Showing 48001 words to 51000 words out of 71336 words

Chapter 17 - BABAN YARO PART 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf

cike da tuhuma."

Me girma governor yaji duk jikinsa yayi sanyi jin yaron yana so yayi masa warwara nan take ya
fara nad'e tabarmar kunya ta hanyar buga tebur din dake gabansa yace." Duk wannan abunda
kake fada basu shafeka ba, lokacin zab'e na futo da kudi Wanda ni kaina bansan iya adadinsu
ba, an rabawa talaka INA so ka sani talaka a yanzu ya fi bukatar ka bashi Dari biyar ko ka bashi
sabulun Wanka sink'i d'aya akan 'yan cinsa, saboda haka rik'e alkawari da sauransu duk bai
shafe ka ni dai ga hukuncin da na yanke! Idan kuma kak'i karb'a kai kanka sai mun rusa ka da
duk abunda kake tak'ama dashi."

Murmushi me ciwo yayi ido jazur yake kallon governor din yace." Ita kuma rantsuwar da kayi fa?
Allah ba abun wasa bane."
Governor ya daga masa hannu a fusace! Yace." Kai kasan Allah ne ? Dubi askin dake kanka,
duk abunda kake muna da labarin sa ka bude hotal har guda biyu ana tata iskanci a ciki kai
kanka kana iskancin ka da mata zaka zo kana fada min Allah anan gurin." Murmushi Amjad yayi
cike da takaici wai shi governor zaiyi wa gurin yana Neman mata, mutumin da kowa yasan shi
mugun asharari ne me mugun son mata da shaye-shaye shiyasa lokacin zab'e 'yan daba ya
baza ko ina suna raba kudi tare da tsorata alumma da jajayen idonsu mik'ewa yayi a fusace! Ya
kalle shi yace." Ina nan kan bakana babu gudu babu ja da baya company kuma yana zaune
daram! Sannan kuma bazan kara farashin kaya na ba." Yana gama maganar sa ya futa daga
ofis din cikin zafi.!


Governor ya bishi da kallo da baki a sake, waya ya d'auka ya kira shugaban kasuwar k'wari
yace." Yanzu-yanzu a rufe a shaguna kuma a watsa 'yan tebur da suke kan hanya.

Aikuwa haka ce ta kasance 'yan kasuwa na hidima da kaswancin su tare da customs kawai

sak'on shugaban kasuwa ya riske su, da ya yawun me girma governor, hankali a tashe suka
fara rufe shaguna kowa na fad'in." Albarka cin bakinsa.
Tun kafin ya isa gida labari ya riske shi, ranshi a b'ace ya dauki wayarsa ya kira governor din shi
kuma a nashi b'angaran ya dauki wayar da sauri yana wani mugun murmushi ya d'auka Amjad
din ya sauko daga kan kudirinsa yasan dai yanzu labari ya same shi, muryar shi sama-sama
yace." Ina kan hanya ta ta komawa gida na samu labarin abunda ya faru yanzu, ina so in fada
maka wani abu, daga nan ba zan zame ko INA ba sai gidan redio zanje in warware musu zare
da abawa." Saura kad'an governor yayi hantsile daga kan kujerar da yake zaune baki narawa
yace." Kar ka kashe min waya ka bari kaji abunda zan ce da kai." Murmushin takaici yayi yace."
A banza abunda baka sani ba shine duk wata shira da ta gabata a tsakanina da kai ina d'auke
da ita cikin wayata so a tafin hannuna kake." governor ya goge wani zazzafan gumi da yake
tsatstsafo masa a goshi lallai yaron nan bashi da mutumci wato ya samu zagin da jama'ar gari
suke masa kwana biyu ya lafa shine zai dawo dashi, baki na rawa yace." Kar........Amjadu ya
katse ta hanyar fadin " baka da abunda zaka ce min a halin yanzu kawai ka janye kudirin ka
nima in janye nawa." Governor yace." Na janye gobe kowa ya futa kasuwa kai kuma ka saurari
abunda zai biyo baya." Murmushi kawai yayi ya kashe wayar ba tare da yace uffan ba."
.governor ya tsaya kawai yana kallon fuskar wayarsa yana mamakin yaya akayi yaron ya samu
dama akanshi har ya raina shi, da matsayinsa yana matsayin shugaba amma yake kashe masa
waya lallai ya zama dole ya hukunta shi.


Rai a bace ya shiga gida ana ta kiran sallahar magariba alwala ya d'aura nan cikin bedroom
d'insa yayi sallah, waya ya kira Rambow ya je ya siyo masa abunci domin wata yunwa yake
ji,ga uban hayak'in sigari da ya babbakawa cikinshi a mota sai da ya shanye a kwali guda kafin
su shigo gida.
Mintuna ashirin tsakani Rambow ya shigo dakin hannunsa rik'e da wata Leda me kyau da k'yalli
ya aje masa tare da jira ko akwai wani umarni daga masa hannu kurum yayi alamun ya futa,
cike da bin umarni ya futa daga dakin. Ledar take away din ya jawo yana dubawa abuncin be
masa ba ya rufe jingina yayi jikin gadon shi yana tunanin yanda za'ayi ya warware wannan
Matsalar da take tun karo shi.


*******
11:00 dai-dai abun ya afku gidajan redio na shirin rufewa suka samu labari babu shiri suka tafi
domin d'auko rahoto, yana zaune inda yake tun d'azu ya fara jin kira na shigowa wayoyin shi,
daukowa yayi yana dubawa Wani d'an kasuwa ne da ya shara ya kira shi suka gaisa hankali a
tashe yace." Yallab'ai Ashe abunda ya faru kenan kai Ubangiji Allah ya tsare ya kiyaye gaba
gaskiya muna cikin tashin hankali." Amjad ya kasa fahimtar maganar sa kawai ya aje wayar ya
dauki dayar zance dai guda ake masa, Zumbur ya mike ya futo parlor yana shirin bude kofa ya
futa sai suka buga karo da rambow zai shigo hankali a tashe, abunda ya d'auke masa hankali
abunda yaji wani Dan jarida na fada a wayar Rambow inda yake cewa" *Inna lillahi wa ina ilahi
raji'un, a yanzu ne muka samu labarin mummunar gobarar da ta afku a katafaran company nan

na Amjadu ABUL Abbas company da ya shahara gurin kawo kaya masu kyau da karko gami da
sauk'i da saukakawa talaka......."*














*26/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: [10/26, 11:33 PM *BABBAN YARO*




*Mallakar_BINTA UMAR*






*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*





*30*




*Innalillahi wa'inna ilahi raji'un."* shine abunda ya futo daga bakin *Amjadu* da sauri ya koma

bedroom din nasa jikinsa na kyarma! Ya dauki wayarsa yana laluben numbar manager, har
wayar ta katse bai d'aga ba, ya kara kira a karo na biyu shiru bai d'auka ba. Parlor ya futo yana
kara kiran wayar.wannan karon tana shiga manager ya d'auka babu abunda ya futo daga bakin
Amjadu sai "Bashir ina fatan babu Wanda ya rasa ransa ko."? Manager yace." Eh yallabai babu
Wanda ya rasa ransa sai dai akwai wad'anda suka samu rauni gurin ceton ransu." Yace." Maza
ka had'a Kansu Ku wuce hospital me zaman kansa ganin zuwa." Manegar yace." Insha Allahu
haka za'ayi." Kashe wayar yayi ya dauki dayar da take aje kan bed an kira yafi sau goma, Sam
bai tsaya daga wa ba domin yasan duk zance daya ne. Futowa yayi rambow da doh-doh suka
rufa masa baya.

Kai tsaye company suka nufa cike da tashin hankali da tarrarabi, kafofin yad'a labarai sun rud'e
da zancan ko wacce ka kamo maganar gobarar ake wanda suke fad'in an rasa meye
musabbabin ta. Kafin kace kwabo labari ya watsu a birnin kano da kewayen ta, cikin daran 'yan
kasuwa suka dinga futowa daga gidajansu suna jajantawa junansu kungiya wasu sukayi suka
nufi company cike da alhini da tashin hankali.


Ido jazur!! Yake bin company ninsa da kallo ya k'one kurmus! Ko ina ka d'aga kai sai hayak'i
yana tashi gurin ya hautsine da 'yan kwana-kwana gami da mutanan gari kowa na bada
gudumar sa." 'Yan jarida sun kewaye shi sun fi su goma dukaninsu suna son suji ta bakinsa.
Duk inda yayi sai sun bishi suna fadin." Young millionaire *Amjadu* "Ko zaka fad'a mana wane
irin hali kake ciki na wannan Abu da ya faru da company min ka me tarin albarka muna bukatar
jin ta bakin ka." Shiru yayi musu kawai hannusa goye a bayansa yana zaga loko da sako na ko
ina hannunsa ya mik'a ya karb'i wayarsa gurin rambow, nan ma 'yan jarida suka yi masa
caaaa!!! Masu d'aukar sa hoto nayi masu vedio nayi masu kafa masa lasifika a dai-dai bakin sa
nayi, wai Dole sai sunji me zai ce a wayar.
Numbar Manager ya kira bugu d'aya ya d'auka tare da fad'in." Ranka ya dad'e." Cikin jarumta
da dakiyar zuciya yace." Yaya ina fatan babu wata matsala duk Wanda yake bukatar taimakon
gaggawa ayi mishi kan lokaci. " manager yace." Insha Allah ranka ya dad'e gashinan ma ana
musu dressing raunin ka da suka samu." "Kuna wane hospital ne."? Manager yace." Malam.
Aminu kano." Ok ganin zuwa." Ya fad'a yana kashe wayar." Yuuuuuuuu!!! Suka bi bayansa tare
da sake maimaita masa maganar d'azu. Doh-doh ya juya da sauri yana zare musu ido!! Oho ko
a jikinsu, hummm! D'an jarida da nacin tsiya. Wani ne yayi tsagal!! Ta tari gabansa ya kafa masa
lasifik'a a baki Tare da fadin." Ranka ya Dade ka taima kayi mana magana muna mutukar
bukatar muji ta bakin ka akan wannan al'amari da ya afku."!!
Murmushi yayi Wanda kana ganinsa kasan na bakin ciki ne, yace." Kuna so ku ji ta bakina."?
Duka suka ce k'warai kuwa ranka ya dad'e. Cikin basarwa yace." Komai dai ya samu bawa
daga Allah ne cikar mutum mumini yarda da k'addara me kyau da mara kyau.amma wani abu
yakan samu d'an adam wani ya zama shine mujaza faruwan al'amarin,saboda haka ina me
tabbatar muku da cewar wannan abun da ya faru to daga sama ne kuma wasu ne suka zama
silar faruwan shi, zan muku misali. D'azu misalin k'arfe shida da rabi na yamma kun Sanar a
k'afafun yad'a labaran Ku cewar 'yan kasuwa su dakata da futa sai zuwa ranar da gomnati ta
umareshi, kafin awa guda da yad'a labaran Ku kuma Ku k'ara 'yada wa cewa umarni daga gidan

gomnati wannan magana an janye ta, da wannan nake rufe magana ta, dukkanin ku kuje ku
tsaya kuyi binkice kanta sai Ku samu abun yad'awa a duniya." Tsitt!!! Gurin yayi tun sanda ya
fara magana har ya k'are kowa na sauraren sa, wucewa yayi da sauri yaran shi suka rufa masa
baya. Kafin kace kwabo gurin ya kara hargitsewa kowa na fad'in albarkacin bakinsa, mutane da
dama sun fi zargin wannan al'amari daga abokan adawar sa ne, wasu kuma suna zargin daga
gidan gomnati ne kowa dai da abunda yake fad'a.
Kai tsaye hospital Malam Aminu kano suka nufa, sai da ya tabbatar da duk Wanda ya samu
hadari a jikinsa ya samu kulawa sannan hankalinsa ya kwanta. Suka kara dawo wa company
Wanda har yanzu ake aikin gurin tare da futo da kayan da sukayi dame ji wasu a jibgi-jingi
wasu sun ci wuta wasu kuma ta fara cinsu basu gama k'one wa ba, sama da k'asa ko ina ka
kalla bak'ikirin babu kyawun gani babu wani abun da za'a mora a gurin. Wani ofis ne a harabar
gurin, nan yaranshi suka shiga suka gyara mishi dake akwai guraran da wutar bata same su a
kasan gurin, nan ya shiga ya kwanta kan wata k'atuwar kujera ya rintse idonsa zuciyarsa kamar
zata futo fili.babu Wanda ya fad'o masa a rai sai mahaifin sa, a take ya mik'e ya dauro alwala ya
shimfid'a abun sallah dai-dai ta tsayiwarsi yayi gaban sarki jallah wa ala yana mik'a mishi
bukatunsa, sosai yayiwa iyayansa addu'a ya shafa, sai yaji zuciyarsa tayi sanyi, a gogon
hannunsa ya kalla uku da rabi na dare, har yanzu yana jiyo hayaniya,jama'a a waje da alama
har yanzu basu gama futo da kaya ba, mik'ewa yayi ya nufi window tare da dage labulen yana
lek'en gurin. Aiki kurum suke kamar kara cab'a gurin suke, ga uban kaya nan dila-dila a watse a
harabar gurin duk sunyi dame ji. Ko mawa yayi ya zauna yana tunanin wane mataki zai d'auka
kansu Alhaji Hashimu me citta dashi kanshi me girma governor nan.
A takaice dai *Amjad* da duk wani me kaunar sa a ranar kwana sukayi cike da bakin ciki gami
da damuwar abunda ya faru. K'arfe shida dai-dai na safe k'afafun yad'a labarai suka fara
labaran su, inda kowa ce tasha ka kunno a lokacin sautin muryar *Amjadu* ce inda yake yiwa
'yan jarida baya ni. Tofaaaa!! Gari ya haustine kowa na zagin me girma governor tare da fadin
cewar da sanya hannunsa haka ta faru tunda shi Amjadu a baya nin da yayi yayi magana me
kamar jiryewa Wanda hausawa suke cewa me kamar Wanka. Tuni k'ananun'yan kasuwa suka
shirya zanga-zanga tare da makamai da tayoyi suka nufi gidan gomnati. Matasan gari marasa
aikin yi suma suka rufa musu baya. Hankalin me girma governor ya kai k'oluluwar tashi! Sam!
Ba zaici haka jama'ar gari zasu tada hankalin su ba, tuni ya baza matakan tsaro cewar a tsare
hanya kar a bari kowa ya k'araso a rufe titi gami da dakatar da ababen hawa.


Muna zaune a rumfa ni Mimi Ummanmu muna karyawa sai ga Yaya Aminu ya shigo hankali a
tashe! Umma tace." Yaya ka dawo kuma."? Cike da tashin hankali ya zauna kusa da ita tare da
fad'in" Umma ina naga ta futa zuwa skull gari ya hautsine!!! Tace." Me yake faruwa ne. " yace."
Wai ina redion ki ne tun jiya ake tashin hankali a gari an je an kone company nan me zaman
kansa. " tace." Wane company ni ne."? Baki na rawa Aminu yace." *Amjadu AbulAbbas
materials* dummmm!!!!!? Gabana ya buga na tsurawa bakin Yaya Aminu ido ina kallonsa.
Umma tace." Ni ko a bakin wa naji wannan sunan."? Mimi tace." Bakin aunty Hauwa." Tace
"yawwa hakane " sai kuma ta rafka salati tana tada hannunta cike da tashin hankali.
Ni da Mimi muka kalli juna rai duk babu dad'i. Umma tace." Ni ina zan sani redio ta ta lalace
dama wayata nake kunnawa to kasan jiya bamu kwana da wuta ba." Yaya Aminu yace." Aikuwa

gari a hargitse yake domin 'yan kasuwa sunan nam suna zanga-zanga kuma an hana futa da
abun hawa. Umarni daga governor. "
[10/27, 12:00 AM] 👄: Umma tace." Gaskiya na jinjina wannan al'amari ikon Allah ko meye ya
haddasa gobarar oho. " yaya Aminu yace." Mutane dai suna zargin 'yan adawarsa ne, wasu
kuma suna zargin da sa hannun gomnati har yanzu dai an kasa gano meye ya haddasa
gobarar." Cike da al'ajabi Umma tace." Ai dole yaron nan yayi makiya da mahassada wallahi
tunda yana son talakawa da tsoron Allah, kaga kuwa masu kud'in kasa zasu sanya shi a gaba."
Yaya Aminu ya mike tare da fadin 'Bari in karb'i wayar Garba yayi rocouding din muryar shi
lokacin da yake jawabi ke kanki Umma ki ka sauarari maganar sa zaki San abun shiryayye ne."
Futa yayi ya barmu da jiki a sanyaye, niko tsabar zura jiki sai na fara tunanin ko a wane hali
yake ciki.har na k'agara Ya Aminu ya kawo wayar inji muryarsa wani irin mugun tausayin sa na
damun zuciyata, to b'angaran Mimi ma haka yake domin ita har ta fara k'ananun hawaye.

Ya Aminu ya shigo da waya a hannunsa ya zauna kusa da Umma ya kunna mata voice din
*Amjadu* lokacin da yake magana da 'yan jarida jiya.

Tunda ya fara maganar nayi sak! Ina sauraron sa, muryarsa radau! Kamar Wanda baya cikin
tashin hankali babu karaya da rawar murya a lafazin sa, kana ji kasan shine me gaskiya, Umma
tace." Ai daga jin wannan maganar ma kasan shiryayyiya ce makirci ne, kawai da hassada
kuma zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi." Yaya Aminu yace" Wallahi kuwa Umma, nake
fada miki, guy yayi a rayuwa yana mutukar kaunar talaka da cigaban matasa Sam dukiyarsa
bata rufe masa ido ba, dukiyarsa ta talakawa ce gami da mabukata da marayu, to Kin San an
ce mutum tara yake bai cika goma ba, duk da haka mutanan gari suna zarginsa da neman mata
wai har hotal ne dashi da karuwai suke watse wa." Umma tace." Wa'iya zubbilah kai jama'a
mutane ba a iya musu dama hakane duk inda Allah ya daukaka bawa to sai ya samu yan
hassada Allah kasa mufi k'arfin zukatanmu." Yaya Aminu yace" ameen suma ameen. Suka
cigaba da tattauana maganar.ni da Mimi shiru babu bakin magana, tunda ya Aminu ya fara
maganar sa nake addu'ar Allah yasa sharrin mutanan gari ne guy baya Neman mata, domin a
lokacin ji nayi wani irin Abu yazo min wuya na bakin ciki. Wani gefe na zuciyata Yace min a
kanki zaki gazgata shin shi din mane min mata ne ko kuwa bayan ke ga Alina,, kuma zuciyata
ta dinga min sak'e-sak'e a kanshi gefe guda kuma ina tunanin ko wane hali yake cikiA yaanzu


******
Duk inda aka zauna can kenan gungun matasa da magidanta 'yan kasuwa kai har da
ma'aikatan ma suma wasu daga cikinsu suna jajanta al'amari, waya kuwa *Amjadu* har daina
d'agawa yayi da k'arshe ma da abun ya dame shi, rambow yasa ya kashe wayoyin gaba d'aya.
Ya kulle kanshi a daki shi kad'ai duk irin mutanan dake zuwa gurin shi ya hana a shigo dasu."
Tv ya k'ura ido yana kallon labarai na k'arfe goma dai-dai tashan NTA sosai ya girgiza ganin
yanda matasa suke tashin hankali a gari tare da kona tayoyi had'e da rigima da 'yan daba
mutanan me girma Governor jama'ar gari sai gudu suke, wannan al'amari da ya faru ba iya
kacin najeria ya tsaya har kasashen waje suma sai da suka nuno Company tare da rigimar da
ake yi a kano din cikin labarai su na safe.

Mik'ewa yayi da sauri ya futa waje. Suna ganin futowar sa suka k'araso dukkanin su. Ya kalli
Doh-doh tare da umartar sa da maza yaje gidan redio na express ya d'auko masa d'an jarida
daya yana so zai yi magana.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login