Showing 24001 words to 27000 words out of 71336 words

Chapter 9 - BABAN YARO PART 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf

cin alwashi a kansa.
Governor da yaga abun yana so ya shige gona da iri sai ya tsawatar amma duk da waha wasu
basu bari ba sai da suka gama fad'ar abunda yake bakinsu sannan suka koma suka zauna
suna huci!! Yana zaune yana kallonsu fuskarsa d'auke da kwantaccan murmushi, da alama
abunda sukayi din bai dame shi ba, shiyasa dukaninsu yake musu kallon mahaukata wadanda
basu San me suke ba kuma masu son Kansu da iyalinsu. Hakan da yayi musu ya mutukar tun
zura zucuyarsu sun so ya tanka musu su ci masa mutum ci sosai sai yayi aiki da iliminsa ya
kyalesu a matsayinsa na me k'ananun shekaru akan su sai ya dauki girman kawai, shi kanshi
governor yasan shi yake da gaskiya, tun farko da suka kai masa maganar to amma don kar
suce ya goyi bayansa yasa ya amunce da zuwa taron gashi sun zo suna hauka.
Yace."Young ina ganin abu d'aya zamuyi Wanda zai kawo maslaha a tsakaninmu." Duk sukayi
shiru suna sauraron sa me girma governor ya cigaba da cewa." Zaka k'ara farashin kayanka
akan yanda ka sauke a da sukayi raga-raga Wanda hakan yasa sauran 'yan kasuwa kasuwar
su ta tsaya saboda duk wani me Neman sauk'i sai ya gudu company ka domin ya d'auko kaya
ina Neman wannan alfarmar a gurin ka ka d'aga 'yan ?uwanka kafa suma su samu nasu
kason." A lalace *Amjad* yake kallon me girma governor ranshi in yayi dubu ya b'aci a
matsayinsa na shugaban aluma talaka da me kudi har wani da bashi da mukami a gomnati ya
iya sadaukar da kudunshi duk dan a kan talaka yaji dad'i amma shi yana maganar ya tsawwala
farashin kayansa domun a kuntatawa talaka abunda bazai yi wu bane. Da karsashi yace."
Yallab'ai wannan magana da kake fada Sam baza ta samu ba ka sanja wata domin ni nan daka
ganni dukiya ta ta talakawa ce so ina ganin babu Wanda zai nuna min ga yanda zanyi da ita."
Sosai sukayi mamakin abunda ya fadawa governor shi kansa yayi mamaki lallai yaron yana da
tsaurin ido a matsayinsa na shugaba yace ga abunda za'ayi amma yace bazai yi ba ran
governor ya mutukar b'aci sosai da sosai. Alhaji Hashimu me citta yace." Ranka ya Dade kaga
kaima ya nuna maka halinsa ko ai da ni na tun yau ba nasan yaron nan DOMIN tun ubanshi na
yawon haya da bin kasuwanni karb'o kaya nasan bashi da mutumci ubanshi Abbas mugun Dan
taurin bashi ne a wancan lokacin kafin 6a mutu da k'yar na samu ya biya ni kud'ina duk da haka
da wasu a kansa ya tafi kuma baya fe masa zanyi ba, Alhaji Sunasi me leshi yace." Gashi ya
mutu ya bar baya da kura zakuwa mu dauki mataki." Kafin ya k'arasa *Amjad* ya mike tsaye a
zafafe! Ya daki k'aton tebur din dake tsakiyar su robobin ruwa da Lemo suka dinga tsalle suna
fadowa kasa, muryarsa a sama! Alhaji Hashime kake kome ? To ka kiyaye ni wallahi bani da

kyau, na fuskanci kai baka san ka girma ba idan baka sani ba ina so in sanar da Kai ku in kara
tuna maka kana magana ne da *Amjadu d'an Asali Amjadu Dan Abul Abbas* ko a wannacan
lokacin da muka gwabza da kai ba samu riba ballanta na yanzu saboda haka ina kasanar daku
dukkaninku Ku rike girmanku kar Wanda ya shigo gonata zamu sanya k'afar wando guda
dashi.!!! Yana gama maganar shi ya d'ibi wayoyinsa ya fuce, da zafin zuciya tafiyar da yake
tamkar zai dasa tayal din gurin.
Tsit!!!!!! Gurin yayi kowa yana mamaki abunda Amjadu ya aikata tabbas yaron ya cika tak'adiri
kuma mara tsoro. Me girma governor ya sauke ajiyar zuciya ransa a bace yace." Yaron nan
bashi da kunya ko kad'an kuma dole gomnati ta dauki mataki a kansa za mu nuna masa mulki
da izzarsa zai da k'arfin mulki zamu nuna masa shi ba kowa bane tun fmda har yak'i ya bamu
hadin kai mun zauna domin a samu sulotion mu samu mafita ya karya doka ya nuna ma bashi
da lokacin mu to duk Ku kwantar da hankalin Ku zaku ga abunda gomnati zata aiwatar akansa."
Dukaninsu fara mik'a godiyarsu ga governor, ya rufe taro da addu'a kowa ya watse zuciyoyi
babu dad'i!!


*****

Yana kwance ya bayan mota da karan sigari a hannunsa ya kusa shanye kwali guda kana
kallonsa kasan ransa ya bace yake saboda yadda jijiyar kansa tayi rad'ad'a busa sigari kawai
yake yana shawarwari a zuciyarsa ta yanda zai bulluwa magautansa, Ciki da ladabi Doh-doh
yace." Sir ina muka nufa."? Shuru yayi masa sai da ya kara maimaitawa sannan yace."
Gyad'igyad'i gidan Granny". Rambow yace" Sir yau ka tuna da ita kenan."? Shiru yayi masa
kawai ya lumshe idonsa.

Suna shiga get din gidan masu gadi gami da masu aiki suka dinga zuwa suna kawo gaisuwarsu
ya futo daga mota a tsanake ya na amsa musu ya wuce ciki gidan cikin kakkarfan takunsa.


Wata lafiyayyir dattijuwa na gani zaune a wani kayattacan falo da ya gaji da haduwa komai na
more rayuwa akwai kwata-kwata farlon baiyi kama dana tsohuwa ba tana zaune cikin kujera me
cin mutum guda sanye take da Riga da zani na atamfa ammata dinki irin na tsoffafi idanunta
sakaye da farin glashi na kara k'arfin gani carbi na gani a hannunta tana ja ta zubawa tv ido
tana kallon tashar sunnah tv malam jafar mahamud Adam na tambihi *Allah ya jaddada rahama
a gareka malam*
Granny kenan kakar *Amjad* ta gurin ubah sunanta na asali Saratu bafulatana ce usul duk da
ta tsufa amma har yanzu da hasken ta tamkar tsada k'afar nan kamar ka matsa jini yayi
sartuwa, sai ince muku duk kamaninta *Amjad* ya kwaso sosai suke da kyau kamar ka sace ka
gudu. Tana zaune ta dinga n k'amshin turaransa da sauri ta kalli kofar shigowa aikuwa shi ta gani
sunkuye yana k'okarin cire takalman sa, d'auke kanta tayi da sauri ta dauki goranta ta b'antara
k'asa-k'asa tace." Bazan kula ka nima tunda sai ka ga dama zaka zo gareni kallonta ta cigaba
da yi kamar bata San ya shigo farlo ba, abun mamaki sai taga ya nufi inda wasu

tangama-tangama hutuna suke jingine yana zuwa gurin ya tsunguna tare da sanya hannunsa
yana shafa jikin hotan, gabanta ya fad'i tace." Yau a n tab'o zuciyarsa kenan." Mik'ewa tayi ta
biyo bayansa shi kuma ya rungume hotonan a k'irjinsa yana kukan zuciya wasu zafafan
hawaye suka biyo kucinsa. Granny ta dafa kafadarta muryarta a tausashe tace." Tashi muje ka
fada min wanene ya tab'oka dama tunda na ganka nasan akwai dalili ka aje hotan an Wanda ya
mutu ya Riga ya mutu addu'a ce kawai tsakanin mu dasu." Da k'yar granny ta shawo kansa ya
aje hoton a inda ya mike ta kama hannunsa suka bar gurin ni kuma da sauri na kalli hoton wasu
mutane nagani mace da namiji jikin hotan da alama mata da miji ne namiji yana tsananin kama
da granny macan kuwa kana ganinta kaga a salin bahaushiya domin bak'a ce amma kuma me
kyau hanci har baka. Tausayi *Amjad* ya bani sosai ganin yana tsiyayar da hawaye da alama
yana da alak'a da mutanan dake jikin hotan. Farlo na bisu domin jiyo muku me suke
tattaunawa.


*Wanene Amjadu?*


Zamu had'u daku a pege na gaba.











*18/October/2009*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA
FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN
TA.

*21*






Abul Abbas mutumin Chadi ne inda nema ya kawo shi garin Kano bayan rasuwar mahaifinsa
sai ya d'auko mahaifiyar sa, Saratu sukayi kaura daga mahaifarsu suka dawo Kano gaba d'aya.
Suka bar 'yan uwansu da abokanan arziki a can sai dai suna zuwa duk shekara su duba su,
tunda Abbas ya dura a garin na Kano bai zauna ba duk wata kasuwa da ta shahara a garin
yana shigarta ya nemi kudi a cikinta yayi Hulda da mutane sosai da sosai hakanan kuma ya
karb'i kayayyakin mutane ya juya har Allah ya sa ya samu nasa jarin inda ya kafa tebur a bakin
titi kafin kashiga ai nihin kasuwar. Babu laifi yana samun kudi sosai saboda duk Wanda ya
kwana ya tashi cikin garin Kano ya San da zaman kasuwar k'wari yara da manya kasuwa CE
me albarka da d'umbun tarihi cikin ikon Allah ya siyi gida maidaidaci can rijiyar zaki sai suka
tashi daga hayar da ya kama musu. Nan mahaifiyar sa ta matsanta masa da dole yayi aure,
lokacin Neman kudinsa ne kawai a gabansa yace kawai ta nema masa mata,aikuwa batayi
sanya ba ta nema masa Aishatu 'yar kusa da d'akinta dake gidan da suke hayar basu kadai
bane, Aisha yarinya kntsatsaya me hankali gami da ilimin addini, nan take iyayenta suka yadda,
to shima Abbas da mahaifiyar sa ta fada masa bai musa ba domin dama yana yaba kamala da
nutsuwar yarinyar, lokaci guda aka sanya rana Abbas ya hada lefe abunka da Dan kasuwa
komai yayi na bajinta lokacin buki yayi akayi cikin aminci da yardar juna amarya ta tare gidan
mijinta dake rijiyar zaki. Daki da rumfa manya sai k'aton tsakar gida,dakin Inna na gefe guda
can wajan kofar futa.rayuwa suke ta fahimtar juna dake Inna bata da sa' ido kan suruki shiyasa
suke zaune lafiya cikin ikon Allah Aisha ta samu ciki, to tundga samuwar cikin nan arziki yayi
musu sallama Abbas ya bude k'aton shago can cikin kasuwa ya fara harkokinsa da manyan yan
kasuwa, makotansa na kasuwa cikinsu akwai Alhaji Hashimu mai citta sai Alhaji d'an Akushi,
sai suka Dora masa ido sosai da sosai kyashi gami da haddasa duk suka dame su gashi dai
suma suna ciniki suna samun rabonsu amma sun d'ora ido kan abunda Abbas yake samu a
cewar su shi na Dan gari ba yazo yana cin albarkar gari.nan suka farayi yi masa bita da
k'ulli,hakan da suke sai ya zame masa alkairi domin kofofin samun sa ne suka kara budewa,
*Dama Annabi ya fada cewa a yayin da kake wa mutum hassada to a lokacin Ubangiji zai
cigaba da d'aga shi a duniya idan kun faya kun ta sauka a kan bawa to babu wani mahalukin da
ya Isa yace ba haka ba Allah ta tsare mu da ciwon hassada domin babban bala'ine*

Lokacin da Aisha ta haifi *Amjadu* sai da talakawa sukayi farin ciki dama lokacin cikin azimi ne
dab da sallah Abbas ya sauke farashin kaya ko na ko wane shagunan shi a lokacin sun kai
bakwai cikin kasuwar k'wari uku na takalma ne uku na kayan sawa daya na mayafai ne, haka ya
dinga bonanza mutane suka dinga zuwa suna siyarwa iyalinsu kaya DOMIN suyi bukin sallah,
sosai WANNAN abu da Abbas yayi ya dugun zuma rayukan 'yan kasuwa bari ma su Alhaji.
Hashimu take suka fara shirya masa sharri Wanda suke so ya tattara ya bar k'asar gaba daya

ya koma tasu k'asar.
*Amjad* yaro kyakyawa bafulatani usual tun yana yaro yake da miskilanci gami da rashin son
magana, kakar shi tayi ta tsokanar shi da suna k'ato uban 'yan muskilanci lokacin yayi ta jin
haushinta ko d'akinta baya shiga ita kuwa ba ta fasa kiransa da k'ato uban 'yan musklaci dake
*Amjad* irin masu GAF!GAF din jiki ne yayi mutukar saurin girma sosai shekararsa shida sai
kace shekara goma saboda girma ga Abu yanayi irin na manya a lokacin Alhaji Abbas ya gina
gida k'aton gaske cikin *Jambulo* suka koma da iyalinsa lokacin arzkinsa ya kai ya kawo duk
sati biyu suka zuwa umara shi da iyalinsa aikin hajji kuwa baya wuce su KUMA duk shekara
yana d'iban mutane goma cikin 'yan uwa da abokan arziki ya biya musu su sauke farali. *Amjad*
tun yana yaro yake da zuciya kwata-kwata ba ayi masa Abu ya k'yale sai ya rama babu ruwan
shi da shiga sabgar da bata shi ba, in ya ga dama ko Maman shi baya yiwa magana sai ya ga
dama hakama a skull ba kowa yake kulawa ba Sam bai yarda da abokai ba, yawanci ma
abokan shi mata ne Wanda sune suke nace masa gami da zuwa inda yake wai ya duba musu
jarrabawa dake akwai brain sosai nan zai karb'a ya nuna musu inda basu gane ba.

*****

Alhaji Hashimu me citta sai da ya san yadda yayi ya jone harkar kasuwanci sa dana Alhaji
Abbas domin ya cimma wata manufa tashi, Sam Alhaji Abbas be san da wani kudiri a zuciyar
mai citta ba kacokan ya mik'a masa yardarsa tare da amuncewar sa suka cigaba da gudanar da
harkokinsu na kasuwanci, kamar babu wani k'ulli a zuciyar me citta.

*Amjad* na kammala scondry skull ya wuce London ya fara karatu kan harkokin kasuwanci
ra'ayin sa ne haka kuma ra'ayin mahaifinsa yana mutukar so yaga ya gaji mahaifinsa kan sanar
shi to shima Alhaji Abbas din nashi b'angaran haka yake. Lokacin *Amjadu* na da shekara
ashirin da hudu inda yayi wani irin girma tsayi da fadin k'irji gami da kuzari sai kace wani Dan
shekara talatin tunda ya fara zama saurayi yake da akidar turawa dakin shi duk dics din
mawak'a ne na kallo dana ji ko da yaushe kunnen shi mak'ale da airphone yana jin music
*Amjad* yana sauraren wak'okin tsohowan mawak'in nan bom marly da macaal Jackson 2pac
Sisqo Joy BIG da sauransu. Cikin mawak'a mata kuma yana sauraron wakokin Cilen dion
Janeepar Burandi Tony da dai sauransu, gashi dai bai zo a zamaninsu ba amma yana bala'in
son wakokinsu Dan bai fiye sauraran mawakan na lokacin ba, gwara Usha da wzky yana
sauraron nasu, kallon Hausa ko jin wakokin Hausa Sam bai dame shi ba, gashi dai yana jahar
Kano dandalin Hausa da film din Hausa a cewar sa duk shirme suke da shashanci don in yaga
Adam A zango yana Abu na nigogi Dari kwai yake masa ya wuce abun yana bashi mamaki in
yaga yadda matasa suke kwaikwayonsa.

Duk sutturun shi babu namu na Hausa duka kananu ne ga wani uban gashi da yake tarawa a
kanshi kunsan dai yadda bafulatanin mutum yake da kyawun gashi gami da baki to haka ma na
Amjad yake saboda tsabar gyara da yake sha gami da mayuka masu tsada har wani tattatewa
yake askin shi abun kallo ne har inda ya futa ba tare da mota ba 'yan mata susucewa suke yi
sai su dinga ganin kamar d'an India Wato Allu arjun DOMIN suna mutukar kama dashi, shiyasa

yake wayan shiga mota ko da ko tafiyar da zaiyi ba me nisa bace , gudun kallon matan Kano
Wanda yake ganin hakan tsabar k'auyanci ne da gidadanci sai kaga mace har mace ta tsaya
tana kallonsa wasu ma yana cikin mota suna mota zasu dinga zuro kai suna lek'ensa tsaki
kurum yake ya d'auke kansa Maman shi me damuwa da yanayin shigar shi tayi tai masa fada watarana in taga ya sanya
siririyar sark'a a wuyansa turke shi take tace dole sai ya cire domin bazai futa da ita ba, ita ko
granny dake haka ya ke kiranta tace masa bata son wannan sunan domin na arna ne yak'i ya
daina saboda ya lura bata so duk sanda ya kirata da wannan sunan sai taki amsawa sai ya
kirata da Innah sannan zata amsa. Cewa take ki kyaleshi dai ya cigaba da irinn wannan shigar
Cikin kano sai ya rasa matar aure domin 'yan Matan kano idan ba jampa da kufta kayi musu
ado dashi ba babu me auran ka nu kuma ka dawo gare ni in ce a kai kasuwa. Dariya yake duk
lokacin da tayi wannan maganar sai yace." Ke an fada miki ni zan auri 'yar kano gidadawa dasu
Wanda babu abunda suka iya sai kallo da ihu! Ga Adam A zango ga Ali nuhu dama me suka
sani in banda bleccing." Granny tace." Ranar da bakanuwa zata rike maka wuya yanan zuwa"
tsaki kurum yake ya barta a gurin. Ganin ya tsaida sallolinsa biyar yasa Alhaji Abbas baya ta
kura masa kan abunda yake yi domin sallahr Asubah bata wuce *Amjad* yana riga kowa tashi a
gidan to itama Hajiya Aisha sai ta kwantar da hankalin ta.


Ko da yaje London sai Abu ya kara k'aimi saboda haduwa da yayi da turawa masu irin ra'ayin
shi harda bakaken fata ma "ya gari daban-daban, sai ya saje dasu kawai ya koma tamkar wani
bature har ta kai ta kawo yana zuwa barbing saloon Wanda ya amsa sunansa ya zube kudi
masu kyau! Ayi masa kitso Wanda muke kira zane manya ake masa guda shida ko biyar, ya
futo abunsa babu Wanda zai kalleshi tace. Mahaifitarsa bakar fata ce KUMA ya hada jib'i da
Hausa Fulani saboda yadda ya saje ya koma tamkar d'an sarauniyar Ingila.
Shekararsa biyu a can, wata rana Dady dinshi yayi masa waya cewar zasu je Chadi ziyara, yaji
ina ma yananan aje dashi yayi musu fatan dawo wa lafiya tare da cewa a mik'a masa gaisuwa
gurin 'yan uwa, aikuwa haka a kayi suka shirya tsaf suka bi jirgi 1:00 pm tare da guzurinsu ga
'yan uwa Innah sai murna take da farin ciki zata ga 'yan uwanta, daf da zasu sauka daga jirgi
Allah ya saukar da al'amarinsa i n jirgi daga sama ya samu tangard'a nan take ma'aikatan
hankalinsu ya tashi suka fara kai kawao drabobin jirgin suka gigice domin son su shawo kan
matsalar inahh! Duk abunda Allah ya hukunta zai faru sai ya faru duk k'okarin su na son su
sauka kasa Allah bai nufa ba daga sama jirgin ya tawo a gicceye a sauka cikin wani daji take ya
fara hayak'i kafin kace kwabo ya fara wuta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login