Showing 30001 words to 33000 words out of 71336 words
Chapter 11 - BABAN YARO PART 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf
ta daina zuwa gurimu dimu Nace." Wallahi Mimi na
tsani inga mace tana kazanta shiyasa na takurawa Hafsa in ta fahimta sai ta gyara haba!tasan
zata shigo cikin makaranta cikin mutane baza ta tsaftace jikinta ba nifa wallahi mijina zai ga
tsafta domin shi kanshi kullum cikin kyalkyale masa ji nake." Mimi tace." Ga manyan mata
hummm mijin da bai zo ba ana masa tanadi lallai wannan me sa'a ne." Nace fad'i ki kara Mimi
duk namijin da ya same ni ya tsinci dami akala domin sai na sanja masa rayuwa ummm! Mimi
kenan ni nasan wacece ni." Mimi tace "maganar Umma ta futo lallai Asma'u aure kike so."
Hararata nayi nace "don Allah tashi ki saka kayan ki , e aure nake so Mimi waye zaiki sinnar
Annabi muhammadu." Mimi ta mike tana saka kaya tace." Babu gaskiya kam Allah dai ya zab'a
mana nagari." Nace ameen ya rabbi.
Mun futo a kintse Sosai mu kayi kyau Mimi tasha kwalliyar fuska ni ko hoda kawai na saka sai
kwalli Dana zirara ko man leb'e ban saka ba, Umma ta kalleni tare da fadin " Asma'u ban ce ki
daina saka atampar nan ba haka kurum kinje an miki lalataccan dinki ko."? Nace Umma duba fa
ki gani atampar da kyaunta kuma ni duk cikin kayana nafi sonta wallahi." Umma tace." Ke kika
sani ai ba kyawun atampar ne abun dubawa dinkin ne." Nace Umma na kai wa Ummi makociya
ta gyara min hannu" shiru kawai Umma tayi min domin tasan duk tsarina ne, tace." Kar Ku kai
magariba baku dawo gidan nan ba." Muka ce to Umma" tace Ku daina min da Kawun NAKU
da Mamansu Munubiya" muka je zata ji insha Allah. Nan muka futa muna taku dai-dai
mussaman ni sau kace wata 'yar gidan shugaban kasa. Da kafa muka k'arasa bakin titi muka
tsaya domin jiran abun hawa. Wasu 'yan mata suka zo wucewa ta gefenmu nace " Mimi kinga
irin handbag dina ko ajikin waccan" Mimi ta kallesu tare da fadin "aikuwa irinta CE." Nace."
Anya ko Mimi bazan je in d'auko kayata ba" tace" kin dai ji abunda Umma tace don Allah kar ki
jawo mana wata Matsalar " shiru nayi mata kawai ina sak'e-sak'e. A dai-dai ta sahu ta tsayar
mana tayi ciniki dashi tare da fada mana inda zai kaimu, muka shiga, mun Dan yi nisa Mimi
tace." Idan mun futo daga gidan Kawu Nafi'u mu biya gudansu Hafsa mana tunda kusa ne."
Nace "muje mana ai babu komai. " Mimi hira take min ni ko ina can tunanin yadda za'ayi in
d'auko handbag dina gidan guy nan . mu ka sauka Titin wajan gidan marigayi Ummaru ta'ambu
da kafa muka dinga shiga lungunan kafin mu Isa gidan Kawu Nafi'u muna shiga yaran gidan
suka rungume Mimi suna ihu!! Kallonsu nake INA dariya nace" nu baku sann ba kenan" su
dawo kaina nan Mamansa Munnu ta futo tana mana maraba tace Ku shigo ciki yara sun hanaku
shigowa . nan muka shiga parlor me d'auke da kujeru biyar da kafet malale a tsakiyar gefe friji
ne sai kayan kallo lavuleye kewaye a parlor ka hotunan shuwagabbanin kasa a manne a bango
kana ganin tsarin gidan kasan na 'yan boko ne
Muka gaisa da ita Sosai tare da fada mata sak'on Umma tace." Tana amsawa tare da cewa "ai
duk laifin Ku ne da bakwa zuwa akai akai sai Ku d'ebo wattani ba kuzo ba ke Mimi haka dangi
zasu yi ta cigiyar ki." Mimi ta sunkyar da kanta cike da kunya nace." Mamansa Munnu Kawu Ba
yanan ne." Tace." Bai jima da futa wallahi" nace Munnu fa." Tace" yanzu ta shiga ban daki tana
Wanka " muka mike muka shiga dakin Munnu kan katifar ta muka zube ni da Mimi Munnu ta
baza hotona kan katifarta tana kallo duk irin tsaffin hotanan ne na makaranta da wasu lokacin
muna yara. Wani hoto Mimi ta mik'o min tace." Asma'u kin ganki a nan"? Karb'a nayi ina
dubawa Mimi tq fashe da dariya, da sauri na yi yunk'urin yaga hoton cike da takaici hoton anyi
mana shine farko fara zuwa makarantar mu lokacin muna kwailaye muna sanye da sabbi
unporm ko wanne da k'atuwar jakarsa sai murna muke mun shiga secondary skull Mimi ta fuzge
hoton tana dariya tare da fadin" kin San Allah Asma kina kama da 'yar film din nan Nafisa
Abdullahi" hararata nayi nace." Kin cuce ni Mimi". Tace. OK kina nufin kin fi Nafisa kyau
kenan."? Nace" nesa ba kusa ba wallahi . Mimi tace "bari Munnu ta futo ta fada miki gaskiya."
Aikuwa sai ga Munnu ta shigo dakin tana goge kanta da k'aramin towol tace." Ku kuma 'yan
iska yaushe kuka zo" nace." Babynaaaaaa!!! Cike da tsoka na fad'i maganar Munnu ta kawo
min duka tana warce hoton dake hannuna dariya na fashe da ita ina nuna ta da hannu. Ita ko
Mimi dake mayyar dariya ce kwanciya tayi kan katifa tana sheka dariyarta. Munnu ta wuce mu
cike da takaici take fadin "banza ye kawai wad'anda basa manta Abu." Ina dariya nace." Ya
za'ayi mu manta Munnu ta Shamsu kenan baki da aiki sai kallon hoton Shamsu ki ishi mutane a
skull da Baby na yayi kaza babyna yace zai siya min kaza hummmm! Shamsu ya San takan
sace zuciyar 'yan mata gashi ya sace taki ya gudu ya barki da ciwon sonsa"
Mimi tace" wallahi kuwa kin San ko a skul aka zagi Shamsu sau kunyi fada da ita ko ta d'aura
gaba dakai, ummm! Ni kaina sau nawa Munnu tana gaba dani duk akan ina mata magana ta
rabu da Shamsu Dan yaudara ne.'' Nace." Nifa WALLAHI duk son da nakewa Namiji bai Isa na
nuna masa ba sai dai ya gani a aikace." Munnu tace." Ni Ku k'yaleni don Allah kuyi min addu'a
kawai Allah ya cire min son Shamsu daga zuciyata" nace." Munnu kina so ki rabu da soyayyar
Shamsu a zuciyar ki amma kike kallon hotan sa." Shiru tamin nace." Kinga to" juyowa tayi tana
kallona na daga hoton Shamsu dake hannuna na zaga shi gida uku na watsar nace" wannan
shi yafi dacewa dake amma kullum kina kallon hoton sa ta Yaya zaki mance dashi." Mimi tace
kinyi min dai-dai da kika yaga wallahi" Munnu ta juya ba tare da tace mana komai ba ta cigaba
da kintsa jikinta mu kuma muka cigaba da caccakar Shamsu gami da tsine masa sabo yaudarar
da yayiwa Munnu wacce ta saki jiki dashi sosai ya gudu ya barta.Bayan ta gama shirya ta juyo
tana fuskantar mu tare da fadin " INA kukaje ne kula biyo tanan domin nasan dai ba takanas
kuka zo nan ba" Mimi tace" aikuwa kin fad'i ba dai-dai ba takanas muka zo nan domin mu wuni
amma za muje gidansu Hafsa me warin Ham!! Munnu ta fashe da dariya tana nuna Asma'u
dariya muka kwashe da ita dukan mu sai kace wasu tab'abb'u.
*****
B'angaran Hibbah kuwa tana zaune har wajan goma na dare tana jiran dawowar *Amjadu* shiru
bai dawo ba kamar ta fasa kuka haka take ji gashi bata da numbar sa ga wata sha'awrsa na
damunta tunda ya d'and'ana mata zumarsa a baki shikkenan taji tana son kara kasan cewa
dashi, jiki babu k'wari ta futo daga dakin tana sakkowa kasa taga haske tar mutane sai kai kawo
suke tamkar rana domin wasu ma a lokacin suke shigowa gurin cikin motocinsu wasu da 'yan
matansu wasu da abokan su gasu nan dai. Duk tarin mazan da suke Binta da kallon sha'awa
Sam basa gabanta domin yanzu ita babu Wanda take gani a gabanta sai Sadauki *Amjadu* shi
kadai ne burin ta. Motar ta bude ta shiga ta futa daga hotal din.
**********
Bayan munci abunci munyi sallah azuhur ne sannan muka sake kintse jikinmu domin zuwa
gudansu Hafsa muka futo mu ka sanarwa da Mamasu Munnu tace" to daga can zaku wuce
kenan."? Nace "Eh daga can zamu wuce gida" d'akinta ta shiga tana fadin "Bari in zo to" mu
kowa ni da Mimi hanyar futa muka nufa saboda mun San halinta kullum in muka zo sai tace
zata bamu kudi." Aikuwa sai gata ta futo hannunta da gudar Dari biyar tare da wata Leda me
Zane Zane. Ta mik'o mana tana fadin Ku karb'a Ku kara kud'in mota" nokewa mukayi cike da
kunya Mimi ta karb'i ledar tana fad'in "zamu karb'i wannan amma ki bar kud'in naki" Munnu ta
karb'i kud'in tana fadin" Umma kyalesu suna so wallahi munafurci ne" kawai na basu in mun
futa" Ummansu Munnu tace" to Ku gaida gida Ku gaishe min da Umman taku " mukace "zataji
sosai wallahi.
Muna futa na warce Dari biyar din hannun Munnu nace." Bani to salon mu manta mu tafi ki rike
ko ai na gano ki" Munnu tace" to mayyar kudi kar ki jimin ciwo a banza" Mimi tace "Munnu har
kij tuna min da wani Abu da ya faru shekaran jiya" Nan Mimi ta kwashe haduwar mu da guy nan
ta fada mata harda watsa masa kud'in da nayi
Munnu ta dinga min masifa kamar wata uwata take "fadin WALLAHI kin cuce mu na rantse da
ina gurin sai nayi miki duka kuma na tsinka ki a gurinsa ke wacece da zakiyi watsa da kudi
masu yawa a daure a kyauwa 'yar bura uba kina fama da kod'add'iyar atampar ki haitaget sai
shegen girman kan tsiya malam" ta k'arashe maganar cike da takaicin abunda na aikata, Mimi
dariya take kamar Cikin zai ciwo ni ko sakin baki kawai nayi INA kallon Munnu tana zuba min
masifa kamar ta ari baki, dariya ta kufce min na fada soron wani gida na zauna inayi biyo ni
sukayi duk da haka Munnu bata daina surutai ba, nace." Munnu WALLAHI ban tab'a ganin me
mugun son kudi ba irinki tabd'ijam!!! Munnu!! Na fada ina dariya. Tace" wallahi da ina gurin sai
naje na tsince kudin na bashi hakuri, Um!!!! A wannan zamani yanda kudi suke wahala ana
bahariyar tsiya" na mike tsaye tare da fadin"in kina so sai in raka ki idan zaki same shi ki bashi
hakuri dama na manta handbag dina a gidan shi" Munnu tace"wallahi muje zan bashi hakuri sai
dai Allah yasa ya bamu kudi" bani kadai ba har Mimi dariya take, nace" Munnu ya ishe ki
WALLAHI kar ki mai damu mahaukata a hanya sai faman dariya kike saka mu. Tace" Ku muje
na daina" muka futa daga soran gidan muka cigaba da tafiya babu Wanda ya sake cewa komai.
Daf da zamu shiga gidansu Hafsa ne Munnu tace"Asama da gaske fa nake muje gidan guy nan
don Allah" nace" zamu je in dare bai yi ba". Mimi dai shiru tayi mana muka shiga gidansu Hafsa
da sallama. Tana zaune kan kujera 'yar tsungo tana gyara wake ta mike da sauri saura kad'an
ta zubar da waken nace" hankali dai ki zubar ki daku wallahi" da ihu!! Tayo kanmu tana murna
nayi saurin gocewa don kar ta rungume ni inji tsaminta, duk sun gane dalilina nayin hakan har
ita Hafsa din, dake ta san halina bata damu ba, ta rike hannunsu Mimi muka shiga d'akinta,
nace." Ke Hafsa INA mamanku" kamar me jin tsorona tace"ta tafi unguwa" nace"sai kije ki siyo
mana ruwa da Lemo mai sanyi"
Tace" Ke fa kin fiye Abu kinga ban kawo muku bane." Nace "si hali na sani ne rowa da......... Na
ki karasawa ina b'oye dariya Hafsa ta d'auke kanta cike da jin haushina ta cigaba da hira dasu
Mimi ni kuma na dinga bin dakin Hafsa da kallo ina kunshe dariya. Ta mike da sauri tare da
fadin" ai yau ina da manyan baki bari in sanya yaro ya siyo muku ruwa da lemo ta futa da saurin
ta.
Mimi ta kalle ni had'e da bata fuska tace"Asma'u babu kyau cin fuska don Allah ki k'yale baiwar
Allah nan haka wallahi tana d'aga miki kafa" nace" me nayi mata to" Mannu tace"ki daina
kiranta da me warin HAMMATA" nace" na daina shikkenan" suka cigaba da shirarsu ni kuma ina
kalle kalle a dakin can na hango Wani rubutu jikin bango anyi shi da blue din maka tare da wani
k'aramin hoto an manna gurin
Mik'ewa nayi na isa gurin INA fadin "Su Hafsa 'yan gayu ken..... Magana tace ta mak'ale a
mak'o gwarona sakamakon gani fuskar guy nan jikin picture din dake manne a bango gaba na
fad'uwa na bi rubutun ina karantawa, abunda nagani an rubuta ya gigita ni gami da dimauta ni.
_*Ilov my love my sweetheart yaya na farin cikina Amjadu ina bal'in son ko zuciyata tana
azabutuwa da kaunar ka zan iya kashe kaina saboda kai ina mutukar kaunar ka yayanaaaaa!*
Na nemi miyau na rasa a bakina ya bushe k'amas na fara tunanin meye hadin Hasfa da guy
nan to? Gashi tana kiransa da yayanta kai duk yanda akai da akwai alamar tambaya, idan
Hafsa suna da alaka da guy nan me ya jawo musu talauci haka duk tsiya si zai taimaka musu.
Motsin shigowar Hafsa naji nayi saurin komawa na zauna jikina na tsiyayar da gumi, Sam su
Mimi ba su ankara da komai ba suna can suna hira, Hafsa ta shigo dakin hannuta rike da ledar
ruwa pure watar da Lemo cocarcolar a ciki guda uku ta aje gabanmu tunda ta shigo nake zabga
mata harara ina mata wani irin kallo, ita ko sai washe baki take tana mana labari,, sai dariya
take tace"Asma'u ga lemon nan" hararata nayi ita da lemon nata ta d'auke kanta kurrum tana
murmushi.
Hirarasu sukeyi babu ni a ciki sai dariya suke yi Hafsa sai tsoma ni take cikin hirarar tasu ina
gwaleta.
Daf da magariba nace "Ku tashi mu tafi haka ke Munnu dama a gida kike". Mik'ewa sukayi a
tare Munnu tace." Kin manta da maganrmu ko"? Nace" ban manta ba" nayi waje na kyalesu tare
suka futo har Hafsa ta raka mu har bakin titi tana godiya sune kawai suke amsa mata ni ko ko
kallo bata ishe ni ba.
Har aka idar da sallahr bamu samu abun hawa ba kun San dai tadda titin k'ok'i yake a baude
bayan haka kuma muna tsakiyar kasuwar kurmi. Sai muka fara tafiya a kasa, gashi gari ya
soma duhu, Wani me a dai-dai sahu yazo ya tsaya gabamu tare da fadin " INA zakuje 'yan mata
"? Nace." Rijiyar zaki scound get Cikin Jambulo " Mimi ta kalle ni da sauri nima na zare mata ido
tare da fad'in" in zakije kawai ki shiga mota mu tafi." Baki na rawa tace " INA tsoron fadan
Umma kina ji fa tace." Kar mu Kai magariba ba ko." Ko sauronta banyi ba naja hannun Munnu
muka shiga Mimi ta shigo duk jikinta a sanyaye mai a dai-dai ta yaja motar muka tafi.
*Tofa*
My fans ko me zai faru a haduwar Asma'u da Amjad a karo na biyu
Ku muje zuwa dai
*21/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA
FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN
TA.
*24*
Dai-dai jaction muka sauka nace "Mimi bashi kudinsa" nan take ta ciro Dari biyar ta bashi ya
dauki Dari uku ya bamu canjin Dari biyu, muka tsalla a nutse. Estate din shiru kamar babu wani
mahalukin da take rayuwa a cike sai dai haske dal-dal a ko ina duk da cewar gidaje uku ne
kawai a ciki,muna shiga karnukan da suke ciki suka fa ihu!! Tare da yowa kanmu duk suka
tsorata ni ko na dake yare da cewa"idan kuna nuna razanar Ku a fili sai su zata b'arayi ne."
Munnu tace." Wallahi asma'u na fara da na sanin zuwa fa" gaba nayi ban saurare ta ba, suka
biyo ni a baya. Daga can nesa na hango shi ya futo daga massalacin dake jikin gidansa, zai
shiga gida yana sanye da doguwar jallabiya fara tas!! Irin ta Larabawa kwata-kwata su Mimi
basu ganshi ba nice na ganshi, nima kuma da suffar shi na gane shine. Muna zuwa bakin get
din me gadi ya bimu da kallo irin na tuhuma nayi saurin cewa" munzo gurin me gidan ne."
Kallonmu yake cikin nazari yace." Kunyi b'atan kai 'yan mata banan bane" nace" kaga malam
wai ba nan bane gidan *Amjad* ba" yace" nan ne 'yan mata" cike da bada umarni nace" to sai
ka bude mana malam" yace." Me gidan bai bada izini ba domin da yasan da zuwan Ku zai fada
min a bude muku get Ku shiga" haushin sa ya kamani na masa wani banzan kallo tare da cewa"
kai malam kalle mu da kyau ka gani ba tsiyace ta kawo mu nan ba arziki ne, kuma mu 'yan
uwan me gidan ne idan kana tamtama kaje ka tambayo shi kaji" kallona yayi naga yayi saurin
risinar da kansa, dama ni haka nake da mugun kwarjinin tsiya in na zuba ma mutum idona baya
iya ketare hukuncina to haka ce ta faru da me gadi bakinsa na rawa yace" bazan barku Ku
shiga ba domun bansan da me kuke tafe ba, amma bari inje in Sanar da masu tsaron kofar shi
halin da ake ciki." Ya ya bud'e karamar kofar ya shiga yana k'okarin kullewa babu zato yaji an
buge hannunsa yayi saurin cirewa na fada cikin gidan INA kiran su Mimi suka shiga da sauri,
nace" tunda mun shigo si munyi me wuyar kuma.
Duk abunda yake faruwa yana kallonsu ta CCTV Camara d'inshi ya cire rigar jikinsa daga shi
sai shout nickar da kwalin Lemo a hannunsa yana sha, murmushi ne kwance a fuskarsa yana
mutukar mamakin taurin kai irin na yarinyar mamaki yake sosai yanda akai har suka samu
nasarar shigowa bayan sun baza karnuka a gurin