Showing 45001 words to 48000 words out of 71336 words

Chapter 16 - BABAN YARO PART 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf

mana Asma'u
ai na San hanya,kawai sai ki dinga min tsawa kamar uwata wallahi baki isabah!!!"" Tsaki naja na
futa daga d'akin fuuuuu!! Umma na zaune a rumfa tana lissafa kud'in cinikinta na shiga da
sallama, kallona take cikin nazari sai nayi saurin gyara yanayin fuska ta na zauna kusa da ita
ina gaisheta.Ta amsa babu yabo babu fallasa tace." Me ya hanaki tashi da wuri yau abunda ba
sabon ki bane." Kasa nayi da kaina ina shiryo k'aryar da zanyi mata. Tace." Tambayar ki nake."
Da sauri nace." Umma kin San dama bana sake wa a gidan mutane inyi bacci Wallahi jiya
kwata-kwata banyi bacci a gudansu Munnu ba shine dalilin da yasa na makara." Tace." Yayi
kyau hakan." Yanda ta fad'i maganar yasa na soma zargin kaina sunkuyar da kaina nayi ina
addu'ar Allah yasa kar ta fahimci wani Abu. Kamar daga sama naji tace." Nishi! Da surutun me
naji kinayi jiya da daddare." ? Gaban yayi bala'in fad'uwa." Jarumta na aro da dauri na d'ago
kaina ina kallonta nace." Umma nishi! Kuma."? Hararata tayi ta cigaba da lissafin ta, tace." Ko

k'arya nake."? Girgiza kai na nayi nace." A'a."! Murmushi tayi kawai tana girgiza kai
tace."Asma'u nice na haife ki babu abunda zaki layance min, dukanin Ku a tafin hannuna kuke
na dad'e da sanin halin da kike ciki saboda haka nake baki shawarar ki tsare kanki da martabar
ki ta d'iya mace ki kula kada sha'awa tasa ki jefa kanki cikin halaka kad'a shaid'an ya ribace ki ki
aikata sab'on Allah ko kice zaki nemi hanyar biya wa kanki buk'ata ta ko wace siga ki tsare
kanki daga nan har lokacin da Allah zai futo miki da mijin aure." Umma ta k'arashe maganar ta
babu abunda ya dame ta.
Wata irin kunya ce ta lullub'e ni dama nasan Umma sai ta fahimta nasan ta da mugun saka ido
akanmu sunkuyar da kaina kawai nayi domin bani da tacewa. Haka Mimi ta shigo ta same mu
,da sauri na mike na futa ko sallama banyi wa Umma ba, Mimi CE ta tsaya ta karb'ar mana
kud'in abun hawa.
Ban jira Mimi ba nayi tafiya ta har na Isa bakin titi bata k'araso ba, tsaki naja kawai ina kallon
hanya can na hango ta ta tawo na d'auke kaina cike da haushin ta, me a dai-dai ta na tsayar
mana, muka shiga tare da fad'a masa inda zamu . haka mukayi tafiyar kowa zuciyarsa babu
dad'i.
Tun daga bakin get din makarantar mu muka soma cin karo da k'awayenmu da ihu!! Suka zo
suna rungume ni tare da taya mu murna ni da Mimi mun ci jarrabawa nima sai na saki fuska
sosai na kutsa cikin jama'a domin idona ya gane min, duk mun cinye maths ne kawai muka
fad'i shima ba sosai ba, wasu na murna wasu na bakin ciki nima tsabar murna tasa na manta
da komai na shiga cikin k'awayenmu muka fara ihu! Da dariya wadan da suka fad'i ciki ko har
da Alina tana tsaye jikin motar ta kamar ta kurma Ihu! Munnu na kalla cikin dariya na nuna mata
Alina ina fad'in" Munnu dubi Alina da fuska sai kace soyayyan k'osai sai maiko take cikin rana."
Munnu ta shek'e da dariya tana fadin" shegiyar ba fuska taci bleecing ciki ko oho dama yaushe
zata ci jarrabawa tana can tana yawon iskan ci." Dariya muka shek'e da ita. Mimi tace." Ku
Wallahi kun fiye Neman fitina kuzo mu tafi tunda dai mun gama abunda ya kawo mu" hararta
nayi nace." Wallahi baza mu tafi yanzu ba sai nagama kallon 'yan bakin ciki da masu kuka irin
su Ooo" na nuna Alina da bakina . a fusace! Ta tawo inda muke tsaye ta nuni da ya tsa tare da
fad'in" ke Ki shiga hankalin ki wallahi ko in sauke fushina a kanki yanzu". Kallon banza na watsa
mata nace ."da gaske kike." ? Tace." Zan sanya ne ayi min k'asa-k'asa dake shigeya 'yar gidan
malam Shehu sai tsabar girman kan tsaya." Wawan mari na Kai mata ta dafe kuncin ta cike da
tsoro! Ina numfar fashi nace." Wato har kin manta dabi na dake ko? Shine kike ikirarin sawa a
dake,to don durun Uwar ki ki saka ayi gunduwa-gunduwa dani shine kad'ai zai nuna min ke 'yar
gidan Bulget ce ubanki ba Santana ba ne."

Ca kumo wuyana tayi ta hau d'ura min ashar!! Idonta yayi jazur!! Kafin ta Ankara na daki bakinta
da gwiwar hannuna nace." Dama Neman ki nake ruwa a jallo shegiya karuwa." Ai kafin kace
kwabo gurin ya soma cika da mutane Alina ta fad'i a gurin tana wani k'ifkifta ido bakinta na
kumfa,dama ta saba daga zarar an fara fada da ita zata fad'i kasa tana burgima wai ita me
aljanu.

Mimi da Munnu hankalin su ya tashi suka nufi offece din principal da sauri sauran 'yan

makaranta suka fara guduwa domin sun tsorata da abunda Alina take ni ko ina tsaye a kanta ko
d'ar ba nayi. Malama Rakiya ce da aunt Lahira suka k'araso gurin hankali a tashe suka fara yi
mata tofi, mintuna kusan ashirin sannan ta dawo dai-dai duk suka tattaramu suka tasa mu gaba
zuwa offece din principal me gaba d'aya. Fad'a sosai shugaban makaranta yayi mana tare da gargadin cewa idan mun San rigima za mu
zo muyi ta zai soke mana shagalin murnar da mu tana da ranar candy sai kawai kowa yazo ya
karb'i takkadun sa, ya tafi, hakuri muka bashi sosai sannan ya sallame mu muka futa daga ofis
din gruop-gruop an tsaya sai gulma ake haka Alina ta futo jiki babu k'wari ta shiga motar ta ta
tafi, mu kuwa sai bayan sallahr azuhur sannan mukayi sallama da k'awayenmu bayan mun
tsaida ranar da zamu gudanar da murnar kammala makaranmu sati guda me zuwa, tare da
futar da anko har kala uku duk ranar zamu sanya shi. Muka futo titi muna Neman abun hawa
rana ta kwalle sosai gumi kawai nake ga wata irin yunwa na damuna dama ban karya ba gwara
Mimi ta karya da k'yar muka samu a dai-dai sahu muka shiga, ya dauki hanya sai gida. Hira
muke sosai cikin adai-dai tar kowa na fadin albarcin bakinsa, danja ta tsai damu, cike da jin
haushi nace." Na tsani ina cikin abun hawa danja ta tsaidani wallah.........maganar tawa ta katse
hango gefan fuskar sa da nayi kwance a cikin wata mutsiyaciyar mota silver sai shak'i take a
can tsallakenmu, da sauri na d'auke kaina gabana na dukan uku-uku addu'a nake kar Allah
yasa Mimi ko Munnu wata ta hango shi, a sace na k'ara kallon gefan haguna sai naga ya
mak'ala airpix a kunne shi tare da gyara zaman shi ya d'ora pcap me wani irin ado a jikinta gani
nayi yayi min wani bala'in kyau ban gane ko wane dressing ne a jikinshi ba, amma na tabbata
k'ananun kaya ne tunda INA hango hannunshi yana latsa wayar sa, ga Rambow a gefan shi sai
zare ido yake.

D'auke kaina nayi jin miyan bakina ya daskare ban tab'a tsayuwa na kare masa kallo ba sai yau,
a zuciyata Nace "Ashe haka yake da bal'in kyau!!!!!












*25/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*




*29*





Ban sake kallon gefan da yake ba har aka bamu hannu, muka wuce Munnu ta kalle ni tare da
fad'in"wai ya kikayi shiru sarkin kaud'i." Ya mutse fuska ta tanayi nace." Yunwa nake ji Wallahi."
Tace." Ba Dole ba wannan uban ihu da kika sha, shiru kawai nayi mata zuciyata nacan ga
tunanin guy nan, cikin zuciyata nace sai kyau amma babu kyawun hali. Munnu aka fara
saukewa ta kalli ni tare da fad'i wa kika ce zamu bawa dinkimu "? Nace." Kinsan dai ba zamu
bawa Ummi ba ta lalata mana yadi maza zamu bawa dinkimu." Tace." Shikkenan yaushe zamu
gidan aunty Hauwa ko kuma da kanmu zamu shiga kwari." Nace." Ki rabu da aunty Hauwa
kawai muje da kanmu."tace." To shikkenan sai goben" muka ce "Allah ya kaimu ni da Mimi .me
a dai-dai ya ja mu muka tafi ita kuma Munnu ta tsallaka titi ta shige layinsh.



A hankali motar ta silala ta shiga cikin harabar gidan. Rambow ya futo da sauri ya bud'e masa
kofar motar tare da k'okarin karb'ar wayoyin hannunsa.
Girgiza masa kai kurrum yayi ya wuce shi cikin sassarafa, suka rufa masa baya.


Dattijiwa kamillaliya na zaune cikin kujera tana sanye da atampah Ghana kamar ko da yaushe
sai kamshi parlor yake tana zaune tana kallon tv tashar sunnah tv suna wa'azi, gefan ta wata
matashiyar budurwa ce a zaune tana kallo ita.

Ya shiga da Sallama a bakinsa. Da sauri Hafsa ta kalli kofar shigowa jin muryarsa taji wani
sanyi na kwarara a cikin zuciyarta. Cike da kunya ta d'auke kanta.

Granny tace." Dan halak kaki jinin ambato dama yanzu nake fada miki zai shigo tunda yau
juma'a."

Hafsa ta yi k'asa da kanta tana murmushi . cikin yanayin tafiyar sa ya k'araso kusa da kakar
tasa ya zauna gefan ta, tare da gaishe ta. Ta amsa cike da walwala da farin ciki tace." Ga
k'anwar ka nan tana zaman jiran kazo Ku gaisa." Cikin rashin fahimta yake kallon Hafsa dake
sine kai yace." Granny wacece wannan."? Cike da takaici tace." Hafsa zaka ce baka sani ba kai
kuwa." Sosa kansa yayi tare da fad'in" banda abunki to a ina zan santa na dai ga tana kama da
Innah Suwaiba." Granny tace." To 'yar autar ta ce ai." Sosa kansa yayi a karo na biyu yace."
Ayya! Ai kin San ni ba sanin 'yayan ta nayi ba sosai wallahi in banda Musbahu da Zaraddini
suka kadai zan sheda a cikinsu."

Granny tace." Ai dole kai da ba ziyara kake ba dole ka kasa saninta , sunanta Hafsatu."
Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya kalli Hafsa a nutse yace." Hafsa ya gida ya makaranta." Ba
kinta na rawa tace." Lafiya Lou alhamdullahi. " yace." Ina Ina Suwaibah tana lafiya."? "Lafiyan
ta lau tace ma a gaishe ka tunda ka daina zuwa." Murmushi yayi kawai be komai ba." Granny
tace. "Ai ka saba dama da anyi magana ka sosa kai ya kamata dai cikin wannan satin kaje."
Yace." Insha Allah zanje ayyuka ne suka min yawa ke kanki kin sani." Tace" na sani amma ai
ana barin halak da kunya." Shiru kawai yayi mata tana surutai wayarsa yake dannawa yayin da
Hafsa take ta satar kallonsa tana ji kamar ta had'iye shi ta huta.

Ina Suawaiba mahaifiyar Hafsa yayar Aisha ce wato mahaifiyar Amjadu itace babba a d'akinsa
Hafsa kenan a matsayin kanwarsa take.

Kallon da take masa ne ya dame shi kwata-kwata a rayuwarsa ya tsani kallo shi kam, b'ata
fuska yayi ya mik'e tsaye tare da kallon agogon hannunsa, ya kalli Granny tare da fad'in ni zan
tafi." Cike da mamaki tace" zaka tafi kamar yaya? Baza ka tsaya ka ci mutumin naka ba gashi
na kwad'anta maka." Tana nufin zogale. Girgiza kansa yayi kawai ya nufi hanyar futa, kallo tabi
shi dashi cike da takaici tace." Ka tsaya ka ragewa Kanwar ta hanya mana." Ba tare da ya wai
wayo ba yace." Ki bata kud'in abun hawa mana." Yayo fucewarsa ya gane manufar granny na
aje yarinyar da tayi Dama wancan satin da yazo ta fada masa tayi masa budurwa lallai granny
tana da aiki a gabanta.

Hafsa kuwa ji tayi kamar ta tashi ta dawo dashi domin Sam bata gaji da kallonsa ba, ita dai
Allah ya sanya mata k'aunarsa a ranta tana fatan Allah ya sa granny tace dole ya aure ta tunda
ta lura Sam bata gabansa amma tayi mamaki sosai yanda ya amsa mata gaisuwarta a sake ta
d'auka yana da girman Kai ashe ba haka yake ba.
Yana futa wayar shi ta fara k'ara dubawa yayi cike da mamaki numbar me girma governor ya
gani, sai da ta kusa katse wa sannan ya daga wayar da muryarsa irin ta jarumai, suka gaisa da
shi cikin nutsuwa daga d'ayan b'angaran me girima governor yace." Kazo Gidan gwamnati
musalin k'arfe biyar na yamma ina Neman ka." Yace." Insha Allah inan tafe." Sallama sukayi
gaba dayansu kowa ya kashe wayarsa. Murmushin gefan baki yayi kawai yasan karshen
zancan wato shime governor yana goyawa su Me citta baya kenan , lallai dole ya tashi tsaye
akan haka.

*******

Tunda nayi masa wannan ganin shikkenan na nemi kuzari na na rasa haka muka shiga gida
jikina babu k'wari Mimi CE kawai take ta murna tana baya Umma labari, itama sai murna take
tace." Nasan kun kwaso yunwa to ga abunci can cikin Fula's a kicin yau har nama na siya muku
na sanya muku a miya." Mimi ta tashi da sauri taje ta d'auko mana, tare da d'ebo mana ruwa
me sanyi na cikin randa, cin abuncin kawai nakeyi kwata-kwata bana jin tes d'insa a bakina,
ganin Umma tana kallona a fakaice yasa na fara yak'e INA biyewa Mimi muna ta labari. Mimi
tace." Umma kinga ankon da muka futar za muyi." Umma ta karb'a tana dubawa tace." Aikuwa
dai atampar tayi kyau kuma daga ni me tsada CE." Nace." Umma ai material din yafi ta tsada
shi dubu goma sha biyu ne fa." Umma ta b'ude bakinta cike da mamaki tace." Da ubanku ina
zan samu kud'in siya muki har dubu ashirin da hudu bayan kud'in dinki." Nayi karaf nace."
Umma gaba daya Dana lissafa kud'in sun kai dubu arba'in da bakwai da atampar da material
din da shaddar." Umma ta gyad'a kawai tare da fadin " kun shirya ruguza ni kenan yo ni ina
naga dubu arba'in har da bakwai a Hamsin kad'an ne babu, so kuke in rusa jarina inyi muku
anko kunga daga baya sai mu koma mu tsuguna muna tsotsar tsamiya." Jin abunda Umma tace
yasa gabana fad'uwa dan gaskiya bana kaunar harkar k'aranta a rayuwa ta bana so ace ba
muyi ko wane anko ba, in San samu ne ma da sabbin takalimi da jaka da mayafi." B'ata fuska
nayi ina cin abuncin kamar bana so. Ta kalle ni a nutse tace. " naga kin b'ata fuska don ubanki
so kike in siya muku anko ni kuma Ku karya ni ko, to bazan siya duka ba, Ku zab'i daya a cikin
guda ukun, dama si kullum abunda ake fada muku kenan Sana'a tana da dad'i da kuna Sanar
Ku da duk babu abunda zai gagareku, ko kuyi bakwa yi da aunty Ku tasan duk hanyar da zata
bi ta nemi kudi saboda haka ni babu ruwana." Shiru mukayi duk murnar mu ta koma ciki. Wasu
hawaye ne suka fara zubo min na takaici! Mimi ma ina kallo idonta duk ya ciki mda k'walla
Umma tace "kuyi kukan jina ma ni babu ruwana." Yaya Aminu ne ya shigo dakin da sallama a
bakinsa Umma ta amsa masa ya zauna yana kallonmu cike da mamaki hankalin shi yafi karkata
kan Mimi yace." Meye suke kuka." Nan Umma ta warware masa abunda yake faruwa.

Dariya yasa tare da nuna Mimi da hannu yace." Sam kuka baya yi miki kyau gwara ma ki
daina."Mimi ta zumb'ura bakinta yace." Nawa ne kud'in atampar."? Da sauri nace" dubu hudu ce
." yace." To zan bada shikkenan ko." Sakin fuska mukayi dukaninmu nace "to shaddar fa."?
Hararata yayi yace." Wannan kuma sai Ku nemi Wanda zai siya muku." Mimi tace." Asma'u ina
ganin in muka samu guda biyu ma ai mungode Allah." Shiru nayi mata domin ba haka naso ba."
Umma tace "sai Ku nemi kud'in dinki don wallahi kuka d'auko dinki me tsada me cin kayan dinki
to bazan biya ba." Nace. " Umma kinsan shi material din fa dole sai anyi masa bauta an siyi
shafi da sauransu gaskiya zai ci kudi sosai, bayan haka kuma don Allah ki siya mana sabbin
takalma". Hararata tayi kawai ta juya suna magana da Ya Aminu.


******
Biyar dai_dai yana gidan gomnati nan aka yi masa ido har ofis dine me girma governor ya
zauna kan wata lumtsime miyar kujera suka gaisa a tsana ke, me girma governor ya kallashi sai

ya ji gabansa na fad'uwa ganin yanda Yaro yayi masa mugun kwarjini, yace." Bisimillah ga ruwa
kasha." Amjad yayi murmushi tare da fadin." Nagode me girma shugaba." Bayan yasha ruwan
ne me girma governor ya kalle shi a nutse yace." Hausawa suka ce maganar gizo bata wuce ta
k'ok'i na San ka fahimci dalilin da yasa na kira ka."? Yace." Ban fahimci komai ba ina Neman
Karin bayani." Governor ya gyara zama tare da fadin." Har yanzu muna kan bakanmu na ka
rushe company naka ko kuma ka tsawwala farashin kayanka, saboda ni kaina na zauna nayi
nazari da tunani ba 'yan kasuwa kad'ai abun yake tab'awa ba har da gomnati ina fatan ka
fahimta, gomnati na karb'ar haraji a hannun 'yan kasuwa idan ba k'ara farashin kayan ka ba to
tabbas zamu tsawwala wa 'yan kasuwa kud'in haraji kuma za mu rushe shagunanmu Wanda
gomnati ta gina zamu kori duk wani dan tebur da Wanda bashi da shago zamu watsa su daga
kan titi, wannan shine matakin da muka d'auka.

Ido jazur! Ya d'ago kansa yana kallon governor din yace."Allah shi baka nasara da kanka kake
wannan ikirarin? Wato har kamanta ranar rantsuwa kenan ? Ka manta ranar da ka dafa alk'urani
me girma ka rantse dashi? Ka manta ranar zab'e da wahalar da talakawa suka sha akanka rana
zafi sanyi ruwa talaka ya tsaya kai dafata ya dangwala maka kuri'a duk ka manta wannan ranar
me girma Governor. " ya k'arasa maganar tasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login