Showing 9001 words to 12000 words out of 69832 words
yayi yayi brush yadaura towel yafito yana kallon saman gadon inda tundaga kan takalmi
har zuwa kan agogo an jeramai akan gadon tsaf dazai saka wasu kayan sarauta ne masu kyau
sunsha aiki, anatse yake komi ya shirya cikin kayan da aka musu aikin royalty ya feffesa turare
yadan juya yakallo kanshi amadubi yayi wani irin kyau na ban mamaki hulan dayasa yasake
maidashi wani cikakken mutum bude kofa yayi yafito daga bedroom din wasu bayi ne ma’aikata
a falon suna ganinshi suka duka dukansu. “Takawanka lafiya Yarima Riyad, taho a sannu dan
kwalisa abin begen Sarauniya Maryama, barka da fitowa, Allah yakara maka lafiya, makiyinka
fadawanka, duk wanda yaja dakai ya shirya yasha kasa….” Wucewa yayi fuuuu yafita danshi
bayason wayan nan surutun nasu, da Munir yaci karo yana kokarin shigowa flat dinsu hakan
yasa ya tsaya yahade rai kaman suna fada Munir yace “katashi, are you feeling better can you
walk”? Gyadama Munir kai yayi yay gaba kawai, Munir yabishi abaya direct inda aka binne sarki
yayi yana zuwa ya shiga wajen batare da an hanashi ba yayi shiruuuuu idanunshi sukai ja,
almost everyday indai Mai Martaba baida wani uzuri saiya kirashi da daddare yaji yayake ina
kuma yake, kullum cikin fada yakemai daya daina yawon kasashe yakan yawan cemai yanda
yake gudunma gidan nan da alamu shine wanda gidan nan zai rike kuma gam, ana cewa
sarakuna basu da lokacin yaransu shidai mahaifinshi nada lokacinshi, Baba ya fara koyamai
business how to make 1naira yakoma billions, Baba guides him through everything, duk
business dazai fara saiya kira Baba, sai Baba ya amince zai farayi, kuma bai taba takura mishi
ba, hawaye yaji sun taru a idanunshi da sauri ya runtse idanun yana fuzar da iska dan baiso
suma zubo but he’s deeply hurting, da ace yasan Baba zai rasu dabaiyi tafiyan nan ba, sosai
yama mahaifinshi addu’a sannan yafito Munir yagani awajen da Kabeer dasu Shaibu yan
uwanshi dukansu yajiki sukamai ya amsa sai kallonshi suke Kabeer yace “kasha magani kuwa
you still look sick? Ko zaka koma ka kwanta ne”? Gyadamai kai yayi ahankali yace “nasha, I’m
fine thank you” dannewa Kabeer yayi ganin yanda yakemai magana kaman alfarma yakemai
dayake amsashi yadai daure yace “to mutafi fada” atare dukansu suka wuce fada, sauran
yayyinsa da yan uwansa natamai hira da uhm a’a kawai yake amsasu cus gashinan ne kawai,
gaida mutane sukayi sai yima Riyad gaisuwa ake ana kiran sunanshi shi baimasan ya akayi
akasanshi hakaba dan baicika zama ba, su Waziri dai duk suna kallon komi, kowa yazo
saiyamai gaisuwa amai yajiki, yanda ma ake kallonshi sai abin yasa yaji sabon zazzabi na
nema ya lullubeshi.
Mom nazaune afalonta tana jan charbi ita dawasu kawayenta wanda suke mata Sarkin daga
wasu garin dasuka kawo mata gaisuwa aka shigo flat din Matan Waziri ne da babban diyarta
Haleema da ake kira da Lims, tana sanye da doguwan riga abaya black ta yana gyalen akanta,
tanada tsayi da dan jiki kadan duka duka bazata wuce 24, 25 ba, tana shiga dasauri tawuce
wajen Mom kafinma Mamanta tai gaisuwa tace “Mom ina kwana” takalli sauran matan wajen
cikeda girmamawa tace “ina Kwanan ku” amsawa sukayi Mom tamata murmushi tace “Halima
ba kina school ba yaushe kika dawo”? Mahaifiyarta tace “nima ganinta nayi agida da safen nan
ta iso daga London wlh na aika driver yaje yakawota tunda taji rasuwan Mai Martaba hankalinta
yakasa kwanciya” sosai Mom ke kallonta akunyace Haleema ta sunnar dakai Mom tace “school
fa idan kikai missing exam ko test fa” Maman ta tace “project ma fa takeyi this month zasu gama
komi da komi” babu wasa kan muryan Mom tace “kibi first available flight ki koma school gobe
kinajina” gyadama Mom kai tayi ahankali tace “to Mom” Mom bata sake cewa komiba tacigaba
da magana da manya, ahankali Haleema kebin dakin da kallo gabanta na faduwa addu’a take
Allah yasa suhadu ta ganshi, Allah yakawoshi side din nan dudda tasan ba lallai yadawo ba
barinma yaji da baki adakin amman tasan inhar yana gari yafi zama wajen Mom da bangarensu
na samari.
Kallonta Mamanta tayi tace “tashi kije wajen su Batul mana” juyowa Mom tayi takalleta tace
“tashi kije wajen yan uwanki” batai musu ba tashi tayi tawuce tafita Matan Madaki tabita da kallo
tace “yarinyar akwai natsuwa ga kunya ga kawaici ta dace da Riyad sosai yanda shima baida
maganan nan” wani kalan dadi Matan Waziri taji Mom tai dan murmushi batace komiba.
Ahankali take tafiya ita kadai tana danna wayanta kamshin turaren dataji yasa ta dago kanta
dasauri Riyad tahango yafito daga fada yana shigowa nan compound din Mom wlh kusan duka
yaran sarki tasansu da yaran yan uwa dan afadan nan aka haifeta anan ta girma bata taba
ganin yaro mai kyau da farin jini da aji irin Riyad ba kap gidan nan babu wanda yakaishi kyau,
ga tsayi ga gayu ga jidakai ga miskilanci ga kudi kudinshi na kanshi bawai kudin Baban su ba
dan babu wanda yakaishi kudi a yaran sarki, gashi Mai Martaba na sonshi, ga kakanshi na
bangaren Mom Attorney General yafi kowa tsatso mai kyau da gata ayaran sarki.
Faduwa gabanta yayi sosai amman tadaure ta tsaya awajen jikinta har bari bari yake, tahowa
yayi wajen batare daya kalle inda takeba zai wuce dasauri tace “Yarima Riyad!” Tsayawa Riyad
yayi chak batare daya juyoba dasaurinta Halima taje ta gabanshi ta tsaya adan kunyace tace
“ina yini ya hakuri?” Dan kallonta yayi trying to remember waye ita, shifa wasu kannin nashima
ba saninsu yagamayi ba dan baya shiga lamarin gidan nan baison komi game da sarautan,
dauke kanshi yayi ganin yanda take murmushi tana kallonshi, kaman ance dole yayi magana
yace “who are you”? Wow the way he talks is super adorable, da kyar ta iya controlling
zuciyanta dake neman fitowa ta danne kome takeji tace “Haleema” dan kallonta yayi irin kallon
okay but still baigane ta ba and he doesn’t care din nan yajuya zai wuce dasauri tace “Ya Riyad
sabida kai nazo gobe zan koma school” dan tsayawa yayi wannan karan yajuyo kalleta da kyau
shifa har yanzu bai santaba and sabida shi tazo? Akan wani dalili? Are they related in anyway?
Infact baida karfin bude baki ma yayi all this questions hakan yasa yadan tabe baki yace
“thanks” kawai yawuce ya shiga flat din Mom……
Jin akwai baki abangaren Mom yasa yajuya yagazaya ta baya yashigo gidan yaje ya kwanta.
**
Yana zaune adakinshi dashi da Munir har yanzu bai gamajin sauki ba yana sanye dawani
3quater da singlet wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Mom yasa yadauki wayan
kai tsaye tace “kazo dakina ina son ganinka” ahankali yace “okay Mom” tashi yayi ahankali
Munir dake taba wayanshi yace “ina zaka?” Slippers yashiga sawa yace “Moomm” yadauki wani
farin t-shirt yasaka kawai yawuce Munir daya gane abinda yake nufi wato Mom nakiranshi
hakan yasa yacigaba da abinda yakeyi ahankali yabude dakin Mom tana zaune kan couch din
dake dakinta ganinshi yasa tanunamai gefenta tace “taho nan” shigowa yayi ya maida kofan
dakin yarufe yataho wajen kujeran zama yayi saikuma ya kwanto yayi filo da cinyanta he’s really
feeling mutuwan mahaifinshi so duk walwalanshi bayanan, hannunta Mom tadaura saman
kanshi ta shafa tai shiru kafin tasauke ijiyan zuciya tace “kasha magani kuwa? Dr zai zo anjima”
ahankali yace “nasha” dan ijiyan zuciya tasauke tace “da banson namaka maganan nan yanzu
cus nasan kanajin mutuwan Babanka, I know how much you love mahaifinku Riyad but I have
to dan kowace matan sarki maganan da datake ma danta maza kenan, nima dole nama nawa”
dan dago idanunshi yayi ya kalli Maman nashi baice komiba, ahankali tace “inaso kai aure
Riyad!” dawani irin sauri Riyad yatashi zaune daga jikin ya kalleta yama kasa magana cus
maganan yazo mishi ne bagatatan, Mom dake kallonshi itama looking damn serious tace “and
bakowace kalan yarinya nakeso ka auromin ba Riyad, inaso ka auri yarinyar da zuciyana ta
aminta da ita yarinyar da nice na zabeta, all yammatan zamanin nan yanzu burinsu is suyi aure
su raba yaro da mahaifiyarshi I will never allow you marry such girls, I have a girl a mind dina
gaskiya” haderai yayi kana ganin fuskanshi kasan bama yason maganan dasauri yace “Mom
aure!”? Wani mugun kallo tamai tace “kaga Riyad banson shirme don’t even start all abinda
kakeso kace, I supported you duk yawace yawacen dakake kana touring round the world
bantaba hanaka ba dan nasan it’s your hubby, bantaba takuraka ba dudda normally normally ba
tun yau yakamata kai auren ba, but yanzu lokaci yayi it’s an order you have to settle down, aure
zakayi and i have a girl danakeso ka aura diyar Waziri Haleematu, ita nakeso ka aura!” Wani
kalan tashi yayi dasauri yamike tsaye yana kallon Mamanshi da babu wasa akan fuskanta itama
tabishi da kallo tazubamai idanu rass aka tace “kaine the most successful child acikin yaran
sarki, you’ve archived alot Riyad at a very young age, ga ilimi kwali daban daban gareka, ga
businesses da companies daka bude, ga natsuwa ga kamala ga kwarjini, naji kishen kishen
dama mai Babban daki kaine zabinta sabida yanda mahaifinku ke sonka, Waziri shima nasan
kodan yanda diyarshi ke sonka kuma yana mata kwadayinka kaizai dangwalamawa, to yaji
maganan kuma kanason auren diyarshi komi yazo cikin sauki idan yana bangaren mu zai mana
aikin yima sauran manyan fada maganan a zabeka, instead of su Kabir yan uwanka ko kannen
babbanku dake neman kujeran sarautan, gwara kai dana kaikafi kowa chanchanta and bazan
hutaba saina maidakai sarki, ai tsoron kada ka zama sarki yasa daga shigowanka garin suna
neman halakamin kai amman Allah bai basu iko ba, kuma naji dadin abinda yafaru hakan
yanunama jama’a cewa an tsaneka ana tsoron kada ka zama sarki saisa har anfara yunkurin
kasheka, saisa saida na tabbatar kowa yasan abinda yasameka”.
WANNA TALK TO NI M SHAKUR DIRECTLY?? KIMIN MAGANA A WATSAPP
+2347012181461
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI
✍M SHAKUR
KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA
AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA?
MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???
JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA
GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI
SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA
CHAT ME UP DON SHIGA
+2347012181461
EPISODE 6️⃣
Wallahi kanshi ma sarawa yafarayi jin maganganun da Mom kemai, first of all duk wani abun na
sarautan su bayaso saisama baya iya zama agarin, baison hayaniya baison how they do things
cus is always fighting, makirci and politics, and baijin tunda ya girma yatabayin cikakken
2months like good 60days agidan ba bini bini yabar country, lokutan salla ne yasan dole yake
dawowa sabida yanda Baba ya maida abin mandatory yanason duka yaranshi to be home
sabida hawan salla and other activities na al’adu, shi mutum ne da baisan mulki he prefer
business nashi, he derive joy a business, it gives him purpose, for aure kuma dudda yasan
culture nasu ne amaka aure abaka mata but shi kwata kawata baitaba sanin Mom zatamai
hakaba cus Mom is highly educated and expose, itama bata cika biyema culture ba saisa ma
take barinshi to live his dream life, ko kadan bai shirya aure ba cus bayason commitment for
now, his plan is nan da 2yrs zaiyi aure yanzu kawai aure baya lissafinsa, dukawa yayi ahankali
gaban Mom yadafa kafanta kaman zaiyi kuka yace “Mommmmm” ahankali itama Mom tana
kallonshi tace “Riyaddddd! You don’t have to say abinda zaka fadi kasan nasanka sama da
kowa aduniya ko?” Gyadamata Kai yayi Mom tace “I know how you despise sarauta, mulki
infact bakamasan komi akaiba, I know for auren zakace baka shirya ba bakasan damuwan
mace da sauransu” sai kawai takai hannuwanta tai cupping face nashi cikin tattausan lafazi tace
“dama akwai abinda zan taba so aduniyan nan dabaza ka iyamin ba Riyad”? Ahankali Mom
tace “I thought nine number 1 dinka like you always say”? Dasauri cikin raunin murya Riyad
yace “Mom u are my number 1 kema kin sani” kai tsaye Mom tace “inhar nine number one din
naka then karka karamin gardama kan maganan nan it’s an order allow me to do everything am
I clear?” Yadade yana kallonta yanda take kallonshi babu wasa kan idanunta yasa ya sauke
kanshi kasa alamun dai baiso but baice komiba, baya iyama Mahaifiyarshi gardama, cikin fushi
Mom tace “kamin shiru? Ban isa dakai bane ko ban isa nace maka haka nakeso kayi kayiba”?
Tai maganan tana shaking leg in anger, abu yahadiye awuyanshi har saida taga motsin adam
apple nashi asanyaye yace “okay” tsayarda shaking leg din tayi tai murmushi sai kawai ta matso
ta mannamai peck agoshi tace “I wish kowacce uwa zata sami d’a mai mata biyayya kaman
Riyad dina data zama very very lucky, Allah maka albarka kaji, Haleema is a good girl tana
matukar sonka tun tana yar yarinya, she will keep my son happy I’m sure of that, so karka
damu, zancen sarauta kuma I will teach you everything and you will do well kaji”? Gyadamata
kai yayi zuciyanshi duk ba dadi duka duka kwanan Babanshi nawa da rasuwa but kowa is after
kujeranshi, look at matayensu kaman ba mazajensu ne suka rasu ba dukansu kokarin daura
yaransu kan Sarautar suke sunma manta da rasuwan shima yanzu yazama sarkin one day
haka matarshi zatayi kenan itama yana mutuwa all focus dinta will be yanda danta zai gajeshi
bamatada lokacin yimai addu’a tashi kawai yayi yajuya yayi kofa.
Mom tabishi da kallo ranta fess, dolema Riyad dinta yadinga intimidating kowa, yafi duka yaran
sarki kyau ga kwarjini ga haiba ga natsuwa, ga jan aji, ga kudi, ga rashin magana, ga rashin
shiga mutane, gashi baida kallon mata shi kadai keda qualities na sarki and bazata hutaba saita
maidashi sarki wannan alkawari ne!.
Dakinshi yashiga Munir dake danna laptop yabishi da kallo ganin yanda mood dinshi ya chanza
tashi daya, Wucewa yayi yafada gado yakife cikinshi tareda lumshe idanu Munir baicemai
komiba yacigaba da abinda yakeyi abinshi.
Yana fita Mom ta daga wayanta takira matan Waziri da ake kira da Mariya ringing daya ta daga
wayan tace “ranki shi dade Uwardakina, Allah yaja zamaninki Umman Riyad” dan murmushi
Mom tayi kafin cikeda isa da jiji dakai tace “dole gobe Haleematu zata koma makaranta ne”?
Dasauri Mariya tace “ai Uwardakina ko makarantan kikace karta kara zuwa saita zauna” jinjina
kai Mom tayi tace “tom inaga bazata tafi goben ba dan zan turo Riyad yazo ya ganta inaso
nahada su aure inyaso bayan yaganta zata iya tafiya” wani ihu Mariya tayi cikin waya saikuma
ta zube kaman tana gabanta tace “nagode nagode Uwardakina da wannan karamci naki, kidubi
kowa na gidan nan amman kuka zabinma Yarima Riyad Haleematu nagode, namiki alkawari
bazaki taba samin matsala damu ba, I will forever be loyal to you, Haleema zata bautamiki
Uwardakina, kuma da yardan Allah kujeran sarautan nan ta Yarima Riyad ce ai naji jita jita, da
yardan Allah shine magajin sarki” dan murmushi Mom tayi tace “Waziri ya shigo yakirani” tana
maganan ta katse waya wani ihu Mariya tayi tamike da gudunta tafice zuwa dakin Haleematu
kai tsaye tabude kofan yarinyar na zaune sanye da rigan bacci tana kokarin hada kaya Maman
kawai ta dagata tana juyawa tana rawa abinma saiyasa Haleematun dariya tace “Mommy
menene kike murna haka”? Cikeda jin dadi tace “yanzun nan Sarauniya Maryama takirani tace
tanason hada aurenki da Yarima Riyad gobe ma zata aikoshi gidan nan” wani kalan zaro idanu
Haleema tayi she can’t believe abinda taji tun tana yar yarinya takeson Yarima Riyad yahadu ne
over wlh, lips nata rawa suka fara farinciki yahanata magana tace “Mommy mekikace? Yarima
Riyad mene? Dan Allah maimaita”?Kyalkyacewa da dariya Mama tayi tace “dalla cewa nayi za’a
aura miki Riyad zaki zama matan sarki dan ina mai tabbatar miki shi za’a bawa Sarautan”
ihuuuu tayi tareda wani kalan tsalle ta rungume Mamanta sai kawai tahau tsalle sosai lekowa
dakin Waziri da shigowan shi kenan yayi ganinsu yayi murmushi waya na kunnenshi Mama
zatamai magana yadaga hannu yace “inajinki ranki shi dade” wucewa falo yayi yazauna Mama
da Haleema suka biyoshi a speaker yasaka wayan dashi da Mom ke magana suna shirya komi
kaman ba mutuwa aka musu ba, planning auren da yanda zasu sami kujeran suke hankali
kwance.
**
Wuraren 10 yafito daga dakinshi yana sanye cikin wani farin yadi da akamai dinkin jumper
yamai kyau sosai sai kamshi yake zubawa kaman zaije gasan turare, binshi da kallo Mom tayi
tana murmushi tace “Son katashi? Munir yashigo yakai sau uku nacemai bai isa yatasheka ba,
bayan kunyi sallan asuba tare a mosque” karasowa yayi yazo kusadab da ita yazauna ahankali
yace “morning Mom” as usual pecking nashi tayi a goshi tareda shafa kumatunshi tace “morning
Riyad, yaya jikin? Zakai breakfast yanzu ne”? Girgiza mata kai yayi alamun no, dasauri tace “to
maza je Gwaggon ku ta aiko dazu akiraka kadawo saikai breakfast kafin kafita fada ko”? Dan
gyadamata kai yayi yatashi ahankali yayi kofa haryasa hannu zai bude kofan tace “idan tamaka
maganan auren Haleema kai naam” dasauri yajuyo da kanshi ya kalli Mom dauke kai tayi
kafinma yamata wani maganan, dan jim yayi sannan yabude kofa yafita ma’aikata fada sun cika
wajen yawanci Mom bata barinsu falo so anan waje suke yashe kaman kaya, gaishe gaishe da
kirari sukahau mai ya wuce abinshi ko kadan baison zuwa wajen Gwaggo shi kadai hakan yasa
yaciro wayanshi daga aljihu dailing number Munir yayi ringing daya yadaga yace “kana’ina”?
Daga dayan bangaren yace “ganinan daure da towel wanka zan shiga” dan yatsine fuska yayi
yace “be fast to” ya katse wayan baiso ya koma ciki dan baiso Mom tasan baijeba kuma baison
yayita tsayawa awajen hakan yasa yawuce flat din su