Showing 63001 words to 66000 words out of 71336 words
Chapter 22 - BABAN YARO PART 1 BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE.pdf
tab'a samun yarinyar da ta shiga zuciyarsa ba irin
ta ya rasa meye dalili?? Kawai dai ya San yana mutukar son bakinta mussaman in tana tsiwa
yanda take da zafi-zafi haka bakinta yake da tes miyau ta yayi masa sosai uwa uba albarka tun
k'irjinta masu taushi gami da girma Wanda yake kasa ritsa su da hannunsa,, yarinyar tayi ta ko
wace siga, d'an ya tsansa ya dago yana kalla, murmushi yayi had'e da Dan Sosa kanshi a fili
yace." *Asma'u!!!!* zan San yanda nayi kika dawo gidanan domin kin d'an d'ana min zumar ki,
mai wahalar mantawa.... Wayarsa ce tayi k'ara alamun ana kira. Yana dubawa yaga sabuwar
numbar, Kamar kar ya d'auka sai kuma ya mik'a hannunsa ya dauki wayar tana daf da k'arshe
yace." Salam"" Hibbah ta saki ajiyar zuciya jin muryar gwarzon zuciyar ta. Tace." My Apple gani
nazo gidan ka masu gadi sun hana ni shigowa wai sai na nuna shaida." Mik'ewa zaune yayi
sosai jin muryar kamar ya San me ita, kai tsaye yace." Wacece ke."? Wata irin shashshekar
kuka tayi tace." Ka manta da kankanaty ka ko.? Nice Hibbah!!!" Take ya tuno yarinyar 'yar gidan
me citta CE." Cikin basarwa yace." Oh! Hibbah ya kike? Ya gida."? " lafiya Lou Nazo yi maka
jaje banzayen masu gadi sun hani shigowa kamar basu San wacece ni ba a gurin ka."
Murmushi yayi yace." Akan aikin su suke so ina ganin basu da wani laifi anan... Nagode da
kulawa, kije kawai ba sai kin shigo ba." Hibbah taji kamar ta kurma ihu!! Guy nan yana abunda
yake so fahh!! Ta fada cikin zuciyarta a fili kuwa cewa tayi." Amm!!! Ai ina so in gan ka ne,
kasan nayi missing din numbar wayar ka ranar na manta ban k'arba." Shiru yayi na minti biyu
Daga bisani yace." Ok kashe wayar zanyi magana da rambow yanzu." Cike da farin ciki ta
kashe wayar tana watsa wa masu gadi harara.
Wayar rambow ya kira yace yaje ya shigo da ita.
*Pls kuyi hakuri don Allah wallahi in da wadataccan chaji ni me faranta muku ce, Ku dai cigaba
da bina yanzu aka fara kafcan*
*30/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*
*mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA*
*35*
Mik'ewa yayi ya nufi wardrobe ya ciro wata shart fara k'al, ya sanya a jikinsa had'e da short
nickar blue coular mai aljihuna gaba da baya had'e da wasu sark'ok'i a jikinsa, sosai yayi kyau
lafiyayyar fatar sa tayi luki sai shek'i take yi, a haka ya futo palo ya zauna yana jiran shigowar
Hibbah, ta shigo cikin takun k'asaita, suna hada ido dashi tane mi kuzarin ta ta rasa, tarasa
wane irin kwarjini ne da guy nan Wanda daga zarar ka hada ido dashi shikkenan sai ka rasa
nutsuwa. Kallo ya bita dashi har ta k'araso kusa dashi ta zauna jikinsa sosai tana masa wani
Dan iskan kallo cike da tsantsar sha'awar sa."
Hannu ta kai zata shafa sajan fuskar shi. Ya rike hannun yana d'an hararata tare da fad'in" Ina
fatan lafiya ko." ? Lumshe idonta tayi ta bude had'e da tsare shi dasu tace." My love lafiyar ce ta
kawo haka, na kasa daurewa ne wallahi kayi min mugun kyau *Amjadu* ina mutukar kaunar ka
a raina." Kallon baki da hankali yayi mata, yace." Dama abunda ya kawo ki kenan." ? Girgiza
kanta tayi had'e da lumshe idonta ta d'an ciji lips dinta tace." No Nazo nayi maka jaje sannan na
kalli wannan kyakkyawan fuskarta taka da nayi missing." Murmushi yayi had'e da cewa" bani ya
kamata kiyi wa jaje ba 'yanta." Gyara zama tayi tana wani marmar da ido cikin sigar Jan hankali
tace." Ban fahimce ka ba." Sajanshi ya shafa as'usuel yace." Ina nufin ki fara yin jaje a gidan ku
tun kafin ki iso nan, ko kina nufin zaki ce min bakin San har da sannun mahaifin ki akan abunda
ya faru dani ba ne."? Cikin alhini da damuwa ta kalle shi tace" ka yarda dani my love wallahi ban
san kan al'amarin ba, nasan dai tunda muka taso muke ji sunan mahaifin ka a bakin mahaifin
mu, yace suna da kyakyawar alaka dashi kafin ya mutu, kaine da bakwa shiri da juna." Gyada
kansa yayi har yanzu hannunshi na kan gemun shi yana shafawa yace." Hakane ni da mahaifin
ki kamar kura da nama ne,ba ma ga muciji da juna, kije ki tambaye shi dalili zai fada miki."
Kamar zata yi kuka tace" ni kam babu ruwana da alak'ar ka dashi me kyau ko mara kyau
soyayyata kawai na sani a cikin zuciyarka." Kai tsaye! Yace." Baza ki samu ba." Wani irin abu
taji cikin zuciyarta ta kalle shi bakinta na rawa tace." Meya sa."? Kallonta yayi fuskarsa a had'e
yace." Ke baki Isa na fada miki dalili ba.". Kuka ta fashe dashi sosai had'e da girgiza masa
kanta tana fad'in"kar muyi haka da kai my love wallahi ina ji wata muguwar soyayyar ka cikin
raina ina ganin zan iya rasa rayuwa ta a kanka, na San waye kai so bazan tab'a yin sakaci gurin
ganin ka sub'uce min ba."
Kuka take har da shashsheka! Yana kallonta hankalinsa a kwance, mamaki. Yake mace har
mace ta dinga kuka Hibbah dai ta cika mace ta ko wane fanni tana damar auran duk Wanda
take ra'ayi amma abun mamaki tana kuka har da sharb'e duk a kansa shi kam abun mamaki
yake bashi. Mik'ewa yayi ya bar mata kujerar a nutse ya Isa gurin frige ya d'auko gwangwani
Lemon cocar cola guda yayi sanyi sosai! Romot ya d'auka ya canza tasha sannan ya zauna
kujera dake daf da kofar futa ya bude lemon shi yana shan abunshi hankalinsa na kan tv.
Hibbah taji kamar taje ta rungume shi haka take ji, wato yayi banza ma da ita lallai guy nan
yana ji da wulakaci, fuskarta ta goge ta mik'e ranta babu dad'i ta Isa kusa dashi
Hannunta ta d'ora a kafadarshi tana d'an matsawa kad'an, ya dago kanshi Yana kallon
fuskarta, kyau iya kyau gashinan amma bashi ne a gaban shi ba,zuciyarsa nacan tana tunanin
wani Abu,
A hankali tace" ni zan tafi tunda ka wulakanta ni, Ashe dama laifin uba yakan shafi d'iyar sa,
wato don na zubar da daraja ta a gurin ka yasa kake min kallon ban Isa b.......hannu ya daga
mata fuskarsa a turb'une yace." Ke kike maganar Isa a gurin nan, tun farkon fara haduwa take
na fada miki cewar ni bana maimaita Abu guda ko suttura ce in na gada yau idan na sanya ta
zai iya bada ita, tsarina ne haka." Ya cigaba da kallonsa hankali kwance. Cike da tsantsar b'acin
rai! Hibbah ta futa daga parlor kamar zata kifa, tsaki ya ja kawai yana tab'e baki.
********
Sai da muka kammala komai sannan muka dawo gida, hatta da kud'in dinki sai da muka biya,
Munnu ta dinga murna tana fadin ta samu kudi, domin ba zata mayarwa da Kawu kudinsa ba,a
cewarta ta siyi wani abun ita...aunt Hauwa sai wani ji dani take ni kuwa ina shareta DOMIN har
yanzu ban gama sakko wa ba, muna koma wa gida Umma ta gama abunci don haka na zage
naci sosai dama akwai yunwa sosai a jikina
Bayan mun gama cin abunci ne a na zaune ana hira nace"Umma ki bani dubu goma sha biyu a
cikin kud'in I'n siyi waya."
Tace" INA taki take."? Nace" Umma wayar nan dama lallab'a ta nake wallahi jiya ma ta fad'i
gurin chaji ya lalace." Tace" kuma sai a kace Dole sai mai tsada zaki siya ko ina zaki kai wayar
dubu goma."? Marairaice fuska nayi nace" Lallai Umma Don baki ga wayoyin 'yan ajinmu bane
rafka rafka ko Mimi."? Nafada INA kallon Ta. Tace" hakane Umma dom Allah ki bata kin ga sai
muje da karfinmu babu raini." Hararata Umma tayi tace." Saboda rashin kishin kai ke Kin yarda
ita ta rike waya ke baki da ita." Dariya Mimi tayi tace."Ummanmu kenan a wayar ta kamar tawa
CE." Tace" duk da haka dai baza ta siya ita kadai ba ga dubu goma sha hudu kuje Ku siyi 'yar
dubu bakwai bakwai ta ishe ku."
Bata fuska nayi nace"Umma wayar dubu bakwai ai me madannai ce ni da nake son toching."
Aunt dake k'okarin shigowa dakin bayan futowar ta DAGA band'aki tace" sai ki siyi Vivo kawai in
dole ne sai Kin rike babbar waya wannan ragowar kud'in da kika sakawa ido zamuyi amfani
dasu ne gurin kara jari ki cire idonki daga Kansu, " ta karasa maganar ta tana shirin ta da
sallah. Nace"aunty ko Vivo zamu siya tafi dubu bakwai indai sabuwa CE." Umma tace" sai Ku
siyi ta hannu ai duk waya CE." Shiru nayi kurrum domin bana kaunar yin jayayya da Umma.
Sai daf da marigaba aunt Hauwa tabar gidan.Mimi ce kawai ta karata hanya ni ko kwanciya ta
nayi ina jin haushin yanda take k'ara zuga Umma akan komai,wani lokacin ko Umma bata yi
niyyar yin abuna to aunt Hauwa da Ya Aminu sai su sanya ta.
******
Yaya Aminu ne ya shiga kasuwar 'yan jagwal ya siyo mana Vivo ko wacce da ta ta, dake namiji
ne sai suka bashi me kyau DUK bata wani sha jiki ba, yau saura kwana biyu Party mu duk mun
tashi hankalin mu ni da Mimi mun fara gyaran jiki kamar wasu amare dilka da halawa kullum sai
munyi aikuwa fatarmu ta goge mussaman ni da nake da chocolate din fata sai take wani irin
k'yalli abun gwani sha'awa
Munnu muke jira tazo domin yau ne mukayi niyyar zuwa kunshi ja da baki can kabuga zamu je
wata 'yar kawar Ummansu Munnu ce take yi, duk mun shirya Munnu kawai muke jira tazo
Goma da minti goma ta shigo ko zama ban Bari tayi ba na azazzale ta, a tsaitsaye suka gaisa
da Umma muka kama hanya.a dai- adai ta sahu guda muka d'auka har kabuga muka sauka da
kafa muka shiga lokon su Bahijja me kunshi.
Babu jama'a a gidan Dan dama mun sanar mata da cewar in mun zo baza mu bi layi ba, aikuwa
dama lallanta a had'e yake kawai ta fara aikinta. Ja ta farayi mana, bayan shi dai d'aura mana
baki a kai, wai!!! Kafin kace kwabo mun fito Tass!damu gaskiya Bahijja ba dai Iya kunshi ba,
dunu uku na mik'a mata tace baza ta karb'a. Ummansu tace" akan Me zata karb'a kuje fa kud'in
ku ai Ku na gidane." Aikuwa zura kud'in nayi a jakata dama a titi da muna tafiya naga wani gurin
kwalliya gami da gyara gira. Muna futa nace dasu Mimi mu tsalla titi muje shagon kwalliyar can."
Munnu tace"wane irin kwalliya kuma. ? Nace "ke dai muje." Suka biyo ni a baya cike da
mamaki.
Duk kab'ilu ne a gurin, suna ta aikinsu ga wasu had'addun 'yan mata anayi musu kitso irin na
gashin doki.. Sai hira suke gami da taunar cingam. Cikin turanci nace da wata in ya mura muna
so a gyara mana gira ne kuma za mu siyi gashin ido muna son su nuna Mana yanda zamuyi
amfani dashi.
Aikuwa sunga costomas tuni suka bamu gurin zama muka zauna. Mimi ake wa ina kallonta
naga tayi kyau sosai, murmushi nayi nace"Mimi kin ganki kuwa."? Fuskarta ta shafa a hankali
tayi dariya. 'Yan Matan nan ne naji sun kwashe da dariya nayi saurin kallonsu cike da zargi,
kawai idona yayi min tozali da budurwar nan da mukayi fada da ita shekaran jiya a
Mudannsir&brots, shan kunu nayi sosai tare da tsare gira
Naji tana fad'awa kawarta duk abunda ya faru.kawar tata tace." Kawai ki karawo su Salmanu a
waya suzo su sab'a mata kammani." Na fuskanci ni suke nufi. Mimi da Munnu Sam basu gane
komai na sun fi tunanin cewar 'yan Matan hirarasu kawai sukeyi irin ta kawaye.
Bayan an gama wa Mimi sai Munnu nice ta k'arshe sosai nace su gyara min saboda ina da
yawan gashin gira sosai...aikuwa suka shiga fed'e min had'e da red'e ta sai da ta dawo sirirya
sosai tayi wani irin kwana sannan suka bar ta, mudubi na kalla naga nayi kyau sosai, handbag
dita na bude zan Ciro kudi kawai naji an wafce da sauri na d'ago kaina ina kallon su, wasu
matasan samari ne sun sha askin 'yan iska leb'ansu bakikkirin dashi. Wannan vudurwar suka
kalla tare da fadin "ita ce ko."? Gyda kanta tayi Tare da mik'ewa da niyar tafiya dama an gama
musu kitson su....d'aya daga cikin masu aiki a shagon ta k'araso da sauri cikin turanci tace" me
yake faruwa ne.? Safiyya ta mik'a mata kud'in aikin su ba tare da tace da ita komai ba taja
hannun kawarta suka futa daga gurin
Kaina suka yo suna jamin mayafi cikin sigar rashin mutumci! Da sauri na Mik'e tsaye ina gudun
kar su cire min mayafi gani a kan hanya kuma a bakin titi domin daga inda muke muna ganin
shige da fuce na jama'a gami da zurga zurgar ababen hawa.Mimi da Munnu suka mike hankali
a tashe suna basu hakuri . ni ko cewa nake." Ku rabu dasu suyi min abunda aka sanya su Mimi
sai ta fara kuka ganin har sun cire min mayafi. Duk ma'aikatan gurin suka rufe mu suna basu
hakuri d'aya daga cikinsu ce ta dauki wayarta domin ta kira aunty su wato wacce ta bude gurin,
ita kuma d'aya ta futa waje da sauri domin kiran jami'an tsaro.saboda wani lokacin suna zama
bakin hanya kasancewar titin kabuga babban Titi ne bayan haka akwai many an masu kudi
sosai a nahiyar saboda haka dole sai Da tsaro. Mimi ma futa tayi da gudu ta tsaya bakin titi ta
diririce sai zare ido take......Fuuuuuuuuuu!!! Motar tazo ta wuce, yana kwance ciki ya hango
Mimi da sauri ya mik'e zaune gami da bawa dravar sa umarni ya koma baya....doh-doh ya bi
umarnin da aka bashi. Dai-dai santar shagon motar ta tsaya, ya hango duk abunda yake faruwa
a ciki. Asma'u ce tsaye babu mayafi babu d'ankwali ga wasu maza tsaye a kanta. Sai mata uku
suna kare ta.. Dake motar me tintac ce babu Wanda ya ganshi a ciki cikin tsantsar b'acin rai
gami da bak'in ciki da takaici ya kwatsawa rambow tsawa tare da fadin yayi maza ya bud'e
motar nan yaje ya kawo masa 'yan iskan samarin nan, har da ita kan ta Asma'u.
Rambow ya bude motar da sauri ya nufi shagon, tunda nesa ta hango rambow sai gabanta ya
fad'i tana mamakin me ya kawo shi gurin? Fad'uwar gabanta ne ya tsananta da ta tuna nan
hanyar gidan shi ce tsakanin kabuga da jambolo ko da kafa mutum ya karasa, taji dadin zuwan
rambow tasan zai taimake ta daga hannun 'yan iskan samarin nan. Wanda suke k'okarin yi
mata tsirara, daya daga cikin ma'aikatan gurin ce ta rike rambow tana fadin" please oga zo ka
taimake mu ka futar Mana da wad'ancan 'yan iskan samarn." Rambo ya shiga ciki sosai take
'yan iskan suka shiga hankalin su, domin sun yi wa rbow kyakyawan sani, yace." Me ya hada
Ku da ita."? D'aya daga cikinsu yace." Oga sunyi sa'insa da wata ne kwanaki shine ta kira mu
muzo muyi mata tsirara." Shi kanshi rambow da yaji abunda suka ce sai da ya tsorata, mayafin
ya d'auka ya mik'a mata da sauri yana waiwayen bayansa, yace." Ku muje mota dama akwai
aikin da zakuyi mana a company ." aikuwa suka wuce da sauri suka tsaya jikin motar su duk a
tunansu babu kowa ciki rambow ne kurrum, To shima *Amjad* din yana sane yaki futowa
saboda gudun idanun jama'a DUK da haka yana kallon yanda mutane suke zurga-zurga a gurin
motar tunda duk inda motocinsa suka shiga dole a gane saboda sunanshi dake mak'ale a
bayan motar wato *AA AbulAbbas Mai nasara*.shiyasa yak'i futowa amma dukanin abunda
yake faruwa yana hangowa, rambow ya kalli Asma'u yace." Ku muje in kai Ku gida, don Allah
Ku daina kula irin wannan 'yan iskan samari marasa kamun kai."
Fushina na sauke a kansa na watsa masa harara tare da fadin" kaga munyi kama da 'yan
iskane da zaka fad'i wannan maganar, mtssss." Su Mimi da ma'aikatan gurin suka Bini da kallo
cike da mamaki! D'ankwalina na d'aura sosai na ya fa mayafina kudinsu na mik'a musu,nace"
Ku mu tafi." Su ka biyo ni abaya , Rbow ko dake yasan halin rashin kunyar yarinyar bai damu
ba, kuma yaga ogonshi yana ji da ita, shiyasa yake kaffa-kaffa.
Tsayuwa mukayi bakin titi rayukanmu babu dad'i mussaman ni tunani kawai nake hanyar da
zanbi in rama rashin mutumcin da wannan 'yar iskar tasa akai min a bakin titi don ma mutane
nasu ankara ba, da kunyar da zanji sai Allah.
Tunda ta futo daga gurin yake kallon har suka zo suka tsaya bakin titi bai d'auke idonsa daga
kanta ranshi in yayi dubu ya b'aci! Ya kalli 'yan iskan samari yana nazarin su. Meye alakatar
dasu ? Da har take biye musu suna shirme a titi ko dai maganar da 'yan uwanta suka fada a
kanta gaskiya ne, in ko hakane tabbas zata fuskanci hukunci a gurin shi, take yaji k'irjinsa tayi
masa wani mugun nauyi zuciyarsa na kara fada masa haka ne dama can tana biyewa 'yan
iskan samari su lalube ta, shiyasa ta saba kuma take da sha'awa sosai! Idanunsa sukayi jazuri
lips d'insa na kasa ya ciza had'e da dukan kujerar mota da k'arfi! Doh-doh ya juyo da sauri yana
kallon ogan nasa alumu sun nuna ogansu ya fad'a tafkin so, a hankali yace." Sorry