE DAGA WAJEN M SHAKUR KUKE KUGA KALAN PRICE DAZA’A BAKU
ME RAHUSA

JOIN NOWWWWW
https://chat.whatsapp.com/KGCjEvBSvUk3TY9ZHC2iWv


EPISODE 5️⃣
Ahankali yake bude idanunshi kadan kadan sama sama yaji ance “Son” dudda idanunshi akulle
but ahankali bakinshi ya furta. “Momm” shafa mai kai matan tayi ta duko ta manna mai kiss
agoshi cikeda tsantsan so tace “gani nan yarona open yourself Riyad no one is gonna hurt you
again” gently yake bude idanunshi kafin ahankali ya saukesu akanta gently ya yunkuro ya shige
jikinta kaman dan karamin yaro yace “Mommm” bayanshi ta shafa tana murmushi tace “meya
sameka what happen? Who did this to you”? Murya chan kasa yace “wasu mutane wanted to

kill me….” Kankameshi tayi sosai tace “babu wanda ya isa ya cutarmin dakai ko yadauki
rayuwanka as long as ina raye, u are safe already ana investigating abun sai inda karfina
yakare” takara kankameshi kaman dan karamin yaro tace “I love you Riyad kaine kadai sanyi
idanuwa na”lumshe idanu yayi saikuma ya yunkuro yatashi daga jikinta yakalleta da muryanshi
da bata fita sosai yace “Baba”? Kallonshi tayi saikuma ta sauke dan ijiyan zuciya tace “tashi
kaje kai wanka ka shirya kafito ka gaggaisa da mutane idan zaka iya, sannan kaje kama
Babanka addu’a a makwancin sa” dan runtse idanu yayi abin yamai ciwo yaso Ya sallaci
mahaifinshi, fuskanshi Mom ta taba hakan yasa yabude idanunshi dasukai ja yakalleta
murmushi kadan tamai tace “nasan yanda kakeson mahaifinka but he’s in a better place yanzu
trust me, all abinda yake bukata awajenka is addu’a, jekai wanka za’a kawo maka kayayyakin
dazakasa” gyadamata kai yayi agajiye yace “Mom please ke kikawomin banson hayaniyan
kowa” tsayawa tayi ta kalleshi ahankali tace “tom zan kawo maka da kaina” dagoshi tayi yatashi
tsaye ahankali yawuce bayin dake nan bedroom din, girman bayin yayi girman wani gida,
wanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login