Showing 33001 words to 36000 words out of 69832 words
jikinta keyiba bazaka gane kuka takeyiba,
ahankali yaduka yadauki jakanta yashigo dakin yakawo gefen gadon ya ijiye saikuma ya zuba
hannayenshi a aljihu yana kallonsu, takai 3min ahaka sannan ta taso da sauri ta dauki Dr note
dake saman table na gadon ta shiga karance karance magungunan da alluran dake wajen ta
shiga duddubawa tana karantawa har drip din da aka samata sannan ta sauke ijiyan zuciya
tasake zama bakin gadon takama hannun Mama tarike gam tana kallonta, kawai kana ganin
Rashida kasan yanda takeson Mamanta, ta dade ahaka tana kankame da hannun Mama
sannan tasaki hannun takai hannayenta ta share fuskanta tajuyo tareda tashi tsaye ta kalleshi
hada ido sukayi da sauri ta dauke kai cikin muryanta dahar ya chanza sauti sabida kuka tace
“nawa ka kashe nabiyaka inaso akira Dr ya sallameta na nemo keke napep nakaita chan
asibitin datake amfani dashi” yana kallonta right in the eye yace “which hospital”? Ahankali tace
“teaching hospital” kai tsaye cikeda izza da iko kaman Mamarsa yace “kibarta anan” da sauri ta
kalleshi sake hada ido sukayi cikin konewan idanu Rashida tace “wannan kuma nice next of kin
nata i decide and make decision for my Mom not you, nawa nidai ka kashe” yadade yana
kallonta baitaba ganin feisty mara kunyan yarinya irin this girl ba, yana kallonta yace “idan Dr
yazo ki tambayeshi” yajuya zai wuce tace “eh zan tambaya and i will pay you back cus banson
any favor ko taimako from anybody zan kawoma kudinka” dan jimm yayi sai kawai yabude
kofan yafita, mota yawuce yashiga yatada yayi dialing number Dr yana dagawa yace “Dr on no
condition zakai releasing that patient without letting me know, don’t let the Daughter take her to
another hospital, sign them up for abinci” cikeda girmamawa yace “to Ranka shi dade” dan
yatsine fuska yayi ahankali yace “and about that!” Yadanyi shiru chan yace “don’t disclose my
identity to anyone nor address me ahaka in front of anybody” Dr yace “shikenan Riy….” Harya
katse wayan ya bala’in gaji hotel yakoma ya kashe mota ya sauke ya shiga ciki ana gaidashi ko
amsasu baiyiba yawuce office nashi straight yana budewa ya shige ganin desktop a kunne
yasan Munir na ciki, hakan yasa yawuce ciki Munir na kwance yana buga game a tv dagashi sai
singlet da 3quater ganinshi yasa ya ijiye remote yataso yace “ance Maman yarinyar tazo and
she fainted kasata a mota hospital ka kaita” yana cire riga yace “eh” tsayawa Munir yayi yana
kallonshi yace “I know the girl itace wacce saved you but are you sure zaka barta tacigaba da
aiki kai the girl have quiet a temper” batare daya amsashi ba kawai yawuce yafada bayi wanka
yayo yafito daure da towel a waist turaruka ya tsaya ya fesa sannan yazo yazauna, Munir tace
“Mom takirani yafi sau goma nace mata we are not together tace she will call back in the next
5mins idan ban hadata dakai ba zata kai karana wajen Ammi” Shiru yasakeyi hakan yasa Munir
yadafa kafadanshi yace “common mana fushin ya isa haka before kasa karyan vakada lafiya da
Mami tayi azo asani please go back home” yatsine fuska yayi yace “I’m hungry Muneer, please
kaje gida ka kawomin abincin Ammi” tashi Muneer yayi yace “okay”.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: SANYI DA ZAFI
✍M SHAKUR
EPISODE 1️⃣5️⃣
WHEN WAS THE LAST TIME KIKA SAYI SABON PANT? TALK TRUE
BRA DINKI SUN KOMA RUWAN KASA TSABAGEN SAWA KULLUM
TO IDAN NACE YAU NAKAWO MIKI HABISHMA UNDERWEARS FA SUNA SAIDA
PANTS, BRAS, NURSING BRA, MATERNITY GOWNS, NO LEAKAGE PANTS NA PERIOD,
KAYAN BACCI DA SAURANSU
SUNADA MOST AFFORDABLE KAYA GA VERY CHEAP DELIVERY NATIONWIDE GO AND
BUY NOWWWW!!!
https://www.tiktok.com/@habismaunderwears?_t=8lzVAMnAhgk&_r=1
Da gangan Munir yabar wayanshi awajen yadauke car key yafice, tashi Riyad yayi yawuce
yasaka pajamas yadawo ya kishingida tareda lumshe idanu, wayan Muneer ne yahau ringing
hakan yasa yabude idanu kadan yakalli screen din ganin Mom R yasa yayi shiru yana kallo
wayan na dab da katse wa yasa hannu ya dauka yakai kunnenshi yaki magana daga ta dayan
bangaren Mom tace “Son” ahankali yace “Mom ina yini” ijiyan zuciya Mom ta sauke she really
miss him chan tace “sabida I questioned you zakai zuciya kabar gidan? Riyad when did you
grow dahar zakabar min gida sabida namaka fada? Riyad I still see you as my little baby boy da
I have to guide every step of the way, your are my purpose, you are the reason I become a
Mom, did you really leave house yau kwana biyu sabida na tambayeka game da abu Riyad”?
Mom tai maganan muryanta na tsinkewa kaman zatai kuka, Riyad yayi shiru Mom abin ya
matukar bata mata rai tace “ko kakai 100yrs of being a man I will always see you as my little
child, I will always tell you do this and that, I agree raina abace yake ranan datamin maganan
dan kunnen nan and I wasn’t thinking clearly, but still inada right nai fada, Babanka yayi aure
aure but tell me menene fa’idan hakan yanzu? Kullum gidanshi cikin rikici makirci da fada ake,
kalli Baffan ka tunda yama Amaryanshi koran kare bai sake marmarin kara aure ba sabida yaga
implications din gashinan shida Jummai are living peacefully and happily, wat I’m saying is mata
dayawa masifa ne, bazan taba bari ka auro wata wacce ban sani ba ko ban aminta da ita
kaman Haleematu ba kafin azo arabani da d’ana that is the reason namaka fada and asked you
ranan, and gashi nakosa naga Haleematu tai ciki amman shiru, dakaina nakai yarinyar taga
gynecologist ance she’s fine kaine dai baka cika nemanta ba, kuma ita Haleematun tagayamin
yawanci koka nemeta ba rannan ovulation dinta bane saisa har yanzu batai ciki ba, mesa
kakemin haka Riyad? Kai ba dan gidan nan bane bakaga yanda matan yayyinka ke haihuwa
shekara shekara ba? Duk shirin da Babanku yakema yaranshi maza tun suna yara kaima an
maka amman narasa mesa kakeda sanyi a harkan raya sunna” da sauri Riyad yacire wayan
daga kunnenshi yanajin wani irin kunya da nauyi idan Mom namai irin maganganun nan, danna
wayan kawai yayi a speaker ya ijiye agefense yana jinta. “Kap yaran family nan wlh basama
matansu wasa kai har rama matan suke sabida yanda yaran Mai Martaba Baba Ali fire for fire
ne akan matansu” wannan karan Riyad baisan sanda ya dafe kanshi yace “Mom can we
change the topic please” cikeda bacin rai Mom tace “Kaci gidanku da change of topic Riyad,
nabaka gobe come back home and continue kaga yanzu kayi skipping 2days babu abinda ya
shiga tsakaninka da Haleema, kubani grandson nagaya maka saida safe” ta kashe wayan,
ijiyan zuciya ya sauke yakoma ya kwanta tareda lumshe idanunshi.
Har Muneer yadawo a kwance yasameshi yace “ina tuki natuna wani abu daya faru dazu yanda
dayar ma’aikaciyar yarinyar tace ma Masifaffiyar mamanta nada HIV” dagokai Riyad yayi yamai
wani shegen kallo yace “and so”? Dan sosa kai Muneer yayi yace “bakomi kawai natuna abin
ne” juyar da kansa yayi sai chan yace “HIV is just like any other ciwo, having it doesn’t mean
you are bad ko karshenka yazo, stop with the stigmatization” dasauri Muneer yace “haba noo
bana stigmatization sai kace Baffan mu da akace ya kori matarshi mai ciki da akace tanada shi,
ko tana ina oho”? Tashi Riyad yayi yace “let’s eat” abinci suka shiga ci he ate alot kam yana
gamawa yadauki laptop yafara aiki daman yunwa yahanashi yi.
Cikin bacci taji ana tabamata kai sabida tsabagen yanda bacci yau bai shigeta ba taba cikin
tashin hankali firgigit ta farka.
Cikin dare sau biyu cikin dare Dr da Nurses sukazo duba Mama duk tana zaune bata runtsa ba
harsaida Dr yace “kihau gado ki kwanta kusada ita mana ko ga babban sofa kihau” girgizamai
kai tayi tana zaune kan yar kujeran dake gaban gadon, cikin sanyin murya tace “zan zauna
anan” gyadamata kan Dr yayi yawuce harzai fita tace “ina bill dinmu?” Dan juyowa yayi yace
“your bill has been cleared receipt duk suna cikin ledan drip dinta” yana maganan yabude kofa
yafice from yanayin mutanen kawai yasan Mai Martaba taimakonsu yake.
Tashi tayi dasauri tawuce wajen ledan drip din da duk za’a sama Mama tabude taciro takardun
receipt wanda na farkon na meal tagani 2 person breakfast 2person lunch dinner da snacks na
3days taga 270k, abincinta itada Mama kullum 30k for 3days 270k zaro idanu tayi takai
hannunta tana dafa kirjinta, tadauki dayan receipt din single room dasuke dakeda gado sofa
fridge da bayi is 25k per day kwana uku 75000, sai magungunan Mama gabaki daya da drip da
allurai taga 497,250 wannan karan saida ta fada kujera ta zauna, duka kudin 842,250naira,
kusan miliyan daya ta ina zata fara neman kudaded nan? No gobe zatasa a sallamesu, but ko
an sallamesu sunyi kwana daya which is 25k daki, sai kudin magunguna 497,250 dole saita
biya ta ina zata fara, hawaye taji sun zubomata sai kawai ta gogesu da sauri tahada duka
receipt din ta linke tasa a jakanta tadauko kudinsu ta kara kirgawa duka savings dinsu kenan
150k tadade ahaka saita maida jaka ta kama hannun Mama ta rike har aka kira asubahi
idanunta biyu tashi tayi tawuce bayi tayo alwala tafito tabude jaka ta ciro dadduma anyi alamun
gabas aşaman dakin hakan yasa ta kabbarta salla ta idar tai azkar tana zaune kan dadduma Dr
yakara shigowa dasauri ta tashi ta linke dadduma Dr yaduba Mama yajuyo yakalli Rashida datai
zuru zuru yace “Alhamdulillah BP yasoma sauka, maganin zai saketa soon zata farka bada
jimawa ba” gyadamai kai tayi, murmushi Dr yayi yace “Maman ki will be fine kinji” gyadamai kai
tayi ahankali tace “thank you” wucewa yayi yafita
Zama tayi har bakwai da rabi kallon Mama take sai alokacin tafara hamma sai kawai ta kifa
kanta anan bakin gado ko 1min batayiba bacci yayi awon gaba da ita.
Wajajen 10 na safiya Mama ke bude idanunta ahankali bakinta dauke da kiran sunan Allah,
saman dakin ta kalla sannan ta sauko da idanuwanta ta kalli drip da ake samata kafin ta sauke
idanun kan Rashida dake zaune kan kujera ta kwantar da kanta bakin gadon kusada hannunta
tana bacci, ijiyan zuciya ta sauke ahankali komi daya faru jiya na dawo mata, ta tuna yanda
tagama magana da bawan Allah nan mai kirki tafara tafiya tafadi tabbas taga bawan Allahn
hankali tashe yazo yana kiranta Mama Mama dishi dishi take gani bama ta iya magana dağa
baya kuma taga shida security sun kaita mota daganan kuma bata sake sannin inda kanta yake
ba, ahankali cikeda karfin hali irin nata ta cire drip din ta sauka tana tafiya da kyar tawuce kofan
data gani ta bude ta shiga bayi ta dauro Alwala tafito ta sanya hijabi taje ta sauna kan
dadduman data gani tai salla dağa zaunen datake tun magrib da isha’i tahada dana safiya
sannan ta dawo ta lallabo ta zauna agadon jin jiri na neman yakara dibanta motsin da gadon
yayi yasa firgigit Rashida ta bude idanunta ganin Mama zaune da hijab dinta yasa da sauri ta
tashi tace “Mama kincire drip din” takama hannun Mama dasauri tashiga maida mata drip din
tace “mesa baki tasheni ba har yanzu BP ki is high Mama, you can fall at any moment”
Yanda take maganan Mama take kallo kaman ba Rashida ba duk ta tsure harta rame idanunta
sun fada ciki sosai, hannunta Mama takai ahankali ta kama habarta hakan yasa gently tadago
fuskanta ta kalli Mama duk yanda taso taboye damuwanta takasa da duka zuciyanta tafashe da
kuka sosai atsaye hawayen na sauka kan hannun Mama, cikin kuka tace “Mama dan Allah
kiyakuri I keep causing you pain koda yaushe, Mama I know how sick you are but kullum kara
miki damuwa nake Mama, akan mene bazanyi hakuri na dinga danne komi ba, komine sainayi
fada akai, is because of me BP ki yatashi, Mama kiyakuri kiyafemin dan Allah” har sheshekan
kuka take, zuwanshi kenan yakai hannu kenan zai knocking kofan yaji sautin kuka da maganan
datake hakan yasa ya tsaya chak.
Ahankali Mama ta girgiza mata kai tace “shiiiiii don’t ever blame kanki for ciwo ba cus ba laifinki
bane ko daya, stop crying to bagani nan naji sauki ba, gashi nan duk kin bata fuskanki jibi
yanda idanuwanki sukai ja sabida kuka bari kiga” Mama sai kawai takama bakin hijabinta takai
kan fuskanta tashiga sharemata ta shafa kumatunta tasake murmushi tace “I have the most
beautiful yarinya wlh idan tai kuka sainaga idanun nata ma sunfi kyau” dan murmushi kadan tayi
wasu hawayen na taruwa, Mama tace “ai kaga abin karki kukan ya isa nace, yanzu dai tafi gida
ki shirya kitafi school idan zaki dawo saiki biya wajen gyaran wayanki” baki Rashida tabude
zatai magana akai knocking kofar just once kallon kofan sukayi dukansu, Mama tace “jeki bude
kofan muga ko likita ne natafi gida” but Dr direct yake bude kofan tai maganan aranta tasa
hannu ta goge fuskanta tass sannan tawuce wajen kofan tasa hannu ta bude ido da ido tayi da
Riyad dake sanye cikin wata shadda yau sky blue jumper kanshi ba hula tashin Kansa ya
kwanta sidik tunda take bata tabajin kamshin turare mai dadin nashi ba, da sauri ta dauke kanta
dağa kallonshi Mama hangoshi yasa tace “bismillah bawan Allah” anatse akamilance yashigo
har gaban gadon yaje yaduka dasauri Mama tace “tashi tashi haba zauna ga waje” tabashi
kujera ijiye ledan dake hannunshi yayına gefen gadon yace “ya karfin jiki Mama ina kwana”
murmushi Mama tayi tace “jiki Alhamdulillah naji sauki, nagode da kulawa ka kawoni asibiti
banda bakin maka godiya Allah maka Albarka” takalli Rashida dake tsaye wajen kofan tai
folding hannu tace “baki iya gaisuwa bane ko akwai abu abakinki ne” dan juyawa tayi da kyar
tace “ina kwana” baki Mama tasaki tana kallonta ganin baka yasa da kyar tace “mungode”
dasauri Mama takalleshi tace “Ya sunanka ne?” Ahankali yace “Riyad sunana” daidai lokacin
akai knocking tareda shigowa dakin wata ce tana sanye da uniform na ma’aikata tace “good
morning Ma dazu nazo nakawo muku breakfast naga kuna bacci natafi dashi dan karyayi sanyi
yanzu zanje nakawo muku” tawuce tafita daga wajen kofan akunbure Rashida tace “Mama
kicemai yasa a sallamemu mutafi asibitin mu” dan juyowa yayi daga inda
Yake yazuba mata ido dauke kai tayi strictly yace “Dr yace 3days Mama zatayi anan and hakan
ne zai faru” dasauri Mama tace “Riyad kaga ai dawainiyan zaiyi yawa ta ina zamu sami kudin
biyanka? Dan Allah kasa asallamemu naje general dana saba zuwa kaji, Allah yamaka Albarka
Allah yakara daukaka” daidai lokacin aka kawo abincin breakfast ne omlete da bread toast
sausage tea dakuma bowl na fruits yarinyar ta saukar dama da Mama wajen ijiye abinci kan
gado sannan takai dayan abincin kan table sannan takalli Riyad tace “Sir do you need
anything”? “No thanks” yafadi atakaice, Mama ta kalli Rashida dake tsaye kikam har lokacin
awajen kaman mai gadi tace “zokiyi kari kitafi school don’t even tell me bazaki ba” kaman zatai
kuka tace “Mama ni banso naje wazai zauna dake natafi” “I will be here with Mama” dağa Mama
har Rashida dukansu kallon Riyad sukayi, hakanan Mama kawai taji tanason natsuwan yaron,
abin yana mata ma kaman tasanshi batason tai rubbing in his face hakan yasa tai murmushi
tace “to kinji Riyad zai zauna yatayani hira zoki ci abinci kitafi school kinyi katti already banson
kina fashi a school kije gida ki shirya kitafi” bataso taje school ba but abinda yafima damunta is
wannan mutumin dayakeyi kaman irin ya sansu din nan ko su yan uwa ne saiwani shishigi yaje
musu mutumin da shekaran jiya ta sanshi, batason tai gardama sabida Mama batada lafiya
hakan yasa ta taho wajen gadon gefen Riyad ta ballama jakan abubuwan dayakawo harara
karaf akan idanunshi sannan tadauki jakanta dake wajen ta taso tajuyo hada ido sukayi tadauke
kanta tajuya Mama tace “abincin fa” akufule tace “ni bazan ci ba” tawuce wajen wardrobe na
dakin taciro kayan jakan an Mama daya kawo ta maidasu ciki kudin taboye karkashin kayan
sannan tawuce tai hanyar kofa tace “natafi” tabude kofan tafice ijiyan zuciya Mama tasauke
tasa cokali ta a abinci tace “I have a very stubborn yarinya Riyad” dan murmushi kadan Riyad
yayi baice komiba, Mama tai shiru kaman mai tunani tace “she’s all abinda na mallaka aduniyan
nan” saita dauki fruits takai bakinta tafara taunawa sai kawai tafashe da kuka as if she’s holding
on to something ahankali Riyad yace “Mama stop crying she will stop being stubborn soon duk
yarinta ne, zata dena nan gaba, stop crying kinji Mama is not good for you zai hanaki warkewa”
ijiye spoon din tayi takai bakin hijabinta ta goge fuskanta tace “ciwo na bana warkewa bane, HIV
gareni Riyad” tadanyi murmushi tace “I don’t even know why nake fadamaka nasan kariga
kasani Rashida tacemin agabanku abokiyar aikinta tace inada shi” tai shiru sai kuma ta zufar da
iska dağa bakinta tace “I’ve caused Rashida pain tun tana ciki na, yarinyar nan