Showing 12001 words to 15000 words out of 71336 words

Chapter 5 - BABAN YARO PART 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf

ita na mike ina gyara zaman hijab

dina,gefe guda kuma ina tunanin k'aryar da zamu sharara a gida, domin ina sane na kashe
wayata saboda nasan za'ayi ta damuna da kira bani da amsar bayarwa.



Muna futa bodyguard d'insa na tsaye bakin kofa duk suna sanye da bakaken kaya hannunwan
su da safa bak'a kana kallon fuskarsu zaka San babu wasa.



Suka fara kawo gaisuwa gurin ogansu, kallon banza nayi musu nayi gaba Mimi ta biyo bayana
Simi-simi.



Doh!-doh ne naga yazo ya wuce ni da sauri yaje ya bud'e wata arniyar mota ba irin ta jiya ba,
wannan daga ni ma sabuwa ce kalar ta ruwan zuma ne gaskiya motar ta burge ni.



Tun kafin ya k'araso saboda k'arfin hali irin nawa naje na kama murfin baya zan bude in shiga.


Wata azabbabiyar tsawa doh-doh ya buga mun fa sauri na saki murfin na m ma gefe ina zare
ido.



Cike da karsashi ya k'araso ya shiga Alina ta shiga ta zauna kusa dashi, harararta nayi ina jin
wani mugun haushin ta. Doh-doh ya maida murfin ya rufe ya zaga da sauri ya shiga Mazaunin
sa.



Rambow ne ya zauna kusa dashi sai Alina sai ni Mimi ce ta k'arshe shiga.


Cike da ladabi Doh- doh yace." Boss ina muka nufa ne."?


Mimi ya d'an kalla da gefen ido yace." Wace unguwa ne."? Baki na rawa tace." Badawa ne
wajan giginyu."

Yace." To kaji ko".?

"Yes sir." Doh-doh ya fada yana k'okarin futa daga gidan.


Shiru motar babu wanda ya ce ci kanka gudu kawai take kan kwalta. Ina kallonshi a fakaice, ya
makala airphone a kunnenshi sai gyad'a kai yake yana bin wak'ar da yake ji, ba daina najin
muryar mawak'iyar daga bakinshi na fahimci janeefar Lopez ce.cikin wak'ar me taken *a into
mamah.*


Kalle kalle nake domin in tantace wace anguwa ne muke ciki, *Jambulo* sai yanzu na gane
unguwar akwai wata friend dinmu dake unguwar mun tab'a zuwa duba mahaifin wani lokaci da
yayi hatsari. Muzo dai-dai kan kwana inda wasu gungun almajirai suke zaune da 'yayansu maza
da mata.


A hankali naji yace." Tsaya anan."

Doh-doh ya samu guri yayi parking. Da sauri shadow ya futo ya bude masa kofa ya futa. Ido na
bishi dashi cike da mamaki ganin yana zuwa gurin almajiran nan. Aikuwa suma suna ganinshi
suka fara gyarawa


D'aya bayan d'aya ya dinga binsu yana saka musu kudi Wanda ban San adadin su nasan dai
'yan dubu-dubu ne. Duk yawansu sai da suka samu.



Cikin sauri ya dawo motar Shadow ya maida murfin ya rufe muka bar gurin.


Gaskiya ni da Mimi munyi mamaki sosai da sosai da lamarinsa daga k'arshe muka cigaba da
tunanin yadda zata bulle mana a gida.




Kallon shi nake so nayi zuciyata tana hana ni, a sace na d'ago kaina muka had'a ido dashi ta
mirror wani miskilin murmushi ya Sakar min yana sosa sumar shi. Na kauda kaina INA jan

k'aramin tsaki, har yanzu da akwai k'ulli a kaina dangane da Alina.



Kwanar gidanmu Mimi ta nunawa Doh-doh nayi saurin dago kaina tare da fad'in." Kai sauke mu
nan ma k'arasa da k'afafun mu."

Ina da manufa ta tafad'ar haka.


A hankali motar tayi parking gefen hanya. Na kama murfin motar da sauri zan bude na kasa sai
da Shadow ya futo ya bude mana, na futa ina gallah masa harara.


Ido yayi wa Shadow magana naga ya zura kansa ta window motar wani abu ya mik'o masa,
yana dagowa naga kud'i daure da kyuare 'yan dubu-dubu.


Shadow ya mik'o min tare da fad'in".Gashi oga yace a baki."

Kud'in na kalla shekeke ina sauri mubar gurin domin nasan halin 'yan unguwar mu abun
magana baya yi musu wahala.


Mimi sarki 'yan san kudi ta dinga zungurin kafad'a ta wai in karb'a



Tuni zuciya ta tafara min wasiwasi kan wannan uban kud'in da yace a bani,wato yana nufin ya
biya ni kud'in iskancin da yayi min kome oho,me yasa bai bawa Mimi ba.


A tunzure na karb'i kud'in kai tsaye gurin shi na nufa, na zura kaina ta window na motar na cire
kyauran dake daure da kud'in.



Kallon juna muke ni dashi, fuskarta babu fara'a na fara zuba masa kud'in a jikinsa tare da
fad'in." Wannan kud'in da ka bani basu isa su siye ni ba, baka da abunda zaka yaudare ni dashi,
kasani inanan sai nayi maka illah a rayuwar ka tunda ka sake ka shiga rayuwata sai kayi daka
sani wallahi."

Da mugun gudu Shadow ya kawo min duka na kifa kaina cikin motar har ina buge goshina. Da
sauri na dago Shadow ya daga hannu zai kwada min mari!!!!!!!


"Shadow!!! ".
Ya fad'a cikin wata irin murya wacce ban san shi da ita ba, muryar dai tafi kama da ta Wanda
yake cikin tsantsar b'acin rai."!


Shadow!! Ya sauke hannunsa yana wani irin huci!! Jikinsa sai tsuma! Yake.


Ni kuma duk na furgice so nake kawai Shadow ya bani hanya in wuce kar wani Wanda muka
sani ya futo daga cikin layin mu."



K'asa-k'asa naji yace." Shigo mota mu tafi." Shadow yayi min wani irin kallo me nuna zamu
had'e dake ne watarana ya bude mota ya shiga.



Ina Kallon Alina tana kwashe masa kud'in da na baza a jikinsa sai harararmu take.


Tsaki naja na matsa gefe ina taufar da yawu.


Hannun Mimi na kama muka fara tafiya Mimi bina take simi-simi jikinta DUK yayi sanyi da
abunda nake aikata wa.


*Ajiyar zuciya!* kawai yake saukewa zuciyarsa tana masa sak'e-sak'e akan yarinyar tunda yake
a rayuwa babu macan da ta tab'a yi masa Abu irin Wanda yarinyar tayi masa.

Sam baya so ya nuna mata hakikanin waye shi baya so ya nuna mata mugunta saboda shi
mutum ne me tausayin talaka a duk inda yake ya lura kuma takalawa ne sosai babban abunda
ya kashe masa jiki dasu jin abunda d'ayar take fada masa jiya cewar su marayu ne babu uba ya
tabbata mahaifiyar su tana fama dasu, amma ya lura sai ya saita yarinyar domin abun nata yayi
yawa, yanzu dai tayi na farko tayi na k'arshe kuma sun rabu domin babu ita a rayuwarsa a
yanzu amma mutukar ta shigo gonar sa ko Allah zai sake had'a su a wani guri to tabbas zai
nuna mata true colour d'insa sai ya gigita mata rayuwa, da wannan tunanin ya cire abunda tayi
masa a ransa ya bawa Doh-doh umarnin tafiya.

Cike da tsoro muka lab'e soran wani gida nida Mimi muna shawarar wace irin k'arya zamu
girbawa Umammu in muka je gida.




*Meye Asalinsu ne*?


Asalin su shine.............


Zamu had'u dake a pege nagaba
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA
FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN
TA.



*16*




Malam Sulaiman mai madara shine mahaifin Asma'u d'an Asalin garin kano unguwar k'oki a ka
haife shi, su goma sha shida ne gurin iyayensu maza goma mata shida maihaifinsu da
mahaifiyar su duk sun rasu ba dadaewa ba, lokacin ma an haifi Asama'u kasancewar dama ba
wani arziki ne dasu ba yasa babu wani gado da suka bar musu 'yan uwansu mata duk sunyi
aure suna gidajan mazajansu suna sana'oinsu da zaman aure to suma haka take a garesu duk
suna da aure da yara ko wanne na buge bugen sa na kasuwanci da aiki yanda zai rufawa
kansa asiri, kwata-kwata basu da zumumci ga junansu kowa kansa ya sani da 'yayansa idan
ba wani taro ake ba babu me ziyartar d'an uwansa daga matan har mazan duk da cewa 'yayan
mutu d'aya ne kowa harkar gabansa yake.

******
Malam Sulaiman yana aiki a company madara ta cowbell wanda yake sharad'a dake ya jima
yana aiki sai suka bashi gida a Badawa sai ya bar hayar da yake yana murna ya koma gidan
kansa tare da iyalinsa.


Matar shi Mariya 'yar nan makotansu ce sukayi auran soyayya suna da yara hud'u maza biyu
mata biyu Hauwa'u itace ta farko tayi aure a giginyu kusa dasu tana da 'yarta d'aya Islam.
Aminu shine na biyu yanzu haka yayi diploma da dabara yana so ya cigaba DOMIN ya samu
digree babu kudi sai buge-buge yake, Asma'u itace ta uku gurin iyayen ta, ta kasance Mara jin
magana me taurin kai tunda ta taso haka take da bushashiyar zuciya ko fada suke da yara bata
kuka, tana tsananin kama da mahaifin ta sosai shiyasa yake mutukar kaunar ta duk abunda tayi
dai-dai ne

Asma'u tana da kyau na ban mamaki da tsarin jiki me kyau b'aka ce amma ba sosai ba Sam
baza a sakata a layin farare ba, tana hanji da manya ido gami da k'aramin baki, tana da yalwar
gashi kanta da gira gashin idonta gazar-gazar dasu sun kawata mata ido tana manya nonowa a
tsaye k'yam dasu sharp dinta ya futo sosai cikinta a dame yanayin tafiyar ta sauri-sauri yanayin
zafin ta da yanayin saurin bakinta domin wata maganar ma in ta fada mutum bazai ji ta saboda
saurin bakin ta.



Mimi marainiya ce 'yar k'anwar Mariya ce Umma kenan mahaifiyar su As'amau ta d'auko ta ta
shayar da ita tare da Asam'au Mimi ta girmi Asma'u da wata hud'u.babu Wanda zai ce ba
Mariya ce ta haife ta ba duk abunda za tayiwa Mimi tare take musu shima Sulaiman ya rike ta
amana kamar 'yar cikinsa



Yanzu haka suna da shekaru goma sha shida a duniya matakin karatu kuma sunyi saukar
alk'urani me girma, b'angaran boko kuma suna ajin k'arshe a suna jarrabawar futa makarantar
da sukeyi ta kudi ce sosai da sosai wan Baban Mimi shine ya tsaya musu dake lecturer ne yana
da hanyoyi da dama suna gane karatu sosai da sosai.

Alina 'yar wani hamshak'in me kud'i ne anan unguwar babanta me fada ajine Sam bai damu da
abunda 'yayansa suke ba shima sharholiyar sa yake da Matan bariki duk 'yayansa maza ne
Alina ce kawai mace shiyasa duk shekara momynta sai ta had'a mata birthday a guri me tsada
anyi b'arnar kudi sosai Tuntuni 'yan class d'inmu suke zargin Alina da karuwan ci, nice me

zak'ewa ina cewa k'arya ne tunda basu ganta ba to su daina shedar zurur, Alina tana ji dani
sosai a jinmu ganin yanda nake kare ta gurin kawayen mu, masifa ta yasa idan na saka baki sai
suyi shiru ita kuma sai ta mik'o min tamfatsetsiyar wayarta k'arar Samsung ina karb'a zan shige
karkashin bainci in bude ma'adanar aje video na fara kallon blue film dake tana dasu sosai a
wayarta ina fara kallon a jikina zan san ya sanja tsigar jikina ta tashi k'uruciya ban San kome ye
ba, zan ta mutsu-mutsu in naji suna nishin nan sai naji idona yana wani irin Abu,, yayin da zanji
nonowana suna k'aik'ayi amma don jaraba bazan fasa gani ba, sai nagama zan futo ina matse
cinya ta, ranar duk karatun da akayi ya wuce ni haka zan yini sukuku dani.



Mimi Sam bata San me nake kalla ba domin ko da wasa bata lekowa saboda tsoran masifa ta
sai zatayi ta damuna da tambayar me yasa taga idona sun kankance sunyi jajazur, kawai zan
ce Mata kaina ne yake ciwo shikkenan sai ta bar maganar


Muna komawa gida nake zubewa kan katifarmu in ta murk'ususu ina jin wani fleengs Wanda
ban san ko menene ba, sai in kwana in yini kafin in samu sassauci amma fa sa'i da lokaci
marata zatayi ta daurewa ban san KO menene ba, haka Umammu zata gaji da tambaya ta tayi
shiru ta k'yaleni.


Tunda na gano kallon blue film din nan ne yake saka ni shiga irin wannan halin sai na daina in
Alina ta bani wayarta ko da wasa bana bude video sai dai in kalli hotuna in wuce zatayi ta
damuna da cewar ki shiga video akwai sabbi sunyi sosai zasu d'ebe miki kewa, masifa nake
mata ince na daina kallo ita taje tayi tayi tunda baza ta daina ba. Sai tayi min Dariya kawai ta
bar maganar saboda tasan halina.




Mota ce ta banke mahaifin mu yayin da yake kan mashin d'insa ya Bari gurin aiki da niyar
komawa gida take a mutu ko shurawa baiyi ba, mun shiga rud'u da tashin hankalin rasuwar
Babanmu nayi kuka kamar babu gobe kasan cewar nasan shine jigonmu madogararmu ni da
'yan uwana Yaya Aminu bashi da k'arfi Asalima buge-buge yake na makaranta Aunty Hauwa'u
kuma mijinta bashi da k'arfi itama 'yan sana'oi take a gidanta tana rufawa kanta asiri.



Kun San dai yanda Aikin company yake baka da fansho balle garatuti farin cikinmu guda shine
gidan da muke ciki Company ya mallakawa Babanmu ta kardun ma suna hannunsa bamu da
fargar wannan.

Tunda 'yan uwan Babanmu sukayi mana taimako na marmari sai kowa yaja zugarsa suka gudu
suka barmu da wahalar mu,


Inda Allah ya taimake mu ma abokan aikin Babanmu lokacin da suka zo. Gaisuwa sun bamu
kudi sosai har da masu kayan abunci fa sutturu shine muka rufa kanmu asiri

Ummamu da Aunty Hauwa suka fara harkoki da sauran kud'in da sukayi mana saura a hannu
Inda Aunty Hauwa take shiga kasuwar kwari tayi sare sare na atamfofi mayafai da takama tazo
ta raba cikin unguwar su, ita kuma Umammu ta fara sana'ar siye da siyarwa na cikin gida kamar
su mai kalanzir gwayi bussasun kayan miya da ice da sauransu, da wannan muka dogara Yaya
Aminu ya dage yana ta karatu inda k'aramin kaninmu me bina kenan Mussad'iq yake k'aramar
makaranta zasu jarrabawar futa.


*Wannan shine tak'aiaccan tarihin Asma'u*




*Cigaban labari*



Mimi tace." Anya Asma'u shawarar da kika fada tayi kuwa wallahi ba lalle ne aunty Hauwa ta
yarda ba kin San halinta."


Nace muje muyi wannan k'aryar zanje gurin SQ in karb'i kati bashi in sa a wayata zan bugawa
aunty in lallab'ata ko tazo gida tace hakane."


Mimi ta gyda kai kurrum tace." Shikkenan muje Allah yasa kar Ummamu tayi fushi wallahi
tausayin ta nake ji."


Nace." Nasan yanda zanyi da ita kawai kiyi addu'a kar Allah yasa Ya Aminu baya nan kin san
halin masifarsa ko Ummamu ta hak'ura zai iya tun zurata."

Mimi tace." Hakane to Allah yasa muje mu tarar ya tafi makaranta." Nace." Amin dai.


Muka futo a tsane ke muka doshi kofar gidanmu yara na shiga wasu na futowa masu siyayya
kasan cewar safiya ce yanzu.




Umammu na zaune a kujera 'yar tsuguno tana durawa wata yarinya kalanzir cikin wata kwalba
mukayi sallama muka shiga.



Amsawa tayi ba tare da ta dago kai ta kalle mu ba ta sallami yarinyar ta futa muka k'arasa kusa
da ita Tare da zama kan tabarma da ke shimfide a tsakar gidan


Nace." Ummam..... Dago min hannu tayi Tare da fadin ." dakata!" Shiru mukayi gabanmu na
fad'uwa ni da Mimi tace." Daga gidan ubanwa kuku a ina kuma kuka kwana."


Tuni na sanja shawarar k'aryar da muka shirya bakina na rawa nace." Daga gidan Kawu
Yunusa mike."



Cike da mamaki take kallona tace." Me ya kaiku gidansa bana son k'arya fa."?



Nace." Ummamu ki yarda damu wallahi daga gidan sa muke kuma anan muka kwana ai kin San
wannan kawar tamu Alina ta bayan layin nan 'yar gidan Alhaji Santana ko."



Umammu tace." Na santa mana me ya hadaku da ita mara tarbiyar yarinya."



Mimi tayi sauri tace." Umammu kiyi yafe mu jiya munyi miki k'arya zamuje gidan aunty Hauwa
wallahi ba can muka je ba Alina ce ta gayyace mu birthday dinta shine muka je can."

Salati Umma tasa tace." Kuka je birthday din Alina abunda naji ana cewa ba acikin gari ake yin
sa futa ake akama guri 'yan iska su taru a gurin so kuke Ku jawo min abun magana a gari ni
Mariyatu."
Ta k'arashe maganar cike da takaici.


Nace." Kiyi hakuri Umma wallahi munyi kuskure ."

Tace." Rufe min baki ko i n buge shi don ubanki nasan wannan kaidin duk daga gurin ki ya futo
Mimi baza ta aikata haka ba."

Shiru mukayi. Cike fa tsoron tashin hankalin da muka hango a idon Umma ta cigaba da cewa "
zaku fada min inda kuka kwana ko sai na saka Aminu yaci ubanku



Baki na rawa nace." Gidan Kawu Yunusa ne ki buga waya ma ki tambaya kiji."

Na fad'i hakane saboda nasan bazata buga wayar ba saboda basa shiri dashi wan Babanmu ne
shi Kawu Yunusa.


Tace." Me ya kaiku gidan sa mutumin da ya manta daku a duniyar nan ai babu abunda zancewa
Yunusa ya hofintar da zuri'ar Dan uwansa.



Nace." Wallahi Umma muna futowa daga gurin da akayi birthday din muna tsaye gefen titi muna
neman mota kawai sai motar. Ya Musa tayi parking yace." Mu shigo ya kaimu gida, ganin dare
yayi yasa yace bari ya wuce damu gidansu in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login